← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 173

Sashe 11

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Good yanzu kira ɗaya daga cikin masu tsaronta ya duba mana idan bata farka ba”

A take Uzair ya ciro wayarsa. Najeeb kuma ya nufi gurin mai gadin.
Ɗaya daga cikin yaran ne suka shaida masa har yanzu bata farka ba. Shi kuma ya nufi Najeeb ɗin ya faɗa masa.
Sai da Najeeb ya gama tsarama mai gadi yadda zai yi, sannan ya juyo gurin Uzair.

“Good yanzu kasa su ɗauko ta, su saka ta a mota na, sai ka shiga taka motar ka nuna mana daidai inda ka ɗauke ta”

“Baba Audu zaka iya ko?”

“Ƙwarai Zan iya ranka ya daɗe ai wannan abu ne mai sauki, kuma taimako ne”

Baba Audu ya faɗa da kansa. Sai Najeeb yayi murmushi.

“Zamu baka dubu ɗari idan aiki yayi kyau, zamu baka wasu dubu ɗari na rufar sirri, ka tabbata dai ba'a samu matsala ba”

Har ƙasa Baba Audu ya risina yana godiya baki har kunne.

“Allah Ubangiji ya saka da alheri, ai ni ko baka bani komai ba, zan iya maka fiye da wannan”

Najeeb ya nuna masa Mota.

“Kaga Mota can je ka shiga gidan gaban”

Sai kuma ya kalli Uzair

“A fito da ita yanzu”

Cikin sauri Uzair ya nufi gurin, be daɗe ba ya fito, wani namiji na ɗauke da ita. Ita kuma ta langwaɓe kamar wacce ta mutu.
Najeeb da kansa ya bude Motar suka saka ta gidan baya. Sannan Najeeb ya shiga driver seat, Baba Audu ya shiga front seat, Uzair kuma ya shiga Motarsa, sai ya shiga gabansu dan nuna musu hanya.

Cikin mintuna suka isa gurin. Can nesa da gurin suka faka, sai Najeeb ya buɗe motar ya fito da ita. Uzair ya nuna dai-dai inda ya ɗauketa sai Najeeb ya ajeta a gurin, yasa car key ɗinsa ya ɓarke mata Hijabi, ya yagashi, ya barƙa rigar afamfar dake jikinta, har rabin breast ɗinta ya fito.
Sanna ya ɗago ya kalli Uzair

“Ta fito da waya?”

“Yes ga wayar ta nan hannu na”

Ya faɗa yana ƙoƙarin cirota daga aljihunsa. Najeeb ya miƙa masa hannu

“Wani wayar zan taka ta da mota, kuma ka bani layin da ka kira ta da shi”

“Why?”

Najeeb yayi masa wani kallo

“Haba Uzair ya kake abu kamar ba wayaye ba? Baka san za'a iya amfanin da wayar a gano sawon hannunka ba? Za a iya gano ka idan kana amfani da layi, kuma yanzu ai amfanin layin ya ƙare”

Kamin Uzair yayi magana, kiran Amira ya shigo wayarsa. Da sauri Najeeb ya tambaya.

“Who's calling?”

“Her Best friend”

“Did she know?”

“Yes tare da ita muka haɗa komai”

“Karka yi picking call ɗin nan it risk, let's go kar wani ya gan mu”

“Da wahala wani ya gan mu, baka ga yanayin gurin ba? Ko da rana ba a cika wucewa ba balle yanzu pass 11 fa”

Najeeb yayi murmushi, irin na har yau baka waye ba Uzair. Sai kuma ya kalli Baba Audu

“Da ka daina hango hasken Motar mu, zaka fara ihun”

“Toh ranka ya daɗe”

Cikin sauri suka nufi motocin su, Najeeb sai wage-wage yake kamar mai neman wani.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa09.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

*PAGE - 9*

A lokacin da Baba Audu ya daina hango su, sai ya buɗe dukanin muryarsa ya kwarara uban ihu yana neman taimako.

“Wayyo Allah jama'ah a taimaka mana, a ceto rai, jama'ah ku kawo agaji”

A yanayin gurin, ba kowa bane zai iya saurin fita, saboda yanayi na tsoro da ake ciki, gashi ta bayan layin unguwar ne ba mutane sosai.
Cikin ƙarfi hali da bugawar zuciya, Baba Audu yake ta kwarara ihun yana wage-wagen jiran wanda zai fito.
Tsinta-tsinta aka fara fitowa ana nufar gurinsa, sai tambayarsa suke lafiya. A nan ya soma ƙirƙiro hawayen ƙarfin hali yana faɗa musu abunda Najeeb ya tsara masa.

“Wallahi wasu mutane yanzu suka jefo da wannan yarinyar daga mota, kuma suka zo suna ƙoƙarin taɓa mata mutunci”

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Shine abunda kowa yake faɗa, dan makamacin wannan be taɓa faruwa a unguwar ba. Wani dattijo ya kai hannu ya gyara mata Hijabinta, ta yadda zai suturta mata breast ɗinta dake buɗe.
Waɗanda suka santa sun gane ta, sai dai kowa mamaki yake, yana tunanin suye ne suka mata haka? kuma a ina ta haɗu da su haka.
Wani saurayi ne ya kawo ruwa aka zuba mata, amman shiru bata farka ba, haka akayi ta zuba mata ruwan but still bata motsi. Anan mutane suka ce a ɗauke ta a kaita gidansu

*** *** *** ***
Babu irin kiran wayar da Anty Amarya bata yi ma Namra ba, tun tana ringing har aka kai ga kashe wayar.
A lokacin hankalinta ya tashi sosai, ita da Maryam har Aisha da Hindatu sai da hankalinsu ya tashi.
A take Anty Amarya ta fara kuka, tana tunanin abunda ze samu ƴarta, kuma tana tsoron kar Abbah yaji, sai duk tabi ta rikice ita da Maryam. Aisha da Hindatu suka ce zasu je bayan layi su duba ko Allah yasa zasu same ta.

Anty Amarya ta share hawayenta.

“Babu inda zaku je cikin daren nan, bayan layi da yake da duhu idan wani abun ya same ku fa, ban san abunda yasa Namra ta raina ni ba, ta ya zata saka ƙafa ta fita ba tare data faɗa min ba? Duk abunda ya same ta ita tajawa kanta”

Maryam ta ɓata fuska.

“Gaskiya Anty Namra bata kyauta ba, amman da kin bari munje mun duba ko zamu ganta”

“Babu inda za ku je, idan Abbah ku ya gani kuce masa me?”

“Abbah ba ze gani ba, tun da yana part ɗinsa, kuma ba daɗewa zamu yi ba, dubowa kawai zamu yi mu dawo”

“Babu inda za ku je yanzu goma ta wuce, inda har kuna jin magana ta, toh karku je ko ina nemanta, ai ita ta kai kanta, ina zaune falo tabi ta ƙofar kicin ta fita, ba dai-dai bane tasa ƙafa ta fita ba tare da sani ba”

Anty Amarya na gama faɗar hakan, ta tashi ta nufi falo tana hawaye. Yanzu kan babu abun ɓoyewa dole ta faɗa ma ƙannenta abunda yake faruwa, su kansu basu jidaɗi ba, sai laifin Namra suke gani, wai taya zatayi haka kamar wata ƙaramar yarinya.

Haka suka yi zaune jugum, kowa sai addu'ah yake, babu irin roƙon da Mama Zainab bata yi ma Anty Amarya ba akan ta bari suje su dubota, amman ta hana.
Har kusan shaɗaya babu wani labari, sai shabiyu saura kwata, suka soma jin hayaniya a habarar gidan, sai doko musu sallama ake da muryar maza.

Wani irin faɗuwa gaban Anty Amarya yayi, har sai da ta dafa zuciyarta ta lumshe ido. Mama Zainab da Hajiya Raliya ne suka riga fita, Aisha da Hindatu suka rufa musu baya.
Maryam kuma ta tsaya kusa da mahaifiyarta ganin halin da take ciki. Cikin ƙarfin hali Anty Amarya ta tashi, Maryam ta ɗauko mata hijabinta ta saka sannan suka nufi ƙofar fita.

Ko da suka fito har Hajiya Barau ta isa gurin, Abbah kuma ya fito daga part ɗinsa ya nufi gurin da mutane suke tsaye, riƙe da Hannun jikan Imam jikan Hajiya, da alama shi ya je ya faɗawa Abbah.
Cike da kasala Anty Amarya ta ƙasara gurin ita da Maryam. Tana ganin halin da Namra take cike gabanta ya ƙara faɗuwa, a take kasala ta sauki mata. A nan Maryam ta fara kuka ganin Namra kwance kamar matatta ga Hijabinta a yage.
Abbah ya kalli mutanen cikin tashin hankali.

“Miya faru? Ina kuka ɗauko Khadija?”

Kowa sai ya nuna Baba Audu yana faɗin shi ne san abunda ya faru, tun da yace musu a gaban idonsa akayi. Tun kamin Abbah ya tambaye shi ya shiga yi masa bayani.

“Na fito ne gidan ƙanena can baya, sai na hango wata ƙatuwar mota mai kamar ta ƴan makaranta ta tsaya, a gefen gurin sai aka jefo wannan yarinyar , sai kuma suka fito su huɗu suna ƙoƙarin cire mata tufafi, shine fa sai na fara musu ihu suka gudu suka shige motar, bayan sun wuce ne, na ƙarasa inda take ina neman taimakon jama'ah ganin halin da take ciki, da jama'ah suka fito sai suka ce sun santa a nan gidan take, dan ni ba ɗan unguwar nan ba ne ban san ta ba Wallahi”

Wani irin abu ne ya taso ma Abbah, tun daga kan ɗan yatsan ƙafarsa zuwa ƙasan zuciyarsa, a take kalar idanunsa suka canja, wata jijiyar ɓacin rai ta taso masa, ta ratsa gefen wuyansa zuwa kansa, a hankaɗe ya kalli Anty Amarya.

“Yaushe ta fita?”

“Wallahi... Ban ...san ...ta fita ..ba ...”

Anty Amarya ta amsa murya na rawa. Abbah ya katsa mata tsawa

“Baki san ta fita ba kamar ya? Taya zata fita ba tare da kin sani ba?”

Kamin Anty Amarya ta ƙara bashi amsa, sai mama Zainab ta yi ɓaranɓarama, a ƙoƙarin kare Anty Amarya.

“Wallahi duk muna falo ta fita, babu wanda ya san da ita, ta hanyar kitchen ta bi, wai zata yi sallama da saurayinta”

Anty Amarya jin tayi kamar ta matse bakin Mama Zainab amman ba dama.

“Junaidu!”

Hajiya Barau ta ƙwalawa mai gadin kira. Da sauri ya amsa dan yana kusa da ita, yana kallon Namra dake kwance cike da mamaki.

“Ya aka yi Namra ta fita? Ba dokar gidan nan bace idan anyi magariba ba wanda ze fita?”

Jikinsa ya hau ɓari, yana ƙoƙarin ƙare kansa.

“Wallahi sai da na yi mata magana, sai tace wai saƙo zata karɓo nan kusa, ni sam na manta ma da bata dawo ba sai yanzu”

Abbah ya kalli Baba Audu

“Kasan mutanen ne? Zaka iya gane su?”

Baba Audu ya yi shiru kamar mai nazari.

“Gaskiya ba zan iya gane su ba, amman dai na ji suna faɗin Aasimu ko Ƙasimu, suna ce masa ya yi sauri su tafi”

“Asim..!”

Abbah ya amsa da ƙarfi. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya, ya kalli mutanen.

“Na gode sosai, Allah ya saka ma kowa da alheri”

Sai da suka masa Allah ya kyauta, sannan suka fita kowa bakinsa ƙunce da magana, wasu kuma mamakin fitar da ta yi suke, ga kuma ɓarin zancen da Mama Zainab ta yi.

Maryam ta nufe ta tana faɗin
Chapter 11 · 0% Book details