← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 173

Sashe 119

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faɗa yana zama kusa da ita. Agogon ɗakin ta kalla ta ga sha ɗaya har da kwata.

“Kai ya aka yi nayi bachi haka?”

“Kin gaji ne, shiyasa ban tashe ki ba”

“Amman kai ka karya ko?”

A maimakon ya amsa mata sai kawai ya sakar mata ido yana kallonta, fuskarsa da mirmushi. Ɗan sunkuyar da kai ta yi itama tana maida masa da saƙon murmushin.

“Amarya ta”

Ya faɗa, tana mai cigaba da kallonta.

“Amaryar ka tana nan zuwa, ni kuma na zama uwargida a yanzu”

Murmushi yayi mai sauti, dan yaga kishinsa a cikin idonta.

“Ai ba gida ɗaya zaku zauna ba, kuma ita zata zauna da yara ne, that's means ke ce Amaryar”

Kai ta girgiza tana dariya, kamin ta mike tsaye.

“Bari na je na wanki bakina”

“Lemme help you”

Ya miƙe tsaye shi ma suka shiga banɗakin tare.

NAMRA POV.

Tun da ta shige ɗakin, bata fitowa sai idan fitsari zata yi ko shan ruwa, duk ta bi ta damu kanta, ta takura kanta. Duk yadda Neina ta so ta fito waje su yi fira sai ta ƙi, haka ta wuni da yunwarta daman can ba abinci take ci ba, sai Maltinar da Lamido yake badawa ana siyo mata, yau kuma ko maltinar ta ƙi ta sha.

Bayan sallame sallar isha'i yaro ya shigo, da sallama yana riƙe da kwanonsa ya bara yace

“Sallamu alaikum wai ance ana sallama da Namra, wai Abdullahi ne daga Katsina”

Tana cikin ɗaki ne, amman hakan be hanata jin abunda almajirin ya faɗa ba, sai kawai ta lumshe ido tana sauraren tsaran da kanta ke mata.

‘Wannan wane irin mutum ne?’

Ta tambaye kanta, tambayar da bata da amsa.

“Je ka ce bata nan”

Cewar Lamido zuciyarsa har wani kawowa take.

“A'a kai je ka ce gata nan zuwa”

Yaron na ficewa Neina ta kalli Lamido ta ɗora da

“Saboda girman Allah ka rufa mana asiri, muna neman abunda za mu ci ka jefa mu cikin wani halin kuma”

“Amman Neina tun da bata so ai ba ci aka ana cilasta ba”

Cikin yaren fulatancin ta mayar masa da amsa.

“Lamido babu ruwanka baka san yadda abun nan yake ba, kai dai ka cinto gefen tiri baka san tsakanin su ba, ka kama kan ka, ɗan Sarki ne fa”

Tana gama faɗar hakan ta nufi ɗakin da Namra take.

“Namra tashi kije yana kiran ki”

“Ni babu inda zan je”

Ɗukawa Neina tayi kamar zata zauna ta haɗe hannayenta.

“Ki yi ma girman Allah ki rufa mana asiri kije, haba Namra kar ki ba ni kunya mana na faɗa masa ga ki nan zuwa, dan Allah ki tashi ki je”

“Neina ko naje mi zan ce masa? Ni na riga na faɗa masa karya sake dawowa ƙofar gidan mu”

“Wallahi ban ce ki faɗa masa komai ba, saurarasa zaki yi, ki rufa mana asiri Namra”

Magiya Neina ta riƙa yi ma Namra kamar zata fasa mata kuka, sannan Namra ta tashi cikin ɓacin rai da zafin zuciyata ta fita.
Gurin da ya tsaya ɗazun a nan ya sake tsayuwa, duk da dare ne hakan be hana farin wata haskar fatar jikinsa ba, ga manyan idonsa da ya tsare ta da su har take ƙoƙarin faɗuwa kamin ta ƙaraso kusa da shi. Kasa furta masa komai ta yi, duk wasu kalamai da take da unƙurin faɗa masa sai ta kasa, suka tsaya mata iya cikin cikinta zuwa maƙogaronta, dan bakinta ƙin bata haɗin kai ya yi, ga ƙamshin turarensa da ke ta kaiwa hancinta hari.
Hannayensa dake rumgume aƙirjinsa ya cire ya maida cikin aljihu.

“Bude ba ki kiyi magana, faɗa min duk kalmar da kike tunanin ta cancanta a da ni, ki yi duk abunda kike ganin idan kin min saki samu salama.
Ayau na tsayu gabanki ne saboda kawai na ji tarihin rayuwarki, ban je neman auren ki, amman nasa a min bincike akan ki, tsakanin jiya zuwa yau labarin ki da hawayen ki sun nuna min akwai abunda kike boyewa”

Hawaye ta fara, tana ƙoƙarin ture kalamansa dake son su yi tasiri a zuciyarta.

“Ba lallai ne na cimma burina akan ki ba, mman lallai ne na faranta miki rai, kuma na taimaka miki ki cimma na ki burin, ina roƙon ki ki bani kaɗan daga tarihin rayuwarki ko zan samu sukunin rayuwa, Namra ni ba ƙaramin mutun ba ne, kuma ba wasa ya kawo ni nan ba, ki taimaka min wata ƙila ni ne silal farin cikin ki”

Ɗaga kai ta yi ta kalleshi.

“Ta ya farinciki zai dawo ga yarinyar da ta butulcewa iyayenta? Taya farinciki zai dawo ga macen data zaɓi saurayinta sama da iyayenta? Faɗa min ta ya?”

Yayi shiru yana karantar kalamanta. Yawun bakinta ta haɗiye.

“Ba kowa ba ce ni, fa ce wacce ta butulcewa iyayenta, da zabi saurayinta sama da su, wanda shi ne ya kai ni ga hakala.......”

Ƙoƙarin tsagaita kukanta take, dan ta samu damar labarta masa tarihin rayuwarta ko zai samu salamar rabuwa da ita. Zagayawa yayi ya buɗe bayan motarsa ya ɗauko carpet ya shimfiɗa mata. Sai da ta zauna sannan shi ma ya zauna nesa da ita zuciyarsa cike da tsumayin jin labarin nata.
Sai da ta share hawayenta, sannan ta soma bashi tarihin rayuwarta...

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *73*

Idonsa sun kaɗe sosai sun yi ja, duk ɗigar hawayenta ɗaya sai ya ji kamar an watsa masa ruwan zafi, ya kasa ɗauke kansa daga barin kallonta, har cikin ransa yake jin kukanta da kuma zubar hawayenta, samun kansa yayi da mugun tausayinta.
Ita kuma ta rumgume ƙafafunta sai kuka take, ba ƙaƙƙautawa.

Handkerchief ya riƙo daga aljihunsa ya aje mata, ba tare da ya ce da ita komai ba. Hannu ta kai ta ɗauka ta share hawayenta sannan ta fyace majina.

“Kin yi kuskuren zabar saurayinki sama da iyayen ki. Shiyasa Allah ya jarrabe ki, bayan Ubangiji babu wanda ya cancanci girmamawa sama da iyayenki”

Ɗagowa tayi ta kalleshi idonta taf da hawaye.

“Amman wanda mahaifina yake son na aura ba cancance ni ba...”

Ya tari numfashinta.

“Amman ai ya baki damar fitar da wanda kika so, sai kika nace sai shi saboda kar ya ce kin yaudareshi, ko ba haka kika faɗa min ba yanzu?”

Ta yi shiru tana sauraren hawayen dake bin fuskarta.

“Daga ƙarshe sai kuma ya yaudare ki, ya ci amanar ki, da ace kin aure wanda mahaifin ki yake so, babu yadda za a ayi ya guje ki, wata ƙila sanadiyar hakan sai ya shiryu, kuma duk abunda yayi miki dole su ne da laifi ba ke ba, baki san fushin Ubanguji yana tare da fushin iyaye ba? Idan iyayen ki sun yarda da ke, to haka shi ma Allah ya yarda da ke, kin yi aure mahaifinki yana fushi da ke taya za ki ga ribar auren?

Kin yi kuskuren rashin komawa gida Namra, ko yanka namanki za su yi su dafa su ci, bai kamata ki dawo nan ki tare ba”

“Idan kuma suka ƙi karɓa ta fa? Mahaifina ya ce karna kuskura na dawo gidansa da sunan saki ko yaji”

“Komai ya ce miki haka ne, saboda yana cikin fushi ne, da kin koma ai ba zai iya korar ki ba, idan kuma har idonsa ya rufe ya kore ki, to duniya zata miki masauki, su kuma ta juya musu baya, jama'ar gari kuma su zage su, har sai shi da kansa ya koma neman ki”

Ta bikita ɗaƴan ɓangaren na handkerchief ya share majiyar data cika mata hanci.

“Na yi nadama yanzu, na gane gaskiya”

“Kin yi nadama a lokacin da bata da amfani, kin sake tafka kuskure a cikin kuskure. Namra ba mutum kika aura ba, mutum mutume ne mai kama da mutum, siffarsa da kamarsa tasa kika ɗauka mutum ne, har kika masa inuwa, shi kuma ya saka ki a rana, mutumen da bai shirya haɗa zuri'ah da ke ba, amman Namra da yanzu a ace m cikin ki yana nan, a nan za ki zauna ki haihu kenan? Ba tare da kin koma gurin iyayen ko ba?”

Miƙewa ta yi tsaye ta yi tsaye ya saka takalminta, da zimmar komawa cikin gidan. Sai shi ma ya miƙe tsaye.

“Can i have my handkerchief!”

Juyowa ta yi ta kalli handkerchief ɗin, sannan ta kalleshi.

“Yayi ƙazanta”

Ya faɗa cikin muryarta mai gaf da yin kuka.

“Please...”

Ya ɗaga mata gira ɗaya, like he's serious. Ta ɗan ɗauki mintuna kamar mai shawarar miƙa masa abunda yake mallakinsa na ne.

“Please stop cry..”

Ya faɗa cikin muryarsa mai rawa kamar mai shirin yin kuka. Sai kawai ta miƙa masa handkerchief ɗin cike da ƙyama. Shi kuma ya miƙa hannu ya karɓa idonsa na kan fuskarta. Bata tsaya komai ba ta shigerwa tana ƙirƙirar wani sabon kuka.
Damƙe handkerchief ɗin yayi da dukan no ƙarfinsa, kamar abunda za a ƙwace masa, ya kai fuskarsa ya lumshe ido.

Har cikin zuciyarsa yake jin sanyin hawayenta, ya samu mintuna biyu zuwa uku a haka kamin ya buɗe motarsa ya shiga. Still da handkerchief ɗin a hannunsa yake driving.

“Da kin auri wanda Mahaifin ki yake so wata ƙila da ba mu haɗu ba, da ba zan iya kawowa rayuwarki ɗauki ba”

Ya faɗa yana mai sa ɗayan hannunsa ya fiddo wayarsa, sai da ya hau babban titi sannan ya rage gudun da yake ya danna ma Mai Martaba kira.
Ta ɗan jima tana ringing kamin a ɗauka.

“Assalamu alaikum”

“Wa'alaikassalam, Allah ya taimaki Mai Martaba”

“Babana kana lafiya?”

“Lafiya ƙalau Mai Martaba, Mai Mairtaba yanzu idan Madina (Sister sa wance suke uba ɗaya) ta zaɓi saurayinta sama da kai ya zaka ji? Bayan kuma kai ka yi mata zaɓi?”

“Ba zan ji daɗi ba, sai dai kuma ba zan hana ta aurensa ba, amman kuma ba zata ga da kyau ba, ba kuma dan ina mata fata ba, no saboda ba kasafai auren da iyaye basa so yake zama alheri ba”

“Idan kuma bayan ta yi auren mijin ya sake ta fa? Bayan ya gana mata azaba, sai ta dawo gare ka, ya za kayi?”
Chapter 119 · 0% Book details