← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 173

Sashe 51

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya amsa fuska a haɗe kamar ance iyayen Namra suna gurin. Lokacin da Namra ta fita, sai tayi can gefe nesa da inda masu jinya suke shinfiɗa dan shan iska, sannan ta riƙe wayar tana kuka. Sai ga kiran Anty Amarya ya shigo, cikin sauri ta ɗauka ta kara a kunne, tana cigaba da kuka.

“Lafiya Namra? Miyasa ki?”

“Ma....Ma...”

Yau kam da Mama ta kira Anty Amarya, sunan da be taɓa zuwa a bakinta ba tun tashinta, saboda sabo da yadda kowa ke kiranta da Anty Amarya.

Anty Amarya jin kukan ƴarta take har cikin ranta, bata san abunda yasa Namra kuka ba, sai kawai ita ta fashe da kuka tana dafe zuciyarta.

“Namra faɗa min minene? Miye damuwarki ƴata faɗa min? Indai kuɗi ne na turo miki 300,000k a account tun jiya, ko ba za su isa ba na ƙaro miki?”

“Mama ina son ganin ki, i miss you”

“Okay ki faɗa ma mijin ki idan ya bar ki zan turo direba ya ɗauko ki kin ji? Akwai wani abun ne? Jikinsa dai ƙalau ko?”

“Ya..ji sauƙi”

Ta amsa da in'innar kuka.

“Namra ki kwantar da hankalin ki kinji? Komai zai wuce? Rayuwa bata tabbatuwa haka nan dole ne za a jarraba bawa”

“To Anty na gode”

“Ki sayi waya ki saka layin ki, ki kira ni kin ji”

“Tau”

Ta kashe wayar, sai ta duƙa a gurin ta riƙa rusa kuka kamar wacca akayi ma mutuwa. Ko da ta tashi har hijabinta ya ɓace da hawaye, sai ta cire ɗankwalinta ta ɗora saman hijabinta, ta koma ward ɗin.

HILAL POV.

Tun bayan fitar Rashida daya gama shirya ma yaransa abun kari, sai ya ɗauko tsohon result ɗin ya ɗora a saman gadon Rashida tare da takardar rubutun da yayi mata. Sannan ya koma yayi wanka ya kwashi yaran suka wuni gidan Hajiyarsa, tayi farinciki da murna sosai, sai da suka yi sallah isha'i sannan yace ma Kalsoom ta tashi tayi shirin zuwa gida. Ita kuma sai ta riƙa kiran yaran da zimmar su zo suje gida sai ya riƙe mata hannu ganin babu kowa falon.

“Ba da su zamu je ba”

“Amman....”

“Don't talk gobe da yamma direban hajiya zai mai da su gida, suna jindaɗin zaman nan let them enjoy themselves”

“Amman suna zuwa islamiya da safe fa”

“Just for one day, please a daga musu kafa mana, yau bana son jin muryar yaran nan a gida”

“Saboda me? Wai Doc miyake damun ka?”

Ya kwanto da kansa saman jikinta, kamar wani ƙaramin yaro.

“Ke kike damu na? Son ki ne yake wahalar da ni”

“Ba so na bane wannan, wata damuwar ce ta daban, dan Allah ka faɗa min abunda yake damun ka”

“Tashi muje kar muyi dare”

Ya tashi da zimmar kawar da maganar dan baya son faɗa mata komai.
Shi ya fara zuwa yayi ma Hajiya sallama sannan ita ma tayi masa, suka kama hanya, tun da suka hau titi bata ce masa komai ba in ban da ido ta da sakar masa tana kallon yanayinsa, a fuskarsa take karantar damuwarsa, zuciyarta na nasalta mata lallai akwai abunda yake damun Mijinta.

Parking taga yayi a gefen ti-ti, sai ya juyo ya kalleta yana murmushi, kamin ya kai hannu ya jaka izuwa ƙirjinsa, ya rumgumeta. Ya ɗauki dogon lokaci a haka sannan ya tashi motar suka ƙarasa.
Jikinsa ne ya bashi ba lafiya ba, tun daga lokacin da yayi parking ɗin, sai kuma ya soma jin rashin dacewar abunda yayi ma Rashida, ko ba komai uwar ƴaƴansa ce, sai dai babu yadda ya iya tun da hiv indan be zama aids ba, akan iya kamuwa dashi ta hanyoyi da dama, tun da a yanzu  shi dai ya samu tabbacin shi da Kalsoom da ƴaƴansa basa ɗauke da cutar.

Sai dai ya san Rashida ba zata iya rayuwa babu shi ba, yasan yadda take ƙaunarsa, amman zai gogeta a ransa matuƙar result ɗin ƙarshe ya fito, kuma ya tabbatar da a sex ta samu cutar.
  Sai da ya raka Rashida har ɗakinta, sannan ta fito ya shiga ɗakin Rashida. Yanayin yadda ya ganta ya tsorata sosai, tana kwance cikin jini babu numfashi. Be san lokacin daya ɗauke ta ya fito da ita da gudu ya nufi mota.

AMIRA POV.

Daga rarrashin da yake mata, sai wasan ya sauya salo, ya fara bin jikinta yana wasa da dukan ɓangarorin jikinta, har yayi nasarar jan hankalinta, ya biya buƙatarsa.

Sannan ya nufi ɗakinsa ya kwanta, ita kuma ta nufi wani ɗakin, tayi wanka ta shirya cikin wasu tufafin ta fito kamar ba ita ba.
  A falon ta dawo, ta buɗe freezer ta ɗauki lemu tasha tana ƙoƙarin kawar da damuwar dake cikin ranta dan samawa kanta nishad.
Ta zauna, saman kujera tana ƙoƙarin canja MBC bollywood, zuwa AIT, program ne suke akan yadda za'a magance matsalar tsaron data addabi Nageria, har zata canja sai channel sai kuma ta tsaya tana kallon yadda Abdool yake watsa turanci yana koro bayani kamar wani ba'amerike, hakan ya ɗauki hankalinta har ta kula da kyausa, da kuma muƙaminsa, kamin su sake naɗo sunansa.

“Major General Abdullah Ahmad Mai-Doki, wow nice guy, nice work, nice name, everything perfect”

Ta furta a hankali tana mai maida hankali ga kallonsa sosai. Dif nefa suka ɗauke wuta, wani irin buga ƙafa tayi, ta sosa hancinta.

“Oh they Fuck up”

Zata tashi sai ga mutumen ɗazu ya dawo, yana bata rahoton Doc Sabo. Dafe kai tayi tana tashi tsaye.

“Eyyyyyy karka cika ni da wani magana, ga wayana nan ka duba number ta ansa banker ka tura mata text ɗin abunda zata biya, sannan kace Samuol ya tada mana injin”

Tana kaiwa nan ta nufi ɗakin da Guy son ya shiga ɗazu.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

                               _Write by_
                       *Khadeeja Candy*

*PAGE - 38*

NOT EDITED ⚠

Ko da ta shigo ɗakin ta same shi tare da Mama suna magana, bata iya zago zancen da suke amman jikinta yana bata kamar maganar ta ne suke. Cikin Ladabi ta miƙawa Mama wayar.

“Kun gama maganar ko?”

“Eh mun gama”

“Tau madallah”

Yanayin yadda ta tayi maganar ya tabbatar ma da Namra da biyu tace haka ɗin, sai ta tashi ta fice daga ɗakin ta basu guri.
  Da kallo Namra ta bita har ta fita sannan ta zauna kusa da Asim

“Anty ta aiko min da 300,000k, zan bawa Dillaiya su in yaso sai ta bini hansin ɗin”

Asim yayi shiru be ce komai ba, sai ma yayi kamar ba dashi take magana ba, baya son nuna mata be jidaɗi ba, sai dai a can kasa zuciyarsa rashin jindaɗin ne, ganin ba shi Anty ta aikowa kuɗin ba, tun farkon fara rashin lafiyarsa har zuwa yanzu babu wani abu daya fito daga hannunsu izuwa gare shi da sunan yayi lalura da su.

Hannunshi ya kai ya riƙa nata hannun.

“Namra ya zaki ji idan aka ce yau Mama bata son ki kuma kina auren ɗan ta?”

Tayi shiru tana nazarin inda maganarsa ta dosa, tambayace yayi mata mai ma'ana ɗaya, dan kai tsaye ta san da ita yake.
Sai kawai tayi murmushi tace

“Be zai dame ni ba, saboda Kai na aura ba Mama ba, sannan ban aure ka ba dan wani abu naka sai dan son da nake maka, to dan me wani abun zai rufe min ido har na zarge ka?”

“Uhmm”

Ya janye hannunsa, yana kallon ƙofar ɗakin kamar mai jiran shigowar wani.
Can kuma ya kalleta

“Ina ganin idan an gama min allurar nan, ya kamata ace mu koma gida saboda asibitin nan in ban da kashin kuɗi babu abunda suke ja mana”

“Gidan ma sai an gyara za'a zauna, saboda gate ɗin ya ɓangale gefe ɗaya, kuma BQ nan tsoro take bani”

“A haka dai zamu daure mu zauna”

“Da ace da hali da an gyara gate ɗin, in yaso BQ ɗin sai a share a wanke”

“Sai ki gyara da kuɗin da Anty ta aiko ai zasu isa”

“Amman ba kaji nace bashi zan biya ba? Sai dai na siyar da sarƙa na gold a gyara”

Ya kalleta a kai-kaice

“Ina kika samu sarƙar gold? Ba kin ce komai ya ƙone ba?”

“A hannu Mardiya na gani ɗazu har da wayana ma, ita ce ta satar min”

“Mardiya? Ya akayi kika gani?”

“A ƙasan a kwatinta, saboda jiya na saka kuɗin daka bani a cikin kayanta, gurin nema ne sai na wayar har da sarƙar ma, da wasu ƴan kunne da Hajiya ta taɓa raba mana lokacin data dawo makka”

“Amman ya akayi Mardiya ta shiga har ciki ta ɗaukar miki sarƙa har da waya ma?”

“Ban san yadda ta ɗauka ba wallahi kawai dai na kamata da su ne a yau, kuma nayi mata masifa ita da Mamanta”

“Aikowa baki kyauta ba, yarinyar duk hidimar da ake ta zuwa asibiti da ita ake yinta, anya ma ita ta ɗauka? Dan gaskiya yarinyar nan tana da natsuwa da tarbiya”

“To idan ba ita ta ɗauka ba ya za'ayi na gani a akwatin ta? Kuma fa  taji lokacin da ina nema”

“Yanzu idan kin siyar me zaki yi da kuɗin? Namra wai kin faɗawa Abbah mun yi wuta kuwa?”

Ƙasa tayi da kanta.

“Ban faɗa ba, babu wanda ya sani”

“Nima bana son kowa ya sani dan muna da maƙiya za su mana dariya, amman dai su ai kamata ace sun sani, rayuwa tayi haka? Namra ki duba halin da nake ciki, babu wani taimako sai na Allah, yanzu idan kuɗin nan da muka ranto suka ƙare kina tunanin akwai inda za mu sake dubawa? Ban san miyasa rayuwa ta zo mana a haka ba, kana neman ka ɗaga kayi gaba, amman sai baya kake  abubuwa suna ƙaruwa”

Ya ƙarasa maganar idonsa cike da hawaye.

“Inshallah zan faɗa mata idan na je, tace na tambaye ka idan ka bar ni sai naje”

“Gurin me?”

“Tace tana son gani na ne”

Har zai ce wani abu, sai kuma yayi shiru yana nazari, idan har ya barta yaje be san abunda zata samo ba, musamman idan ta faɗa musu halin da suke ciki.

“Amman ba zaki daɗe ba ko? Kije amman kwana biyu za kiyi ki dawo”

Hannayenta tasa ta rumgume shi, tana murmushin jindaɗi.
Chapter 51 · 0% Book details