← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 173

Sashe 81

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ai kowa ya ji dalilin ka dole ya ɗaga maka ƙafa, amman ni gasjiya ban baka shawarar zama da matar nan ba”

Agogon hannunsa ya kalla.

“An kira Salla bari naje kar na rasa jan'in”

“Muma ai tashi za mu yi, amman wa xai kwana da shi?”

“Ni zan kwana da shi gida zan koma na canja tufafi sai na dawo”

“A'a ga Balki da Amina ai zasu iya kwana a nan”

“Akwai abubuwan da zan masa idan ya farka, so zai fi kyau na kwana da shi ɗin”

“Allah ya sauwaƙe ya bashi lafiya”

“Amin ya rabb”

Tare suka fito, sai da ya raka su gurin mota sannan ya nufi masallacin asibiti yayi salla isha'i.
Bayan ya fito daga masallaci ya koma office ɗinsa ya kulle office ɗinsa sannan ya nufi ɗakin Rafiq ya duba ya fito ya nufi gurin da aka tanadar likitocin asibitin su yi fakin ɗin motocin su.
Motarsa ya shiga, yayi mata key. Har ya fita harar asibitin be daina jin baya son zuwa gida ba. Be ƙara jin gidan ya fita ransa ba sai da yayi farkin harabar gidan. Ya ɗan daɗe cikin motar sannan ya fito.ya shiga cikin gidan.

Da gudu Ezzah da Ulfah suka zo suka rumgume ahi suna masa sannu da zuwa. Durƙusawa yayi a gurin yana shafa kansu.

“Dady Anty tana ta kuka tun ɗazu tace min Rafiq be da lafiya wai yana asibiti”

Ulfah ta faɗa tana wasa da rigarsa.
Be ce musu komai ba sai kawai ya nuna musu kujera alamar suje su zauna. Ezzah ce ta riga zuwa dan yau tana cikin nishaɗi, ganin Kalsoom na kuka duk yasata jindaɗi kamar wata kishiryarta.

Tashi yayi ya shiga ɗakinsa. Kwantawa yayi saman gadon ya lumshe ido yana sauraren kansa da ke tsarawa. Buɗe idonsa da zai yi ya ga Kalsoom tsaye a kansa hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta, ta canja kama sosai fuskarta ta ɗan zurma idonta kuma ya kumbura har bata gani sosai da shi.

“Ya aka yi?”

Ya tambaya yana tashi zaune.

“Ya jikinsa?”

Maimakon ya amsa mata sai kawai ya miƙe tsaye ya soma cire kayansa har ya ɗaura tawul be ce mata komai ba sai kawai ya shige bathroom. Ta so ta nuna masa takardar sammaci da ɓoye a bayanta wanda Rashida ta aiko mata, amman rashin samun damar haka yasa ta juya ta koma ɗakinta, cikin wani irin baƙiciki da take jin kamar ta mutu a yau ta huta.

Bayan ya fito wanka ya saka wasu tufafin ya ɗauki abinda yasan zai buƙata ya fice daga gidan. Har ya kai gurin mota sai kuma ya dawo yayi ma yaransa sallama tare da shafa kan su ya samu albarka sannan ya fice.

ANTY AMARYA POV.

Ta daɗe kwance a gurin tana jin zujin da zuciyarta take mata ga numfashinta dake ta sama. Daker ta unƙura ta tashi ta ɗauki ruwan da aka kawo ma Yasmin ta sha. Sannan ta samu ɗan saussauci.
Ko da Aisha ta fito har abun ya ɗan kwata mata. Ita ma sam bata jidaɗi labarin da Anty ta faɗa mata na Namra ba, duk da tana ƙarama amman sam be mata daɗi ba, kukan Anty Amarya yasa ita ta fara rera tana kukan tana bawa Anty haƙuri.

Sai kusan la'asar Maryam da sauran ƴan gidan suka dawo, suma duk ba su jidaɗin yadda suka samu Anty ba, dan abinda suka zo dashi na walima sai duk suka kasa a ci.

“Ni daman na yi mamakin hana mutane zuwa gidanta da take wallahi daman nasan ba ban xa ba”

Cewar Maryam tana riƙe da hannun Anty Amarya dan tausasa mata zuciyarta.
Anty ta share hawayen ta

“Zuwa zan yi na zo da ita, gobe goben nan, bana son na mutu na barta a cikin halin damuwa, ita ce yayarku idan bana da ita za zata riƙe ku. Ba ina ƙyalar talauci bane amman wannan rayuwar sam bata dace da Namra ba”

“Amman Abbah zai bari kuwa?”

Cewar Hindatu dan tasan halin Abbah idan yace A'a to a'a ne no matter what.

“Ba zan faɗa masa da ita zan zo ba, sai idan na dawo ya ganta, idan kuma ya ce ba zata zauna masa a gida ba, to zamu bar masa gidansa ni da ita, ban san minene yake bibiyar Namra ba, ina jin tsoron wannan rayuwa nata”

Maryam ta sauke ajiyar zuciya.

“Amman Anty kin san Abbah ba zai bari kije ba”

Anty tayi shiru tana sauraren sanyin ac dake tsara jikinta. Duk wata magana da suka yi a tsakanin su suka yi ta Anty bata sake cewa komai ba, dan jin take zuciyarta ta riƙe har cikin bayanta. Sai dare ta nufi part ɗin Abbah a lokacin ta tabbatar ya gama cin abinci duk da tasan yau ba girkin ta ba ne.

Yana ganinta yasan akwai damuwa a fuskarta, dan ya karanci matarsa sosai, yakan gane nishaɗinta da kuma akasin haka, a duk lokacin daya kalli fuskar sahibarsa.

“Lafiya dai ko? In ce ba ni nayi laifi ba?”

Tun kamin tayi magana yayi mata tambayar ƴana kallon yanayinta, gaba ɗaya hankalinsa ya tattara ya koma gurinta. Ita kuma ta kasa magana saboda Hajiya da ke badroom ɗinsa tana gyara zanen gwadon da bata samu canjawa ba ɗazu saboda fitar da suka yi. Sai da ta gama abinda za tayi ta fita sannan Anty ta zauna dai-dai gaban Abbah tana shirin masa kuka ta soma magana cikin muryar data san shiga ƙwaƙwalta, dan tasan Abbah baya son kukanta, duka kuwa da ita ɗin ba ƙaranar yarinya ba ce amman wani lokacin haka zata sashi gaba tayi ta masa kuka akan abubuwa.

“Gobe da safe ina son naje katsina, sai na dawo da yamma”

“Gurin me? Miya faru?”

“Namra bata da lafiya ina son ganin ta”

Yayi shiru kamar be ji ba. Babu abinda yake tunanin sai maganganun Hajiya Barau data faɗa masa shekaran jiya akan halin da Yasmin ta samu Namra.

“To ki shirya sai direba ya kai ki, amman dai ganin kawai zaki yi, karki ɗauko min ita, dan ba zata kashe aurenta tazo gidana ta zauna ba, ko bana da rai ban lamunta ba”

Anty bata musa masa ba, dan tasan idan ma tace xata tsaya jayayya dashi sai su kwana a nan suna yi abu ɗaya. Amman dai tasan idan har ta dawo da Namra, duk abinda zai faru sai dai ya faru idan ma ya tsaya haƙai akan Namra ba zata zauna masa a gida ba ita zata bar masa gidan wanda ta san ba zai so haka ba.
Tashi tayi ta karɗe jikinta ya fito daga part ɗin xuciyarta da ɗan sanyi barinta da Abbah yayi taje gurin Namra.

Tun cikin daren Anty ta soma shiri, ta kuma kira driver ta faɗa masa sai yaje gidan man Abbah ya cika motar dan ta faɗa masa tun 6 zasu kama hanya dan samun dawowa da wuri.
Duk yadda Maryam ta so binta Anty ƙiyawa tayi dan tasan zasu iya rigima da Asim can, Aisha da Hindatu kuma makaranta.

*WASHE GARI...*

Kamar yadda tace tun da tayi salla asuba ta shirya, sai dai bata ci komai ba dan bata jin cim abinci daman haka take idan zata yi tafiya balle kuma tana cikin rashin daɗin rai.
Har gurin mota suka rakota. Hajiya Barau kam ta window ta tsaya tana leƙenta tana tabe baki zuciyarta cike da gulma kala-kala, ganin Anty amarya bata faɗa mata inda zata ba tasan baya da buƙarta ta san inda zata je, ita kan ta bata tabbacin inda zata ɗin dan Abbah ba lallai ne ya faɗa mata ba, dan ba kasafai yake faɗa ma sirrin wata matar ga wata matar ba.

Tun da suka kama hanya babu abinda Anty taje sai salati da istigifari. Duk bayan awa ɗaya Maryam take kiranta ta tambaye ta ya hanya, Hindatu ma da take makaranta ba abarta a baya ba, ta kan kira ta tambayar.

Hakan suka share awa shida suna tafiya a hanya ba tare da sun tsaya ba. Ba laifi direban yana ɗan gudu dan Anty ce ta buƙaci hakan ta matso ta ganta gurin ƴarta. Ana saura awa ɗaya su isa Katsina motarsu ta fara basu matsala, Anty ta tsorota sosai ganin a hanya suke, sai direban ya riƙa ƙoƙarin kwantar mata da hankali akan cewar zasu isa lafiya kamin ta tsaya in yaso sai su samu wanda zai duba musu ita a can katsina ɗin.

Sun isa Katsina lafiya, sai a mararraba motar ta soma gaba tana baya, hakan yasa direban fakawa gefe ya fito yana duba motar.
Anty ma fitowa tayi tazo ta tsaya gaban motar gurin da direban yake tana duba abinda yake taɓawa tare da tambayar abinda ya samu motar.

Motocin dake kai da kawo babu wacce ta tsaya, sai wata kafirar mota mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ita har ta wuce sai ta dawo kusa da su ta faka.
Buɗe motar Abdool yayi ya fito ganin dattijowa kamar Anty a cikin zafin ranar nan ya hana shi wuce ce, dan daga gani yasan motar ce ta tsaya. Cikin wani irin taku ya ƙaraso gurin, shi ba na sauranta ba ba kuma na yana sanye da kakin soja ba.

“Lafiya me ya samu motar?”

“Wallahi muna tafiya ne ta fara bamu matsala ina jin ko ingin ne”

Matsawa yayi ya duba motar ya buɗe abubuwa ya gani, sai ya koma motarsa ya ɗauko ruwa da baƙin mai ya zuba mata sannan ya maida komai ya gyara shi kamar yadda yake.

“Shiga ka tashi motar mu ga”

Da sauri direban ya shiga ya tashi motar yayi baga yayi baya yaga ta dawo normal sai ya faka ya fito yana godiya.

“Mun gode Sosai”

“Ba komai amman a riƙa kula da irin waɗannan idan za'ayi tafiya mai nisa”

“Inshallah mun gode”

“Allah yayi maka albarka”

Anty Amarya ta faɗa tana ɗan murmushi, dan tasan ko waye Abdool tun da tana ganinsa a tv, sai dai bata tabbatar da shi ɗin ne ba tun da ya tsaya ya taimake su, sai dai kuma kakin dake jikinsa da stars sun nuna haka.

Ɗan rinawa yayi yana murmushi.

“Amin Mama na gode”
Chapter 81 · 0% Book details