← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 173

Sashe 4

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Zo ki fice, amman ki rubuta ki aje duk kika kuskura fitar da wannan maganar sai na salwanta rayuwarki”

Daga haka ya fita ya bar mata kitchen ɗin.
Ita kam bata yarda ta fito ta nan ba, sai ta buɗe ƙofar baya ta kitchen ɗin ta fita gabanta na mugun faɗuwa, har ta shiga Motarta jikinta rawa yake, zuciyarta na raya mata karta ɓoyewa ƴar'uwarta kuma aminiyarta abunda mijinta keyi, gani take idan har tayi haka bata yi mata adalci ba.
    Tana fita daga gidan ta faka gefen ti-ti ta dannawa Yasmin kira, three miss call tayi mata amman bata ɗaga ba, ta san ba zai wuce tana cikin kotu ba, sai kawai ta yanke shawarar tura mata saƙo.

Ko da ta isa gida Anty Amarya bata nan, part ɗin kuma babu kowa, ƙannenta duk suna makaranta, hakan ya bata damar shiga ɗakinta ta baja kolin hajar tunaninta.

UZAIR POV.

Lokacin da Uzair ya ga Namra ta fita sai ya gargada ƴan iskan friends ɗinsa, ya gyara gidan  tas kamar komai bai faru ba. Ba ayi minti Arba'in ba, sai ga Yasmin ta dawo gidan, cikin sauri ta shigo parlor tana dube-dube.
   Uzair na zaune saman kujera yana kallonta, hankalinsa kwance kamar ba komai, sam be yarda ya nuna akwai wani abun a fuskarsa ba, tashi yayi ya tare ta, tare da rumgumeta yana kissing

“Lafiya wife?”

Ta sakar masa jikinta sosai

“Wallahi miss call ɗin Namra na gani da text ɗin ta, wai na yi sauri na zo gidana, shine duk hankalina ya tashi”

Dariya yayi sosai a zuciyarsa yana jinjina ƙarfin hali irin na Namra.

“Haba dai sai kace baki san Namra ba? Zata iya disgaki fa ai ba yau ta saba ba, karki tashi hankalinki”

Juyowa tayi sukayi kissing ɗin junansu sannan ta ce

“Ta katse min aiki na, ina fatar dai tayi maka kosan kazar?”

Hancinta ya laƙata

“Namra bata ma zo nan gidan ba, friends ɗina kuma har son kama hanyar Abuja daman ɗaurin aure suka zo”

Da haka ya shammace ta ya cigaba da kissing ɗinta.

NAMRA POV.

Duk yadda ta so ta labartawa Anty Amarya abunda ke cikin ranta na game da Uzair sai ta kasa, haka ta wuni tana tunanin abunda ya faru tsakaninsu da Asim, da kuma shawarar da Amira ta bata, a ɗayan ɓangaren kuma ƙwaƙwalwarta na ɗauke da hoton abunda taga Ya Uzair yayi.
   Har bayan Sallah Isha'i tana kiran wayar Asim amman ya ƙi ya ɗaga, ta tura masa massage no reply, abun duniya duk ya bi ya dame ta.

Shigowar Anty Amarya ne yasa ta tsaita natsuwarta, har tana ƙoƙarin gyara zamanta.

“Abbanki yace na faɗa miki baƙonki ba zai samu zuwa ba”

Anty Amarya ta faɗa yayinda take ƙoƙarin zaunawa saman gadon kusa da ita. Namra ta ɗan kalleta kaɗan

“Miyasa?”

“Nima ban sani ba, amman na naji a  waya yana cewa wai kin masa ƙarama, kuma yana jin nauyinki”

Namra ta ɗan yi murmushi ƙaɗan ta kwanta jikin Anty Amarya.

“Shima dai yasan ni ba sa'arsa bace”

Anty Amarya ta shafa kan ƴarta.

“Allah dai yayi miki zaɓin da yafi alheri, ya yaye miki damuwarki”

“Amin Mamana”

KALSOOM POV.

Around eight thirty Kalsoom ta fito ɗakinta, a lokacin Saleena har ta wuce makaranta. Ita ta haɗa musu breakfast bayan ta gama, ta zuba ma Dad da Momy nasu ta ɗauka ta nufi part ɗinsu.
Bayan ta gaishe su, ta aje musu abincin tana ƙoƙarin rasowa Momy tayi mata tuni da zuwa gidan ƙanwarta Zainab.

“Ban manta ba Momy, yanzu idan na shirya can zan fara zuwa na aje kayana sannan na wuce aiki”

“Hakan yayi Allah ya kawo miki naki mijin”

Sai da ta amsa sannan ta tashi ta fice. Kala biyar ta ɗauka a maimakon uku, dan tasan sai ta fi kwana uku a can, cikin ƙaramin akwati ta saka su, sannan ta shirya kanta ta fice.
Kamar yadda ta tsara sai da ta fara biyawa gidan ta aje kayanta sannan ta wuce gurin aiki. Biyu da rabi ta tashi daga aikin direct gidansu ƙawarta Salma ta wuce.

Ta taki sa'ah, tana shiga mijinta na fita. Sai da tayi Sallah Salma ta ɗebo mata abinci ta ƙoshi sannan ta ɗauko mata zance.

“Kalsoom wani gari ne nake son muje tare da Ruƙayyah ita zata kai mu, ance malamin yana aiki sosai dan mutane da dama suna dacewa”

Kalsoom ta sauke ajiyar zuciya

“Ni wallahi har na gaji da irin wannan shige-shigen, kullum ana abu kamar ba'ayi, wani gurin ace aljanu ne wani su kuma su ce sihiri ne, na rasa gane kan matsalar nan, Wani lokacin har ji nake kamar na kashe kai na”

Salma ta dafata

“Subhanallahi, haba Kalsoom ki daina wannan maganar mana, Allah ya baki aikin da zaki iya taimakon kanki, Allah ya rufa miki asiri aure ne kawai Allah bai kawo miki ba, shine kuma kike ƙoƙarin butulce masa, kina wannan maganar sai kace ba musulma ba?”

Kalsoom ta lumshe ido ta buɗe ta kalli Salma cike da damuwa ta ce

“Salma duk abunda Allah ya ban da wanda zai ban bai kai kamar aure ba, aure shine cikar mutuncin ko wace ƴa mace, ni fa ba dotse bace Salma ina da sha'awa ina tsoron abunda zai kai ni ga halaka”

Salma ta riƙata tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali.

“Roƙon Allah baya faɗuwa ƙasa Kalsoom, komai zai zo ya wuce kamar ba'ayi ba, kuma ba asan inda rabo take ba wata ƙila mu dace”

“Ni dai ba zan sake zuwa ko ina ba, na haƙura ballantana kinsan Ruƙayya ba a sirri da ita, kuma ko munje ba wani dacewa za muyi ba, tun da babu wanda zai iya matso maka da nesa kusa, babu wanda zai iya goge abunda Allah ya rubuta maka, sai dai kawai su ci kuɗinka, na fawwalawa Allah komai daman da shi na dogara”

Duk yadda Salma ta so ta lallaɓa Kalsoom su je, sai taƙi dan ita yanzu ta riga ta sadaƙar. Sai da Yamma Kalsoom ta bar gidan Salma.

__________________________________

How about dis journey?

#threefamily
# Vote
#Comment
#TeamNamra
#TeamKalsoom
#TeamHilal
#Candy
#Blog

Always check my website for more.

BEST REGARDS💖
Khadeeja Candy 🌺

www.khadeejacandy.com.ng
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

*PAGE - 3*

DOCTOR HILAL POV.

Bayan ya gama abunda yake ya shiga ya yi wanka, sannan ya fito falo ya yayi breakfast, sai kuma ya sake dawowa ya tashi Rafiq ya shiya sannan ya fice.

Kamar yadda ya saba gidan Hajiya ya nufa dan kai Rafiq ɗin, kasancewar Hajiya na da ƴan aiki da yawa masu kula da shi, wani lokacin ya kan aje shi a falo yace a shiga dashi gudun kwankwamin Hajiya, ko kuma ya aje mata shi ya yayi saurin barin gidan.
Sai dai yau bai yi sa'ah dan yana shiga ya ci karo da ita cikin falon tana karyawa, sun-sun-sun yayi ya gaisheta.

“Hajiya Barka da tashi”

“Barka dai mijin Hajiya, har ta tafi aikin ko? Bari dai kaji na faɗa maka na kusa barin rainon ɗan ku”

Maganar tayi masa zafi, sai dai babu yadda ya iya tun da mahaifiyarsa ce, kuma idan sabo ya saba da irin waɗannan kalaman daga bakin Hajiya da Alhaji, Murmushi yayi ya shafa kan sa.

“Hajiya haƙuri dai za'ayi, kisan ƴan rainon nan ba tsoron Allah suke ba”

“Kai ai kana tsoron Allah, tun da har kakr barin Matarka tana shiga cikin maza tana gogaiya, ace mace idan ta fita takwas na safe ba zata dawo ba sai cikin dare? Bata da lokacin mijinta balle na ƴaƴanta”

“Hajiya kin san aikin banki ne, kuma ita ce Manager ta banki dole ne ta riƙa bada lokacin can”

“Toh ta bar aiki mana dole ne? Amman ace mace ta bar Yaro ƙarami mai shan nono dan kawai ta je aiki”

Murmushi kawai yayi ya tashi yana shafa kai yana faɗin

“Bari na wuce”

Har ya kai ƙofa bai ji tace masa komai ba, sai ya juyo yana murmushi yace

“Hajiya ni fa bana son fushin nan da kike da ni”

Wani kallo ta watsa masa

“Yaushe na ce ina fushi da kai?”

“Toh ai ban ji kince Allah ya tsare ba”

“Ko ban ce ba ai Allah tsare ka zai yi”

Wata irin dariya yayi, ya dawo yayi mata side hug

“Allah ya bar mana ke Hajiya, i love you”

Dariya tayi tana faɗin

“Jeka ka aikinka kamin Alhaji ya fito, kasan nashi faɗan babba ne”

Ficewa yayi yana dariya, zuciyarsa cike da shauƙin son mahaifiyarsa.
Uku da ƴan mintuna ya tashi aiki, sai da ya biya ya ɗauko Yaransa daga makaranta sannan ya dawo gida, sai da suka yi sallah sannan ya zuba musu abinci suka ci, wani lokacin lokacin ta kan tashi da wuri ta dafa musu abinci, wani lokacin kuma sai dai yayi musu takeaway. Bayan sun gama ci suka shirya suka tafi Islamiya.

Haka Doctor Hilal yake fama da irin wannan kaɗaicin kamar marar mata, gashi shi ba mutun ba ne mai son yawa fita, indai ba gurin aiki ba kullum zaka tararda shi a gida.
Matarsa kuma ota da gidan sai dare, babu yadda ya iya tunda babanta ya tsaya kai da fata akan lallai sai tayi aikin banki kasancewarta babbar ƴarsa, tana da ƙanne maza amman ya tsaya akanta dan kawai yaga ya kashe mata aure, tun asali ba Doctor Hilal ya so ta aura ba, shiyasa baya ƙaunar surikin nasa ko kaɗan, shi kuma baya jin zai iya rabuwa da ita saboda yana son matarsa ita kuma tana sonsa.

Ulfah da Ezzah na dawowa daga makarantar islamiya, suka ɗauko Homework ɗin su Doctor Hilal ya yi musu.
Gimbiyar tasa kan bata dawo gida ba sai bayan Isha'i. Da sallama ta shigo amman ko inda take bai kalla ba balle har ya amsa mata sallamar, sai ta kwanto jikinta tana masa shagwaɓa

“Yanzu zan yi sallah ka kasa amsa min haba Dear”

“Yaran ki har sun gaji sun yi bachi, yau kwatakwata Rafiq bai sha nono ba, idan ni ina iya haƙuri na su kuma ba? Rashin ba su lokacin ki da kike shi zai sa ki kasa karantar wane hali ƴaranki suke ciki”
Chapter 4 · 0% Book details