← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 173

Sashe 72

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta karanci abubuwa da yawa a rayuwar Abdool tun daga yanayinsa na rashin son magana da kuma shisshigi, ba kasafai yake dariya ba, ko murmushi sai idan ta kama ne yake yi.
Sai dai hakan be hana annurin fuskarsa bayyana, ya kan mata kwarjini sosai idan ta kalleshi. Sai dai har yanzu matsala ɗaya ce tayi mata tsaye a rai nasa, rashin sakewa da yake da ita, sannan idan zata shekara tana kuka ba zai iya bata haƙuri ba, sai dai ya tashi ya bata guri. Lokuta da dama ta kam ƙirƙiri kukan ne dan ya tausaya mata amman bata taɓa ganin alamun tausayinta a fuskarsa ba.

Wata ƙila baya da tausayi ne, ko kuma ba shi da kula da lamarin wasu, a yadda ta karanci rayuwarsa kamar ma yana kula ta ne by force.
Abu ɗaya zuwa biyu take ta ƙoƙarin yaƙar zuciyarta akansa, faɗuwar gaban ta take samu idan ta kalleshi, da kuma damuwar da take shiga idan ta wuni bata sashi a ido ba.
Sai dai har yanzu ta kasa, ɗan zuwan nan da yayi katsina ya kwana biyu ya dawo ji take kamar shekara biyu yayi. Tunani take idan ya rabu da ita ya zata kasance? A yanzu kam bata da gurin zuwa tun da Guy son ya mutu, kuma ta san Abdool ba zai barta ta zauna a tare da shi ba, wanda ɗaga ido ma ya kalleta yake masa wuya balle yayi mata masauki a inda yake.

Sai yanzu take nadamar abunda tayi ma Guy son, tabbas bata kyauta ba, dan me zata butulcewa wanda ya ɗauki ɗawainiyarta, dan kawai ta ceci ran wanda kallon ma mai tsada ne?
Lallai tayi kuskure kuma bata bi hanya mai ɓullewa ba. Ya kamata ta yaƙi rayuwarta dan samawa kanta yan ci, taya zata bar Abdool ya tafi haka nan ya barta ta dabon ciwo da kuma na zuciya, bayan duk akansa tayi wannan? Ashe bata cancanci fiye da haka a gareshi ba? Sam bata ga alamar karaminci a tare da shi ba, sam be san darajar ɗan'adam ba, ya kamata ace a iya zaman da tayi yayi ƙoƙarin kawar mata da damuwarta, amman sai nuna mata halin ko'in kula yake mata, sai tambayoyin banza da yake tsare ta da su wani lokacin.

Ta share hawayen idonta ta miƙe tsaye tana shafa kafaɗunta ta nufi window ɗakin tana sauraren zance da zuciyarta take mata.

‘Idan kika na bar Abdool ya kuɓuce min, lallai nayi babbar wauta kuma na yi hasara, taya zan ceci ran mutum kuma ya juya min baya? Ya kamata fa ya nemawa kai na ƴanci haka na yi ta sake har Namra ta ci galaba a kaina, tun da har na butulcewa Guy son dole ne na samu wanda zai maye min gurbinsa.

Sometimes ina abu kamar ba ni ba, zama da Guy son ya kamata ace na ko yi abubuwa da dama, amman sai kasa gazawa nake, a yanzu babu kowa a kusa da ni, ya kamata ace na zama mace. Amman sai kasawa nake, i will fight the spirit ghost of me, i will surely be my own boss, i have to answer my own name’

Ta kai hannayenta ta dafa window, dan ta ji motsin shigowar mutum kuma ta san Abdool ne dan shi kaɗai yake mata haka. Yi tayi kamar bata ji shigowarsa ba ta ƙirƙiri hawaye, ta soma magana cikin sanyin murya kalar tausayi.

“Allah ka zama gata na Allah, bana da kowa sai kai, ya Allah idan mutuwa hutu ne a gareni Allah ka karɓi rai na na huta, Allah na tuba ba zan ƙara ba”

“Ai ba haka ake tubar ma Allah ba”

Ya faɗa yana tsaye jikin ƙofa sanye da ƙananan tufafi, sai faman danna waya yake kamar ba shine yayi maganar ba.
Juyowa tayi ta sauri ta kalleshi like bata ma san yana gurin ba. Be kalleta ba, amman hakan be hana ta ganin ƙwajininsa ba saboda yadda tufafin suka karɓi jikinsa suka masa kyau sosai kamar daman can dansa kawai aka yi tufafin.

Lumshe ido ta yi tana sauraren bugun zuciyarta, hancinta na shaƙar ƙamshin turarensa daya game ɗaki, hawaye ne suka silalo mata.
Yadda zuciyarta take amsa irin kiran da Abdool yake mata ya tabbatar mata da shine mutumen da take mafarki, shine burinta a duniya bata taɓa ɗora idonta akan wani namiji taji abunda take ji akan Abdool ba, ita kwata-ƙwata a rayuwartaa bata taɓa mutumen da take so ba sai Abdool, duk wanda zata so sai dai ta soshi dan kuɗinsa ko kuma da wani abun na dabam.

Amman tana jin Abdool ko bashi da komai zata iya zama da shi, ballantana ma ya haɗa komai da ake so ga namiji, a rayuwarta bata taɓa ganin kyakkyawan mutum kamar Abdool ba, sam be yi kama da ƴan nigeria ba. Ga tarin dukiya da kowa wacce mace take so a gurin Namiji, ga shi kuma ɗan Sarki wata rana zai iya zama sarkin gaba ɗaya.

“Da ace hawaye za su miki magani da sun miki tuni, kuma tun lokacin da kika saka ƙafarki kika bar gidan ku ya kamata ace kin yi kuka kin dawo sai yanzu? Lokacin da nadamar ki bata da amfani, do you know what? I don't believe in fiction, idan har da gaske kin yi nadama ya kamata a ce yanzu kin kama hanyar gidan iyayenki”

Yayi mata maganar ne from the bottom of his heart, like he's seriously saying what is inside him, daman can shi ba mutum ne mai tausayin mace ba, indai zaki shekara kina kuka Abdool kam ko a jikinsa, wata ƙila dan ba shi da lokacin matan ne, ko kuma dan har yanzu idanuwansa basu ga zubar hawayen wacce zuciya take muradi ba. Sannan shi sam baya ganin tausayin ko kuma mutucin yarinyar da ta bar gaban iyayenta, da ma ace korarta suka yi ba ita ta gudu ba.

Babu yadda Amira za ta yi da shi duk da kalamansa sun taɓa zuciyarta, ta daɗe da karantar be iya lafazi ba, kuma babu ruwansa da tauna magana idan zai faɗa.
Sai dai hakan be sa taji haushinsa ba ko kuma ta ji ta tsane shi, sai kusanci da shi take so, dan ta koya masa yadda zai zauna da ita.

“Amman idan na koma da wane ido zan kallesu?me zan ce musu? Ya kake tunanin duniya zata kalle ni?”

“Tun kamin ki baro gidan ku ya kamata ki yi ma kan ki wannan tambayar, idan kika gudu me zaki ce musu? Da wane ido zaki kallesu? Ya kuma duniya zata kalle ki? There's no point of crying dan ke kika sai da mutunci da hannu ki”

Wani irin kallo ta watsa masa da jajayen idanuwanta, sai dai kwarjininsa be barta ta masa kallon daƙiƙa biyar ba ta kau da idon, cikin kakkausan lafazi ta ce .

“Amman mi yasa baka bar ni na mutu ba? So that na huta da rayuwar gaba ɗaya?”

Ya gyara tsayuwarsa ya ɗaga daga jikin ƙofar da yake tsaye yana sa hannayensa aljihu.

“I'm sorry I'm not harassing you I'm just telling the truth”

Har ya juya sai kuma ya juyo ya kalleta.

“Park your things, Doc zai baki sallama, around 10am driver zai kai ki gida”

Be tsaya jiran abunda zata ce ba yasa kai ya fice. Rasss! Rasss! Rasss! Gabanya ya yanke ya faɗi.

“Wane gida? Gidan su ko gidan mu? Ko kuma wani gidan na dabam?”

Ta tambayi kanta, dik sanyin ɗaki be hana gumi zubo mata ba. Babu inda ya fi tsaya mata a rai a kamar gidan su. Wayyo Allah ji take kamar mutuwa za tayi idan har aka maida ita gidan su, ita kanta tana son zuwa gidan amman bata iya iyawa, bata san dalili ba.
Ta kasa sukuni sai safa da marwa take har Doc ya shigo ɗakin, bata ga alamun rahama a fuskarsa ba balle ta tambaye ko yasan inda Abdool zai kai ta, kai ba zata iya tambayarsa ba kar Abdool ya zargi wani abu.

Sai kawai taja bakinta tayi shiru, sai dai tasha alwashin indai gidansu ne ba zata taɓa zuwa ba sai dai komai zai faru ya faru.
Sai da likitan yayi mata binciken ƙwa-ƙwaf sannan ya rubuta takardar sallama ya miƙa mata, ya fice. Kamar yadda Abdool yace 10 na bugawa sai ga wani yazo cikin uniform ɗin soja yace mata ta fito suje. Nan ma sai da gabanta ya faɗi.

“Ina... za...mu....je?”

“Katsina yace a kai ki, gidan Mahaifiyarsa”

Ta lumshe ido na wasu ƴan daƙiƙu, wani irin daɗi ya ziyarci zuciyarta har ta samu maida yawun daya tsaya mata a maƙoshi.
Bata buƙatar ɗaukar komai, daman can duk kayan da tayi amfani da su shine ya kawo mata, dan ita ko waya bata da a hannunta balle wani kayan kuma. Farincikin dake zuciyarta ya kasa ɓoyuwa har sai da ya nuna a fuskarta.

Ko da ta fito Abdool na tsaye kusa da motar, da alama ita yake jira, sai dai kwata-kwata hankalinsa baya gurinta yana wani wajen dabam.
Ɗaya daga cikin boys ɗin sa ne ya buɗe mata mota ta shiga, idonta na kan Abdool.
Yayi kusan minti biyar yana magana da mutanen biyu sannan ya suka shiga motar da take sai kuma wata mota dake gabansu cike da sojoji suka kama. Shi kuma ya juya ya koma cikin.

Juyawa tayi ta cikin motar tana kallonsa. Tana ayyanawa kanta zama abokiyar rayuwarsa, dan wannan karamcin kawai da yayi mata ya isa yasa tayi sha'awar hakan. Mutum me daraja da ƙima kamar wannan? What if ta zama matarsa?

KALSOOM POV.
Chapter 72 · 0% Book details