← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 173

Sashe 22

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba suyi wata doguwar hira ba suka yi sallama, ko lemun da ta kawo masa be sha ba.
Cikin rashin jindaɗi ta nufi shiga falo, har ta nufi kitchen ta aje lemu na ɗauke da kalaman da Asim yayi mata. Idan tace ba zata iya zama a can ba zai zargeta, sai dai har ga Allah bata jin zamanta acan ɗin zai fi.
Bata yarda ta labarta ma Anty Amarya komai ba, sai kawai ta shige ɗakinta tana shawarta zucuciyarta, da nema musu mafita.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa17.html

🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺

                            Wattpad @
                  KHADEEJA CANDY

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

Wannan shafin sadaukarwa ce ga SANAH S MATAZU. Namra da Kalsoom sun ce a gaishe ki😘

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 17*

KALSOOM POV.

Sun ɗauki dogon lokaci kamin su fito. Ko da suka fito har Kalsoom tayi nisa da cin abincinta.

“Sorry mun bar ki kina cin abinci ke kaɗai”

Rashida ta faɗa tana ƙoƙarin zama. Kallonta kawai Kalsoom tayi ta cigaba da cin abincinta. Hilal ya lura da yadda yanayin Kalsoom ya canja hakan yasa ya zauna a kujerar dake daf da ita ya ɗauki abincin ya mai da agurin.

Sosai da sosai hakan ya sosa ran Rashida, for the first time in history jikin mijinta yana gugar jikin wata mace. Wasa da riƙayi da abinci ta kasa ci. Hilal ya lura da yanayinta amman be kulata ba har ya gama cin abinci tare da Rashida. Tashi Rashida tayi zata kwashe kwanukan sai ya riƙe mata hannu.

“Bar su kawai je ki shirya kan ki zan kwashe kayan, nima na iya aikin ai, amman kamin nan zauna zamu yi wata magana”

Ba musu ta koma ta zauna. Sai da yaja dogon numfashi sannan yace

“Rashida Kalsoom ina son ku bani aron hankalinku, Ban auri Kalsoom ba dan na wulaƙanta Rashida, kuma ban auri Kalsoom ba dan bana son Rashida ba, yanzu nauyin ku duk ya hau kai na, dan haka ina fatar zaku taya ni sauke nauyin da Allah ya ɗora min, ba wai ku tada min hankaliba, zan fu kowa jindaɗi idan kuka haɗa kanku.

Zan iya zama abun kwatance idan kuka kwantar min da hankali, ba zan iya gane wace tafi so na ba sai ta sai ta hanyar kwantar min da hankali da kuma kyautatawa. Bana son wani rashin jituwa ya shiga tsakanin ku, kuma ban da ɗauka anyi ance duk wanda take ganin ba ayi mata dai-dai ba zata iya magana”

Kalsoom ce ta fara magana bayan ya kai aya.

“Inshallah zaka same me mai biyayyah, ni ɗai indai gefe na inshallah ba za a taɓa samun matsala ba, kuma ina fatar wasu abubuwan da zanyi a cikin rashin sani Ammyn Rafiq zata tunatar da ni”

“Inshallah ina fatar nima zaki tunatar da ni Allah ya bamu haƙuri zama da juna, sai dai sai kin yi haƙuri dasu Ezzah saboda basa jin magana”

Rashida ta faɗa tana mai jin sassauti a zuciyarta.

“Ba komai Ai yara na kowa ne, yaran ki ai nawa ne”

Hilal ya jidaɗin yadda yaga sun ɗan sake da juna, yasan nan gaba komai ze wuce kishi ne kawai wanda ba a rasa ba.

Bayan sun ɗan yi fira ta tashi ta nufi ɗakinta, Rashida kuma ta nufi ɗakin yaranta, dan ta tashesu.
Shigar da tayi a ɗakin ya bata damar kallon irin dukiyar da mahaifinta ya zuba mata, ta jidaɗi matuƙa sai da ta ƙare ma ɗakin kallo sannan ta ɗaga hannu sama tayi ma Allah godiya. Sannan ta nufi bathroom ɗinta tayi wanka, cikin koriyar atamfa ta shirya ta tsaɓa ado. Sannan ta ɗauki wayarta ta kira Momy da Daddy ta gaishe su.

Guraren biyu da rabi Salma tazo gidan, aiko Kalsoom kamar ta haɗeye ta, sai duk taji kamar ta daɗe bata ganta ba.
Ɗakinta ta kaita ta kawo mata abinci da abun sha. Sai da Salma ta ci ta ƙoshi sannan ta kalli Kalsoom tana dariya tace.

“Komai mai lokaci, yau dai gashi na ci abincin gidan Kalsoom”

Kalsoom tayi dariya. Salma tace

“Ya dai zaman ku babu wani matsala dai ko?”

“Eh toh babu matsala zuwa yanzu, ban sani ba dai ko gaba. Amman a yadda na lura kamar yana son matarsa da yawa”

Salma ta saki baki.

“Kalsoom kenan ke kin fi son ki auri mijin da zai riƙa wulaƙanta uwargidansa? Irin wannan mijin ai ba mijin aure bane, idan ya gama da ita akan ki zai yo.
Kuma Hilal ai dole ya so matarsa tun da matarsa ta gina masa sonta a zuciyarsa, kema ki gina naki mana, yana son matarsa cikin bata bashi lokacinta bata kula da gidanta a yadda ya dace, me kike tunani idan ke kika masa duk abunda yake so?

Aure ba abun wasa bane Kalsoom sai kin kai zuciyarki nesa, babu ruwanki da sashenta indai ba har ta kama bane, wani abu da gangan zata yi dan ki gani amman ki riƙa kauda idonki dan samawa kanki masalaha.
Ban da nuna masa ke maki son matarsa, wallahi komai take miki karki nuna masa baki son matarsa balle kuma ƴaƴansa, sai dai idan tayi miki wani abun na laifi ki nuna ɓace ranki ki yi magana dan ƙwatar yancin ki. Karki kuskura zagin matarsa gaban idonsa, kina ida kina haka ko da ita ta nuna masa bata son ki ita zai riƙe da abun a zuciya ba ke ba

Kuma ki kama ƴaƴansa ki riƙe kamar naki, babu ruwanki da ƴan anyi ance, ban da ɗaukar zancen maƙota, ban da biye son zuciya, duk wani kishi da zaki ji ki danneshi ki sawa ran ki sassauci, ban da faɗin sirrin miji, musamman na al'amarin auratayya. A duk lokacin daya buƙace ke ki nuna masa kin fisa buƙatarsa, ki sake jikinki ki yiwa mijinki duk abunda yake so. Ke ai baki da matsala da wannan matar tun da bata da lokacin kanta ma, yara kuma kullum suna islamiya da boko kin ga ai gidan ma kusan naki ne ke ɗaya

Ƴan uwansa ki kama ki riƙe ki maida su kamar naki, ki girmama mahaifansa, ki girmama abokansa, ki tarbi kowa da far'ah idan kina da abun basu ki basu, ki zama mai yawan alheri, gidan ki ya kasance mai ƙamshi da tsafta, abincin ki ko yaushe a ready.
Kin ga waɗannan abubuwan da na faɗa miki? Sune mallaka na musamman wanda mu mata basu san da ita ba, idan kina wannan wata mace ba zata iya gane kan mijinki ba, sai dai kiji ana ta mallake shi ai baya da magana sai nata”

Kalsoom tayi dariya tana mamakin yadda Salma take jero mata waɗannan bayanan kamar wata tsohuwar mace.

“Salma.yaushe kika ɗauki wannan karatun?”

“To ai ke sabuwace mu kuwa mun tsufa a lamarin, ke bari na baki wani sirrin, idan zaki bawa mijinki abinci ki laɓe a inda ba zai ganki ba ki riƙa karanta masa Bismillah kafa shirin da tara ko sha tara, ki tofa masa a ruwa ko wani abu kamar alawa haka ko dabino, a lemu ma zaki iya amman idan kin ƙanƙare, sannan ki karanta masa Hal'ata alal insanu har zuwa samin'an basira, sai maimaita sami'an basira sau bakwai ki tofa masa a abinci, ki yawaita lalle idan mijinki mai son lalle ne, ko kuma ki karanta ayatul kursiyo ki tufa masa a ruwa, kuma ko yawaita cin fruits da tsarki da ruwan ɗumi, ki riƙa masa shagwaɓa dan zama suna son shagwaɓa sosai, hmmm ƙawata sauran soyayyar ki nemeta gurin Allah kawai, amman sai kin ba labari”

Taɓawa sukayi, Salma ta ɗora

“Ai shiyasa bana da shakku akan mijina, nasan ko aure yayi ba dai wata ta ɗauke masa hankaƙi ba, sai dai ma ta rasa gane kansa”

Salma ta daɗe tana yi ma Kalsoom lacca har aka kira la'asar, bayan tayi sallah suka je tare a ɗakin Rashida Kalsoom ta gabatar mata da Salma sannan ta fito, har gurin gate Kalsoom ta raka ta.

NAMRA POV.

Washe garin ranar da sukayi maganar da Namra, Asim ya sanar mata a wayar Maryam cewa iyayensa zasu zo ganin Abbah ya saka musu rana. Ita kuma sai ta faɗawa Anty Amarya tayi masa magana, ya saka musu ranar lahadi.
Ranar lahadin na zuwa suka zo, Abbah yayi musu tarba daidai gwargwado, sai dai basu ga annurin fuskarsa ba ko kaɗan.
Dubu Hansi yayi musu sadakinta, yasa musu date 23 ga wata mai biwa wanda zai shigo, su kuma suka tafi akan sai sun yi shawara.

A Ranar Namra kuka tayi kamar zata mutu, sai dai bata yarda ta faɗa ma Anty Amarya ba, balle Maryam, a ɗayan ɓangaren kuma tana tunanin ƙawarta Amira.
Sai da dare Asim ya kirata a wayar Maryam, a lokacin tana zaune falo sai ta tashi ta shige ɗakinta, sannan ta amsa wayar.

“Assalamu alaikum”

“Asim ya kake?”

“Lafiya ƙalau Dear, yau dai kin ga kamar mafarki an yanka min sadakin ki”

“Daman inda haƙuri ai komai mai faruwa ne”

“Haka ne Allah ya bani ikon biya”

“Ameen, amman Asim nace kana ganin zaman a can zai yiyu ko dai haya zamu kama”

“Haya kuma? Haba Namra ina naga kuɗin kama haya a yanzu, ni da nake tunanin sadakin ki da lefe kuma?”

“Ni zan biya kuɗin hayar, kuma zan taimaka maka da kuɗin da zaka haɗa lefe, amman Asim bana son kabar karatun ka”

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke.

“Amman gaskiya Namra ba zan bari kiyi gaka ba, ni ban aure dan kiyi min haka ba”

“Ban maka hakan dan wani abun ba, sai dan nema maka mutunci da girma”

“Zan yi tunani a kai, amman gaskiya wannan shawarar bata yi ba”

“Kayi tunani Asim, matuƙat Abbah yaga inda zaka aje ni ba zai bari na aure ka ba”

“Allah yayi mana mafita”

“Amin”

Daga haka suka yi sallama. Sai ta tashi ta nufi falo dan mayarwa da Maryam wayarta. A lokacin ne Anty Amarya tace mata

“Namra wai ya maganar karatun ki? Kin san kwanan ki nawa baki je makaranta ba kuwa?”

Tsaye tayi cak kamar hoto tana kallon fuskar Anty Amarya.

A waje Asim yayi waya da Namra, ya daɗe a gurin zaune yana nazari sannan ya tashi ya shiga cikin gida. Aiko Mahaifiyarsa kamar jira take ta hau shi da masifa.
Chapter 22 · 0% Book details