Sashe 35
Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Namra suka tarar zaune a kujerar dake ɗakin tana bawa Asim tea. Ba laifi alamun sauƙi ya bayyana a yanayinsa, wanda a ada ma idan ya ɗaga ido sai yayi saurin rufewa yanzu kuma gashi har yana shan tea.
Farinciki gurin Mama ba'a magana, sai ta zauna saman gadon kusa da shi, tana murmushi
“Mashallah Ibrahim, Allah ya ƙara maka lafiya”
Ɗan murmushi yayi kaɗan irin yana jin zafin ciwon nan yana ƙarfin hali. Mama ta kalli Namra
“Yaushe ya farka?”
“Tun da asuba, har likita ya duba shi ya bada wata takardar ta gani yace allura ce za a masa guda bakwai, kullum ɗaya saboda jinin daya bugu a kansa”
“Allah yasa dai babu tsada”
“ Pharmacy asibiti sun ce duk ɗaya, dubu tara ne, ga kuma maganin da suka rubuta shima sai yaci dubu biyar”
Mama ta rafka uban tagumi.
“Tau ai fa kaji matsalar babbar asibiti, yanzu ina za a samu wannan kuɗin kuma? O Allah”
Namra ta saci kallon Mardiya da idonta ke kansu, tace
“Mardiya kuje waje ke da Hajara”
Tashi tayi ta fice ita da Hajarar. Sannan Namra ta kalli Mama tace
“Akwai kuɗin da zan siya da su, amman da abinci naso mu siya dan abincin mu ya ƙare”
Kai Mama ta girgiza
“Wai Namra iyayenki haka zasu zura miki ido, babu wani taimako? Naga dai suna da shi, amman ko ɗan abincin nan ai sa taimaka muku da shi, amman ace kayi ta sai de sai de anya haka yayi?”
Wani kallo Namra tayi mata.
“Iyayena sun yi iya ƙoƙarinsu duk kan abuɓda zasu min a yanzu kyautatawa ce, amman ba dole ba, balle kuma mijina ”
“Haka ne, daman can ai ba son auren su suke ba, sun fi son ku yi ta wahala kamar ba ƴarsu ba”
“Mama ya kamata ki kina tauna magana kamin furta ta, iyayena, iyayena kuma sun min komai tun da har suka bar ni na auri Asim”
“Amman idan ga mutunci ai da ke da shi kun zama ɗaya, ki duba kiga ko dubiya har yanzu babu wanda ya sake leƙowa daga danginku, Kuma wallahi inda wani guri ne dole ne su ɗauki nauyi naganinsa tun da da motar gidan yayi haɗari, amman sun ɗauki ƙiyayyar duniya sun ɗora masa akan auren ki kamar wanda ya kashe musu wani abu”
Zuciyar Namra ta kawo sosai, a take idonta ya cika da ƙwalla.
“Asim yayi haɗari da motar gidan mu saboda an rubuto zai yi haɗarin, wai Mama mi na tare miki ne? Miyasa kike abu kamar wanda bata yarda da ƙaddara ba, miyasa zaki ɗauki laifin haɗarin motar da Asim yayi ki ɗora min?
Kin manta da ni matarsa ce wace mace ce zata so mijinta ya kasance a halin da Asim yake? Duk abunda na masa baki gani ba? Mahaifiyarsa ce ke amman sisi ban tambaye ki na siyer da kayan ɗakina na biya masa kuɗin magani, amman duk wannan be isa a goge laifina ba? Kin kira aure na da ƙaddara kina tunanin hakan yayi min daɗi? Me kike son na masa ne? Rai na kike son na cire na bashi ko kuma ciwon kike son na maida jikina?
Haba Mama ku bar ni na ɗaya mana, da matsalar iyayena zan ji ko da ta mijina, ko kuma wanda kike ƙoƙarin sani, ke uwace wata maganar be kamata tana fitowa daga bakin ki”
Mama ta cika da mamakin jin furucin da Namra tayi mata, wani dogon numfashi taja ta sauke tana taɓe baki.
“Kin goge ladarki Namra, daman kin masa duk abunda kika masa ne dan ki faɗa kin masa, ai kaji tsiyar taraiya da mai arziki, so kike ace ɗana ya cinye miki komai ko? A ƙaƙaba masa, kamar yadda aka masa na satar ki ko? Ni da zuciya ɗaya na bar ɗana ya aure ki ba da wata manufar ba”
Ta ƙarasa maganar da kuka har da hawaye. Uffan Namra bata ƙara cewa ba, sai kawai ta ɗauki jakarta ta fice.
Sai da ta biya gurin da su Mardiya suke ta karɓi keys sai Mardiya ta biyo ta suka yi gida tare. Tun a Napep Namra ta soma yi ma Mardiya faɗa.
“Dan me zaki faɗawa Mama na siyar da gado na ? Ina ruwanki da rayuwata tana mijina? Jaka zaki tallata ni a unguwa? Ko akai na farau? Abunda ya shafi mijina da mahaifiyata nawa ne babu ruwanki a ciki, dan haka ki iya bakin ki”
Ta ƙarasa dai-dai lokacin da mai Napep ɗin ya sauke su ƙofar gida, Namra ta miƙa masa kuɗinsa ta nufi gate ɗin ta buɗe ta wuce cikin gidan a fusace. Mardiya ta rufa mata bayana tana ƙoƙarin wanke kanta.
_______________________________________
Yau yayi kaɗan ko? Bana son na bar ku babu post ne. Idan Allah ya bani iko zan yi dogon page gobe.
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*
Website
www.khadeejacandy.com.ng
*PAGE - 27*
NOT EDITED ⚠️
Namra na saka ƙafarta cikin falon Mardiya ta saka nata, ta zauna kusa da Namra ta marairaice tana ta ƙoƙarin kare kanta.
“Dan Allah ki tsaya ki saurare ni, Wallahi Dillaliya ce ta shigo lokacin da zamu fita da su, nace mata baki nan shine tace ga cikon kuɗin ki kuma tana son ta ɗauki gadon, shiyasa har ta ji, idan ma baki yarda ba zan iya zuwa na kira Dillaliyar ki tambaye ta ki ji”
Namra ta sauke ajiyar zuciya tana son danne fushinta.
“Na ɗauka ke kika faɗa, da nace baki min amana ba”
“Haba Namra nikam miye ruwana da sha'aninku tsakanin ki da miji da yan'uwansa babu ruwana a ciki. Dama tazo nan babu irin maganar da bata yi ba a kan iyayenki amman uffan ban ce mata ba, ke ma kuma ban faɗa miki ba”
Wani ɗogon numfashi Namra taja ta sauke, tayi shiru kamar mai nazari.
Mardiya ta tashi tana kaɗe jiki.
“Ni kam na tafi sai wata rana kuma”
Namra ta yi saurin riƙe mata hijabi.
“Haba Mardiya ki yi haƙuri mana, rashin fahimta ne kin ga ai ko kece ba zaki jidaɗi ba”
“Haka ne amman kin ga zama da rashin aminta da mutum ba daɗi, matsalar mijinki ma kawai ta isashe ki”
“Shine abunda ya fi damu na, yanzu ma wani maganin suka rubuta min, ina ganin sarƙa na zan siyar na haɗa da kuɗin da suke hannun dillaliya na siya masa maganin abunda ya rage mu siye abincin”
Gaban Mardiya yayi dakan uku-uku jin Namra ta ambaci zancen sarƙarta, take taji natsuwar dake tare da ita ta tafi. Sai ta tashi tana karkaɗe jiki
“Bari naje gida, daga can zan yi ma dillaliya magana nace kin dawo”
“Yauwa dan Allah ki faɗa mata, ai kin san inda ake sai da zinari ko?”
“Gaskiya ban sani ba, amman zan bincika miki”
“Yauwa na gode kin ci abinci ai ko?”
“Eh na ci, sai an jima”
Kamar walƙiya haka ta fice daga falon, zuciyarta kamar zata fito daga ƙirjinta saboda tsoron kar Namra ta nemi sarƙar ta, bata gani ba, kuma tasan ita kaɗai zata zarga tun da ita ta saba shigar mata ɗaki.
Bayan fitar Mardiya Namra ta tashi a gajiye ta shiga ɗakinta, tufafin jikinta ta cire ta ɗauki tawul ta ɗaura ta shiga wanka.
Ta daɗe tana wankan sannan ta fito cike da jindaɗin jikinta, ta buɗe lalulayen ɗakin kasancewar babu nepa, ta kwanta saman godon ba tare data saka wasu tufafin ba, saboda gajiya da kuma bachin dake cikin idonta. Nan da nan bachi yayi gaba da ita.
ANTY AMARYA POV.
“Nifa na damu da rashin kiran Namra, idan an kira ba a samu ita kuma bata kira, Allah dai yasa lafiya”
“Lafiya ƙalau Inshallah, kin san halin da Asim yake maybe ta siyar da wayar”
Cewar Hindatu tana dannar wayar dake hannunta.
“Amman kin san ba mu kyauta ba? Rashin sake zuwa duba shi da kuma kira a ji ya jikinsa? Ko a kan Namra ya kamata mu yi haka”
“Toh ai matsalan ba a samun wayarta”
“Ki je gidan su Asim gobe ko anjima ki karɓo min line sa, ko shi mu kira sai muyi magana da Namra ɗin”
“Amman ba Mamarsa taje Katsina ba?”
“Eh amman ai ba a rasa mai number ba a gidan”
“Zan je anjima inshallah”
Maryam dai na jinsu amman uffan bata ce ba, sai karatun ta take.
NAMRA POV.
Da ƙarfi taji tsawar mota a harabar gidan. Da gudu ta fito daga kitchen ta nufi gurin da motar take tsaye. Ga mamakinta sai ta ga Asim ya fito daga motar jikinsa ƙam kamar be taɓa ciwo ba, wani irin tsale ta daka ta dire saboda murna, tana shirin gudu izuwa gareshi sai kawai wasu karnuka suka taso ta bayansa suka yi cikinta suna ƙoƙarin cizonta.
Hakan be hana ta gudu da isa gare shi ba, ta rumgume shi, sai kawai taji ya ƙyalƙyale da dariya ya luma mata wata ƙatuwar wuƙa dake hannunsa. Wani irin ihu ta saka ihun da bata san har a fili tana yinsa ba. Kirgigi ta farka daga bachin tana wani irin haƙi da ambatar sunan mahallincinta.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, A'uzubillahi”
Har yanzu jikinta rawa yake, kanta sai rasawa yake, saboda mummunan mafarkin da tayi. Ta daɗe a haka sannan ta yi unƙurin tashi tana kallon agogon ɗakinta. Har biyu da rabi ta gota tana bachi bata yi Sallah.
Da sauri ta nufi banɗakin dan yin alwala, kamin ta ƙarasa ta tsaya cak, saboda abunda ta ji yana zubo mata daga ƙasanta zuwa ƙafafunta, dubarwa da zata yi sai ta ga jini sare-sare yana zuba kamar an tunkuɗo shi.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un”
Shi ne abunda ta furta da ƙarfi tana mai jin tsoron halin da take ciki, kamin ta ankaro ta soma jin wani irin mugun ciwon mara marar misaltuwa, a gurin ta zube tada dafe ƙasan marar nata dake mata wani irin mugun zugi.
Mulmula ta fara yi tana kuka, tawul ɗin dake jikinta ya kwance amman bata kula ba sai neman ceto take gashi gidan babu kowa.