← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 173

Sashe 62

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta faɗa a fili tana share hawayenta. Sai kuma zancen da Asmee ta faɗa mata ya dawo mata na zargin kanta da take tana ɗauke da cutar, ita kuma ta san tana mu'amala da mijin Asmee. Jefar da fillon dake saman gadon tayi ta wani irin matsa gashin kanta.
Haka ta kwana har safe tana kuka idonta ya kumbura sosai kamar an zuba mata wani abu a ciki, bata fita ɗakinta ba, abincin da Momy ta kawo mata bata ci ba, sai kawai ta shiga banɗaki tayi wanka ta saka abaya, ta fito falo, ba dan tana jin ƙarfin jiki ba, sai dan tafitar ta zame mata kamar dole ne.

Momy na ganinta ta cika da mamakin ganin ta fito da shirin fita.

“Ina zaki je?”

“Ina son na ɗan fita ne, zan je office na ɗauki hutu sai na je gidan Asmee”

“Haba Rashida yanzu cikin wannan yanayin zaki fita sai kace wanda bata son kanta?”

Idonta ya cika da ƙwallah

“Momy ina son fitar ne ko zan samu gwarin jiki, kuma na sha iska, ko damuwa zai rage min”

“Kuma Sisters naki duk sun tafi school balle su raka ki, zaki iya driving ma”

“Zan iya”

“Shiga ɗaki ki ɗauka keys ɗina”

Momy ta faɗa cike da tausayawa. Ɗakin Momy ta shiga ta ɗauki makullin motarta, dan ita yanzu komai nata yana can gidan Hilal babu abunda aka ɗauko.
Cikin ƙarfin hali take driving ɗin, kamin ta ƙarasa office ɗin ta tsaya gefen titi tayi parking, ta kira number Malamin nan. Bayan sun gaisa ta koro masa da bayaninta.

“Malam aiki nake son ka min akan kishiryata”

“Me kike son a mata a kashe ta ko a haukatata?”

“Bana son a mata ko ɗaya, wani daban nake son ka mata wanda mijina zai gaji da ita ya rabu da ita sai ka min wanda zai dawo gare ni, a halin yanzu mijina ya rabu da ni”

“Me kika masa? Ina labarin waɗancan mutanen dana haɗa ku da su?”

“Ba mu yi aikin ba, saboda auren ya riga ya mutu, kuma wallahi ina son miji zan iya mutuwa idan babu shi a kusa da ni”

Ta faɗa cikin wani irin kuka, kamar ance mata malamin yana gabanta ne.

“Ya isa daina kuka, ai wannan mai sauƙi ne, akwai aikin da zamu masa ya dawo gunki da gudu ma, ita kuma za mu sakar mata jini sannan mu saka mata warin jaɓa idan ya gaji da ita zai sake ta, amman zaki kashi kuɗi”

“Kuɗi ba matsala bane zan baka ko nawa kake so, amman ina son a buga min ƙasa a bincika min komai nawa”

“Zan miki haka, duk abunda ƙasa ta faɗi zan faɗa miki idan kin zo, amman idan kin shirya aikin ki zo da tulo da zanen haila wanda ita kishiyarki take amfani da shi”

“Malam ya za'ayi na same shi yanzu, bayan bana gida kuma ai kasan yanzu ba'a amfani da irin wannan abun yanzu duk pad ne ake sawa”

“Pad ɗin shima ai zai yi, ki bincika a bolar gidan, idan kuma ba zaki iya ba, kisa zo ki biya kuɗi mu zamu sa aljani ya ɗauko mana”

“Zan zo nan da kwana biyu, na gode”

Daga haka ta kashe wayar ta ɗora kanta saman sitarin motar, kamin ta ɗago ta cigaba da tuƙin.
Wata pravate hospital ta nufa dan yi gwajin jinin so that ta tabbatar da zarginta.

AMIRA POV.

Har suka sauka garin Abuja bata wani farinciki musamman data ga hoton wanda ake son su kashe ɗin, sai duk jikinta ta mutu, ta tabbatar mutumen ƙwarai ne dan in ba haka ba babu abunda zaisa wasu su nemi a kasheshi.
Mutumen data taɓa gani a tv she can't recall his name, amman dai tasan shine wanda aka taɓa tattauna da ashi akan tsaro har ta ji ya kwanta mata a rai.

“Guy please karku taɓa mutumen nan”

Hancinsa yasa yana gogawa a kumatunta.

“Ina son ki sosai Amira, amman akan aikina zan iya ɓatawa da ke, so ki daina sa baki a kan aikina”

Ya ciro wayarsa dake aljihu ya kara akunne

“Hello ....Okay”

Ya kashe wayar yana kallonta

“Wai ya fita, zo muje”

“Tun yanzu za ku kashe shi?”

“A'a zamu fara farautarsa ne, yana Sahaba Restaurant, akwai yara dana aje Sahaba Hotel, kisa da inda yake, nima kuma can zanje amman sai gobe”

Ajiyar zuciya ta sauke ta janye hannunta daga riƙon da yayi mata.

“Ba zan je ba ku tafi kawai”

Duƙawo yayi ya mata kiss, sannan ya fice.
Ji take bata da natsuwa idan bata faɗawa masa abunda yake faruwa ba, sai dai kuma taya zata faɗa masa bayan shi ɗin babban mutum ne ganinsa ba hakan ake yi ba. Kuma idan har ta aikata ta jefa rayuwarta cikin matsala.
Sai da ta ji tashin motarsu sannan ta tashi ta shiga binciken gidan, har ta samo paper da pen tayi rubutu akai sai ta sanya doguwar riga dan jikinta inner ne kawai ta fito harabar gidan tana dubi-dubi.
Har tayi tunanin ta hau Napep sai kuma ta tuna Abuja ba ko ina ake farin Napep na shiga ba, sai kawai ta koma ciki ta tashi ɗaya daga cikin yaransa ta ce ya kai ta, yaso ya musa mata amman sanin halinta da kuma yadda Guy ke ji da ita yasa dole yaja mota ta shiga suka kama hanya.

Suna isa Sahaba Restaurant, sai ta hango Sahaba Hotel kamar yadda Guy ya faɗa mata. Nesa da gurin tasa ya aje ta tace ya tafi ya barta zata je gurin Guy, ba musu yaja motar ya koma. Sai da ta daina hangosa sannan ta nufi Sahaba Restaurant zuciyarta cike da tsoro gabanta kuma kar ma zai zube ƙasa.

Guy na daga gefe ya hango Amira ta doshi Restaurant ɗin sai waje-waje take.

“What the fuck, me Amira za tayi can ? Ko ta ɗauka ina can ne?”

Ya tambaya yana kallon yaransa da suke tare da shi cikin motar, wanda ko wannensu ba shi da amsar ba shi. Da sauri ya buɗe motar ya tara hannayensa a baki yana mata fiito (shewa) irin na tsuntsaye. Amira na jin kira ta san Guy son ne, maimakon ya ga ta dawo sai kawai ta ranta cikin na kare.

ABDOOL POV.

Ganin kurciyar ta firanye sai kawai yayi musu alama da hannu akan su koma kawai. Shi kuma ya koma cikin gidan, ya kunna tv yana kallon news, lokaci zuwa lokaci yake jan tsaki saboda lamarin nijeria kullum abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, yau wannan kakeji gobe wani kala ne. Idan ma kace zaka maida hankali akan abun sai tunani yayi maka yawa.

Wuni yayi a cikin sallah ce kawai take fitar da shi gidan, sai da dare ya sauya kayan jikinsa ya fita siyen abinci dan be yarda a dafa masa a abinci duk kuwa da kasancewar akwai masu masa dafa masa, amman baya ci sai dai sauran ƴan gida su ci. Ko a gurin siyen abincin ba guri ɗaya yake tsayawa ba, saboda tsaro.
Bayan ya karɓi takeaway ɗin ya biya sai ya juyo ya nufi ƙofar fita. Yana fitowa ya hango budurwa tana gudu iya ƙarfinta ta doso inda yake, kallon mamaki yake mata yana son tantance abunda take ma gudun.
Sauran taku kaɗan ta ƙaraso inda yake, sai ƙarar bindiga ya tashi, cikin wani irin zafin nama ya riƙota dan ya gane ita aka harba, sai dai haka be hana bindigar samunta, sai ta sulale a hannunsa tana banƙarar bayanta saboda zafi da kuma dafin albarushin da taji ya soke ta abaya.

Daga shi har ita tare suka kai ƙasa, cikin hanzari ya ciro wayarsa ya kira yaransa. Sannan ya kira head quarters.

*🌺🌺 ZAGON ƘASA  🌺🌺*

*© Khadeeja Candy*

Don't read if you didn't pay...!

*PAGE - 44* 

NOT EDITED ⚠

_An kaiwa Major General Abdullah Ahmad Mai-doki hari_

_An yi nasarar kashe waɗanda suka kaiwa Major hari_

_Yarima Abdullahi Ahmad Mai-doki Ɗan sarkin Katsina ya tsallake rijiya da baya_

_Wata yarinya ta sadaukar da ranta saboda ɗan Sarki_

Shine abunda kowa wace jaridar Nigera ta online ta yi ado dashi a fuskarta shafinta, har ma da na ƙasashen waje, bayan mintuna 25 da faruwar lamarin.
Online rumors updated kuma kowa da abunda yake rubutawa, har da masu cewa har shi an harba da masu cewa ma ya mutu, da masu cewa yaje siyen abinci da karuwarsa, wasu kuma matarsa ko dai da irin yadda tayi masa daɗi yake ƙaƙarowa ya rubuta a social media.

Dandazo ƴan jarida suka yi a bakin asibitin da aka kai Amira, dan jin kanun labarai, ko wannen baya son a bashi labari.

Sai dai sojojin da ke zagaye da asibitin basu ba su damar shiga ciki ba, balle har su ɗauki rahoto ko kuma video abunda yake kan faruwa ba.

A bakin kofa Abdallah ya tsaya yana kai da kawo har sai aka fito da ita ɗakin tiyata, bayan an cire mata albarushin.

“Doc is she live?”

Shine abinda Abdallah ya fara tambaya ganin an fito da ita daga ɗakin galalla kamar wanda bata numfashi, a kife take saman gadon asibitin dan a bayanta ne suka mata aikin cirar albarushin.

“She survived,  but she's unconscious now and she will take 28 -32 hours before she wake up”

Likitan na faɗar haka ya suka wuce da ita wani ɗakin, tare da wasu Nurses. Da kallo Abdool ya bita sai da duka shige da ita ɗakin sannan ya sauke ajiyar zuciya ya shafa kansa. Sannan ya zauna a kujerar dake gurin ya lumshe ido yana sauraren wayarsa da ke ringing.

Kira ne kan kira yake shigowa, tun wayar tana ringing da vibration ita kaɗai har cinyarsa ta gara amsawa, saboda yawan kira. Shi dai yasan ba zai iya ɗaukar kira kowa a yanzu ba, dan yasan ba zai wuce masu son jin lafiyarsa ba, abu ɗaya yaji zai iya, magana da ƴan jarida dan tabbatar musu da lafiyarsa.  Hakan yasa ya miƙe tsaye ya ciro wayar ya miƙa PA ɗinsa dake tsaye kusa da shi.
Chapter 62 · 0% Book details