← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 173

Sashe 103

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhajin ya faɗa yana shafa fuskarsa. Asim kan daɗi har cikin kai, hankalinsa da zumuɗi gaba ɗaya sun tattara sun koma gida, babu abunda yake ransa kamar motar nan, a take ya ji duk jikinsa ya warysakr kamar babu wani ciwo jikinsa.

Be bar gidan ba sai da ya ci ya ƙoshi, sannan Alhajin yasa direba ya mai da shi gida.
Yana fita cikin motar sai ga Nably ta kira shi kamar ba zai ɗauka ba dan ya matsu ya ga motar da Alhajin yake ce masa. Sai dai farincikin dake ransa ba zai hana shi ɗaukar wayar Nabila ba.

“Hello my girly”

Ya faɗa cikin wani irin yanayi na shauƙi da annashuwa. Ita kaɗan ta karanci hakan a muryarsa.

“Da alama yau akwai labari mai daɗi a tare da kai..”

Ƙyalƙyalewa ya yi da dariya.

“Labari mai daɗi, na kusa zuwa Abuja na gan ki”

“Nikam ba zan iya jura har jibi ba, akwai birthday friend ɗita da za'ayi yanzu take faɗa min ni kuma na ce dole zan zo ko dan kai”

“Wow Amman gaskiya kin kyauta min, i can't wait to see you”

“I can't wait to see you too, sorry zan katse kiran, Momy na kira na zan kira ka idan mun gama”

Hajiya Sadiya ce ta fito waya a hannunta tana faman kiran waya, fuskarta ɗauke da murmushi, ganin Asim.

Shima Murmushin ya mayar mata ya doshi inda take cike da zumuɗi, sai kawai ta jefa mishi keys ɗin mota ta nuna masa motar tana cigaba da murmushi sai ta nufi wani ɓangaren na gidan tana amsa wayar da aka yi picking yanzu.
Wani irin tsalle Asim ya daga tsinkawo motar da yayi, da gudu ya doshi gurin yana wani irin gurnani kamar mahaukaci.

NAMRA POV.

Abdool na fita Uwani ta karɓi takardar hannun Neine ta duba, tana gani tasan cak ne sai dai bata iya gane ko nawa aka rubuta ba, kasancewar ilminta be kai har can ba, zero da ta ga a rubuce sun mata yawan karantawa.

“Minene?”

Neine ta tambaya, cike da son sanin abunda yake ciki.

“Ni wallahi ban gane kan abun ba, amman dai takardar kuɗi ne”

Uwani ta faɗa, dai Namra ta kai hannu ta karɓa tana dubawa.

“Miliyan ɗaya ne cif”

Uwani da Neina sun daki ƙirji tare da zaro ido.

“Miliyan ɗaya?”

Duk mutane da suka shigo cikin gidan duk ko wanne sai da ya riƙe baki, har ga Allah yawan kuɗin suke gani, Namra kam bat ɗauke su a bakin komai ba, abun ka da wanda yasan kan abu. Wani dogon tsaki Lamido yaja ya kawardar da kansa.

“Sam sam sam mutumen be san darajar mutane ba Wallahi”

Aiko yayi ƙoƙori irin wannan kuɗin haka! Ƴaƴan manyan mutane da da zasu taka rai su bar mutum balle har ya baka wannan kuɗin. Shine abunda mafi yawan matan maƙotan gidan suke ta faɗa.

“Ai dole yayi min mana, tun da ya lalata min Napep dole ya bada kuɗin jinya dan siyen wata”

Neine ce ta saka bakinta wannan karon tana nuna Abdool ya kyauta iya kyautawa.

“Wallahi da wani can ba zai kula ka ba Abdool ba gasu nan muna gani ba, wannan kuɗin ka siye sabon Napep har ka rage. A dole ya nuna wannan halin kasan a jinin su yake, babban mutum kamar wannan”

“Da Sarauta kawai zai fi ni, amman ina tabbacin be fini ilmi zamani ba, balle ma na addini, ji yadda yake kallon mutane warwatse”

Har cikin ransa yake maganar yana mai jin tsanar Abdool sosai. Namra kam bata ce komai ba hankalinta ma gaba ɗaya yana wani gurin, sam bata lura da kallon baƙuwar fuskar da mutanen dake shigowa cikin gidan suke mata ba. Murɗawar da taji mararta na mata ne yasa ta miƙe tsaye ta nufi ɗakinsu. Ƙasa ta zauna tana riƙe tsararta tana dannar baki alamar tana jin zogi sosai. Tun tana juriya a zaune har ta kasa ta kai kwance tana rumtse ido.

SAI MUN HAƊU BAYAN SALLAH 😍
INA NEMAN YAFIYAR DUK WANDA NA ƁATAWA, ƊAN A'ADAM AJIZINE. WATA ƘILA ZAN KAI BAYAN SALLAH, WATA ƘILA BA ZAN KAI BA. KU MIN ADDU'A IDAN LABARIN MUTUWA NA YA SAME KU KUMA KU YAFE MIN ALFARMAR ANNABIN RAHAMA S.A.W 🙏
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *63*

Kasa cin tuwon masarar Namra ta yi sai kawai ta sha ruwan tulun mai jiƙa maƙoshi kamar ruwan freezer.
Da fulatanci matar da ba zata wuce mai shekaru hansin da huɗu ba ta yi ma yaran magana akan ba su gaishe da Namra ba. Sai duk suka taso cikin ladabi suka gaisheta cikin su har da manyan ƴan'mata da kuma ƙanana. Da murmushi Namra ta amsa su sannan ta maida kanta ƙasa tana murza yatsun hannunta.

“Ban wayence ta ba”

Neina ta faɗa da yaren fulatanci tana kallon Saurayin. Shima da yaren ya maida mata da amsa.

“Ni ban san ta ba, kawai na ɗauko daga tasha ne, sai tace bata da gurin zuwa na taimaka mata shine na kawo ta nan”

“Amman Lamido taya zaka ɗauko yarinya baka santa, baka san inda ta fito ba? Kasan ko wace iri ce?”

“To Inna idan na bar ta can ban san halin da zata faɗa ba, kuma kin ga tace bata da kowa nan”

“Bata da kowa a nan zata zo? Lamido karka mana jaye-jaye muna neman abinda mu ka ci”

Da yaren fulatanci suke maganar, a zahirin gaskiya Namra bata jin yaren duk kuwa da kansacewar kakaninta fulani ne. Amman hakan be hanata fahimtar zancen ne suke ba.

“Ni ba macuciya ba ce lalura ce ta kawo ni nan, mijina ne ya sake ni kuma mahaifina ya riga daya gargaɗe ni akan karna kuskura na je gidansa, shiyasa na zo garin kaduna, amman idan ba ku yarda da ni ba ba zan zauna a nan ba, dan ba zan takura ku ba”

Wannan karon cikin halshen hausa Neinah ta ce

“Duniya ce a yanzu ake tsoron mutane, ba kowa ake yarda da shi ba, amman me kika aikatawa mahaifinki ya yi miki haka kuma a ina mahaifinki ya ke?”

“Mahaifina yana garin sokoto da zama, ni kuma a Katsina nake aure, sai dai ba zan iya labarta muku labarin aure na a yanzu ba, ina neman ku min lamani har zuwa gobe zan faɗa muku ba zan ɓoye ba”

Daga Neinah har Lamido shiru suka yi babu wanda ya iya cewa uffan, shi baya son yayi magana mahaifiyarsa ta ga kamar yayi mata katsa ladan ita kuma har yanzu bata gama gamsuwa da ita ba saboda halin da duniyar yau take ciki. Ɗaya daga cikin ƴan matan da suke zaune gurin ne ta taso ta dafa Namra tana murmushi ta ce

“Ba komai mun yarda da ke, ba ki yi kama da mugayen mutane ba, kuma na san ba zaki cutar da mu ba”

“Na gode”

Namra ta faɗa cikin muryar kuka.

“Uwani zuba mata ruwa ta yi salla”

Lamido ya faɗa cikin halshen fulatancin yayinda yake ƙoƙarin miƙewa tsaye ya jefar da ledar kifin dake hannunsa. Cikin ladabi ta tashi ya ɗauko mata buta ta miƙe mata sannan ta nuna mata banɗaki. Kamin namra ta yi alwala har ta shinfiɗa mata tabarma ta ɗosa mata sallaya sama ta aje mata carbi. Sannan ya ɗauko ɗayar tabarmar ta shimfiɗa mata gefe ɗaya ta ɗauko zanen gado ta shimfiɗa mata ta aje mata matashin kai. Sai ta dawo ta ɗauki abincin taje can kusa da tabarma ta aje mata.

Namra bata tashi daga saman sallayar ba sai da tayi salla insha'i sannan ta ƙara faɗawa Allah buƙatarta ta sai ta tashi ta koma inda Uwani tayi mata shimfiɗa ta kwanta. Babu abunda ya zo mata a rai sai gidan su, a ɗayan ɓangaren kuma idan ta tuna irin abunda Asim yayi mata sai ta ji kamar zuciyarta zata rabe biyu tsabar baƙinciki.
Kusa da ita Uwanin ta zo tayi shimfiɗa, ta kwanta, sauran yaran gidan kam sai da dare ƴa raba sannan suka nemi guri suka kwanta. Juyi Namra ta yi ta yi har safe ba yi bachi ba, abun nan da take jin ya tsaya mata a ƙahon zuciya yaƙi saukar mata har yanzu numfashinta ma daker take yinsa.
Bata san kan gidan ba amman haka be hanata tashi da wuri ba dan gabatar da salla azuba, sai duk sakkon tashin da tayi sai ta hango Lamido a ƙofar ɗayan ɗakin 6ana salla nafila, kallo ɗaƴa tayi masa ta ɗauke kai. Sai da tayi alwala tana daf da gamawa sai ga Neina ta tashi sai ta tashi dukan sauran yaran gidan har da waɗanda ba su wuce shekara bakwai ba zuwa takwas.

Bayan sun yi alwala dukan mazan sai suka tafi masallaci su kuma suka yi nasu salla a gida. Tun da Neina ta maida gabanta gaban bata juyo ba sai ta ta gama lazumin da take. Uwani ma ta maida gabanta gabas tana nata karatun ƙur'ane, ɗayar ma da tsawon su zai iya zuwa ɗaya da uwani ita karatun take, duk yaran masu ɗan tsawo da wayo kowa ya kama surar da yake yana karantawa. Ƙananen kawai suka koma bachi, sai ita kuma ta jingina jikin icecen dake tsakar gidan tana tasbihi da hannu. A hankali ta karkata kanta tana kallon Lamido take can ƙofar wani ɗaki yana nashi karatun cikin natsuwa da ƙira'ah mai daɗin saurara.

Hakan ya karantar ita irin tsantsar natsuwa da kuma ilmin da ƴaƴan gidan suke da shi, tun daga yaran su har ƙanana, ta samu kanta da ɗan sakewar zuciya tun bayan daga irin karatun ƙur'anen ta suke, daman sauraren karatun ƙur'ane yana saukar da natsuwa karanta shi kuma yana sa kwanciyar hankali da walwalah.

Bayan duk sun gama sai suka duk suka zo suka gaishe ta, ta amsa musu da far'ah sannan ta gaishe da Neina, kamin ta kalli Uwani dake mata murmushi ta ce.

“Ina kwana?”

“Lafiya ƙalau ai daman na ce sai dai ki gaishe ni, ba dai ni na gaishe ki ba, dan nayi ƙanwa da ke”

“Ni...?”

“Eh mana Lamido da kike gani ni nake binsa kin ga kuwa ni yayarki ce”

“Gaskiya ban yarda ba”

“Ta girme ki ƴar nan, jikin ne haka ba'a gane girman ta, yaran nan da kika gani duka ƴaƴanta ne”
Chapter 103 · 0% Book details