← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 173

Sashe 139

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faɗa yana fesa turare a jikinsa. Sannan ya ɗauki glass ya saka ya ɗauki makullin motarsa ya fice. Kai tsaye gidan ƙanen Babansa ya nufa, daman yasan a irin wannan lokacin yana gida kamin yaje gurin da yake aikin ƙira. Har ciki gidan ya shiga, sai qani ƙyaƙƙyami yake da ginin ƙasa, ya gaisa da matansa sannan suka fito waje suna tattauna maganar auren da Asim yake labarta masa na Mardiya akan maganar tura magaba, a nan suka kitse maganar sati mai zuwa sai nemi sauran ƴan'uwa suke je su nema masa aurenta, sannan kuma ya ɗora masa da maganar gidan da aka ce masa akwai amman milinya takwas ne.

Gidan ba shi da nisa sosai da unguwar hakan yasa suka ƙarasa da mota aka kira Mai gidan ya shiga da Asim ciki ya ga komai. Ya yaba da gidan sosai, komai na cikin gidan sabo ne ga sabo fenti ga fulawowi daman irin gidan nan ne da ake ginawa sababbin a saida. Ko tayawa Asim be yi ba, suka kutse magana akan idan ya dawo daga sokoto zai zo tare da shedu a bashi makulin gida takardu shi kuma ya bada kuɗi. Mutunen sai godiya yake ganin Asim be taya ba ya amince zai ba shi kuɗin. Bayan sun dawo ya aje Ƙanen Baban nasa ya miƙa masa dubu ashiri, sannan ya kama hanyar gidan Hajiya Sadiya yana aikawa Namra kira.....

Tsaki yaja bayan ya kashe wayar, lallai ma yarinyar nan ta raina masa hankali, shi zata yi ma ɓoyun ɗansa? Allah yasa ma da gaske ta zubar da cikin nan ta ga yadda zai yi da ita ƙut! ya yi ƙwafa.

Yayi mamakin ganin Hajiya Sadiya a gidan nata, bayan yasan a wacan take zama saboda ƴarta. Bayan sun gaisa ya zauna saman kujera yana kallonta.

“Mun yi waya da Alhaji yace na same shi sokoto, kuma na samu labarin Namra tana sokoto har ma na yi waya da ita, amman kin san ba lallai ba ne ta amince ta dawo gidana ba ko?”

“Nasan da hakan shiyasa ka ga na dawo nan gidan ai, nasan zaka zo nema na, abunda nake so da kai ka yi ta try har sai kaga ta aminci, idan kuma hakan be samu ba, to zan baka abunda zaka bata, kuma ka tabbatar ya kai ga bakinta, ma'ana ta ci”

“Mi zaki ba ni?”

“Ina zuwa”

Ta miƙw tsaye ta nufi wani bedroom. Shi kuma ya ƙurawa pop ido kamar yau ya fara ganinsa.

“Wallahi duk kika zubar min da ciki ko? Hmmm, Allah yasa ma Ubanki ne ya zubar da shi ta yadda zan fi jindaɗin shari'ah da shi...”

Fitowar Hajiya Sadiya ce tasa ya mai da dubansa gareta yana kallon farin ƙyalen da ke hannunta. Tana ƙarasowa ta warware ƙyalen ta miƙa masa apple ja.

“Ka tabbatar ta ci wannan apple ɗin ko da kaɗan ne, amman sai idan ta ƙi yarda ta koma ɗakinta”

Ya ƙurawa Apple ɗin ido

“Kar fa wani abu ya same ta, i mean kar ta mutu, akwai baby na a jikinta”

“Babu abunda zai same ta, ka yi yadda na ce kawai”

“Okay”

Ya miƙe tsaye tare da saka apple ɗin a aljihu, ya fice. Be yi nisa da barin gidan ba Nably ta kira shi, amman sai ya samu kansa da ƙin ɗauka shi kwata-kwata yanzu ta fita ransa, Mardiya ce on top.

KU YI HAƘURI DA WANNAN🙏

*Ku yi ta yaudarar kan ku da sunan wata ta siya ta ara muku ku karanta, idan mun je can inda baki be magana zamu tsaya gaban Allah ni da ku ya mana hukunci.*

HILAL POV.

SIX MONTHS LATER...
Suna jin ƙarar tsayawar Motar Dadynsu suka fita da gudu suna masa oyoyo. Zaune suka same shi cikin motar yana waya, hakan yasa Ezzah zagayawa a front seat ta zauna tana jiran ya gama wayar ta fara masa complain.

“Dady muna dawowa daga makaranta Mama Teema tasa mu wanki”

Yana sauke wayar daga kunnensa kenan, ta soma labarto masa abinda ya faru yau. Wani kallo yake mata, irin kallon nan na ɗa da ƴa, kamin ya kai hannunsa ya kama fuskarta ya riƙe.

“Ezzah kin yi ƙanƙanta da irin abubuwan nan, kullum sai kin ce Teema ta miki kaza bla bla bla, wannan sam be dace da ke ba, babu abunda Teema zata muku sai tarbiya, ƴar'uwarki bata taɓa faɗar an mata wani abu ba sai ke”

Ta turo baki zata masa magana da kuka a lokaci ɗaya.

“Dady ni bana son ta, a kawo mana Mummie mu”

“Ba za'a kawo ba, kuma kar bakin ki ya ƙara furta kalmar ƙi ga matata, ke kowa ai baki so, har Kalsoom ba haka kika mata ba? Saboda ku Hajiya tasa na auri Teema yanzu kuma ki bijiro min da wannan maganar! Kar na sake ji”

Ya fita daga motar ya kama hannun Ulfah, sannan Ezzah ta fito ita ma tana share hawaye ta rufe masa motarsa, ta rufa musu baya.

Teema na tsinkayarsu dan tana tsaye jikin window ne, sai dai ba zata iya jin me suke cewa ba. Tana ganin ya doso ƙofar falon sai ta bar gurin da sauri ta shige bedroom ɗinta ta zauna bakin gado ta soma ƙirƙiro kuka. Tun da ya saka kafarsa a falon ya ji be ji motsin Amaryarsa ba ya saki hannu Ulfah ya doshi bedroom.
Zaune ya same ta bakin gado tana rusar kuka, zama yayi kusa da ita cikin damuwa, dan yasan dalilin kukan nata baya buƙatar tambayarta.

“Sau nawa zan faɗa miki ki yi haƙuri Teema? Wasu ma sai da suka shekara ashiri a gidan miji sannan Allah ya ba su haihuwa, balle ke da baki yi shekara ɗaya ba ma?”

Ta ɗago kai ta dube shi.

“Hilal ina tsoron kar a'ce ba zan haihu ba ne gaba ɗaya, tun da na zo gidan nan ko ɓari ban taɓa yi ba”

“Idan Allah ya ga dama zai baki just be patient, wani lokacin abun mutum nesa yake, na shigo da farinciki kuma kin rusa min shi”

“Ka yi haƙuri rai na ne yake ɓaci”

Ta share hawayenta, har ga Allah wannan matsalar tana damunta, sai dai ta kan yawaita yi ma Hilal kukan hakan ne gudun kar ya zargi ta ci amanar ƴaƴansa, duk lokacin da ya tarar da ita cikin irin wannan halin ya kan kasa mata maganar yaran, ko da kuwa sun je masa sun kai masa ƙararta ne.

“Kuɗin da na faɗa miki muna jira jiya dai Allah yayi sun fito, dan haka yanzu ki shirya muje kasuwa da yara mu yi siyayya, gobe kuma zan je da Kalsoom Hajiya kuma kuɗi zan bata, sauran kuma sai mu ƙara a account, idan na samu hutu sai mu leƙa waje”

Hannayenta ta kama ta riƙe tana murzawa a hankali.

“Hilal ya kamata ka yi tunanin ma kan ka future, kai kake ta hidima da Hajiya duk da tana da waɗanda zasu iya mata beside Abbah ka yana da rai balle ace ko zata rasa wanda zai mata ne, ya kamata ace ka tanada abun ka har sai ranar da zaka nema ko kuma ita Hajiya zata nema sannan ka ɗauko ka yi amfani da shi, ƴaran ka babu abunda suka nema suka rasa, dan me za'ace a riƙa kashe musu kuɗi haka nan kawai a banza? Ka fara ginawa kan ka rayuwa Hilal, yanzu nan kuɗi ba ƙara ka gina gida da shi ba”

“Ina da gida Teema ba ɗaya ba ba biyu ba uku ba, kuma naga yanzu mi zan yi da gida?”

“Baka mafarki tara zuri'ah kamar ta Mahaifinka? Baka fatar haɗa ƴaƴan da matanka guri ɗaya yanzu? Ni abun da naga ya fi kawai ka kawo ko 150.000k ne asiya mata lace da atamfa, sauran kuɗin kuma ka ba ni nawa ita kuma Kalsoom ka bata ta siya abinda take so, Hajiya na san idan ka bata kuɗin kashewa zata yi amman idan aka siya mata kaya, ko sakawa ta yi ai ka ji daɗi, ni k8ma ina son na fara business”

Miƙewa yayi tsaye.

“Zan yi tunani akai, bari na je na duba Kalsoom ta ce min kan ta na ciwo”

“Ka gaishe min da ita, tun da ka ƙi yarda na ganta, amman ba zaka bari ka ci abinci ba”

“A'a sai na dawo kinsan matsalar mai ciki”

Ya faɗa da murmushi a fuskarsa sannan ya juya ya fice, zuciyarsa da kwankwato, ya lura duk lokacin da ya shigo da zimmar yi ma yaransa ko Hajiya abu sai Teema ta nuna masa ba haka ba, abunda Kalsoom da Rashida ba su taɓa masa ba kenan. Duk da yana tunanin wannan karon ta yi magana mai ma'ana kuma da bada dalili. Miƙewa ta yi ta rakoshi har gurin mota, ya shiga ta maida ganbun motar ta rufe tana ɗaga masa hannu har ya fice.

Ajiyar zuciya ta sauke, ta gaga mallakar mijinta har yanzu, iya shige-shigen da take tunanin zata yi ta yi amman kan Hilal ya gagara mallaka, bata da ƙudiri raba shi da mahaifiyarsa, sai dai tana ganin kamar hidimar da yake mata yayi yawa, tun da ba shi kaɗai ta haifa ba.

“Ulfah, Ezzah..!”

Sai ga su da gudun su, bama Kamar Ulfah da hanjin cikinta ke kaɗawa, dan jikinta har rawa yake kamar zata saki fitsari.

“Uban mi kuke faɗawa Baban ku ɗazu...?”

Ulfah ta yi sauri ɗaga hannunta sama.

“Wallahi ba ni ce ba, Ezzah ceta faɗawa Dady wai kin sata wanki”

Teema ta miƙa hannu ta kama kunnenta har sai da ta yi ƙara.

“Wato dan na saku wankin uniform shine abun magana? Ke komai sai kin kwashe kin faɗawa Dadynki? Sau nawa nake ja miki kunne akan faɗawa Dadynki magana idan na miki abu?”

Ta nuna mata wani ɓangare na gidan inda rana ta baje a gurin, kamar an hura wuta.

“Oya wuce can ki kama kunnenki, kuma karki taso sai na ce ki taso”

Da sauri ta ɗuka ƙasa ta riƙa kafafun Teema.

“Dan Allah ki yi haƙuri ba zan sake ba”
Chapter 139 · 0% Book details