← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 173

Sashe 47

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Saboda na san idan kasan ina da HIV ba zaka faɗa min ba, idan har ya tabba ina da HIV Hilal to ta hanya ɗaya na same shi, wato sex kuma wani namiji be taɓa kusantana ba sai kai, a lokacin dana bar ka ya kusance ni ban san komai ba, sai a ɗazu nasa an nemo min Doc Sabo saboda na tabbatar idan har da gaske ina cutar ne, do you know who i try to protect? You and your dirty wife, Asmee told me everything about your bride but very soon gaskiya zata yi halinta, kuma ba zan taɓa yafe mu ku ba, aje ayi gwajin”

Tana kai nan ta raɓa gefensa ta wuce cikin falon. Juyowa yayi ya bita da kallo zuciyarsa na raya masa abubuwa da dama.
Kalamanta basu kama zuciyarsa ba, amman suna ƙoƙarin zaunawa akansa, what he believe shi dai yana da protection ɗin da ba kasafai cutar zata yi saurin kama shi ba, ko baya da protection, he's Doctor ya san cutar bata saurin kama namiji kamar mace, dan namiji ɗaya mai hiv zai kwanta da mace goma to dukkan su sun zama patient living with hiv, wato sun shiga sahun masu dauke da HIV acikin al'umma.

Amman mace ɗaya mai HIV zata kwanta da namiji 10 a rana, abu ne mai sauki namiji 2 ko 3 suka mu da wannan ciwon mai karya garkuwar jiki. Namiji zai iya daukan HIV kawai idan yana da wata kafa a gabansa abunda ya shafi kurji, yanka ko tsaga.

“He's lie”

Ya furta a hankali, yana murza saman goshinsa, zuciyarsa ta kasa yarda da zancen ta, duk da yasan Kalsoom take nufi, dan ita daya auna jininta be nuna haka ba, amman yasan result ɗin zai fito kuma dole gaskiya tayi halinta.

Shigowa yayi cikin falon cikin tunani da sarƙaƙiya, a saman babbar kujera ya zauna, ya dafe kansa, ɗaurewar da kansa yayi shi ya hana shi bachi har safe.
Har yayi sallah asuba ya dawo, be ji motsin Kalsoom ba, ita daya san wani lokacin ma takan riga shi tashi, a falon ya zauna yayi addu'o'insa sannan ya shiga ɗakinta, yadda ya tararda ita kwance rigingim har sai da ya tsorata, wani irin ninshari take kamarmacijin nan mesa na bachi, yayi mata girgizar duniyar nan amman ina, in ma ban da ƙara nauyin bachi babu abunda take.

Da sauri ya fita ya shiga ɗakinsa duba keys amman be ganshi ba, sai a lokacin ya tuna da suna guri motarsa da Rashida ta saka su jiya, da sauri ya fita daga ɗakin ya nufi gurin motar, ashe ma buɗe ta kwana, shiga kawai yayi ya kunna ta ya bar gidan.

Rashida na jin tashin motarsa ta duba agogon ɗakinta, 6:55am ya nuna, bata damu da rashin warewar gari ba ta tashi ba tare data tsaya wanka ba, ta canja tufafin jikinta zuwa atamfa ta ɗauki abaya ta ɗora sama, sannan ta ɗauki handbang ɗinta ta fice daga ɗakin.

Cikin sauri ta shiga motarta tayi mata keys gudun kar Hilal ya dawo, dan yanzu kam sam bata son haɗa ido da shi.
Gidan su Asmee ta nufa, cikin ƙanƙanen lokaci ta isa, haka ta riƙa musu horn har sai da mai gadin ya buɗe mata gate, kusan da motar Alhaji Bashir ya faka motarta, daman tasan yana nan dan yanzu be isa fita ba. Ƙofar falon ta riƙa bugawa tana sallama kamar zata tashi gidan.

Alhaji Bashir ne ya buɗe mata ƙofar yana tambayar lafiya, dan tun da yaji muryarta hankalinsa ya tashi, a tunaninsa ko tazo tayi masa wani abun ne.
Tun daga samansa ta kalle shi har zuwa ƙasan shi, daga shi sai guntun wando, sai da ta kai zuciyarta nesa sannan ta iya ƙirƙiro murmushi ta yaɓa a fuskarta.

“Matar ka na nan?”

“Lafiya kika mana sammako haka?”

“Lafiya ƙalau, sirrin mu ne, saƙon zan bata”

Kamin ya ƙara cewa wani abu har Asmee ta ƙaraso gurin tana tambayar wanene.

“Nice na doko muku sammako, saƙon ki zan baki”

Rashida ta amsa da kanta, tana mata murmushi. Wani kallo Asmee ta watsa ma Alhaji Bashir, irin ya zaka zo daga kai sai guntun wando haka. Sai kawai ya juya ya shige ɗakinsa.
Asmee ta riƙo hannunta suka shigo falon.

“Ke lafiya kika zo haka?”

“Taimakon ki nake nema, idan har baki taimake ni ba, zamu iya rasa ran mu ni da mijina”

“Subhanallahi miya faru?”

“Mijina ya aiko ni zuwa gare ki, maganar da zan faɗa miki sirri ce bana son kowa yaji, ko da kuwa mahaifiyarki ce ko mijin ki”

“Ban taɓa sirri dake ba na faɗawa mahaifiyarta ba, balle kuma mijina taso muje ciki”

Dar ƙarshen gadonta, Asmee ta kai ta suka zauna, sannan ta kalle ta tace

“Faɗa min damuwarki, matuƙar ina da maganinta wallahi zan miki”

“Irin samarin nan nake nema kidnappers”

Asmee ta daki ƙirji.

“Aka yi da wani ko za'a miki?”

“Wani muke son a a ɓoye mana shi, saboda ta hanyar shi ne kaɗai ne, mijina zai cigaba da rayuwa da ni, dan Allah idan kin san inda irin mutanen nan suke ki faɗa min”

“Ni ɗan maye ma miye haɗina da shi balle kuma ɗan kidnapped, Wallahi ban san wani mai wannan aikin ba”

Rashida ta kama hannayenta ta riƙe ta fara kuka.

“Ko cikin ƙawayen ki ba kisan wacca tasan mai irin wannan aikin ba? Dan Allah Asmee ki ceci rai na”

“Bana da ƙawar da zata iya faɗa min sirrinta har haka sai ke, ko da suna da irin waɗannan mutanen ba zan iya sani ba, sai idan gurin wannan Malamin zaki je, sai ya haɗa ki da wani cikin masu zuwa gurinsa, dan yana basu taimako sosai”

“A ina Malamin yake? Dan Allah ba ni addireshinsa”

“Ba a cikin garin nan yake ba, a ɗan dutse yake da kin shiga garin ɗan dutse kika ce Malam mai gobe da nisa ko ƙaramin yaro yasan gidan sa, bari na baki number wayarsa, kamin ki isa zan kirashi na faɗa masa”

“Na gode Allah ya saka miki da alheri, samin number”

Ta faɗa tana miƙa mata wayarta. Sai da Asmee ta saka mata Number sannan tace

“Amman kin san garin kuwa?”

“Karki damu zan tambaya har na isa garin, ai bada motana zan je ba, gidan mu zan bina na aje motar, saboda gudun sa ido”

“Allah yasa a dace, amman ina jin tsoro Rashida”

“Babu abunda zai faru, ba mummunan abun zan aikata ba”

“Dan Allah aro min niƙab ɗin ki da Hijab”

Ba musu Asmee taje ta ɗauko mata ta saka.
A gaggauce ta fice da daga gidan, zuciyarta har wani ɗar-ɗar take, tana ayyana irin rashin mutuncin da zatayi Doc Sabo, lallai yau zata nuna masa ta fishi zama yar duniya, Zagon ƙasan da yayi mata ƙarami ne, yanzu zata masa babban.

Kamar yadda ta tsara, a gidansu ta biya ta aje motar, ko cikin gidan bata shiga ba, balle su gaisa da Momi, tana rufe motar ta fito ta tari Napep ta shiga, ya ɗauki hanyar tasha da ita.

HILAL POV.

Be daɗe ba ya dawo, daman allurai kawai yaje ya ɗauko, yana shiga ɗakin ya haɗa allurar yayi mata, sannan ya ɗauko tawul ya jiƙa shi da ruwa, ya riƙa dafa mata a goshi.
A hankali ta fara motsi tana nishi da miƙa irin ta gaji sosai ɗin nan, hankalinsa ya ɗan kwanta lokacin daya ga ta buɗe idonta, sai ya sakar mata murmushi.

Daker ta unƙura ta tashi zaune, saboda nauyin da jikinta yayi mata.

“Wane irin bachi nayi haka?”

“Magani na saka miki a tea ɗin, tashi kiyi sallah”

Ta ɗan kalli window taga yadda rana ta fara hudowa, sannan ta unƙura da zimmar tashi tsaye, sai Doc ya kai Hannu ya riƙa hannunta.

“I trust you Kalsoom dan Allah kar ki bani kunya”

Wani kallo tayi masa, irin ban gane ba. Sai kawai yayi murmushi yana ƙoƙarin ɓoye feelings ɗinsa.

“Yanzu idan aka ce ina da hiv zaki zauna da ni?”

Dawowa tayi ta zauna, ta kai hannayenta ta riƙa fuskarsa.

“Idan har kana da hiv zan zauna da kai, kuma idan har kana da shi nima nasan ina da shi, so babu dalilin ƙyamar juna”

“What if aka ce ke kike ɗauke da shi ba mu ba?”

Shiru ta ɗan yi tana nazarin tambayoyinsa, anya Doc zai mata irin wannan tambayar haka kawai.

“Idan har ni nake ɗauki da cutar zan nisanta kai na daga gare ku, gudun kar ku kamu da cutar, har sai ta zama aids, domin wannan kwayan cuta HIV (human immunodeficiency virus) bata rayuwa da keu a wajen jiki, saboda haka akan iya kamuwa da ita ta hanyar kissing ko kuma yin anfani da wani abu wanda me dauke da cutar ke anfani da shi, kamar kofin shan ruwa, abun yanke farce, da brush.

Amman da zarar cutar ta kai marhala na karshe ma`ana AIDS (acquired immunodeficiency syndrome) zan cigaba da mu'amala da ku kamar yadda na saba, saboda ba`a kamuwa da ita ta hanyar kissing, cin abici tare da me dauke da ita, amfani da kayayyakin ko abubuwa da me dauke da ita ke anfani da su, kamar kayan sawa, wayan salula, agogo, wanka a swimming pool, zama a kujera, cizon sauro, ma taci comb, tawul, da kuma tafiya, hada hanu, zama,da yin aiki tare da me dauke da cutar, amman ba zan bari ka kusance ni ba, ko da kuwa zaka na shan magani da amfanin da kororon roba, saboda it's risk.

Sai dai kuma ka sani, rayuwata zata tarwatse zan nisanta da ƴaƴanka, duniya zata ƙyamace ni, kuma dole na rabu da kai”

Ta ƙarasa maganar hawaye na bin fuskarta. Ɗan murmushi yayi ya tashi yana ƙoƙarin ɓoye hawayen da suka cika masa ido.

“Intelligent woman, je kiyi sallah zan haɗa ma yara breakfast”

Har ya fice hawaye take, zuciyarta cike da tunanin abunda yasa Doctor yayi mata wannan tambayar.

NAMRA POV.

Ko ta koma gida, ta samu duk sun tafi walimar aure, ta wata maƙociyarsu, da ake yi yau jumma'ah. Mardiya ce kawai a gidan, ta zauna cikin ɗakin ta rafka uban tagumi.
Sallamar da Namra tayi ma sai da ta firgita ta.

“Ke lafiya kike kuwa? Ke kaɗai aka bari a gidan?”
Chapter 47 · 0% Book details