← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 173

Sashe 78

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da safen ta gurka sabon abinci dan kwata-kwata jiya bata yi girki ba, saboda bata cikin ɗaɗin rai. Bayan ta gama, ta gyara gidan, ta ɗora ruwa tayi wanka sannan ta zuba abincin ta zauna ta ci sai kawai ta fashe da kuka, haka ta riƙa rera kuka har tayi ya isheta sannan ta share hawayenta ta ɗauki abinci ta mayar. Dan bata iya ci. Har zata kwanta sai wasu yara suka shigo siyen magi da manja, sai da ta sallame su sannan ta shimfiɗa tabarma waje ta ɗauko matashin kai zata kwanta kenan sai ga Asimya shigo.

Sai da tayi kamar kar ta masa magana ganin be shigo da sallama ba, kuma be kalli inda take ba, sai kuma wata zuciyar ta hana ta, ko ba komai mijinta ne dole ta yi haƙuri ta zauna da shi a haka.
Binsa ta yi cikin ɗakin, sai ta same shi yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa. Yana ganinta ya wani kawar da fuska, ya ƙara haɗe rai.

“Sannu da zuwa. Jiya baka kwana a gida ba lafiya?”

Ya tsaya daga cire wandon da yake ya kalleta

“Uwata ce da zan sanar miki dole? Ke kike iko da ni ko kuma ni nake iko da ke?”

“Ba ni bace amman ina da haƙƙi, Asim mi yasa kake min haka ne? Ina ta ƙoƙarin taushe zuciyata dan na zauna da kai lafiya amman baka so, look at me, haka nake a da duk na bi na canja saboda kai har kunya nake ji wani ya gani a halin da na ke, kana cin amanata Asim kana zalumtana”

Ya nuna kansa.

“Nine azzalumin?”

Baya baya tayi ta girgiza masa kai, dan ta san dukanta zai yi.

“Yi haƙuri dan Allah”

“Bakin ki ya saba da furta kalami mai daɗi a gare ni ko kuma jikinki ya faɗa miki”

Ɗaga kai tayi ta kalleshi da idonta dake zubar da hawaye, Asim ɗin baya take hangowa Asim ɗin da yake ce mata idan babu ita a duniya ba zai iya rayuwa ba, wanda yake ce mata zai iya sadaukarda komai na sa danta, zai iya bata dik abinda take so, Asim ɗin data watsar da kowa a kansa, wanda ta bijerewa Abbah saboda, wanda Maryam da Anty suka yi ta tunantar da ita akansa amman idonta ya rufe, yau shine yake gargaɗinta. Wani baƙin abu ne mai kamar ƙaho taji ya tsaya mata a zuciya har ƙafafunta suka kasa ɗaukarta ta zube ƙasa tana yaƙi da baƙincikin dake neman numfashimta.

“Kur wallahi kurwata kur sai dai ki ci kan ki”

Ya faɗa yana yatsine ganin kallon da take masa ɗazu. Lumshe ido tayi, ta rarafa ta ƙarasa saman katifar ta kwanta, tana sauraren ciwon zuciyar daya game ilahirin jikinta. Nan take jikinta ya ɗau rawar fever sai kuma zafin jiki. Bedsheet taja ta lulluɓa dan tsanyi take ji ya baibayeta.

Asim kan ko a jikinsa, fita ma yayi daga ɗakin yaje yayi wanka ya dawo ya saka wasu tufafin ya mata waɗanda ya cire a tsakar ɗaki yayi lafiyarsa.

Gurin aikinsa ya koma, daman yayi da abokan aikin nasa zasu je gurin Hajiya Sadiya gyaran gate. Dan haka yana isa suka wuce.
Shine yayi musu jagora a cikin gidan har suka yi aikin suka gama, sannan ya koma ciki ya sanar mata da sun kammala aikin sai ta ɗauko 30k ta bashi akan aikin da be wuce 8k ba. Hannu biyu yasa ya karɓa yana mata godiya.

“Allah ya saka da alheri Hajiya Allah ya ƙara arziki, wallahi halin ki na musaman ne”

Ta yi dariyar jindaɗi.

“Na ce ka iya mota kuwa?”

“Eh na iya mota Hajiya”

Ya amsa da sauri jikinsa har rawa yake.

“Idan ba damuwa, ina son ka riƙa jana a mota dan yanzu bana da direbe, kuma kaga gidan nan yayi min girma da yawa dole akwai buƙatar wanda za a aika a duk lokacin da aka tashi da kuma mai ban ruwan fulawowi da sauran ayuka”

“Wallahi Hajiya duka zan iya, wallahi komai kika sani zan iya”

“To idan ka shirya sai ka min magana, idan ban takurawa aikin ka ba”

“A'a ai aiki ina yi dan na samu na taɓawa, ai ko a yanzu ai na tashi”

“A'a kaje dai kayi shawara dan ni a gidana zaka dawo idan har ka fara aikin”

“Ba matsala Hajiya, zan iya zama a gidan ki”

“Yanzu dai idan ka kimtsa sai mu yi waya”

“Toh Hajiya na gode Allah ya saka miki da aljannah”

Da murmushi ta amsa nasa ba tare data ce amin ba. Sai ya juya ya fito baki har kunne zuciya kuma fal da farinciki.
A bakin ƙofar ya tsaya ya cire 20k ya saka a ɗayan aljihunsa, ya ƙarasa da 10k ya miƙa musu yace su ta bashi. Su kansu sun yaba da 10k ɗin sai kowa ya cire na abin hawan da ya hawo suka komawa Ƙanen Babansa da sauran kuɗin sai ya miƙawa kowa nasa. Duk da 20k dake aljihun Asim be hana shi sa hannu ya karɓi abinda Ƙanen mahaifin na sa ya bashi ba.
Basu tashi aikin ba sai 6 kamar yadda suka ba, sannan suka rufe kayan aikin na su. Sai dai ba su bar gurin ba sai da suka yi sallah magariba.
Sannan yayi sallama da su ya nufo gida, ba kuma gida kai tsaye ba, unguwarsu dai dan be shiga gida ba sai da 10pm. Babu abinda yake ransa sai saƙe-saƙen tunanin yadda zai sarrafa 20k tare da sauran kuɗin da yake ajiya su zame masa millions.

Yana ganin halin da take yasan vata da lafiya, dan tun fitarsa da zazzaɓin ya rufeta bata tashi daga inda take sai idan sallah zatayi, maganin ciwon kai ma sai da wata mai siyen magi ta shigo sannan ta aike ta ta siyo mata ta sha. Amman saboda ƙarfi hali yaƙi yace mata sannu balle tambayarta abinda yake damunta.
Haka ya kwaɓe tufafin jikinsa ya saka ɗan guntun wando data wanke masa jiya ta farar falmara, ya je ya ɗibi abinci ya ci sannan yaje ya rufe gidan, yazo bayanta ya kwanta yana lallubarta. Tabbas bata da lafiya dan yaji jikinta da zafi sosai. Cikin ƙarfin hali ta ɗaga kai ta kalleshi.

“Haba Asim bana jindaɗi”

“Ai na ji Allah ya sauwaƙe ya baki lafiya”

Sai dai hakan be sanya shi daina abinda yake da niyar yi ba....

AMIRA POV.

Tare suka yi breakfast da sukan ƴan matan Ummi, da kuma Ummi ita kanta. Yadda Ummi take ƴaƴanta ya burge Amira ainun hakan yasa ta kwaɗayin shiga cikim familyn dan ita ta zama ɗaya daga ciki. Suna gama cin abincin safe Abdool ya kira Ummi ya gaishe ta, bata iya jin abinda yake cewa duk da taso haka ganin fuskar Ummi da Murmushi alamun wata magana ce yake mata mai daɗi mai kuma muhimmanci.

Tsakaninta da Ummi akwai tazara sosai, dan tana ɓangaren falon ne ita da Haleema. Ummi kuma tana ɗayan ɓangaren ne. sai dai hakan be hanata kashe kunne ta jiyo abinda Ummi take faɗa masa ba.

“Good son haka na ke son ka zama”

“Allah ya kai mu me za a girka maka?”

“To yayi kyau ɗan Mai Martaba kuma Babansa”

Ƙyalƙyalewa Ummi tayi da dariya, ga dukan alama ita ma wani abin yace mata. Haka kawai Amira ta samu kan ta cikin farin ciki, ta san ko ba komai yanzu Abdool.yana can cikin walwalah da farinciki.

Farincikin dake zuciyarta ne yasa ta kai hannu ta riƙo hannun Amal dake shirin aje school bag ɗin a doguwar kujerar da Amira take zaune.

Wani irin ƙyalowa Amal tayi tana yarfarda hannu alamar ƙyaƙyami ta nufi bathroom ɗin falo dan wanke hannunta.

Haleema ta girgiza kai.

“Haka take, ƙyanƙyamin mutane take, Amal ƴar iskar yarinya ce, sai kin yi haƙuri da ita”

Amira tayi murmushi tana nuna abinda a Amal tayi be dame ta ba ko ɗan.

“Ba komai ai wata rana zata daina”

“Yeah amman Amal will never change, bari na koma ciki zan yi bachi”

“Ba ku da class ne?”

“Muna da amman sai da yamma”

“Okay sleep tight”

“I will thanks”

Ta wuce ɗakinta tana rangaji irin na ji da kai ɗin nan. Da Ido Amira ta bita har ta shige sannan ta ƙara mai da hankalinta gurin Ummi dake faɗawa Shukura abinda za a girka musu. Sai da Ummi ta tashi sannan Amira ta bi bayan shukura kitchen ta karɓi girkin ta girka musu white rice and pepper soup. Ummi bata san Amira tayi girkin ba har sai da taga tana jerawa a dinning. Ita kuma tana saukowa daga stairs.

“Shukura...”

Ummi ta ƙwala mata kira. Sai gaba da gudu tazo gaban Ummi ta tsaya.

“Ya kika barta tana jera kaya? Aiki aka ce miki ta zo yi ne?”

“A'a Wullahi Haseya sene yase zse girka ni in tafee”

Ummi tayi murmushin jindaɗi da kuma yabawa da halin Amira.

“To je ki taya ta jera kayan”

Da sauri shukura taje tana taya Amira har suka gama.

YASMIN POV.

Tun da ta dawo tunanin Namra take damunta, tana ganin idan har bata faɗawa Anty halin da Namra take ciki ba bata kyauta ba. Sai dai kuma tana tsoron faɗa musu kar ya zama tayi ma Namra kashin aure ko kuma ita Namra ɗin taga laifinta.
Dan Uzair ya gargaɗe ta akan karta faɗa tun lokacin data faɗa masa a irin halin data samu Namra.
Yau ma nanata mata yake kamar kullum.

“Babu ruwanki da matsalarta idan abin ya dame ta ai ita zata faɗa da kan ta, ba ita ta zaɓe shi ba, kin manta irin cin mutuncin da yarinyar nan tayi min?”

“Komai tayi maka Uzair be kamata mu ƙyaleta a halin da take ciki ba, wallahi baka gan ta abin tausayi, har dukanta yake duk ta canja kala”

“Ina ruwanki da canja kalar ta? Ba auren soyayyah tayi ba? To taje can su ci soyayarsu, wallahi Yasmin idan baki fitar da maganar nan daga ran ki ba, sai mun samu matsala da ke, kiji da cikin da yake jikinki dan Allah”

“Amman Uzair ni lauyace kuma..”

Ya taso ta haɗe bakinsa da nata......

DEDICATED THIS CHAPTER TO ZAGON K'ASA PAID GROUP MEMBERS. I LOVE YOU ALL 💖💖💖
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *53*

KALSOOM POV.
Chapter 78 · 0% Book details