← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 173

Sashe 64

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty tayi murmushi, dan tasan ba gaskiya Namra ta faɗa mata ba.
Hajiya Barau ce ta shigo da Sallama tana faɗin maraba da baƙi.

“Yau garin mu? Ina ji maƙi baƙi”

Anty Amarya tayi dariya ta tashi ta shige ɗakinta. A ɗayan kujerar da Namra take zaune Hajiya Barau ta zauna tana satar kallonta, sai fira suke sama-sama tana tambayar labarin Katsina. Sai nanata mata rashin jindaɗin zuwa ganin Asim da Abbah be barta taje ba.
Sai da dare ya raba sannan tayi mata sallama ta tashi ta fice, zuciyarta cike da gulma.

Bayan fitarta Hajiya Barau, Aisha take labartama Namra wanda zai auri Maryam da Hindatu duk sun zo sun gaida Abbah, kuma sun turo iyayensu, dan tsayar da magana.
Namra ta kallesu tana dariya.

“Eyyyye Amare”

Hindatu ce ta ji kunya har ta rufe ido, Maryam kan dariya ta riƙayi sai ta tashi ta bar falon kasancewar tana waya da angon ne.

“Saura ke”

Namra ta faɗa tana wasa da hannun Aisha, sai Aisha tayi mata wani kallo.

“Ni Anty no da na ss2”

“Ƴar jss ma anyi ma aure balle ss”

Dariya Aisha tayi ta rufe fuskarta. Dammm gaban Namra ya yanke ya faɗi, jin ƙarar tsayawar Mota, zuciyarta na nasalta mata Abbah ne ya dawo, ji take idan ya shigo rufeta zai yi da ruwan masifa. Da sauri ta tashi ta nufi ɗakin Anty Amarya gabanta na ci gaba da faɗuwa.

Tsaye ta tararda Anty Amarya tana gyara tufafin da suke wardrobe ɗinta, kallo ɗaya tayi ma Namra ta ɗauke kai tana murmushi, kamar ta san abunda Namra ta jo ma gudu.

“Ai shine yace aje a zo da ke”

“Amman be ce komai ba?”

“Be ce ba, dan shi kansa yana san kina cikin matsala akwai abunda yake damun ki”

“Babu abunda yake damuna Anty”

Anty ta bar tufafin ta zo ta zauna kusa da Namra

“Farinciki da baƙin ciki abubuwa ne da basa iya ɓoye kan su Namra, jikin ki ma ya nuna haka, dubi kiga yadda kika lalace kika rame kamar ba ke ba, Namra karki ɓoye min damuwarki, ni Mahaifiyar ki ce babu wanda ya dace ya ji matsalar ki sai ni”

“Anty babu abunda yake damu na, kawai na zo na gan ku ne”

“Namra dubi kam ki? Kin ga yadda kika lalace?”

“Ba ni da lafiya ne”

“Me ke damun ki?”

“A nan ƙasan marana iya jin ciwo ne, sai kuma ciwon kai da nake fama da shi, ga zafin jiki”

Duk abubuwan data faɗa gaskiya ne tana jin su sai dai bata jin wata matsala ne ko kuma ciwo, yanzu kuma tayi ma Anty ƙarya ne dan ta ƙyale ta.

“To gobe za muje asibiti likita ya duba ki”

“Allah ya kai mu”

“Amin”

Ta faɗa tana janye blanket ɗin dake saman gadonta.

“Ki kwanta a nan ni part ɗin Abbah ku zan kwana, idan kuma ba zaki iya kwana nan ba ki koma ɗakin Maryam”

“A'a nan zan kwana”

Ta faɗa tana kwantawa saman gadon.
Sai da Anty ta gama gyara komai na ɗakin sannan ta ɗauki wasu abubuwa ta yi ma Namra sai da safe ta fice.

ASIM POV.

Bayan ya gama shan koko Mama ta kalleshi tace

“Yau fa kwana biyu yarinyar nan bata leƙo asibitin nan ba”

“Ai ba zata zo ba”

Ya faɗa yana goge bakinshi

“Saboda me?”

“Faɗa muka yi da ita har ma mareta kuma na faɗa mata maganganu”

“Miya haɗa ku”

“Wani na gani ya rako ta, shine wai nayi magana tace ina zarginta, har da wani wai ta ji maganar da muke ɓoyewa na kuɗin a dashe”

Mama ta riƙe baki.

“Mai kaza aljihu baya jimirin ass, daga magana sai kuma tace ana zarginta? Daman tasan abunda take kenan, ni kai na wallahi naga yarinyar da wani amman ban faɗa ba saboda kar na ɓata muku zama, daman ai na faɗa maka ba da zuciya ɗaya take zaune da kai ba”

“Ai yanzu na gane halinta, dan yi mata magana shine har ta min jawabi wai ba na da komai ta aure na lalata mata rayuwa na rabata da karatun ta”

“Amman Ibrahim ka yi wauta, ai kamata yayi ka sa mata ido ka ga iya gudun ruwanta, kuma yanzu idan ma gidan su ta tafi ai sai tace ka ci amanarta kuma ka zarge ka koreta, kuma kai yanzu ko sallamarka akayi ba itace zata yi hidima da kai ba? Ni fa gida zan koma tun da can ma akwai yara ga sana'a na baro kasan idan ba dole ba babu abunda zai zaunar da nan, tunanin hakan tasa Wallahi ban faɗa maka ba.

Yanzu zuwa kaiwai zata yi ta ɓata maka suna, sannan idan ka rabu da ita a yanzu kana da halin auren wata ne? Ai dole kayi haƙuri da ita har Allah ya nuna maka kaji sauƙi sosai ka warke kayi kuɗi, ka auro wata sannan idan ita rabuwa zaka yi da ita sai ka yi, daman sun saba yaba maka rashin mutunci, kawai ka bata haƙuri kace kayi nadama, ai Allah ma ba zai barta ba ace da aurenka kana zina haba abun ai yayi muni, daman can ba ƴar tarbiya bace shiyasa ta bi mutumen aka riƙa cewa kai ne ka ɗauke ta, har ɗan'uwanta ya fasa aurenta kai aka ƙaƙaba maka ƙaya”

Ajiyar zuciya ya sauke wani irin ɓacin rai me ke ziyartarsa.

“Amman Wallahi Yarinyar nan ta ci amanata sosai”

“Haƙuri dai za kayi, ai babu yadda ban yi ba akan karka aureta amman ka tsaya kai da fata sai ka aureta”

“Nayi tunanin aurenta zai zame min alheri ne shiyasa na yi”

“Ka kirata dai yanzu kace ta dawo, kar taje ta shafa maka kashin kaji gurin matsiyacin uban nan nata mai dukiyar likudi (Kuɗin da ba'a iya ci)”

“Bana jin tana garin nan fa”

“Shiyasa na ce ai ka kirata ba kana da number uwarta ba? Sai ka kirata ka bata haƙuri tun dai lafiya ta samu an kusa sallamar ka, idan ka kira karka nuna musu wani abun ne ya haɗa ku, idan sun ce tace kayi mata wani abu kace kai ƙarya take maka, sai idan ta gaji da auren ka ne, karka yarda ka nuna wani abun ne ya haɗa ku”

Kwantawa yayi saman gadon zuciyarsa cike da baƙinciki abunda Namra ta masa, har yana jin kamar ba zai iya kiranta ba, dan ta ci zalinsa da yawa.

“Baka da wata mafita sai wannan, idan kuma kana ganin akwai wata hanya mai fiddaka sai ka yi”

Ta faɗa tana ɗaukar ledar ƙosai da robar koko ta fice.

RASHIDA POV

Mataki uku ake bi gurin gwajin jinin dan a tabbatar da mutum yana ɗauke da cutar, idan an yi na farko ba a tsallake ba sai ayi na biyu idan shima ba a tsallake ba sai ayi na uku.
Duka an yi ma Rashida kuma results ɗaya ya bada cewar tana ɗauke da cutar, tun a cikin asibitin ta fara kuka, har ta iso gurin motarta. Nadamar taraiya da Alh. Bashir take taraiyarta da shi be haifa mata ɗa mai ido ba, be sata komai ba sai baƙinnciki da da na sani.

Tunanin yadda zata faɗawa Momy take, mutuƙar da faɗa mata gaskiya ta san ita ma gudunta za ta yi, mu'alamarta da kowa zai sauya za a fara mata wani kallo har a gurin aikinta ta san sallamarta za'ayi, duniya zata juya mata baya kowa ya tsangwame ta musamman idan aka ji silar rabuwarta da mijinta, babu kuma wanda zai sake aurenta.
Dan haka ta zaɓi zama da su a haka dan ta rufawa kanta asiri. A cikin mota ta ci kukanta ta gaji sannan ta koma gida, a lokacin yamma yayi sosai duka ƙanenta suna gida. Sai dai bata yarda sun ga fuskarta ba har ta shige ɗaki.

Ta sake ɗasa wani sabon kuka tana jin kamar ta sha wani abu ta mutu.
Sai dai wani ɓangare na zuciyarta na faɗa mata, tana da buƙatar rayuwa saboda Hilal da ƴaƴanta, idan har ta kori Kalsoom daga gidan to Hilal zai iya zama mallakinta har a bada.

A kwana biyu da tace zata yi kamin ta je gurin malamin sai ta kasa, saboda mugun ƙudirinta dan bata son ta samu wata ɗaya a gida bata koma ɗakin mijinta ba.
Hakan yasa washe gari tun da safe ya shirya ba tare da sanin kowa ba ta fita. Napep ta tara ta shiga aka kaita tasha, sai ta ɗauki shatar mota har zuwa garin da Malam yake.

Yau kan bata tsaya bin layi ba, dan tun a hanya ta kira shi ta faɗa masa gata nan zuwa, hakan yasa tana zuwa sai kawai aka mata iso cikin faɗar tasa da yake tsiface-tsifacensa.
Kamin tayi sallama wayarta tayi ringing ko da ta duba sai ta ga Hajiya Basira, wani dogon tsaki taja dan yanzu haushi Alh. Bashir take ji matuƙa.

Guri ta samu ta zauna, ta soma roko masa bayani shi kuma sai kallonta yake yana wasar haƙuransa dake cike da goro.

“Ai na faɗa miki wannan duk mai sauƙi ne, idan ma ba zaki iya ba yanzu nan zamu saka iska su ɗauko mana”

“Amman ya za'ayi su iya ɗaukowa Malam?”

“Ai ko wane ɗan 'adam yana da aljanu, sai sai sun kashi kala-kala, akwai waɗanda zaune kawai suke tare da mutum su basa magana , sune yawanci zaki ga ɗabi'unsu ɗabi'un mutum, sai idan waɗancan aljanun waɗanda ake kira iska sun shiga jikin mutum sune suke nunawa, sai kuma rauhanai su kam ƙarfinsu ma basa iya zama a jikin ɗan'adam.

Irin waɗancan da basa magana ko wane ɗan adam yana da su, duk inda mutum yayi suna tare da shi, musamman idan baya tsare addu'ah, kuma kala-kala ne akwai musulma akwai mushirikai. aljanun da zan tura zai same su ne ya tambaye su inda take aje ƙyalen haitarta ko kuma pad sai su nuna musu su kuma su ɗauko. Abu ɗaya ne zai hana su ɗaukar idan lokacin data jefar tayi bismillah to ba zasu iya ɗauka ba, ko kuma ta ƙona pad ɗin”

“To yanzun nawa zan biya?”

“Zaki bada kuɗin tulu dana jaɓa da kuma na ɗauko shi ƙyalen da za'a haɗa abun da shi”

“Dubu hansin zai isa?”
Chapter 64 · 0% Book details