← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 173

Sashe 50

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wayata ce wannan this is my phone, how... ”

Sai kuma tayi shiru, tana nazari. Da sauri ta barkata kayan ta kai har ƙasan akwati, sai ga sarƙarta, da wasu manyan ƴan kunne nata, da agogon ta. Da sauri ta ɗauki ta miƙe tsaye tana mamaki.
Cikin wani irin bachin rai ta fito waje ta isa har inda Mardiya take zaune suka fira da Matan gida, ta ɗauke ta mari. Namra bata damu da matan da suke cikin gidan ba haka ta shararawa mardiya mari har huɗu tana hawaye.

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

                               _Write by_
                       *Khadeeja Candy*

*PAGE - 37*

NOT EDITED ⚠

Sare saren jini ne ya fara zubar mata, amman hankalinta gaba ɗaya ya tattara ya koma gurin takardar.

‘Ga result ɗin da kike nema nan, da kuma wanda Doc Sabo ya bani jiya, ranar Monday, na biyun zai fito, idan har baki tsallake ba, za'a sake miki na uku, bana son kowa ya san sirrin mu, na yi alƙawarin rufa miki asiri saboda ƴaƴanmu, amman ba zan zauna dake ba Rashida idan har hakan ya tabbata, kar ki kuskura canja komai kar kiyi unƙurin yin komai, har sai gaskiya ta bayyana kuma na baki damar zuwa gida idan kina da buƙata, bana son wata alaƙa ta sake shiga tsakanin ki da su Ezzah a yanzu’

Taya zai mata katanga da yaranta? Taya asirinta zai tono tun yanzu, ba zata iya jure rashin Hilal ba ta shirya sadaukar da rayuwarta a gareshi, tana son mijinta, miyasa zata farka daga bachi tun yanzu? Baya mafarkinta be ƙare ba?

Wani irin ihu ta saka ta silale a gurin.

NAMRA POV.

Faɗuwa Mardiya tayi ƙasa daga kan turmin da take zaune, tana kallon Namra da mugun razana a fuskarta.
Gaba ɗaya matan gida sai hankalinsu ya tattara ya ya koma kan Mardiya da Namra. Babu wanda yace uffan har Inna da take Mahaifiyar Mardiya, dan tasan Namra ba zata mari Mari Mardiya haka kawai kawai ba.

“Ashe baki da zuciyar Imani? Duk zaman amanar da nake dake Zagon ƙasa kike min? Kina ganin yadda na yi ta neman wayar nan, ashe tana gareki kika ƙi faɗa min? Taya kika ɗauki sarƙa ta da ƴan kunne na? Faɗa!”

Namra ta faɗa a tsawace tana mai jin kamar ta kama Mardiya ta ɓanlata gida-gida, ta watsar. A nan matan gidan kowa ya fara sun-sun da kai suna kallon-kallon ma junansu, daman sun daɗe suna jiran zuwan wannan ranar, tun da sun san Mardiya ta na ɗan ɗauke-ɗauke kuma sun san ba zata rasa yi ma Namra ba, tun da halinta ne.

Murje ido Mardiya tayi, ta mayarda hawayen da suke son zuba mata, wani dakewar zuciya ta samu kanta da ita, na mayarda ƙaryarta ta zama gaskiya.

“Namra ya kamata ace kina bincike kamin ki aikata abu, kuɗin ki na canja musu muhalline, sannan ni ban ɗaukar ka miki waya ba balle kuma sarƙa, sai idan wani sherin zaki min”

Tassss Namra ta sake marinta ta turata can baya har ta faɗi.

“Munafuna mai siffar ƴan wuta, nayi farinciki da Allah ya nuna min ko wacece ke tun a yanzu, na yi nadamar sanin ki a rayuwarta, baki da imani ba ki da tausayi Mardiya, duk irin halin da nake ciki sai da kika ƙafe zuciya kika min sata? Ɗaukar haƙƙin wani? kuma ki jira sakamakon ki”

Wannan karon Mardiya hawaye take. Mahaifiyarta ta matso tana hantarar Namra, magangannunta sun ɓata mata rai sosai, tana ganin dan me Namra zata musu haka.

“Amma ke kam ba ƴa bace sam baki da mutunci, ai komai Mardiya tayi miki ya kamata ace kin taushe zuciyarki kin ɗaga mata ƙafa, balle ma bayi ba dan ban haifi ɓarauniya ba”

Namra ta kalleta da jajayen idanuwanta, ta yarfe ta da hannu.

“Kin ji kunya Wallahi, tirr da uwa irin ki mai ɗaurewa ƴarta gindi tana abunda take so, uwar da ƴarta zata sa ƙafa ta fita ba zata dawo sai taga dama kuma hankalin ki kwance, sai murna kike tana kawo miki abunda daɗi, kina da tabbacin inda take zuwa? Idan har kin san hallaci ba zaki bar ƴarki ta ta ɗauki abu na ba, ko da kuwa yana zuba a ƙasa”

Maman Mardiyar ta jinjina kai

“Lallai ɗan adam butulu, lallai mun yi kuskure yi miki masauki min yi kuskuren yarda dake, a nan da kika yi gobara babu uban da yayi miki masauki sai mu, mu baki ci mu baki sha amman shine zaki watsa mana ƙasa a ido ko tafiyar yawon asibitin nan duk da Mardiya akayi shi, amman ki rasa abunda zaki saka mata da shi sai sata”

“Kune kukeyi kuskure, ni nadamar sanin da na yi mu nake, in mamakin bushewar zuciya irin na ƴarki, na yarda da ita ace ita macuciya ce”

Hawaye take kamar an buɗa fonfo, sai ta shiga ɗakin ta kwaso kayanta ta fito da su waje, sannan ta sake komawa ta ɗauke komai nata a ɗakin ta fito dashi waje, sai a sannan matan gidan suka fara saka baki a maganar, suna bata haƙuri tare da Mahaifiyar Mardiya.

“Wallahi ba zata sake kwana a gidan nan ba, indai ƴar halak ce ko ƙofar gidan nan karki sake bi, shi kenan dan anga yarinya bata magana sai a riƙa cin amanarna kowa ya kwaso shararsa sai ya zube akanta, to ta Allah ba taku ba Wallahi, Mardiya nan gani nan bari kashe di uku lahaula bakwai”

Namra ta nuna ta yatsa.

“Karki soma wulaƙanta ni akan wannan gidan, nima rayuwa ce ta canja min da ko a hanya kika haɗu da ni ba ki isa ki faɗa min magana mai ɗaci ba, kuma ni ƴar halak ce zan tabbatar miki da hakan ”

“To mu zuba mu gani, ai mu kujera ne, muna nan zaune zaki dawo”

Namra bata sake ce mata komai ba, uffan ba saboda baƙinciki, da taimakon yaran gidan ta kwashe ƴan tsomakaranta ta kai BQ ɗin gidan ta , sai ta zauna a balcony ɗin gidan ta tsurawar main house ɗin gidan ido, tana hawaye.

Miyasa Mardiya zata mata haka bayan ta yarda da ita? Miyasa duk wanda ta yarda da shi sai ya dawo yana mata Zagon Ƙasa? Ji take kamar ace akwai wani a kusa da ita ta faɗa masa matsalarta ta labarta masa damuwarta, ta faɗa masa abunda Mardiya tayi mata ko zata samu sassauci a zuciyarta.
  Tashi tayi ta ɗauko wayarta, ta riƙe a hannun tana juyata, itace last kyautar da Anty Amarya tayi mata, jin son wayar take ya shige ya, lallai tana buƙartar mahaifiyarta a kusa da ita.

Ƙoƙarin kunna wayar take amman abun ya gagara, ta danna power bottom ɗin amman wayar taƙi ta tashi, sai ta juyar da gefenta da bayan ta tta duba ko ina, bata ga wani matsalar ba, amman wayar taƙi ta tashi.
    Riƙe wayar tayi tana ta kallonta, kamin ta saka ta ajaka, ta tashi ta canja Hijabinta ta fito harabar gidan. Yau kam sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta samu Napep, kai tsaye tace ya kai ta asibiti.

Lokacin data shiga asibitin ta yi ta ƙoƙarin ta ɓoye damuwarta, amman abun ya ci tura, saboda baƙin cikin abun da Mardiya tayi mata ya tsaya mata a rai.
    Ko da ta shiga ɗakin ta tararda likita na duba Asim, yana wasu ƴan rubuce-rubuce, bayan ya gama ya miƙa mata takardar.

“A siyo wannan maganin anjima za a bashi”

Hannu kawai tasa ta karɓa tana kallon likitan har ya fice, sannan ta zauna kusa da Asim ta ɗora kanta saman kafaɗarsa, ta fara hawaye.

“Miya faru?”

Kuka ta fara rarewa a hankali.

“I just need someone to tell everything will be okay”

Zungurarta yayi da kafaɗarsa ta ɗaga daga saman ƙafaɗar tana kallonsa, shi kuma ya wani ɓata fuska.

“Namra miyasa kike abu kamar wata ƙaramar yarinya, ya kamata ace kin san kin girma fa amman sai ki riƙa abu kamar wata ƙaramar yarinya, haba Namra baki ga halin da nake ciki ba, yanzu fa wani maganin ne likita ya rubuta min, ni wannan zaman asibitin ban san ranar da zai ƙare ba, da nasan wannan ƙaddarar zata same ni da ban je ɗauko motar nan ba”

Furucin da Asim yayi a yanzu, sai ya ninka ɓacin rai tazo da shi, tayi tunani zai barta ta faɗa masa damuwarta ne har ya rarrashe ta, amman sai ya ƙara mata wani.

“Miyasa kowa baya fahimtar damuwata, miyasa kowa baya jin abunda nake ji? Miyasa ba a ganin ƙoƙarina? Be kamata ka biye Mama ba, be kamata ace kana irin wannan furucin ba”

“Be kamata ba? To idan ban biye mata ba wa zan biyewa? Ai gaskiya take faɗa, komai ƙaddara ne amman kuma yana da sanadi, nan gaba idan ba bara ba me kike tunanin zamu koma yi? Tun ana baka rance wata rana ai hana ka za'ayi”

Kallonsa kawai take, tana mamakin kalamansa, taya Asim.ya juya ya koma ba shi ba? A yau ita Asim yake kallon tsabar idonta ya faɗa mata irin wannan maganar?
   Turo ƙofar da Mama tayi ta shigo ne yasa tayi saurin share hawayenta, ta sanda kai ƙasa, zuciyarta na mugun ƙona.

“Ga waya mamanki ta kira”

Hannu ta kai ta karɓa, sai ta tashi ta bar ɗakin da saurin saboda kukan dake son cin ƙarfinta.
  Mama ta bita da wani kallo.

“Me kuma aka mata?”

“Oho kukan data saba ne ta zo ta min”

“Hmmm wannan matar ita da iyayenta ba son ka suke ba, duk ta bugo wayar nan ƴarta take kira,ƴar wayar kiran ma ta kasa ta siya mata, ni wallahi ban san me suke nufi da kai, ni Wallahi da zaka bi ta nawa da ka saki yarinyar ka huta ma kan ka”

“Mama idan na sake ta a yanzu wace mace ce zata zauna da ni a haka? Bana da kuɗin auren wata, sannan kina ganin halin da nake ciki, ai ƙara ma na zauna da ita duk wahalar da zamu sha mu shata tare, komai zai ci ni sai ya ci ƴarsu”

“Hmmm Allah ya kyauta, amman wannan sun nuna maka ƙiyayyah zallarta, Allah dai ya azurta ka ya baka lafiya”

“Amin”
Chapter 50 · 0% Book details