← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 173

Sashe 126

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ta shiga motarta ta fara driving bata da wani kuzari, hawayen da take kuma sun ƙi su tsaya mata. Wayarta da ke front seat ta yi ƙara alamar kira, kallo ɗaya ta yi ma wayar ta ɗauke kanta tana cigaba da rera kukan da bata san ranar tsayawar hawayenta ba, Alh Bashir ne, tasan shi ma ba zai wuce ya labarta mata Hilal zai auri ƙawarta ba, ita mamakinta ma ko Hilal ya manta Teema ƙawarta ce? Tsayawa tayi tunanin duk da tasan bata da ƙawaye barka tai hakan amman ba zai rasa sanin Teema ba, wata ƙila yayi mata haka ne dan ya rama abunda ta yi masa. Haka zuciyarta take nuna mata, cikin sauri ta ɗauki wayar ta faka gefen ti-ti, tana tunanin abunda zata faɗawa Hilal, da kiransa zata yi, sai kuma wata zuciyar ta bafa shawarar aika mata da saƙo. Sannan ta jefar da wayar ta cigaba da tuƙinta tana kuka har ta iso gida.
  Ga wayar sai ringing take, friends har da waƴanda suka daɗe basu kira ta ba, yau kiranta suke dan su ji ƙwan. Bata samu gurin faka motarta ba, saboda Motar Ummu Faisak da ke waje ta tare nata hanyar gareji, daman can gidan ba wani yarwantaccen gida ne ba, gida ne na zaman mutun ɗaya.

  Ba ta damu da share hawayen fuskarta ba ta shiga falon a haka. Ganin Momi da Ummu Faisak yasa ta ƙara narkewa ta fashe da kuka har da faɗuwa saman kujera. Nan take Ummu Faisak tasa kuka ganin yar'uwarta cikin damuwa. Momi kan tsawa ta katsa musu daga ita har Ummu Faisak ɗin.

“Miye abun kuka ga hukuncin Ubangiji? Ba ke kika jawa kan ki ba? Ai kin yi arziki da sai da kika fita gidan miji ita zata shiga, kuma ba ƴar'uwarki ce ta ci amanar ki ba! Ai ke kika fara yi ma kan ki zagon ƙasa da kan ki, kika taka mutumcin aurenki kika je kika bada kan ki ga wanda ba muharramin ki ba, ke wannan ma be isheki ishara ba? Cutar da take jikin ki bata isa ta nuna miki Allah ɗaya ne ba? Ai cin amanar miji Rashida ba ƙaramin haƙƙi ba ne, mijina yana can yana fafutar neman abunda zai kawo miki ke da ƴaƴansa, amman ke kina can kina cin amanarsa? Aiki hauka ne? Nasan 95% mahaifinki ne ya ja miki shi da ya tsaya kai da fata akan sai kin yi aiki, amman be ce kije can ki yi lalata ba, ai ba ke kaɗai ce mace ma'aikaciya ba, akwai da yawa waɗanda suke kare mutuncin mazan su da kuma na ƴaƴansu da na su da na iyayensu, ba ga ƴar'uwarki nan ba? Ummu Faisak aiki take, ita bata lalace ba saboda ta san mutuncin kanta, ki ba abun baƙin cikin ki ba ne ace wani namiji wanda ba mijin ki ba ya san surar jikin ki? Kin ɗauki rayuwar turawa kin sawa kan ki, baki da lokacin tarbiyantar da ƴaƴanki, tufafi ko sai waƴanda kika ga dama kike sakawa, nan aka auro miki Kalsoom na zo ina yaba shigar da take irin tarbiyar da ta samu a gidansu, kika ce min na fi son ta, da ke, kika ce  ina miki abu kamar ba ni na haife ki ba, a lokacin ruɗin duniya na ke guje miki amman idon ki ya rufe.

Dan baki da hankali zaki wanke ƙafafu kije gidansu Teema to ki ce mata me? Ki zauna ki yi wa kan ki karantun ta natsu, ki nemi yafiyar ubangijinki, kuma ki nemi yafiyar mijinki tun haƙƙinsa be cigaba da binki ba, dan duk abunda kika aikata da aurensa haƙƙinsa yana saman kan ki, kin yi sa'ah da Allah ya rufa miki asiri tun wuri, dan duk mai cin amanar mijinta sai taga ishara wallahi ko ba daɗe ko ba jima, kiyi taka tsantsan da duniya Rashida dan ta fara barinki tun kamin ke ki barta, karki yarda ki ci amanar wani, ƙara ke a ci amanar ki, balle kuma miji. Tashi muje”

Momi ta ƙarasa tare da kallon Ummu dake gefenta, kana ta miƙe tsaye idonta cike da ƙwallah, ranta kuma a ɓace ta fice, Ummu Faisak ta rufa mata baya tana cigaba da hawaye.

Hannu Rashida ta ɗora saman kai, tana kallon ɗakin kamar sabuwar mahaukaciya.

“Innalillahi Allah kasa mafarki na ke yi, Allah ka farkar da ni daga wannan mummunan bachi, Allah ka farkar da ni Allah, Allah ka tashe ni...”

Ta rushe da wani irin kuka tana dafe da kanta da take jin yana jujjuya mata.

HILAL POV.

_Hilal ka san wacece Teema kuwa, wallahi wallahi bokaye ta ke bi, kuma ta fi karfin iyayenta, karka aure ta Hilal dan Allah, ban yardar ta tarbiyantar min da ƴaƴaba, ka auri ko cece amman ban da Teema_

Yana gama karanta saƙon ya saki tsaki, ya aje wayar saman teburinsa, ya miƙe tsaye ya fice daga office ɗin.
  Duk inda ya wuce ango ake ce masa daman wasu tun jiya ya basu iv wasu kuma sun samu labari, yana isa gurin karɓar results ya buɗe ciki ya shiga. Daya bayan ɗaya ya gaisa da su, sai tsokanarsa suke, wai ango ka sha mai.

“A'a ban sha fa da saura”

Sai duk suka sa dariya har shi Hilal ɗin da yayi magana, ɗaya daga cikin likitocin dake tsaye ward ɗin ya ce

“Doc baka da kunya”

“To kunyar me zan ji kowa ai yasan komai, kai bani results ɗin Amarya ta na gani”

“Amarya ko uwargida?”

“Amarya dai, to duka yaushe na yi auren ?ba ƙaddarori bane dai idan Allah ya kawo babu yadda za'ayi”

“Aiko yanzu na ke shirin kai naka result ɗin, dan kana tafiya Doc Ahmad ya wanka hoton ya ce ina kake nace ya kawo wannan albishir ɗin ni zan yi ma madam shi da kaina”

“Ai ana ɗaukarta Hoton ta sha mun kai na maidata gida, ita dai ciwo take ji, shiyasa kaga na masu na ƙarɓi results ɗin so that na san abunda yake damunta kar mu yi cuta daban magani daban, tun jiya kuka take min wai tana jin abu a mararta kamar dutse sai amai take”

Kamin ya miƙa masa results ɗin sai da ya miƙa masa hannu.

“Congratulations ba dutse ba ne alheri ne, sai dai idan ka duba zaka gani”

Ya karɓa zuciyarsa fari ƙal.

“Wow ka ce na yi aiki Alhaji...”

Sai duk suka kwashe da dariya. Shi kam be ma kula su ba hankalinsa ya tafi gurin Hoton.

“Six months i'm surprise, kwata kwata ban kawo wa rayuwata ciki ba ne, dan tace ƙasan mararta kuma ita pain her, ko tsayin kirki bata iya yi, jiya gaba ɗaya a rikice muka kwana”

“Yeah yayi mata kwance ne, baka ganin yadda yake, sai kun kula da shi sosai gaskiya, Allah ya raba lafiya”

“Amin”

Ya fice da sauri, ɗaukar wayarsa ce ta zame masa dole, ba dan haka ba , ko office ɗin ba zai koma ba, a gaggauce ya ɗauki wayar ya fice. @360 ya bar asibitin tsabar zumuɗi ji yake kamar ma ya rumtse ido ya gansa gida. Cikin ƙanƙanen lokaci ya isa, daman be sa ran zai tarar da ita falo ba, dan haka ya wuce bedroom ɗinta kai tsaye, kwance ya same ta ƙasa ta duƙunƙune da bargo sai rawar sanyi take. Wani irin tausayinta ne ya kama shi, sai ya aje keys da takardar dake hannunsa saman mirror, ya kwanta bayanta ya yaye bargon dake jikinta ya ɗora fuskarta saman nata, jikinta yayi zafi aosai amman hakan be hana shi rumgumarta ba.

Ta buɗe ido da ker ta ɗan taɗo kai ta kalleshi.

“Gadon baya min daɗi”

Ta faɗa da muryar ta nan ta marar lafiya. Lumshe ido yayi yana murmushi.

“i'm sorry dear it's all my fault”

“Dan Allah ka min allura ko zan samu sauƙi”

“Ke da samun sauƙi sai nan da five months”

Ta yi dauriyar sake kallonsa cikin idonta na marar lafiya.

“Whats do you mean?”

“Sweetheart ƴou're pregnant”

Ƙarfin halin tashi ta yi, sai ya riƙa ta tashi zaune da kyau, ya kwantar da ita jikinsa.

“Da gaske?”

“Yes Dear six months”

Ta yi saurin kai hannu ta taɓa cikin, yo hwr surprise cikinta be yi girma ba, impact babu wani alama na ciki na jikinta idan ba wannan ciwon da ta yi ba.

“Amman ko dai one months...?”

“No wata shida dai, kin ga hoton da aka miki ɗazu can”

“Amman na yi menstruation last months fa”

“Nima abunda ya bani mamaki kenan, but kin tuna wacan lokacin da kika samu ciki ya ɓata? Ina tunanin shi ne ya kwanta miki, sai yanzu ya tashi, daman ana samun hakan nan wani lokacin, that's why we need to take good care of it, saboda mu samu ya dawo dai-dai”

Ɗagowa ta yi ta kalleshi, hawaye suka zubo mata.

“Congratulations”

Sai ya aika mata da kiss a goshi.

“Thank you Dear”

Ta ɗora kansa saman wuyanta, hannayensa zube saman cikinta.

ASIM POV.

A can ya kwana gurin Alhajinsa, da safe yasa aka kawo musu abun karyawa, sannan suka yi wanka, yadda Alhaji Nasir ya shirya cikin manyan tufafi ba zaka kalleshi kace yana aikata wani mugun abu ba.

Asim ma ya fito cikin ƙananan kayana kamar wani mutumen arziki, hankalinsa kwance zuciyarsa cike da natsuwar abunda ya aikata. Ba laifi yanzu be ji zafin da yaji da farko ba, sai dai har yanzu be fara jin daɗin da Alhaji Nasir da Hajiya Sadiya suke labarta masa zai ji ba, wata sai ya ƙara gwarewa akan harkar.

Alhaji Nasir ya saka turare ya kalli Asim ya ce.

“Har yanzu baka ƙarasa ƙwarewa ba a kan harkar nan, ya kama a sama maka kasuwan turawa nan ka kalla,dan ina son haɗa ka da manyan mutane ta yadda zaka ƙara gwarewa, ka ci moriyar ƙurciyarka”

Wani daɗi ne ya lumluɓe Asim, dan yasan kuɗi zai samu, daman burinsa kenan ya yi kuɗi.

“Zan ƙoƙarta Inshallah, ina godiya sosai”
Chapter 126 · 0% Book details