← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 173

Sashe 69

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Dole ne kiyi mata abunda na saki dan na samu na koma gurin Daddy ku, na yi muku alƙawari ddana koma kullum gida zan riƙa zama ba zan sake fita aiki ba”

“Da gaske?”

“Wallahi, dan haka ki cigaba da abunda kike, har abunda ban saki ba ma ki aikata indai kinsa wanda zai hassalata ne”

“Zan riƙa yi”

“I Love you”

“I Love you too”

Rashida ta rumgume ta kamar da gayya. Sannan ta ciro chocolates da Sweet Candy dake jakarta ta miƙa mata, ta kuma bata ɗari biyu na kashewa sannan ta tashi ta fita.

Daga nan Asibiti ta nufa. Yau ce rana ta farƙo da zata fara bin shawarar likita wajen ɗora kanta akan magani, dan samun tsawaita rayuwarta kamar yadda likita ya faɗa mata.

NAMRA POV.

Two months later....

A zuwa yanzu babu wata matsala da take fuskanta a gurin Asim, tun bayan da aka sallamo daga asibiti, jiki sai ƙara sauƙi yake yana mirmirjewa kamar ba shi ba.
Duk wani mugun ƙudiri dake cikin ransa, ya danne ya barwa zuciyarsa, dan yasan babu yadda zai yi da Namra a yanzu sai kallo, idan yace zai rabu da ita matsala ne a gare shi tun da baya sgi kuɗin auren wata, shi dai yanzu ba shi da wani buri sai na yayi kuɗi.

Irin yadda yake nanata maganar har tsoro abun yake ba Namra, ahi dai yayi kuɗi dai yayi kuɗi. Haka Namra zata zauna tana masa nasiha akan duniya da abunda ya ke cikinta, amman sai dai ya kalleta kawai ya nuna mata wa'azin ya ratsashi bayan a ƙasan zuciyarsa kuma mamakinta yake, wai ita zata zaunar da shi ta nuna masa illar kuɗi, bayan ga ubanta can ya tara su ita kuma da su take tinƙaho.
Sam baya ganin wahalar da take da shi, bata saba wanki ba ko a gidansu amman haka zata zauna ta wanke nata tufafin ta wanke nasa, ta kai masa ruwanka, amman kullum sai ta matsa masa yake wanke dan ganin yake kamar tana takurasa, Allah ya zuba masa ƙuiyar motsa jikinsa indai a bangaren aiki ne.

Maganganun da Namra take masa akan rayuwa da neman kuɗi da yake magana a ko yaushe sai ya ƙara riƙe ta a zuciyarsa, wai bata son sa da alheri ta fi son yayi dauwama cikin baƙin ciki da damuwa tun da ita tana da mafita.
Ga matsalar da ci masa tuwo a ƙwarya a yanzu, wacce yake ganin kamar da ganganci ne tayi masa haka dan bata son haihuwa da shi. Ita kanta tana nadamar sanar da shi da tayi robar da aka saka mata, sai dai babu yadda zatayi dole ce tasa ta faɗa masa, tun kullum sai ya tunkareta kuma jinin har yau be tsaya mata ba, daman wani lokacin haka robar yake yi mutane dan ta ji maƙonta suna firar lokacin data shiga gidan su ƴar fulani.

Ta aika tambayarta ga wani malami ya amsa mata da cewar duk jinin daya zube bana haila bane ya zama kamar jinin rashin lafiya ne dan haka ba zatayi fashin sallah ba balle azumi.

Hakan yasa robar ma sai ta fita ranta dan ita bata son abunda zai riƙa rikitar mata da addini, hakan yasa ta yanke shawawar zuwa a cire mata robar in ya so sai tasha ƴaƴan zurma, dan maƙociyarta nan ta faɗa mata indai har ta sha ƴaƴan zurma ɗaya yana matsayin shekara ɗaya ne idan kuma tasha biyu kuma yana matsayin shekara biyu ne.
Sai dai ba kowa yake yi ma aiki ba, amman ta ga wani a whatsapp wanda Khadeeja Candy take tallah shi kam idan an sha tabbas zai maka aiki, matsalar kawai ita ba a garin take ba, kuma tana buƙatar ta bincike dan ta jin yadda abun an ce mata texted and trusted ne. Ga Kuma Asim ya dame ta da maganar kullum, dan shi gani yake kamar da biyu tayi haka.

Yau wake ta dafa da shinka (rice and beans) ta saka mai da taji, daman yana cikin favorite na ta, amman Asim duk lokacin data dafa sai ya riƙa ƙin ci yana ganin kamar tana haka ne dan karta kashi kuɗi da yawa tayi musu abinci mai kyau.
Shi yanzu har ya matso jikinsa ya koma.yadda yake ya fara fita neman kuɗi, dan ya ayyana a ransa kuɗinta zai ranta ya fara sana'ar, har hango kansa yake ya zama wani Alhaji.

Kullum firar da ita kenan, yau bayan ya gama complaint ɗin baya son wake, ya ɗasa mata firar idan yayi kuɗi, ba aza a ƙara cin wake a gidansa ba.

Namra ta yi murmushi tana mamakin yadda idom Asim ya bude haka.

“Asim kenan. Idan ma zaka yi roƙon baka cewa Allah ya baka halalinka, kawai dai kai kayi kuɗi”

“Wallahi sai na yi kuɗi Namra, Wallahi Wallahi sai nayi kuɗi, kawai naji sauƙi ne”

»“Ban ce ba zaka yi kuɗi ba, Amman yana da kyau ka riƙa cewa Inshallah kuma ka riƙa roƙon halak, saboda gudun sherin zuciya, idan Allah ya rubuta zaka yi kuɗi zaka yi ko da kuwa kama kwance gida ne sai sun tararda kai, saboda an riga an rubuta zaka yi kuɗin sai dai idan kayi gajin haƙuri zaka iya samun ta hanyar da be kamata ba”

“Namra kina bani mamaki, ke yanzu da ba dan kuɗi ba iyayen ki ai ba zasu wulaƙanta ni ba”

“Wulaƙanci kamar ya?”

“Wulaƙanci ne mana, saboda an mai dani talaka wanda ba shi da amfani shiyasa aka saka miki wannan robar ba tare da sanina ba”

“Ba haka bane, kawai matsala ce ta taso kuma likitan yace dole ne nayi planning”

“To Allah ya kyauta, amman ko ma minene ai nafi kowa kusanci da ke, taya za'ayi ki yi min haka”

“Asim matsala ce fa kai yanzu kana son na samu ciki ya zo ya zube ko kuma nayi ta wahala?”

“Hmm kina dai ganin kamar ba zan iya hidama dake ba ke da abunda zaki haifa shiyasa kuka ɗauki wannan matakin”

Ta aje kofin ruwan dake hannunta

“Ba zan ɗauki halin nan naka ba Asim, babu yadda zaka riƙa cin zarafina dana iyayena, kullum mune marar mutumci a idonka, duk abunda muka maka baka gani, na sadaukar da yawa Asim, har inda be kamata na sadaukar ba na sadaukar amman baka gani”

Kamar mai jira sai kawai yayi cikinta da masifa.

“Me kika min ke da iyayenki? Me kika sadaukar min? Ran ki? Ko lafiyarki? Kullum da kin tadhi magana kin sadaukar kin sadaukar tun da na aure ki me na ƙara shi in ɓa tsiya ba? Ɗan abunda na tara dik ya ƙara na zo na kwanta a asibiti jiyan babu wani ɗan'uwanki da ya ɗauki wani abu ya ba ni, an so na mutu ban mutu ba shine yanzu zaki fara buɗe min wani babin na rayuwa, kina da kuɗi a jikin ki amman saboda baƙin ciki ba zaki fitar aci ba sai dai a mutu? To Wallahi Asim ikon Allah ne, duk wani mai son ganin bayana sai dai ni naga bayansa”

“Magana kake irin wannan zancen kamar mai magana da maƙiyansa, maitarka ta kasa ɓoyuwa har sai ta fito fili? Kuɗina sana'ah zan yi da abu na, dan ba zan zauna kullum ni ce biyar dangi a bani ba, kuma Allah be ɗora min alhakin ciyar da kai ba, ni aka ce ka ciyar ka tufatar, yanzu ka fito a siffar ka sak Asim daman dan dukiyar gidan mu ka aure ni ko, amman sai ka nuna mik baka son komai sai ni, ashe zagon ƙasa kake min ka ɗauki halin samarin zamani ka ɗorawa kan ka, masu auren jari...”

Wani irin mahaukacin mari ya kifa mata ya rufe ta da duka kamar ma dukan namiji.
Shuri yake aika mata ta ko'ina tana cigaba da dukan jikinta kamar ƴarsa.

Dukanta yayi sai da yaji ya daki iya kalaman data faɗa masa sannan ya sassauta mata ya miƙe tsaye yana ɗingishi.

“Kuma Wallahi kije aci miki wannan robar ko kuma wallahi na lahira ya fiki jindaɗi”

A fusace ya juya ya bar ɗakin. Kuka tayi har ta gode Allah sannan ta tashi zaune tana cigaba da hawaye.
Sai ynz take tabbatar da tayi kuskuren aure, ta auri mutumen da be san darajarta ba, mutumen da be san kowa ba sai kansa. Daman haka halin Asim yake abu kaɗan sai duka.

Ta share hawayenta dan itama kanta tasan ba kuka bane abunda take buƙata, sam Asim be cancanci hawayenta ba, a yanxu ta san wa take aure dole ne kuma ta shirya zama da shi. Bata da buƙatar kokawa kowa damuwarta ita ya kamata ta gyara zaman aurenta da kanta.
Ta tatsu iya tatsuwa dan haka yanzu ba zata sake bari guminta ya zuba akan Asim ba.

ASIM POV.

Ta ƙarfen dake hannunsa yana dafawa ya fito gate, sai huci yake kamar wani zaki.
Yau ji yake kamar ace ya rumtse ya bude ya gansa yayi kuɗi, ta yadda zai jidaɗin rayuwarsa. Sai yanzu yake nadamar karatunsa daya bari daman can yayi tunanin ko zai samu wani abun a gurin iyayen Namra shiyasa ya baro garin su da ita ta yadda nan zai ta cin karensa ba babbaka sai yayi ta aikata tana samu matsa kuɗi, amman yanzu ya fahimci itama maƙetaciya ce kuma bata sonsa da alheri.
Gashi yanzu ko sana'ah zai yi yasan ba zai samu kuɗi a tashi ɗaya ba, amman idan yana da karatunsa zai iya samun babban aiki.

“Mtssssss aiko karatun na yi ba aiki zan samu ba tun da nigeriyar sai da gata, su kuma waɗannan iyayen nata matsiyata ne ba aiki za su samomin ba, aiko wallahi duk wahalar da zan sha tare da ƴar su zan shata, sai na yi kuɗi tana ganin zata huta kawai na aikata gidan su.
Har ni za'ayi ma mugunta, ai ko sai na yi muku baƙin ciki dan haihuwa yanzu za a fara”
Chapter 69 · 0% Book details