← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 173

Sashe 101

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗaya daga cikin matasan dake tsaye a gurin masu Napep ya tambaya yana shafe ruwan dake alwala dake fuskarsa. Matashin saurayi ne mai jini a jika fari kyakkyawa da shi, a zahiri akwai natsuwa da sanin ya kamata a shimfiɗe a fuskarsa. Ga sajensa gwanin sha'awa.

“Cikin gari...”

Ta faɗa da muryarta mai kamar zata yi kuka.

“Okay, shiga muje amman zan tsaya a hanya na samu jam'i”

“Ba matsala”

Ya jefar ledar pure water dake hannunsa ya shiga napep ɗin tasa mai kamar sabuwa ya kunna, ita kuma sai ta shiga gidan baya ta zauna tana ta tunanin inda zata ce ya kai ta. Har ya kunna Napep ɗin ya fara tuƙi be tambaye a ina za'a kai ta cikin garin ba, dan shi dai danuwarasa a yanzu ya samu jam'i.
Ba suyi tafiya mai nisa ba ya faka a gafen titi, ya fita yana faɗin

“Bari na yi salla a masalacin”

Kai ta ɗaga masa tana kallon mutane dake ta haɗa haɗa a kan babban titin. Tunanin unguwar da zata ce masa ya kai ta take, amman har yayi salla ya dawo bata samu unguwa ɗaya da zata ce ya kai ta, dan bata san garin kaduna balle yace ga inda zai kaita.

Sai da yayi mata sallama sannan ya shiga Napep ɗin ya tasheta ya hau titi. Can ya ciro wani ƙyale ya kare ƙasar salla dake goshinsa ya juyo kaɗan ya kalli Namra.

“Wace Unguwa za muje?”

“Uh...m ca..an can..gur.in gra”

Ta faɗin hakan ne dan bata san inda zata ce masa ba, amman ta san ko wane gari akwai gra.

“Okay GRA ta gurin ina?”

“Ta gurin manyan gidajen nan”

Daga nan wata kalma bata sake shiga tsakaninsu ba, shi dai ya mai da hankalinsa gurin tuƙinsa, ita kuma hankalinta gaba ɗaya ya tattara ya koma gida da tunanin inda zata kwana yau a garin kaduna. Ganin sun shiga GRA har suna ƙoƙarin wucewa bata ce ga inda za a sauke ta ba yasa yayi mata magana.

“Malama mun shiga GRA ɗin fa”

Sai kawai tayi shiru ba dan kuma bata ji shi ba, sai dai bata san abunda zata ce masa ba. Hakan yasa ya ƙara maimatawa yana mai rage gudun da yake.

“Gaskiya ni ban san inda zanje ba”

Juyowa yayi ya kalleta.

“Baki san sunan mai gidan ba ne? Kuma baki da number waya?”

“Ban sani ba, kuma bana da number, sau ɗaya na taɓa zuwa”

“Amman irin wannan tafiya ai it risk, ace baka da number wanda zaka sauka gunsa kuma ba kan guri ba?”

Tayi shiru bata ce komai ba. Sai a yazu take nadamar zuwan da tayi a kaduna ita kanta ta san tayi wauta.
Jin bata ce komai ba yasa ya ce

“Ina zan sauke ki dan ni akan aiki na ke”

“Wallahi idan ka sauke ni ban san inda zanje ba, dan bana da kowa a kadunar nan sai Allah, tun da ban san gurin wanda zan sauka ba”

Cikin muryar kuka tayi maganar, juyowar da zai ya kalleta sai kawai yaji shesshekar kukanta. Baya iya ganin hawayen idonta dan Napep ɗinsa bata da wutar ciki wance wasu suke sakawa, hasken dake gefen titin be iya ya haska fuskarta har yaga hawayenta ba,amman a yadda ya karanta kamar tana cikin wani hali ne.

“Bawai Allah ke mutum ce?”

“Ni mutum ce wallahi kuma ba cutar da kai zan yi ba”

A nan ta saka ƙafarta ta sauka daga cikin Napep ɗin ta saka hannunta a jaka ta ciro ɗari biyu ta miƙa masa.

“Ba ni canji”

Ta faɗa tana ta ƙoƙarin tare kukanta dake son fitowa. Kasa karɓar kuɗin yayi kuma ya kasa tafiya, kallon fuskarta yake dan yanxu hasken gurin ya haska fuskarta, bata yi masa kama da mugayen mutane ba, jikinsa be bashi zata cutar da shi ba, hakan yasa shi idan har ya barta a nan gurin be kyauta masa ta, kuma besan abunda zai same ta ba tun da tace masa bata da kowa sai Allah.

“Shiga mu je”

“Na gode”

Ta faɗa tana share hawayenta, sai ta shiga Napep ɗin da sauri. Tun da ya soma tuƙin be tsaya ko ina ba sai malali, a mararraba ya tsaya ya miƙa ɗari da hansi aka bashi canji sannan ya ƙarasa ƙofar gidan na su mai cike da rufin asibiti, dan a kira su da talakawa ba kasancewar suna da rufin asiri da wadatar zuci. Sai dai a zahiri kan talakawa ne sosai masu ginin bulu wanda ba ayi ma filistaba.

“Fito muje”

Ya faɗa bayan ya kashe Napep ɗin. Cikin sanyin jiki ta fito tana dansar bakumi saboda mugun murɗa da mararta take mata. Yana gaba tana biye har suka shiga cikin gidan mai ɗauke da ɗakuna uku, duk da dare ne hakan be hanata ganin yalwantaccen tsakar gidansu ba mai ɗauke da bishiyar mangoro guda biyu ɗaya a jikin ɗaki ɗaya kuma a tsakiyar gidan.

“Neine (Inna da yaren fulatancin) ga baƙuwa”

Wacce saurayin ya kira da neiner ta miƙe daga saman tabarmar da take ta nufo Namra tana murmushi.

“Maraba maraba laƙe marhabun baƙonƙa annabin ka, siter ƴata sita (Zauna zauna)”

Ya faɗa lokacin da take ƙoƙarin zaunar da Namra saman tabarmar da take zaune. Namra ta zauna tana kallon yaran gidan da suka kewaye waya suna kallon india hausa a wata ƙaramar wayar hannu. Gaba ɗaya hankalinsu ya tattara ya tafi can sam basu ma san da zuwanta ba.
Neine da kanta ta shiga ɗaki ta ɗauki ma Namra tuwon masara ta aje mata gabanta, sai ta nufi wani ɗan madaidaicin tulu ya bulbulo mata ruwa a kofi ta kawo mata tana mai sakar mata fuska kamar ta santa.

Shi dai yana daga can gefe yana bawa cat ɗinsa kifi, amman hankalinsa yana gurin Namra yana kallon yanayinta.

-----------------------------------------------------------------
I PITY RASHIDA 😢
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *64*

Suna ta gaba-gaba suna tare Abdool kamar wanda wani abu zai same shi, sai kirari suke masa wasu na ture mutane dake gefen gurin dan Abdool ya samu hanya. Mutane sai kallo a ke wasu ma har sun wuce sai suka dawo ganin duka numbobin motar an saka YARIMA ABDOOL, duk wanda kuma yaga jajaye kaya yasan sarki ne ko kuma ɗan sarki.

Abdool be nuna tausayi a fuskarsa ba, na ganin irin raunin da aka yi ma Lamido, sai dai a can zuciyarsa ne yake tausayinsa ganin yadda jini yake masa zuba a kai kuma ya riƙe ƙafarsa sai cizar baki yake alamar yana jin zafi sosai, kowa yaga yadda Napep ɗin tasa ta yi sai ya tausaya masa duk ta lalace kai baka ce ma wanda yake ciki zai yi rai ba, saboda buguwa da tayi da transformer garin ya kauce musu har ya transformer ta faɗo kan Napep ɗin tasa, shi da be yi hanzarin fita ba da Allah kaɗai yasan irin ciwon da zai ji.

Lamido ya kalli Sadauki ya soma magana da shi kaɗan-kaɗan, yana gama maganar ya juya da sauri suka soma take masa baya, suka buɗe masa motar ya koma. Sannan Sadauki ya kalli sauran dogara ya ce

“Yarima ya yi umarnin a kai shi asibiti”

Da sauri Dogaran suka nufi gurin Lamido suka riƙa shi suka saka shi motar su. Sai suka sauya hanya daga masaukin Abdool zuwa Asibiti mafi kusa da su.
  Anyi masa kyakkyawar karɓa, a asibitin, duk da kasancewar basu san Yarima Abdool ba amman suna ganin motoci ya dogarai sun san babban mutum ne.
Duk abinda aka yi aka maga Abdool na ciki mota zaunensa har aka gama dubasa aka saka masa baldeji a kai suka rubuta masa magani, a cikin asibitin dogaren yaje ya siya masa magani sannan suka dawo da shi gurin motar. Da gudu Sadauki ya nufi Motar Yarima Abdool ya ƙwanƙwasa gilashin motar sai ɗayan dogaren dake ciki ya sauke gilashin motar.

“Ran Yarima ya daɗe, an kammala masa komai, sun ce yaji ciwo  kai sai kafarsa da ɗan targaɗe kaɗan”

Da Abdool yake magana amman yayi kamar be jisa ba, idonsa na kan Lamido dake tsaye jikin wacan motar yana kallon titi. Kallonsa sosai Abdool yake a zahiri yana da kyaun natsuwa da kuma kyaun fuska, gashi dogo ga fari ga dogon hanci gashin kansa kawai idan ka kalla zaka gane bafulatani, sai dai hakan be hana Yarima Abdool jin wani iri akansa ba, wata ƙila akwai wani giɓi a tare da shi, ko kuma akwai wani abu a tare da shi wanda Yarima Abdool baya so, dan ya tsanar mutum haka nan kawai.

Haka Abdool ya kwashe daƙiƙu talatin da wani abu be ce da Sadauki komai ba, wata ƙila yau jinin sarautar ni ya motsa har yayi abunda be saba ba, kuma abunda yake ganin kamar be dace ace mutum yana yi ba.

“Za mu bi ta gidan su mu aje shi sai mu wuce”

Ba dan sun saba ba, da ba zaka zaci da su Yarima yake ba, yanayin yadda yayi maganar muryarsa na ƙasa sosai, ko kaɗan idonsa ba su kalli Sadauki ba, har yanzu idonsa suka kan Lamido yana masa kallon rashin dalili.

“Allah yaja zamanin Yarima, an gama”

Ya bar jikin motar da sauri ya nufi gurin wacan motar da Lamido yake tsaye.

“Kai ɗan talakawa shiga mota muje, Yarima mai jiran gado ya ce aje a kai ka gida”

Maganar ta daki zuciyar Lamido har sai da ya kalli Sadauki sai kuma ya kalli Motar yarima duk da baka iya hango wanda yake ciki sai dai na ciki ya ganga. Har zai yi magana sai kuma wata zuciyar ta hana shi, sai kaeai ya rage tsawonsa ya shiga motar, still ransa ya sosu da furucin da Sadauki ya yi masa. Sai da ya shiga motar sannan Sadauki ya dawo a motar ya Yarima ya shiga suka kama hanyar Tudun wada.
Chapter 101 · 0% Book details