Sashe 2
Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anty Amarya ta amsa da “Amin” Tana sauke ajiyar zuciya, sam bata jindaɗin yadda Abbah yake yi ma ƴarta sai dai babu yadda zata yi, ko magana ta yi cewa yake ita ke ɗaure mata gindi tana yadda take so.
Cikin sauri Namra ta taso, ta baro falon zuciyarta cike da zulumi, tana tsaron abunda zai je ya dawo, ta rasa ƙwaƙwaran dalilin da ya saka Mahaifinta ba ya son tarayyarta da Asim.
Har ta shigo ɗakinta kalmar Alhaji Madu ce take mata yawo a kunne, saman gado ta kwanta hawaye na bin fuskarta, sai ta kai hannu ta janyo wayarta, gallery ta shiga ta kamo hoton Asim tana kallo.
“Miyasa Ƙaddarata zata min haka? kin san ba zaki barni na yi soyayyah da shi cikin kwanciyar hankali ba kuma kika haɗa mu? kinsan ba zan auresa kuma kika sa na sansa, Allah kayi min mafita karka ka bar ni da kaina”
Rumgume wayarta ta yi sosai tana kuka da tuna kalaman daya faɗa mata yau a makaranta.
‘Ina son ki sosai Namra duk da jikina yana bani lallai ba zaki aure ni, saboda ni da ke ba ɗaya ba Namra, ga shi mahaifinki baya son na, Mahaifiyata tana yawan faɗa min wai zaki ɓata min lokaci ne kawai ba zaki aure ni ba, Namra ina gudun ranar da zan wayi gari kin zama matar wani magauta suyi min dariya...’
Kuka take sosai har da karkarwa, tana matsar idonta da buga ƙafafunta.
**********
Manjo Usman Zamau tsohon soja ne, mai mata biyu Hajiya Barau wanda ake kira da Mama da kuma Hajiya Larai wanda ake kira da Anty Amarya. Gidan Alhaji Usman babban gida ne mai ɗauke da part uku, part ɗin uwargidan sa da kuma na Amaryarsa sai nasa.
Uwargidansa na da ƴaƴa tara hudu mata biyar maza kuma dukansu sun yi aure, wasu suna tare da ita wasu kuma aure ya kai su nesa, a yanzu bata da ɗa ko ɗaya a gidan sai jikoki da ƴaƴan ƴan'uwa.
Anty Amarya ce aka auro daga baya, ita ce mai yara huɗu dukansu mata, Namra ce babba sai Maryam dake binta da kuma Hindatu da Aisha. cikakkancen sunan Namra shine Khadija mahaifiyarta ta kan mata Alkunya da Namra ne kasancewarta ita ta fari gareta. Namra na 100l a jami'ah ta haɗu da Asin, suka ƙula soyayyar da babu wanda ya sani har suka kai 300l, sai a yanzu ne abun ya zame musu matsala kasancewar Asim ba ɗan kowa bane face talaka mai neman abunda zai sa a bakinsa.
Ita kuma ƴar masu arziki ce musamman yanzu da Mahaifinta yake takarar Senator, daman can mutun ne mai abun hannunsa dan yana da kamfanoni da dama ciki da wajen ƙasar nan.
A duk familynsu da shi suke tinƙaho dan Allah ya yi masa rufin asiri ta ko ina.
Gashi shi ƙaɗai mahaifiyarsa ta haifa a duniya, a duk familynsu ya fi shaƙuwa da Mahaifiyar Yasmin da Kuma Mahaifiyar Uzair kasancewar kakanninsu guda, kuma yana ganinsu mata, yana tausayinsu sosai.
WANNAN KENAN
*********
SECOND FAMILY...
Tun da ta dawo daga aiki take cikin damuwa, abun duniya ya fara isarta komai ya taru ya yi mata katutu a rai, kullum ta fita ta dawo sai anyi da ita a unguwa, ƙawayenta su zolayeta familynsu ayi ta tambaya, kamar ita ta ɗorawa kanta rashin aure.
Kallon kanta take ta madubi tana hawaye, ta ko'ina Allah ya yi mata sura, mace ce abunda ake cewa mace, amman babu mai neman aurenta sai mutanen banza, duk acikin manemanta babu na ƙwarai da zata ware da sunan wanda zata aura, duk wanda ta yi ma maganar aure ba zai sake dawowa ba, sai dai su nuna suna son jikinta.
Sa'aninta duk sun yi aure, sun barta sai kace wanda ta zagi maza, tun tana sa ran idan ta gama karatu ta samu wanda zata aura yanzu ga shi har ta gama ta samu aiki amman ba shiru, ada abun ba ya damun iyayenta amman yanzu ya zame tunaninsu, suna addu'ah amman kamar basa yi, sun aurar da ƙannenta biyu mata ita shiru, babu mashinsshini balle malashi.
Faɗi tashi na neman magani babu irin wanda bata yi ba ita da iyayenta, amman ba wani labari. Yanzu kan har ta fara fidda rai daga samun mijin aure.
Kallon kanta take sosai da sosai a gaban madubi tana mamakin yadda take ƙokarin kare kanta daga zina da alfasha, tana ƙokarin sallah dare da sadaka, amman ta kasa samun mijin da zai aureta.
Hawaye ne suka zubo mata tana tuna irin yawan ƙawayenta, amman babu ko ɗaya duk sun yi aure sun barta.
Ƙarar da wayarta ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, sai ta kalli Screen ɗin wayar Salma ce rubuce a fuskar wayar, cikin sauri ta share hawayenta ta ɗauki wayar ta kara a kunne.
“Hello Salma”
“Na'am Kalsoom ya kike?”
“Lafiya ƙalau, ya Ahmad?”
“Lafiyarsa ƙalau, idan kina da time gobe ki shigo da wuri zamuje wani guri”
Da toh kawai ta amsa mata ta aje wayar, ta san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ko bata faɗa ba ta san ba zai wuce ta kai ta gurin wani Malamin ba, dan duk cikin ƙawayenta ita ce ta fi kowa damuwa da rashin aurenta, ita ce take ta faɗi tashi akan taga ta yi aure.
Kiran da ta ji ana mata downstairs ne yasa ta motsa ta tashi ta nufi ƙofar fita. Karo suka yi da Momy sai ta ja baya da sauri tana faɗin
“Kirana kike yi?”
“Eh yanzu mijin Zainab ya kira wai bata da lafiya tun shekaranjiya”
“Subhannallah miye same ta?”
“Wai maleria ce, amman dai na san ba zai wuce ciki ba, shine nace ki shirya gobe kije can ki yi mata ko da kwana uku ne idan ta ɗan sarara sai ki dawo”
“Haba Momy ni kuma? miyasa Saleena ba zata je ba ni fa yayarta ce kuma ace na koma can na zauna”
“Toh miye a ciki? ai ansan lalura ce ta kai ki, Saleena Exam za su fara gobe kinga ba zai yiyu ta je can ba, amman ke tunda aiki ne ai idan kin dawo sai ki ɗan taya ta aikin gidan da dafa musu abinci”
“Amman Momy ai yana da ƙanne mata kuma za a iya ɗauka mata ƴar aiki”
“Ya san da ƙannensa amman ya zo nan ya faɗa mana, idan mutum yana mutunta ya kamata kai ma ka mutun tasa, kwana uku kawai zaki yi ki dawo kin ji?”
Ta ɗaga mata kai alamar toh, zuciyarta cike da damuwa.
“Allah ya yi miki albarka”
“Amin”
Daga haka Momy ta juya ta sauka ta barta a gurin tsaye. Jinginawa Kalsoom ta yi jikin ƙofar tana addu'ah
“Ya Allah idan mijina yana nesa da ni Allah ka kusan to dashi a gare ni, idan yana kusa da ni Allah ka haɗa mu”
Juyawa tayi ta shiga ɗakinta tana cika ma bakinta iska.
***********
THERD FAMILY....
A-hankali ya ke shafa lallausar fatar jikinta da hannunsa, idonshi a lumshe yana hura mata iska a kunne, daga bisani ya fara tsosar kunnen nata hannunsa ɗaya yana saman ƙirjinta. A take ta lumshe ido tana maida numfashi, tana ƙoƙarin mayar masa da martani, hannayenta tasa cikin gashin kansa kamin ta juyo ta soma masa kiss a ƙirji, ɗayan hannunta na cikin cibiyarsa, da sauri ya kwantar da ita ya zare tawul ɗin jikinta ya soma murza fatarta bakinsa cikin nata suna maida numfashi. Ringing ɗin wayarta ne yasa ta walƙato shi cikin dabara ta dawo saman ta, sai ta yi saurin sauka tana dariya
“Am sorry Sweetheart na yi latti, ka ga har an fara kira na”
Daker ya iya ɗaga jajayen idanunsa ya kalleta yana haɗiye yawu
“No Please karki min haka Ammyn Rafiq, i need you”
Tawul ɗinta ta ɗauka ta ɗaura tana faɗin
“I need you too Babe, but there's nothing i can do, you know how my work is”
Babu abunda zai ce mata, haka take masa time to time, ta kan hana sa haƙƙinsa saboda aikinta, idan ta dawo da dare ta ce ta gaji bachi idan kuma da safe ne ta ce zata yi latti, babu kuma yadda zai yi ya hanata aikin tun da mahaifinta ya tsaya kai da fata akan lallai sai ƴarsa ta yi aikin banki.
Yana kwance a gurin har ta yi wanka ta shirya yana kallonta, sai daf da zata fita sannan ta zo daidai kunnensa ta yi masa kiss
“Take care of yourself okay, idan Rafiq ya tashi ka shirya shi idan zaka je aiki ka aje shi kurin Hajiya, zan ɗauko shi idan na dawo, idan kuma su Ulfah sun dawo abincin su na nan a flask, love you my hubby my Doctor”
Daga haka ta fice tana murmushi, da kallon ya bita har ta fice, sannan ya ɗauke kansa yaja bargo ya lulluɓe ya soma sana'arsa.
_______________________________
Hello my beautiful people, ina fatar kuna lafiya kuma ina fatar wannan tafiyar zata muku daɗi zaku kuma bani haɗin kai kamar ko yaushe.
Wannan tafiyar ba irin wacan bace ce, ba zan baku kunya ba In'shallahu, iyana gayyartar ku a sabon shafina wanda zan riƙa zuɓa duka littafaina a can, zan riga yin update a can sama da ko'ina zaku iya samun shafuka na akan kari Just click the for your updated.
www.khadeejacandy.com.ng
Zan cigaba idan na ji ra'ayoyinku 08036126660 na gode ☺
Best regards 💖
Khadeeja Candy🌺
http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa03.html
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺
_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*
Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated
*PAGE - 2*
NAMRA POV.
Yadda Namra ta ga rana haka ta ga dare, dan kwana ta yi kuka da tunanin Asim, da safe ma bata fito ba sai da ta yi shirin fita, sannan ta leƙa ɗakin Anty Amarya dan gaishe ta, daga bakin ƙofa ta tsaya tana miƙa mata gaisuwar tana ɗan kare fuskarta.
“Anty Ina kwana?”
Yanayin muryarta kaɗai ya isa ya karantar Anty Amarya halin da ƴarta take ciki, daman ta san za'a rina, ko babu dalili Namra ta kan yi kuka balle yanzu da kuka ya zame mata jiki.