← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 173

Sashe 123

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya amsa da “Amin” Yana wani sunsun da kai, shi ala dole ga surukin da ba san da shi ba 😂.

Mai Martaba ya miƙawa Abbah hannu yana murmushi.

“Yanzu kam zamu yi gaisuwar mutunci da kai, kaga har ƙoƙarin raba uwa da ƴa kake.”

Mai Martaba ya faɗa yana miƙewa tsaye. Da sauri Abbah ya miƙe tsaye, da hannunsa biyu ya riƙa hannun Mai Martaba yana dariya.

“Tuba na ke ranka ya daɗe, Allah yaja kwanan ka”

Juyawa Mai Martaba ya juya Abdool ya miƙe tsaye da sauri ya take masa baya. Har turakarsa Abdool ya rakashi farincike shinfiɗe a fuskarsa, Mai Martaba na shiga Babban falonsa Abdool ya riƙa alƙyabarsa ya cire masa ya jingine, sannan Mai Martaba ya cire rawaninsa da kansa ya aje a gefe, da sauri Abdool ya ɗauki rawanin ya aje a muhalinsa. Sannan ya zo ya zauna ƙasan carpet ya dafa ƙafafun Mai Martaba yana dariya.

“Na gode sosai da karamcin da Mai Martaba yayi min, ba zan taɓa manta wannan ba, Allah ya ja zamanin ka”

Murmushi yayi sai da aka ɗauki daƙiƙu sannan Mai Martaba ya amsa da

“Amin. Nan da minti talatin zamu je ɗan dime ƙaddamar da zakka, idan da hali sai ka shirya muje”

“...A...”

Sai kuma yayi shiru. Kallonsa kawai Mai Martaba yayi hakan ya cilastashi ƙarasa maganar.

“Da naso naje ne can Kaduna na kai su inda take”

Mai Martaba ya sake kallon ɗansa, irin kallon nan na akwai wani abu a ƙasa.

“Babana be kamata kana saka kanka a cikin irin wannan rayuwarba, karka manta kai ɗan sarki ne, kuma nan gaba kaɗan kai Sarki ne, sannan kai mutun ne mai babban muƙami a nigeria, be kamata ana ganin fuskarka a ko'ina ba, wani gurin kamata yayi ka aika, ko kasa ayi. Shi babban mutum ba ko ina ake son yana kasancewa ba, musamman ƴaƴan sarakuna, yana janyo raini, wani gurin ma yakan zubar da mutumcin mutum, amman kai sai naga kamar baka damu da hakan ba”

Yayi ƙasa da kansa, dan yasan Mai Martaba ya faɗi gaskiya, sai dai shi kan har ga Allah yana son ya zama na farko da zai fara yi ma Namra wannan albishir ɗin ko ba komai zai ƙara kwarjini a idonta.

“Amman Mai Martaba ina son na kasance nina zan yi ma yarinyar nan Albishir, idan mun kama hanyar Kaduna yanzu kasan kamin yamma mun isa”

Mai Martaba ya shafa fuskarsa.

“Idan har ganinta kake son yi, zaka iya aikawa a taho da ita”

“She's so stubborn ba lallai bane ta zo, kuma abun zai fi burgewa idan iyayenta da kan su sukaje suka ɗauko ta”

Kallon tsab Mai Martaba yayi ma Abdool sai ya ɗauke kansa, tare da ɗaga masa hannu, alamar go ahead.

***        ****      ****

Fitar da Mai Martaba da Abdool suka yi ne, yaba Anty Amarya damar data kai ta ƙare ma Faɗar kallo. Manyan hotuna da ta gani na Abdool ɗaya a cikin kayan sarauta ɗaya kuma a cikin kakin soja, yanzu kan sarai ta tuna waye Abdool. Mutumen da ya taɓa taimaka mata lokacin da motarsu ta lalace ana ruwan sama.

“Gaskiya yana da kirki, matar ka da ƴaƴanka sun yi dacen uba na gari”

Ta faɗa idonta kan hoton Abdool. Abbah dai be ce komai ba, sai fama idonsa abinci yake yana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake tashi faɗar.

Fitowar Abdool ne yasa duk suka maida dubansu gurinsa. Wata shigar ce a jikinsa bata ɗazun ba, wannan ma ta fitar da kyausa, da kuma annurin fuskarsa. Zuwa yayi ya risina gabansu, ya yi ƙasa da muryarsa sosai.

“Idan kun shirya zamu je Kaduna yanzu sai na nuna muku inda Namra take”

“Abunda muke jira kenan”

Anty Amarya ta yi saurin amsawa.

“Mai Martaba yana shiri ne, idan ya fita muma zamu kama hanya”

Ya faɗa yana kallon fuskar Abbah dan yaji me zai ce. Murmushi kawai Abbah yayi ya ɗaga masa kai, yana masa kallon mutum mai hankali da natsuwa.

NAMRA POV.

Murmushi kawai take, sai ɗaga kai tana maidawa, duk firar da ake, bata saka baki saboda itama nata ya isheta, su kansu suna firar ne ɗan kawai su rage mata kewa. Amman ta ƙi ta sake, sai dai a kan yi murmushi ko ɗaga kai, gudun kar suce ta ƙyale su, tun da Abdool ya takalo mata maganar gida sai ta koma wata irin, tunanin rayuwar jindaɗin da take ciki ta baya ta riƙa dawo mata, da kuma tunanin halin da Asim ya jefata, ga halin ko in kula da ya nuna mata, da kuma ƙin son haɗa jini da ita, ace duk tsawon wannan lokacin be neme ta, da gaske baya da buƙatar ta kenan?  A ɗayan ɓangare kuma tana tunanin yadda zata shirya da iyayenta har ta koma ta zauna a tare da su wanda take ganin abu ne mai matuƙar wahala yin haka.

Duk dariya suka sa lokacin da Lamido yake bada wani labari na ban dariya, ita kam Namra sai ta saka kuka tana mai ɗaga murya dan damuwarta tasa ta manta da agaban jama'ah take, babu wanda hankalinsa ya fi tashi kamar Lamido, dan ya tsani ganin Namra cikin damuwa balle kuma zubar hawayenta. Sai da taga hankalin kowa ya dawo kanta sannan ta sassauta kukan da take ta tashi da gudu ta shige ɗaki. Ajiyar zuciya Lamido ya sauke cike da rashin daɗin rai ya ce

“Yarinyar tana cikin damuwa, ni ko bana son ganin ta cikin wannan halin, dan zai ƙara mata damuwar ne kawai, babu abunda yake raina a yanzu kamar na maza sanadiyar farincikinta, zan yi iya yadda zan iya na ganin na cire ta cikin wannan halin inshallah”

Neina ta miƙe ƙafafunta tana kallon ɗanta cike da son sa da kuma tausayinsa ta ce

“Cire yarinyar nan a damuwa abu ne mai wahala Lamido, ga dukan alamu ƴar babban mutunce, shiga irin lamarin gidan su sai yi wahala gareka tun da kai ba ɗan kowa ba ne”

Ɗauke kansa ya yi ya maida gurin ƙofar da Namra take. Sai da Neina ta tashi sannan ya miƙe tsaye yana ɗan ɗingishi ya nufi ɗakin. Zaune ya same ta kusa da ƙofa tana raira kukanta mai ban tausayi da taɓa zuciya.

“Namra kukan nan da zai miki magani da tuni yayi miki, kina ƙara saka kan ki ne cikin damuwa ne kawai”

Ɗago kai ta yi ta kalleshi.

“Idan ban yi kuka ba mi zanyi? Kana tsammanin mace data shiga cikin halin da nake ciki zata yi abota da dariya ko farinciki? Ba zaka gane abunda nake ji ba”

“Nasan kin shiga rayuwa kala-kala amman kuka ba zai miki magani ba, ki taimaka min ki tausaya min ki daina wannan kukan Namra, saboda gani nake kamar nine silar zubar hawayenki, ina damuwa sosai”

Hannayenta biyu tasa ta share hawayenta, sannan ta miƙe tsaye ta nufi gurin katifa ta zauna, ta yo ƙoƙarin tsayardar kukanta ne kawai dan ta lura da damuwar da Lamido yake idan tana kukan, balle kuma har ya kai ga yi mata magana, ita kanta tasan ba kowa ne zai juri zama da ita ta dinga masa kuka kamar ƙaramar yarinya. 
Ajiyar zuciya Lamido ya sauke ya shafa fuskarsa sannan ya juya ya fice. Ba tayi minti talatin da zaman ba, taji yaro ya doko sallama wai Abdallah daga Katsina yana sallama da Namra. Wani baƙin haushi ta ji ya turniƙe ta, yau kuma da wacce ya zo? Me yake nema a gareta ne? Ba zai barta da damuwarta ba! Tana jin motsin shigowar Neina ta yi saurin kwantawa saman katifar ta lafe sosai kamar ta yi bachi.

“Na san ba bachi kike ba Namra, kuma kon ji lokacin da aka ce ana sallama da ke a waje, ki rufa mana asiri ki tashi kije”

Neina ta faɗa zuciyarta Fal da tsoro, dan ita tun da taji ance ɗan sarki ne, duk fargaba da tsoro suka kama ta, kullum zulluminta ɗaya kar yasa ayi musu wani abu.
Sosai Namra ta so tayi pretending like tayi bachi amman jin yadda muryar Neina take mata magana kamar mai magiya, yasa ta motsa har ta buɗe ido ta kalle

“Neina ban san me mutumen yake nufi da ni ba, me zai zo yayi min a yanzu?”

“Kije dai Allah, ko ma minene zaki ji, kin rufa mana asiri Namra, kin ga mu talakawa ne bayin Allah, karki ja mana abun ba zamu iya ɗauka ba”

“Bana nufin janyo muku komai Neina, amman kamar ba ki fahimci abunda nake nufi ba”

“Na fahimta, kawai ki tashi ki tafi, idan kuma har baki jin tafiyar, ni zan iya bashi izinin ya shigo nan yayi magana da ke, wata ƙila ma carpet ɗinsa da daya manta shekaranjiya ya zo karɓa”

Kamin ta Namra ƙara yin magana. Lamido ya ɗaga labulen ɗakin ya kunno kai yana faɗin.

“Neina kina tsoron masu milki da yawa”

“Dole na tsoraci masu milki Lamido, kafi kowa sanin sune sanadin shigar mu wannan halin”

Tana kaiwa nan ta juya ta fice. Shi ma Lamido juyawa yayi ya fice cikin rashin daɗin rai, yakan samu kansa a cikin rashin jindaɗi a duk lokacin da Yarima ya tsaya ƙofar gidansu da sunan kiran Namra.
Namra bata motsa daga inda take ba, sai ga Neina ta dawo ɗakin riƙe da carpet ɗin ta miƙa mata.

“Tashi kije ki kai masa, ko ba komai wulaƙanta ɗan Adam babu kyau, balle babban mutun kamarsa”

Wannan karon Namra bata yi mata musu, ta tashi ta karɓi carpet ɗin ta miƙe tsaye, already tana da hijab ɗinta sanye, sai kawai ta bi bayan Neina suka fice tare, takalminta ta zura, ta nufi ƙofar fita.

As usual gurin daya saba tsayuwa ya tsaya, tana tunkara inda yake tsaye gabanta ya soma faɗuwa, ta rasa dalilin daya saka yake mata kwarjini, tana isa kusa da shi ta miƙa masa carpet ɗin ta ce

“Ga carpet ɗin ka dan nasan ita ka dawo ƙarɓa”
Chapter 123 · 0% Book details