← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 173

Sashe 5

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata yi mamakin kalamansa ba, daman yakan yi fushi da ita wani lokacin, kuma ta lura da hakan tun daga lokacin da samu promotion. Yana tashi tayi saurin sakin handbag ɗinta ta riƙo shi, sai ya ture hannunta

“Zaki iya fushi da ni?”

“A'a ni Wallahi ba zan iya”

Ta faɗa a marairaice

“Toh ki koya daga yanzu, ta yadda za mu iya yin sati ba muyi magana da junan mu ba”

Rumgume shi tayi tana kukan shagwaɓa.

KALSOOM POV.

Ko da ta isa, Zainab na kwance falo tana bachi. Mayafinta ta aje ta ɗauki hijabi ta saka, ta bi gidan gyara tass, sannan ta ɗora musu girki.
Haka ta kwana huɗu tana musu aiki, cikin rashin sakewa dan gani take kamar Zainab ɗin da Mijinta zasu raina ta, ta kan abuɓda bai dace ba amman bata magana, sai dai kwallafawa zuciyarta idan har ta je gidan sai ta faɗawa Mony irin zaman auren da Zainab keyi. A kwananta na huɗun ne Momy tayi ma Mijin Zainab magana ya kawo ƙanwarsa dan ta taya Zainab zama, Ranar da zata dawo ranar ce Zainab ta fara awo cikin, dan haka dole ita ce ta rakata bata je aiki ba a ranar, asibitin ta je aka yi ma Zainab komai, sannan suka dawo gida tare, da zimmar ita Zainab ɗin zata koma gidanta da yamma.
Bayan sun gama cin abinci rana ne, Kalsoom ta ɗauko labarin dan Momy ta ja mata kunne.

“Gaskiya Momy ayi ma Zainab faɗa, ya kamata ace ta canja rayuwa ta riƙa lurar da mijinta abunda ya dace da wanda bai dace ba, kinsan mijinki fa kece makarantarsa ta farko, gareki zai fara ɗaukar darasi”

Momy tace

“Mi akayi?”

“Sam sam sam mijinta baya son alheri kuma baya son yan'uwansa suna zuwa gidan, sannan idan za ayi girki sai dai komai yaje ya siyo ƙire-ƙire kamar ba mai kuɗi ba, idan fa kika saba masa da wannan rayuwar ita zai riƙa miki ko can gaba”

Zainab ɗin ta haɗe rai sosai irin bata ji daɗin maganar ba.

“Nifa gaskiya bana son haka, daga zuwa jinya sai kuma kizo kina faɗar sirrin gida na”

“Ba ina faɗar sirrin gidanki bane, gaskiya nake faɗa miki”

“Toh ya kike son nayi masa? Ai halinsa ne idan yaga dama zai canja, Anty Kalsoom kefa ba auren nan kikayi ba balle kice kinsan yadda abun yake, ki bari har kiyi auren sannan ki faɗa min abunda da zan yi da wanda ba zan yi ba”

Saleena tayi farat tace

“Haba Anty Zainab daga an faɗa miki gaskiya”

Zainab ɗin ta yatsene fuska.

“Wane irin gaskiya, so take na masa bala'i ne ya sake ni nazo na zauna tare da ku”

Momy ta kalli Kalsoom tace

“Ki daina irin haka ba kyau, koma minene ki kyale ta can ita ta sani, ba kyau kana faɗin sirrin ɗan'uwanka, ita fa rayuwar aure sai da haƙuri kuma ke baki yi ba balle ki gane haka, ku daina wannan maganar bana so”

Duk maganar nan da Momy take kan Kalsoom na ƙasa saboda idonta daya cika da ƙwalla, daga bisani ta tashi ta nufi ɗakinta tana hawaye. Saleena ma ta tashi ta bar musu gurin tana harar Anty Zainab.

NAMRA POV.

Ranar Assabar aka yi walimar kamar yadda aka tsara, Namra na cikin ɗalibai talatin da uku da suka haddace wani ɓangare na Alƙur'ane, da ban aka ware su aka karramasu, aka kira manyan mutane suka yi musu kyauta.
Maryam na cikin Ɗaliban da suka sauka bana, bayan walimar makaranta sai da Anty Amarya ta shirya nata walimar a gidan dan karrama ƴarta.
Ƴan'uwa da abokan arziki da dama sun samu halarta, cikin har da Anty Yasmin da Ya Uzair. Anci ansha nama kam kamar mayankansa, ga uban takeaway da Anty Amarya ta
shurya gwanin ban sha'awa.
Ana sallah la'asar Ya Uzair ya tashi zai wuce dan Yasmin tace ita kam sai dare. Anty Amarya ta ɗauko masa takeaway, ƙin karɓa yayi sai yace a bawa Namra ta kai masa. Ba dan ta so ba ta karɓa ta nufi gurin Motarta fuskarta babu annuri. Shi ko yana cikin motar ya hakince yana kallonta.

“Ba nace karki faɗa Yasmin ba? Shine har da buga mata waya ko?”

Ya faɗa bayan ya kai hannu ya karɓa.

“An faɗa mata ba, amman zan faɗa mata very soon dan ba zan bar ta ta cutu da kai ba, ba zai yiyu ka laƙa mata cutar HIV ba ina zaune ina kallo”

“Wai miyasa idonki ya buɗe haka? Alaƙar dake tsakanin ki da Yasmin ita ce tsakani ɓa da ke, kuma Yasmin matata ce babu ruwanki da lamarin mu”

“Idona ya buɗe ne tun daga lokacin dana fahimci kai fasiƙi ne, kuma wallahi sai na tona maka asiri, har nema da kayi sai na faɗa”

Wani dogon tsaki taja, ta juya ta nufi hanyar falo.
Da wani irin kallo ya bita yana jin kamar ya kamo ta ya shaƙure, ƙwafa yayi ya rufe motarsa.

Sai bayan sallah isha'i kowa ya watse, a lokacin ne Maryam da Namra suka samu damar duba kyaututukan da suka samu, Ba wanda suka fi murna kamar na Abbah da yayi musu kyautar Zinari, ihu suka riƙa yi kamar zasu tashi gidan dan murna, ba ma kamar Marya data daɗe tana roƙon Abbah ya sai mata zinari.
A tare suka nufi part ɗinsa dan yi masa godiya, sai suka tararda shi zaune tare da Hajiya barau fuskokinsu shimfiɗe da murmushi.
Guri suka samu suka zauna suna masa godiya, sai ya amsa da far'ah kamar ba shine yake fushi da Namra ba, ita kanta abun ya bata mamaki sai dai kuma ta jidaɗin hakan.
Daf da zasu tashi ne Abbah ya kira sunan Namra

“Khadija”

“Na'am”

Da faɗuwar gaba ta amsa, ta dawo ta zauna tana jiran ta ji abunda zai ce. Sai da yayi gyaran murya sannan ya ce

“Kisan yadda nake da Uzair ko?”

“Na sani Abbah”

“Toh ya aiko Hajiya gata nan zaune ne yace yana son ƙara aure kuma ke yake so ya aura idan na amince masa”

Dakan shida-shida gabanta yayi saɓanin uku-uku dana kowa ke yi, da sauri ta kalli Abbah sai kuma ta sadda kanta ƙasa kamar wanda bata gane abunda suke faɗa ba.
Can ƙasa-ƙasa ta tsinkayo muryar Hajiya tana cewa

“Uzair kam ko wani gurin yaje neman aure ai mu zamu shige masa gaba, balle yace yana son ƴar mu”

Abbah yayi murmushin jindaɗi yace

“Sosai kan, wallahi yaron nan yana da tarbiya, ga hankali”

“Kuma ina fatar Khadija ba zaki bamu kunya ba, zamu yi matuƙar farinciki idan har kika amince da wannan auren”

Cewar Hajiya Barau. Abbah ya kalli Namra fuskarsa babu alamun wasa yace

“Zan baki kwana uku kije kiyi shawara, but lemme remind and warning you for the last time, kar damar dana baki na shawar ki zo ki ce min ba ki amince da Uzair ba”

Bata iya cewa komai ba har na tsawon lokaci, sai kawai ta tashi tayi baya-baya ta ƙara baya baya tana dafa kai kamar wanda zata faɗi, har sai da Maryam ta riƙa ta suka fita.

____________________________________

Yauwan Comments din ku yawan typing dina, comments din ku gwarin guiwa ne a gare ni.

#DOCTOR HILAL TEAM
#NAMRA TEAM
#KALSOOM TEAM
#UZAIR TEAM

#Comment
#Share
#Vote
#Blog
#Threefamily

BEST REGARDS 💖
Khadeeja Candy 🌺
http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa04.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

*PAGE - 4*

NAMRA POV.

Da kuka Namra ta shiga part ɗin Anty Amarya, sai ta zube ƙasa, ta jefar da sarƙar da ke hannunta cikin parlor.
Hindatu da Aisha duk suka kalleta, Anty Amarya kuma ta nufo ta da sauri tana tambayar ba'asi. Maryam ce ta faɗa musu abunda ya faru, dan Namra kuka kawai take kamar wacce za'a cirewa, zaunawa Anty Amarya tayi kusa da ita, ta kai hannu ta riƙa fuskar Namra idonta cike da ƙwallah ta soma magana

“Namra mi yake damun ki ne? Saboda Uzair yace yana son ki shi ne kike wannan kuka? Ni kike sakawa a damuwa, ni kike son jama matsala, duk rashin biyayyar da zaki yi ma mahaifinki laifin a kaina yake, ƙaurin suna zaki yi Namra, matuƙar kika ce ba ki son Uzair, kuma ni za'a zaga, miyasa a duk lokacin da za'a miki maganar wani Namiji sai kiyi kamar ki kashe kan ki? Namra mi yake damunki? Ke ce babba a gareni ke ya kamata ace kina nunawa ƙannenki dai-dai da rashinsa, haba Namra haba, haba, haba”

A take ta ji kukanta ya yanke, sai ta share hawayenta ta unƙura ta tashi, ta nufi ɗakinta.
Saman kujera ta zauna tana tunanin dalilin Uzair na faɗawa Abbah cewar yana son ya aure ta.

‘Miyasa yaje ya faɗa Abbah? Ko ma ya aure ba auren Allah da Annabi bane zai min, baya tunanin zumuncin mu da Anty Yasmin zai iya lalacewa? Ko dai wani abun ya ke nufi da ni ne?’

Tashi tayi ta nufi gurin gadonta tana cigaba da tunani

‘Tabbas idan har na ƙi yarda da auren shi ni za'a zaga, Abbah zai iya ɓatawa da ni, zan saka Umma cikin damuwa,

Wata ƙila yayi hakan ne dan na rufa masa asiri, ta yadda babu wanda zai san abunda yake aikatawa’

Saman gado ta zauna tana murmushin takaici

“Idan kasan wata, baka san wata ba Uzair, kaine zaka zanje maganar auren ka da kan ka, ko kuma na tona maka asiri Wallahi, ba zaka ci riba biyu a kai na ba”

Wayarta ta jayo ta shiga contact ɗinta ta nemo number Ya Uzair ta danna masa kira, ringing tayi har ta katse bai ɗauka ba, haka ta jera masa kira kusan tara amman be yi picking ba at the end sai mai ya kashe wayarsa.
Jin wayar a kashe ya matuƙar harzuƙa Namra sai kawai ta yanke shawarar kiran wayar Yasmin, dan tana tunanin ko saƙo ta tura masa ba zai karanta ba.

Yasmin na kwance jikin Mijin mijinta wayarta ta yi ƙara, sai da tayi kamar ba zata tashi sai kuma ta tashi a kasale ta nufi gun da wayar take.
Da far'ah tayi picking tana mata zolayar data saba mata a duk lokacin data kira ta

“Ke miyasa zaki kira ni yanzu, mijina baya son wayar dare fa”
Chapter 5 · 0% Book details