← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 173

Sashe 170

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Ranar da labarin ɗaurin auren Namra ya same shi yayi kuka har sai da idonshi suka canja kala, tabbas yasan ya cuci yarinyar sai dai ba haƙƙinta ne kaɗai ya ke binshi ba har saɓawa Allah da yayi, saboda ya tsallake iyakarsa, ya aikata laifin da Ubangiji ya hana bayinsa tsarkaka su aikata, yasan baya cikin bayin Allah na gari.
  Kaito! Da wata rayuwa dai ƙara babu, yau gashi baya amfanarda kanshi da komai, ga kuma kunyar duniya ta isheshi, ƙanensa ma basa da lokacinshi, mahaifiyarshi ce kawai take kula da shi, ita kanta da taga abun yayi yawa sai ta nemo mai kula da shi ana biyanta duk ƙarshen wata, saboda ragewa kanta wahalar ita kaɗai.

Sai a yanzu ya gane ashe babu riba a cikin tsaɓawa Allah da cin amana, yayi nadanar da babu amfanin tun da yasan Abbah ba zai taɓa yafe masa ba, abunda Matarsa ta yi masa ma ishara ne idan yaronsa idan ya girma ba zai samu labari mai daɗi ba, ji yake kamar ya mutu ya huta, kunyar duniya ta ishashi a family da abokai babu wanda be ji abunda ya aikata ba, yana ji yana gani jindaɗi da kwanciyar hankali ya gagareshi lafiyarsa jikinsa ma ta tafi ta barsa, komai ya zo masa kamar mafarki, haka wani lokacin zai zauna yayi ta kuka idan ya tuna irin rayuwar jindaɗin da yayi yau ga shi ya koma wani kalar mutun da a gidansu ma uwarsa ce kawai ta damu da shi, sai a yanzu ya gane yayi kuskuren aikata abunda ya aikata sai dai lokaci ya ƙura masa babu ta yadda zai gyara komai ko da kuwa zai so haka, duk ya bi ya rame kamar ba shi ba gaba ɗaya halittarsa ta canja a Wheelchair ma idan ya zauna sai yayi kamar zai koma gefe, sai a ayanzu ya gane ashe cin amana da tsaɓawa Allah babu riba a ciki duk romon da yasha yana ganin kamar ya more ashe sakayyah na biye.

KALSOOM POV.

Tana jin kamar ta fi ko wace mace sa'ar miji a duniya, bata da mtsala ta ko'ina, mijinta na nuna mata so da kulawa ƴan'uwanshi ma haka, ga su Ezzah da suka zame mata kamar ita ce ta haifi yaran.

Wani lokacin ta kan zauna ta auna irin rayuwar da tayi a gida zuwa aurenta irin rigingimun da gwargwarmayar da tasha a lokacin da tayi kishi da Rashida amman yanzu komai ya zama tarihi, babu komai a cikin duniyarta sai farinciki jindaɗi komai ya zo kamar a mafarki, addu'ah da ta daɗe tana yi aje an amsa mata tuni jindaɗin na ne yake nesa, tabbas wani jinkiri alheri ne, kuma bayan wuya sai daɗi, rayuwa bata tabbata a guri ɗaya dole akwai canji ɗan adam baya taɓa zama a cikin wahala kullum maruƙar ka riƙe gaskiyarka kuma ka ji tsoron Allah ka yi haƙuri wallahi sai kaga canja domin dukan tsanani yana tare da sauƙi haka Allah ya faɗa.

Ta zama uwar ɗiya bayan ƴaƴanta uku da ta haifa ga ƴaran Rashida da su a yanzu sun tasa sosai. Shi kansa Hilal sai a yanzu ya fahimci irin tasirin da Kalsoom ta keda shi a zuciyarsa da kuma rayuwarsa, domin gudumawwa take bashi ta ko ina, sai a yanzu ya gane mai haƙuri mawadaci lalla yayi dacen mata, a cikin ɗari yayi nasara zarar ɗaya, komai jindaɗi suke yinsa da kwanciyar hankali ga soyayyar da suke nunawa juna kamar Romeo and Juliet.

LAMIDO POV.

Ya girgiza da Asim yadda ya mayarda ƙaryarsa gaskiya, har ya nemi ƙetare iyakar Allah, be yi mamakin abunda ya same shi a tun a falon ba, a tunaninsa ma ya cancanci fiye da haka. Bayan Mai Martaba ya tashi sai yayi ma su Abbah sallama Abbah yayi masa godiya, sannan ya kama hanyar Katsina.

A gida ne yake labartawa su Neine abunda ya faru, su kansu da basu ga yadda abun ya wakana ba amman sun jinjina lamarin suna yaba ƙoƙarin Asim na ketare iyakar Allah duk da basu san shi ba.

Abinci ya siya musu da kuɗin da Abbah ya bashi da kuma ƴan kayan masarufi, sannan ya koma Neine na masa addu'ah da kuma saƙon gaisuwa ga su Abbah.
   Kwana biyu da komawarsa ya fara aikin a kamfanin Abbah wato Zamau Metals Work kamfanine da ke sarrafa ko wane irin ƙarfe da kuma dukan abunda ya shafi ƙarfi hakaɓ yasa ana yawan bashi kwangila saboda yana hulɗa da ƴan siyasa sosai kuma yana cikin mutane da ake damawa da su ciki da wajen jihar sokoto.

A gidan yake zama lokacin aiki ya tafi idan ya dawo kuma baya komai sai ya zauna a gida, hakan yasa wani mugun shaƙuwa da kula juna ya shiga tsakaninsa da Aisha, har ta kai idan bata ganshi ba sai ta kira shi ita ma haka, babu abunda yake ci mata tuwo a ƙwarya kamar tafiyan da yake akan abun hawa idan zaije aiki ko kuma fita wani gurin daban, wani lokacin ta kan ɗauki makullin motar Anty tasa ya kaota wani gurin, ta saka Abbah gaba da zancen ya siya masa mota sai Abbah ya mallaka masa motar da yake jan namra ada wato wacce yake kaita makaranta. A ranar Aysha ji tayi kamar ta haɗe Abbah dan murna tana ta jindaɗi sosai, daga lokacin duk inda zata je shi yake kaita matuƙar ba aiki yake ba ko kuma zaije ba, shi kansa yana jindaɗin fura da kuma sakewa da Aisha, lokuta da dama tana masa yanayi da Namra, yana samun nishaɗi sosai idan yana fira da ita. Kwana biyu ɗa bashi motar Neine da wani ɗan'uwanta suka zo yi ma Abbah godiya, kwanansu ɗaya suka koma, Yadda Aysha ta riƙa kula da Neine ya karantar da Abbah ba iya mutuncin ne a tsakaninta da Lamido ba har da soyayyar da ma ya lura da irin shaƙuwar da ke tsakaninsu, hakan kuma ba ƙaramin faranta ran Abbah yayi ba, a kullun tunaninsa da ina zai farantawa Lamido ya saka masa da abunda yayi masa, tun daga lokacin da yaje ya bada shedar a faɗar Mai Martaba Abbah ya ji daɗin abunda yayi masa.

YASMIN POV.

Tana ji tana gani kuma tana ciki gari aka yi bikin Namra ta ƙi ta leƙa saboda tana ganin kamar idan taje za a riƙa nunata ne, ko kuma mutane su tuna abunda ya faru.

Duk wani tunani na rayuwa da zullumi sai ta tattarashi gefe ta aje ta maida hankalinta kan aikinta, tun bayan abunda ya faru da Uzair sai ta tattara lamarin namiji ta aje gefe ɗaya saboda tana tsoron faɗawa a wacan halin na baya. Sai dai ba tayi nasarar yin hakan ba tun bayan da ta cika idda sai manema suka riƙa fito mata ciki har da abokan aikinta. Hakan yasa mahaifiyarta matsa mata akan ta yi aurenta zai fi mata mutuncin fiye da zaman gida domin mace bata da wata daraja idan ba gidan mijinta take ba, kuma hakan zai taimaka mata gurin da tarbiyar ɗanta, Allah ta riƙa roƙo akan ya zaɓa mata alherin a cikin manemanta.

AMIRA POV.

Mace ko mai mutuncin ta a yanzu tana wahalar samun miji balle kuma wacce mutane ke ganin ta riga ta zubar da ƙimarta, abunda ta aikata yafi damunta a yanzu saboda zantunkan mutane da kuma tsangwa da take samu a duk lokacin da wani ya nuna yana son ta, daga ya kwana biyu yana zuwa munafukan unguwa zasu labarta masa tsawon lokacin da tayi ba a gida ba sai mutun ya gudu wasu kuma daga gidansu ake labarta musu yarinyar ƴar mutunci ba ce dole mutun ya kama gabansa, tun abun baya damunta har yazo yana ci mata rai, bama kamar idan ta duba duka ƙawayenta sun yi aure ita kaɗai ce a haka, karatun ma ta kasa komawa saboda damuwa da ta sawa ranta, lokacin da maganar auren Namra da Abdallah ya same ta tayi kuka sosai har sai da ta raina kanta, domin har gobe tana son Abdallah. Wani lokacin ta kanji kamar ba zata iya auren ƙaramin mutun ba, sai dai ganin babu sarki sai Allah yasa ta fara kula Sani Engineer, wato mai yi ma Mahaifinta gyaran mota a duk lokacin da ta samu matsala, shi ma kansa ba dan arzikin da yake ganin ubanta na da shi ba da babu abunda zai sa ya aureta saboda familynsa suna yawan magana akan su basu yarda da ita ba, duk kuwa da kasancewar ita ce ta uku a cikin matansa.

Duk wani abu da take ji akansa ta kan yi haƙuri ta danne zuciyarta saboda samawa kanta da kuma iyayenta farinciki, duk da tana jin kamar ba zata samu farincikin da take so tun da ba sonshi take ba, kuma gashi yana da mata da ƴaƴa taya zata jidaɗin zama a gidansa, da ta nemi ya kama.mata haya sai ya ce mata bashi da wannan halin kuma wai shi baya son raba kan iyalansa, a dole tasa Mahaifinta ya kama mata haya, domin ƙannenta ma an aurar da su sai ita, kusan rabin hidimar auren ma duk Mahaifinta ne yayi saboda shi ba mai kuɗi ba ne sai rufin asiri duka abunda aka ɗora masa Mahaifinta ne yake yi saboda ya samu dai ta yi auren.

Assabar aka ɗaura aure bayan anyi ahagulgulan biki kamar yadda ake ma ko wacce Amarya, duk da ita Amira bata so haka ba Ammy ce ta matsa ayi wai saboda asan ita ma tana da gata kamar ko wace yarinya, ba kowa ba ne yasan wanene mijinta saboda ɓoyewa ake wasu kuma indan suka ji ance Engineer sai su ɗauka ko wani babban Engineer ne.
  Ranar da aka ɗaura aure aka kaita gidan mijinta unguwar minannata.

ASIM POV.
Chapter 170 · 0% Book details