← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 173

Sashe 9

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumgume filo ta yi, tana tuna ranar da yake labarta mata irin rayuwar da suka taso ta maraici shi da ƙannensa, da kuma irin wahalar daya sha kamin ya samu kuɗin registration, wanda shi ya hana shi shiga makaranta da wuri.

Lumshe ido tayi, tana buga kanta da hannunta. Wayarta ta sake ɗauka ta kira layinsa still switch off, sai kawai ta aika masa da sako.
Sannan ta kira Amira ta labarta mata yadda suka yi da Anty Amarya, da kuma goyon bayanta da suka yi a yanzu.

************
ONE WEEK LATER...

    Wednesday tun da sanyi safiya Anty Amarya da Maryam suka fara shirya abunda za su tarbi masu kawo lefe dashi, snacks da meatballs da sauran abubuwa Hajiya Barau ce tace zata yi, dan ɓangarenta za'a kai lefen.

Tun safe Namra ta bar gidan, kasancewar ba su da lacca sai kawai ta yanke shawarar zuwa gidan su Amira. A can ta wuni tana aikin kuka, tun Amira na iya rarrashinta har ta gaji ta zuba mata ido.
Sai bayan sallah Azahar Amira take labarta Namra wai jiya taga Asim. Da sauri Namra ta kalleta.

“A ina kika gan shi?”

“Shi ya zo nan gidan, ya kara ni a waya na fito, kuma yace karka faɗa miki”

“Haba Amira? Baki faɗa masa halin da nake ciki bane? Wai da gaske kike ko wasa?”

“Na saba miki irin wannan wasan ne? Babu abunda ban faɗa masa ba akan halin da kike ciki, kuma nayi-nayi ya faɗa min inda yake zaune ya ƙi, Namra karki so ganin Asim duk ya koma wani iri”

Namra ta dafe kanta

“Wayyo Allah na. Da wace number ya kira ki?”

“Wata baƙuwar Number ce”

Ta ɗauko wayarta tana nuna mata number. Cikin rawar jiki Namra ta kofe number tasa a wayarta ta soma kiransa. Ƙasa-ƙasa Amira take kallonta har kiran ya katse ba'a ɗaga ba. Daga bisani sai aka kashe wayar gaba ɗaya.

Har aka yi Magariba Namra nata trying ɗin Number amman kashe.

“Ki haƙura da kiran nan Namra, idan ya ga dama zai kira ki tun da kin tura masa saƙo”

“Baki fahimci yadda nake ji bane Amira, ni kaɗai na san halin da nake ciki”

“Yanzu dai kin ga anyi magariba, ya kamata a'ce kin koma gida, nima kuma ina son na biki dan naga lefen, zaki ci abinci ko na haɗa miki tea?”

“Tea zai fi dan bana jin cin wani abu”

Tashi tayi ta fice daga ɗakin, sai gata ta dawo riƙe da kofin tea, yaji Lipton da ginger da lemun tsami sosai har ya canja kala.
Ta daɗe riƙe da kofin kamin ta miƙa ma Namra.

“Ki daure ki shanye, tun da baki ci komai ba, nasan kina jin yunwa zai taimaka miki”

Ba musu Namra ta karɓa, tayi bismillah ta riƙa kuɓa tea har ta shanye. Sannan ta tashi sukayi Sallah, sai Amira ta ɗauko Hijabinta ta saka suka fito.

Napep suka tsaida, dan Namra yanzu bata da Mota tun lokacin da Anty Amarya ta amshi key ɗin bata mayar mata ba, ita kuma Amira daman ba Mota ne da ita ba.
    Magana suka masa yace zai kai su ɗari biyu, sannan suka shiga.
Be aje su ko'ina ba sai ƙofar gidan su Namra, Amira ce ta biya kuɗin, sannan suka fito suka shiga cikin gidan.

A falon Anty Amarya suka tararda ƙannenta biyu, Hajiya Lariya, da Mama Zainab.
Cikin ladabi Namra ta gaishe su, suka amsa suna mata fatan alheri, sai yaba lefen suke suna shi masa albarka.
Ita dai bata ce komai ba, idonta dai cike da ƙwalla, sai Amira ce take amsawa da

“Amin”

Fitowar Anty Amarya ne yasa Namra tashi tsaye, ta kalleta.

“Kin dawo?”

Nan ma Amira ce ta amsa

“Eh, Anty ina wuni?”

Anty Amarya ta lura da hawayen da suka idon Namra, kuma bata son ta yi kuka har ƙannenta su fahimcin halin da take ciki, sai ta yi saurin cewa Amira.

“Lafiya Ƙalau, Amira ku shiga ɗaki”

Hannun Namra, Amira ta riƙa suka nufi ɗakinta.
Saman gado suka zauna, sai Namra ta kwanta jikin Amira tana kuka, jikinta duk ya mace kamar marar lakka.
   Amira ta ciro wayarta dake cikin pose, tayi ƴan danne-danne sannan ta mayarda wayar, ta cigaba da rarrashin Namra tana bata Haƙuri.

Ba'ayi minti ashirin ba, sai ga kira ya shigo wayar Namra, da number da Amira ta bata tace mata number Asim ce.
   Cikin rawar jiki Namra tayi picking ta kara akunne tana.

“Asim! Asim!! Asim!!! Dan Allah kayi magana”

Shiru ba a amsa mata ba, daga bisani sai aka kashe wayar. Kira ta riƙa aika ma number amman ba'ayi picking ba, bayan kamar minti biyar sai ga sako ya shigo wayarta.

‘Namra ki fito yanzu, ina son na yi wata muhimmiyar magana da ke, ina nan bayan layin ku ta gurin gidan Alhaji Sani’

Tana gama karantawa ta nunawa Amira, sai Amira ta riƙe ta

“Namra karki je...”

Sai kuma ta yi shiru kamar wacce ta tuno wani abu, sai ta kalli Namra da ke kallonta tace

“Amman idan ba wannan ba, ba ki da wata dama ta ganinshi, kuma idan ba kije ba zai iya fushi da ke”

Namra ta sauke ajiyar zuciya

“Zaki raka ni?”

“A'a ni ba zan je ba, kar a shigo ɗakin ba kowa, kuma idan mun fita tare za'a zarge mu, wata ƙila ma Asim ya kasa yin magana da ke idan yaga muna tare, amman me zaki ce wa Anty idan ta gan ki?”

“Nima ban sani ba, kuma idan har na faɗa mata ba zata bar ni naje ba”

“Toh karki faɗa mata, kibi ta ƙofar kitchen ki fita, zan jira ki a nan har ki dawo”

Ba tare da fargabar komai ba, Namra ta tashi ta nufi ƙofar fita.
Sai da ta fice sannan Amira ta ɗauki wayarta ta kira number, ana ɗauka ta ce

“Gata nan zata fito yanzu”

 Namra na fitowa taga Anty Amarya na zaune falo tare da ƙannenta suna hira. Da faɗuwar gaba Namra ta nufi kitchen ɗin, tayi sa'ah babu kowa a ciki.
Hakan ya bata damar buɗe ƙofar a hankali ta fice. Da wage-wage ta isa gate, nan ma a hankali ta soma buɗe ƙofar, sai ga mai gadi ya taso ya nufo ta yana tambayar lafiya.
Dan ya san indai ba dolen-dole ba babu abunda ke fitar da su da zarar anyi sallah magariba, dan Abbah baya son fitar dare.

“Lafiya ƙalau, saƙo zan karɓo nan baya, yanzu zan dawo”

“Toh Allah ya tsare”

Sai ya maida ƙofar ya kulle. Sauri-sauri take tafiya tana wage, sai kiran wayar take amman anƙi picking.
   Sai data kai ƙarshen layin, sannan ta karya kwana ta nufi gurin daya kwatanta mata, jiki babu ƙarfi sai jin take kamar ta faɗi, dan ƙafafunta basa iya ɗaukarta.
  Kamin ta ƙarasa taji kamar ana binta a baya da mota, ta ɗan ji tsoro daman da fargaba ta fito gida, kasancewar unguwarsu ba kasafai zaka ga mutane ba ko da rana balle da dare, ga kuma fargabar kar wani ya ganta yaje ya faɗa a gida. Tsayawa tayi tana kallon ƙatuwar Bus ɗin mai baƙin gilashi.

Wasu maza ne guda huɗu suka fito ɗaga ciki Bus ɗin suka nufo ta ciki har da Uzair, ganin Uzair ne ya hana ta gudu daman can bata jin ƙarfin gudun, sai ta tsaya tana masa kallon mamaki da tunanin me ya kawo shi nan.

‘Daman yana biye da ni kenan? So yake ya tona min asiri yace ya gan ni na gana da Asim da dare ko me?’

Kiran daya shigo wayarta ne ya ankarar da ita daga tunanin da take. Number ce wanda aka turo mata saƙo da ita da sunan Asim ne. Da sauri ta kalli Uzair daya ƙaraso kusa da ita

“Uzair daman kai ne? Ko kuma wayarsa ka karɓa?”

Ta tambaya a kasale, jiri na ƙoƙarin ɗaukarta.
Murmushi kawai ya yi mata, ya kai hannu ya riƙo ta iya ƙarfinsa.
A nan Allah ya bata ikon yin ihu da dukan muryarta. Cikin sauri mutumen dake tare da Uzair ya fitar da wani ƙyalle ya danne mata hanci dashi, daga nan bata sake sanin inda take ba, sai numfashinta ya ɗauke dif.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa07.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

NOT EDITED⚠

*PAGE - 7*

A hannunsa ta suma, sai ya ɗauke ta ya miƙawa mazan da yake tare da su yana faɗin

“Ku shiga da ita, kuma ku tabbatar bata farka ba, har sai na dawo”

“Yes Boss”

Cikin girmamawa suka amsa, suka saka ta cikin Bus ɗin. Sai da Uzair ya ga sun bar gurin sannan ya nufi ƙofar gidan Alhaji Sani inda yayi parking ɗin Motarsa.
Bude Motar yayi ya shiga, ya ɗauko wani turare ya fesa, sannan yayi ma Motar key. Ribas yayi ya dawo ta bayan layin sai gashi a bakin gate ɗin gidan su Namra.
Horn yayi mai gadin ya buɗe masa yana gaisheshi. Guri ya samu a harabar gidan ya yi parking.
Sai ya fita ya taka da ƙafa ya isa part ɗin Abbah, dan yaga motarsa a waje, alamar yana nan kenan.
Hankalinsa kwance ya shiga falo, Abbah na kishimgiɗe yana duba jarida, Uzair ya shigo sai yayi saurin zubewa ƙasa yana kwasar gaisuwa.

Da far'ah Abbah ya amsa, yana nuna masa gurin zaman, bayan sun gama gaisawa, sai Uzair yayi shiru be ce komai ba har sai da Abbah ya kalle shi ya ce

“Uzair kana da wata magana ne?”

Abbah ya tambaya, yana mai jin son Uzair ɗin a cikin ransa, kusan ma ya fi kowa jindaɗin wannan haɗin, dan Allah ya sa masa son Uzair shiyasa komai na harkar kasuwancinsa sai ya saka shi, duk kuwa da cewar shima yana da ƴaƴa maza.

Sun-sun ya yi da kai

“A'a Abbah, akan maganar IV ne na mata, har yanzu Namra bata rubuta ba, kuma lokaci na tafiya, shine Hajiya tace na zo, na mata magana, shine nace bari na gaishe ka”

Abbah ya yi murmushi irin nasu na manya, sannan ya yi gyaran murya yace.
Chapter 9 · 0% Book details