← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 173

Sashe 12

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Abbah akai ta asibiti, duba fa bata motsi”

Juyawa Abbah ya yi ya nufi part ɗinsa rai a ɓace. Hajiya Barau ta ce

“Daga ta zan ɗauko mota akai ta, ai kisan halin Abban ku sai dai ta mutu a nan”

Hajiya Barau ce taja mota, da taimakon Hindatu da Mama Zainab suka sa Namra a mota, suka nufi asibitin dake kusa da su.
Suka bar Anty Amarya da Maryam suna aikin kuka, Hajiya Raliya na bata haƙuri, sai kawai Aisha ta yanke jiki ta faɗa iskokanta suka taso.

*** *** ***

Suna shiga Uduth, aka wuce da ita emergency, da sauri Nurses suka karɓe ta, aka ɗorata akan gado, suka shiga da ita wani ɗaki, taimakon gaggawa suka shiga bata kamin Likitoci su iso.

Ba a fi minti biyar ba, Doctor Hilal ya shigo cikin manyan kaya, hannayensa zube a aljihu, tare da wani likita, hankalin kwance ya ƙarasa inda take kamar ba marar lafiya ze duba ba.
Duk natsuwa Nurses ɗin suka yi suka ja da baya suka bashi guri. Hannu ya kai ya taɓa gefen wuyanta, yana kallon agogonsa hannunsa, sannan ya kalli drip ɗin da aka ɗora mata.

“Ku cire mata drip ɗin nan sai numfashinta ya dawo, ku kira Doctor Adamu ko wani likitan, da wannan ba aikin Likita ɗaya ba ne”

Yana kaiwa nan ya juya, sai Likitan da suka shigo tare ya yi saurin cewa.

“I'm sorry Doctor, Doctor Adamu is not around, that's why i call you”

Juyowa ya yi ya kallesa

“Wannan ba aiki na ba ne, and you know it, tiyata kawai na zo yi garin nan, ba kuma zan ɓata lokaci na akan abunda ba aiki na ba, jirgi zan bi na koma kaduna a can ma ina da aiki”

Yana kai wa nan ya fice. Da sauri wasu Nurses suka fita dan kiran wani likitan, shi kuma wannan likitan ya shiga bata taimako.

KALSOOM POV.

Tana tashi daga aiki, ta wuce gidan ƙawarta Salam dan labarta mata halin da take ciki.
Bayan Salma ta kawo mata abinci ta ci tayi sallah, sai take bata labarin abunda ya faru.
A maimakon ta ga ɓacin rai a fuskar Salma na taya ta baƙinciki irin mijin da zata aura, sai ta ga Salma na murmushi da yima Allah godiya

“Alhamdullah Allah mun gode maka, haba Kalsoom ko dan daɗewar nan da kika yi ba aure, be isa yasa kiyi haƙuri ki auri wannan ɗan'uwan naki a haka ba? Kina ji fa na faɗin da babbar budurwa ƙara ƙaramar bazawara, ƙannenki biyu a ɗaki ke kina nan, haba Kalsoom ki yi tunani mana”

“Ba auren ne bana so ba Salma, halin Sadiq ɗin ne na ke tsoro, ina gudun abunda ze je ya dawo, tun kamin tafi ake shawara ba sai an dawo ba, Wallahi na tsani mutum ne neman mata”

“Dan Allah ki daina faɗar wannan maganar, kar wani ya jiki ya san sirrinki, nema mata yanzu ya zamo ruwan dare, da wahala ki samu namiji me aure ko marar aure da baya neman mata, ko wace mace da kika gani a gidan mijinta tana da nata matsalar, no married friend of yours will ever tell you her marital problems,no woman will tell you her husband's fault amma karya take tace he is perfect,because no one is, dan Allah kiyi auren ki Kalsoom ke kaɗai ce a cikin kawayen mu kika rage baki yi aure ba”

Wani kallo Kalsoom ta yi mata, tana mamakin yadda ta kasa fahimtar ta.

“I have never blame myself for being single, i know I'm pretty, i'm well behaved, i'm Godly,and yet still single. Salma thats just how nature works, that is how Allah has designed it.
Idan duk a cikin ƙawaye na ni kaɗaice ban yi aure ba so what? Ni nayi kai na? Allah who created me differently and created them differently, surely made you destinies different. Komai lokaci ne Salma i don't want to rush into marriage with just any guy just because i want to be married, babu mai son ya je ya yi aure ya fito”

Salma ta dafa ta

“Haba Kalsoom zaki yi auren ne da niyar ki fito? Your idea is inside you Kalsoom, kiyi tunani me kyau, amman aure nan shi ya fi, kawai ki bawa Allah zaɓi”

Hawayen da suka zubo mata ta share ta ɗauki jakarta ta rataya.

“Na gode Salma zan yi tunani akai”

Har bakin gate Salma ta rakota, suka yi sallama sannan ta koma. Tafiya Kalsoom take tana tunani, sai taji ana mata horn, juyowar da zata yi sai taga wata hadaɗɗiyar mota mai kyau, tana binta a baya. sayawa tayi sai mai motar ya zo dai-dai ita ya tsaya, yana sauke gilashin motar.
Dattijo ne mai yalwatacciyar fuska da cikar kamala ta mai kuɗi.

“Shigo mana”

Ya faɗa yana buɗe mata front seat. Bata kawo komai a ranta ba, sai kawai ta buɗe motar ta shiga. Driving yake kaɗan-kaɗan yana gaisawa da ita.

“Ya kike ya gida?”

“Lafiya ƙalau”

“Ina zaki je ne haka?”

“Gida”

“Kuma kike tafiya a rana haka, kar fa rana ta taɓa min ke”

Ɗan murmushi tayi ta gyara yafin gyalenta.
Ba ko kunya ya kai hannu ya yaye mata gyalen

“Haba ke kuwa ya kiƙe ƙoƙarin rufe min kyau nan naki...”

Be karasa ba ta buge masa hannu tana masa wani kallo

“Sauke ni Malam, ni ba irin waɗannan matan bane”

“Haba kyakkawa daga magan...”

“Ka sauke ni nace!”

Ta faɗa a tsawace. Ba shiri ya ya faka motar ta buɗe ta fita tana tsaki.

“Ku ba za ku ce kuna son mace da aure ba sai lalata, duk Namijin da ka haɗu da shi abunda kawai yake ƙoƙari ya kai ga jikinka, ƴan iska kawai marar mutunci”

Haka tayi ta zaginsa, shi dai be bi ta kanta ba ya ƙaɗa motarsa yayi gaba.

_______________________________

Share it please, and drop your opinion. 🙌

Best regards 💖
Khadeeja Candy 🌺
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa10.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

                            _Wattpad @_
                  *KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

*PAGE - 10*

UZAIR POV.

A guesthouse ɗin suka koma. Bayan Najeeb ya fito motarsa sai Uzair ya fito, suka nufi bayan motacin da suke gurin.
Ta inda suka san ba za'a gansu ba suka tsaya. Sai Najeeb ya kalle Uzair ya ce

“Uzair zaka janye maganar auren nan gobe gobe ba sai jibi ba, ka ce ka fahimcin tana da wanda take so, dan haka kai ka haƙura.
Sai idan ka yanje maganar ne sannan za mu je da kai gurin Malam gobe da nisa, dan ba za a yi mata magani kana auren ta ba”

“Amman idan mahaifinta yaƙi yarda fa?”

Najeeb ya yi masa wani kallo

“Ta ya zai ƙi yarda ? Shi ze aure ta ne? Ya kake abu Uzair kamar ba ɗan duniya ba? Sai wani ɓoye-ɓoye kake ai gashi nan ka jawa kan ka”

“Babu babbar matsala kamar ganin da tayi min, yanzu idan ta faɗa dame zan kare kaina”

“Sai kace ai ta saba maka ƙazafi, kai ma ai kasan kayi kuskure na bari ta ganka, kamata ya yi kasa a ɗauko maka ita”

Uzair ya yi shiru yana nazari, tashin hankali bayyane a fuskarsa. Kiran Amira tana ta shigo masa a waya amman yaƙi ɗagawa.
Ƙarfe ɗaya da rabi na dare kiran Baba Audu ya shigo wayar Najeeb. Cikin sauri ya ɗauka yasa hands-free.

“Hello Baba Audu ya ake ciki?”

Daga ɗayan ɓangaren Baba Audu ya amsa

“Na gama komai, na fito ina babban ti-ti, dai-dai inda kace na tsaya”

“Ina fatar anyi nasara?”

“Komai ya tafi yadda kake so”

“Toh ka jira ni, zan zo nan gurin na ɗauke ka”

Daga haka ya kashe wayar, ya kalli Uzair.

“Yanzu ka wuce gida kawai, ni zanje na ɗauko shi, idan ka taso aiki gobe mu haɗu a guesthouse ɗin Jafar, kuma ka tabbatar da ka sallami waɗannan mutane da suka ɗauko ta in case of”

Be jira abunda Uzair zai ce ba, ya nufi motarsa. Sai bayan ya fice sannan Uzair ya nufi cikin guesthouse. Be daɗe ba ya fito ya buɗe motarsa ya shiga, ya ɗauki hanyar da zata kai shi gidansa.

Tun kamin yana yin parking ya kashe wayarsa, sannan ya fito ya nufi hanyar falon.
Yasmin na zaune falo tana duba wasu takardu da system Uzair ya shigo da sallama.
Sai dai bata amsa masa sallamarba ma balle har ta ɗaga kai ta kalle. Kamar hakan be dame shi ba, sai kawai yazo ya zauna kusa da ita ya rufe system ɗin dake gabanta.
Yana ganin ta unƙurin zata tashi, sai yayi saurin riƙe ta ya zaunar, ya danneta da dukan ƙirjinsa ya ɗora mata nauyinsa, yana ƙoƙarin saka mata hannu ciki riga.

“Haba Bloody miyasa kike min haka ne? Dan kawai zan ƙara aure sai na zama maƙiyinki? Ai badan bana son ki zan ƙaro wata ba, sai dan rufin asirin mu”

A kaɗan-ƙaɗan ya raɗa mata haka, cikin wani irin siga na son tada mata hankali, sai numfashi yake sakar mata a kunne.
Ƙoƙarin ƙwatar kanta take amman ta kasa, ta ƙara haɗe rai sosai.

“Sake ni mana, Uzair bana son haka”

“Zan sake ki, amman sai kin faɗa min idan kin daina fushi da ni, idan kuma baki daina ba toh zan janye maganar auren”

“Maganar auren ka be dame ni ba, babu ruwana da lamarin auren ku, dan haka ka daina saka ni a ciki”

“Babu ruwanki da lamarin aure na kuma kike fushi da ni?”

“Amman dan zaka yi aure sai ka rasa wadda zaka aura sai Aminiyata, kuma ƴar'uwa ta”

“Nima ai ƴar'uwata ce, kuma naga kamar zaku fi zaman lafiya”

Wani dogon tsaki taja, tasa guiwar hannunta ta buge masa ciki. Ba shiri ya sake ta ya dafe cikin.

“Yasmin kashe ni zaki yi?”

Tsaki ta sake masa ta wuce ɗakinta, tana cika da batsewa. Da kallo Uzair ya bita yana murmushi, sai da ta shige ɗakinta sannan ya tashi ya nufi ɗakinsa.

Tun da asubar fari Hajiya Barau ta bugo masa waya ta faɗa masa abunda ya faru. Yi yayi kamar be sam komai ba, duk ya firgice yana nuna damuwa, sai tambayoyi yake zubo mata, yana nuna mata tashin hankalinsa kamar ance masa gata nan gabansa.
Chapter 12 · 0% Book details