← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 173

Sashe 102

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lamido ne yake ta nuna hanyar da za abi har aka isa gidansu. Ganin masu jajayen kaya sun fito tare da Lamido yasa mutane suka fara taruwa ana kallonsu, dan kowa yasan daga gidan sarki ne. Masu boko suka karantar number motar, yara kuma suka shiga cikin gidan da sauri suka sanar da Neine cewar ga wasu nan sun zo da Lamido ciki motar sarki an ji masa ciwo. Ba shiri suka fito daga gidan gaba ɗayasu suka nufo Lamido. Bugun gabansa ne ya ƙaru ganin Namra a cikin mutanen dake fitowa daga cikin gidan, ita ma hankalinta a tashe yake kamar wani nata ne aka jima ciwon. Sai da suka saka shi cikin gidan, sannan ɗaya daga cikin dogaran ya zo ya buɗewa Yarima mota ya fito.

Ƙarƙashin itacen mangoro suka shimfiɗe Lamido, uwani ta ɗauko matashin kai a ka aza masa. Kusa da shi Namra ta zauna tana ta kallon kansa tare da yi masa sannu, idonta cike da ƙwalla, har cikin jikinta take jin ciwon Lamido.
    Shigowar Yarima Abdool yasa Namra ta ɗago kai ta kalli ƙofa, karam idonta ciki cikin nasa, sai yayi saurin kawar da nasa idon, ya cigaba da takawa kamar wani ɗawuisu, ya tunkaro tsakar gidan, dogarai na take masa baya. Ita kam kallonsa take da kyau dan tantance wanda ta gani ɗin, da gaske shi ɗin ne ko kuma waninsa mai kama da shi? Daman Ɗan sarki ne? Anya shi ke wacan kuwa na Katsina wanda yayi mata kyautar gida ko dai twins ne?

Har ya ƙaraso gurin idonta na kansa, shi kuma ya ƙi ya kalleta sai kallon ƙyakkyami yake ma gidan abunda ba halinsa ba. Da sauri Uwani ta ɗauko wani Babban tabarma ta shimfiɗa masa, jikinta har rawa yake. Baya cikin kayan sarauta hasalima farar shaddace jikinsa, wanda ta haska kyaunsa. amman hakan be hana ƙwarjinsa fita ba, dan du Ƴaƴan sarakuna da ban suke a duk inda suke.

Be zauna ba, kuma be cewa kowa ko ƙala ba har sai da Neina da sauran matan unguwar suka miƙa masa gaisuwa, nan ma hannu ya ɗaga musu sai dogaran suke amsa musu da sunan Yarima ya amsa, kuma ya gaishe ku.

“Allah ya sauwaƙe”

Shine kawai abunda ya furta, shi kuma iyakar laɓɓansa Sadauki ne ya maimaita dan suji. Sannan ya ciro cak ya miƙawa Sadauki shi kuma ya karɓa ya miƙa wa Neina dan ita yake zaton ma mahaifiyarsa ce.

“Godiya take Yarima”

Hannu biyu tasa ta karɓa jikinta na rawa, badan tasan ko takardar me ne ba. Kuma tsoro ya hana ta tambayar ko minenen.

Juyawa yayi ya sai dogoran suka take masa baya. Tunani biyu ne a zuciyarsa miya kawo Namra gidan ita da take Katsina? Mine alaƙarta da ƴan gidan? Ko kuma ƴar'uwarta ce? Mijin ta ne wacan to wannan fa? Ko dai yayanta ne? To ai ba suyi kama ba. Shine abunda yake ta tunani har ya doshi motar.

_Miyasa ba zaka iya yaƙin zuciyarka ba? Dan me zaka nace abunda ba halalinka ba? Idan ita ce sai me miye ruwanka da ita?_

Iskar bakinsa ya furzar yana sauraren bugun zuciyarsa, da kuma tunanin yadda ƙaddara take kawo masa mai kamaninta.

“Ya Rahman”

Ya furta yayinda yake ƙoƙarin zama cikin motar. Wannan karon hankalinsa ba akan jarida yake ba, gaba ɗaya ya tattara ya koma can gurin Namra daya gani, idanuwansa suna kan titi ruhinsa kuma yana can gurin motar da ba tasa ba.

Daga nan basu tsaya ko ina ba sai masaukinsa, kamin ya fita motar sai da ya duba agogon hannunsa ɗaya saura ya gani, hakan ya sashi ɗan hanzarin fita yana magana da sadauki.

“A kira Mai Martaba a sanar masa mun iso, wayana a kashe yake zan ɗan kwanta na huta”

“Allah ya taimaki Yarima yadda ka ce haka za'ayi”

Gaba ya wuce suka buɗe masa ƙofa, duk jin yake rayuwarsa babu daɗi, kuma be san dalili ba.

HILAL POV.

Jikin ƙofar ɗakin ya jingina yana kallonta da sauraren kukan da take rerawa. Rumgume hannayensa yayi yana tunanin ta ina zai fara. Ita kam bata ma san da shigowarsa ba, ta maida gaba gabas sai rusar kuka take.
Sauke hannayensa yayi ya nufi inta take zaune ya zauna gabanta yana kallon idonta.

“Yanzu abinda kike min adalci ne? Ki zauna kina kuka kin san yadda nake ji kuwa? Na rasa ɗa na ke kuma kin zauna a nan ki na kuka”

Ɗagowa tayi ta kalleshi

“Kai ɗa ka rasa, kuma kana da wasu, ni kuma miji na rasa”

“Ba ki rasa ni, kin san abinda na ke so da ke?”

Ta girgiza nasa kai.

“Zaki zauna nan for a while as zaman idda kamar yadda addini ya ce, ni zan je gida na faɗawa su Momi komai, wannan fushi na Hajiya na kwana biyu ne na nasan nan gaba kaɗan zata sauka, dole ne Hajiya tayi fushi Kalsoom saboda bata fahimce kamar yadda ni na fahimta ba”

“Ta yarda na zauna ne?”

“Bana jin zata hana, abunda na ke so dake ki yi mata uzuri kuma ki bata lokaci. Zan ɗauke ki muje gida anjima a can zan maida aure na”

Kai kawai ta ɗaga masa ta share hawayenta. Har ya mike tsaye sai kuma ya juyo ya kalleta ya ce

“Hajiya ta ce za a maida zaman makoki a can”

Nan ma kai ta ɗaga masa. Sai ya juya ya fice zuciyarsa babu daɗi. Zaune ya hango Hajiya a falon tana kallon ƙofar ɗakin Kalsoom daya fito fuskarta babu annuri. Kai ya girgiza cikin yanayin damuwa ya ƙaraso kusa da ita ya dafa kujera yana kallonta.

“Hajiya karki zama cikin iri surukan nan”

“Ba ƙoƙarin zama nake ba Hilal amman duk abunda yake gaskiya dole a faɗe shi, idan kai ta maka magani ni bata min ba, kuma Wallahi tallahi sai ka ƙara aure ko da kuwa bana numfashi, dole ka auri wacce zata riƙa maka ƴaƴanka mace ƙwarai ba mai ƙoƙarin kashesu ba, ni zan nema maka mata da kai na”

Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita ranta na ƙololuwa a ɓaci. Shi dai da kallo ya bita har ta fice sannan ya saka hannyensa aljihu ya nufi ƙofar ransa a jagule.

RASHIDA POV.

A nasu gidan suke nasu amsar gaisuwar daban, duk da kasancewar waɗanda badu san aurenta ya mutu ba suka je can gidan gidan har sai idan sun tambaya ne sai ace musu gata nan. A harabar gidan suka shimfiɗa tabarma duk da kasancewar yaro ne hakan be hana ayi masu taro ba, sai dai ba irin zuwan nan ake na wuni ɗaya ba sai dai su zo su zauna na ƴan mintu su yi mata gaisuwar su wuce.
Tabarmarta daban tana zaune gefe ɗaya, ƴan gidan suna zaune gefe ɗaya. Idonta kumbura sosai duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata wasu har da Allah ya isa suke mata duk a tunaninsu tana kuka ne saboda rashin ɗanta, sai dai a gurin Rashida abun ba haka yake ba, ita tana kuka ne saboda tunanin makomarta ganin asirinta ya tonu tun yanzu, tasan dole zamantakewar ta da ƴan gidan dole zai canja dan taga alamun hakan tun yanzu.

Misalin biyu da rabi Teema ta zo gidan gurin gaisuwa, sosai take son magana da Rashida amman babu dama saboda mutanen dake ta kai da kawo. Tana gurin kuma sai ga Asmee bayan ta fito gidan Hilal ta nufo nan.
Duk abunda ya faru a gidan sai da ta bawa Rashida labari. A nan Rashida take labarta musu maganar sakin da Hajiya tasa aka yi ma Kalsoom, dan su ba susan da maganar ba. Duk daɗi suka ji har mutenan dake gurin da kuma Asmee da basu san kan abun ba, amman ban da Teema da ita kan tasan komai.

“Amman Hajiya ta kyauta, daman ai ni za ci tuni zata sata shi aikata sakin, duk wanda yayi maka haka ga jika kan ai be cancanci zama da ɗan ka dan wata shi zata hara”

Gaskiya kam. Abunda suka mutanen suka masa da shi, sannan ƙananan maganganu suka biyo baya. Teema ta kada baki ta ce

“Gaskiya Hajiyar ta kyauta daman tun tun tun Hajiyarmu take cewa ya kamata ace Hajiya ta saka Hilal ya rabu da matar nan”

Rashid ta kalleta tana murza idonta.

“Hajiyar ku ta san ta ne?”

“Eh sukan haɗu a harkar siyasa wani lokacin, suna gaisawa sosai”

“Allah sarki”

Cewar Rashida. Sai kuma ta kawar da fuskarta tana kallon Asmee irin kallon nan da ita kaɗai ta san dalilinsa.
Teema kuma wani gurin take kallo tana wani tunanin na daban. Sai da aka kira la'asar sannan Teema ta wuce gida, Asmee kam a gidan tayi sallah sannan ta fice bakinta cike da magangu amman bat samu damar yi ma Rashida ba, ganin Safiya duk yasa ta tsargu, hakan yasa ta yi a zamar barin gidan.

Tashi Rashida tayi ta nufi cikin gidan rayuwarta duk babu daɗi saboda abunda take tunanin su momi sun fara nuna mta na ƙyama tsakanin jiya zuwa yau. Babu abunda ke ranta kamar ta bar musu gidan ta kama wani, tasan hakan zai fi mata kawanciyar hankali.

ASIM POV.

Yana ji a jikinsa akwai rashin dacewa a abinda suka aikata. Musamman yanzu da yake jin abu kamar ƙashi ya tsaya masa a takashinsa, ga wani zafi zafi da yake ji kamar an zuba masa barkono. Wasu ƙwayoyi dattijin Alhajin ya miƙa masa kusan kala huɗu ya ce ya sha, daman kamin su aikata sai da ya bashi wasu, tun jiya da dare suke abu ɗaya har yau da safe, sai yanzu nan ne Asim ya samu kansa. Sai a yanzu yake ƙarema Alhajin kallo, tabbasa ya sanshi a cikin manyan mutane. Amman duk misalin da yake masa jiya be gane shi ba sai yau. Daman tun lokacin daya ji sunansa ta ayyana a ransa ko shi ɗin ne, sai gashi mitumen ya fere ma tun daga biri har wutsiya.

“Na bawa Hajiya miliyan biyu ta baka, na siya maka mota ta miliyan uku. Idan ka riƙe min sirrina nan da ƴan wasu watan ni za'a far ƙirgaka a cikin manyan Alhazai. Zan wuce Abuja yau, idan na dawo zan samr ka a nan ko kuma nas Hajiya ta aika min kai a can sokoto”
Chapter 102 · 0% Book details