← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 173

Sashe 54

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Inshaallah ba zan sake ba, dan Allah ki yi haƙuri ban san kina da aure ba”

Sai a sannan ya janye ya bata hanya, ta raɓa gefensa ta wuce, shi kuma ya juya jiki a sanyaye ya nufi hanyar fita, kallonsa ake tayi a gurin saboda wasu sun san Namra tana da aure, wasu kuma suna masa kallon sani tun da akan nunasa a tv akan matsalar tsaro, kuma sun san ɗan sarki ne, tun da ga fuskar Mai-matarba nan a fuskarsa.
Sam be ji maganar da wani likita ke masa ba har sai da likitan ya cira ƙafa ya cin masa ya dafa shi.

“Manjor ina magana fa”

Ya ɗan kalleshi yana murmushin ƙarfin hali

“Doc Husaini ya aiki?”

“Lafiya ƙalau, ka zo ganin wani ne?”

“No... Eh.. Oh.. Yeah.. Yeah.. Naga wani Cousin na mu ne”

“Allah sarki, tau ya aiki ya kwana biyu? Kun yi kuɗi kun ɓoya”

“Kai ina wani kuɗi aiki ya samu gaba ba sauƙi”

Haka suka jera suna tafiya, suna ɗan taɓa fira har Abdool ya isa gurin motarsa. Jikin sashin kuzari ya buɗe motar ya shiga yana yima Doc Sallama.

“Tau ni kan zan wuce”

“Yanzu kan ganin ka sai manya, tun da baka ma zama garin”

“To ya muka iya, aikin ne a haka ko ina jefa mu ake”

“Allah ya taimaka, sai mun yi waya”

Daga haka ya rufe motarsa, shi kuma ya juya ya koma cikin asibitin. Ribas yayi ya juya hanyar gidan daya baro.
Tuƙin kawai yake jikinsa ba kuzari, kansa yayi zafi sosai, sai hannu yake sawa yana murza goshinsa, lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciya har ya isa gida.

Ya daɗe zaune cikin motar, sannan ya buɗe ya fito, yayi yaƙi sosai da ƙafafunsa kamin ya ci galaba akansu har su samu ƙarasawa da shi falon Ummi.
Be damu da farar shaddar dake jikinsa ya zube saman carpet, ya lumshe ido yana sauraren bugun zuciyarsa. Ya samu minti ashirin zuwa ashirin da biyar a haka, sannan Ummi ta fito cikin wata bugaggar shada ya nufo inda yake hankalinta a tashe.

Saman carpet ɗin itama ta zauna kusa da shi ta kai hannu ta riƙa kansa.

“Son tell me what happen? Larai tace min ba lafiya ba, talk to your Mom please”

Sai a lokacin ya buɗe manyan golden eyes nasa ya kalleta.

“Mom i saw her today”

“Who?”

“The woman i have been dreaming of, i finally saw her in a hospital”

“And...”

“Ummi matar aure ce”

Wani dogon numfashi Ummi taja ta sauke, tana tunanin ta inda zata fara kwantar masa da hankali.

“Abdallah, be patient one day your princess will surely come, miji baya aure sai matarsa, mace ma bata aure sai mijinta”

“I know, but what i don't understand is duk mace da na gani bata kwanta min, sai wannan ita kuma yanzu matar wani ce, zuciyata tana son wahalar da ni”

“Karka damu, komai zai wuce, i will talk to Mai Martaba, zan faɗa masa ya baƙa time, har Allah ya baka wacca kake so, bana son ka auri wace baka so ina son ganin farincikin ka”

“Thank you”

“Anything for you”

Ya ɗan kwanto jikinta, babu abunda yake gani a idonsa sai Namra.

“Allah ka shiga tsakani na da zuciyata, Allah ka min tsari da sherin zuciya”

Be ankaro da fili yayi maganar ba har sai da yaji Ummi ta amsa masa ta Ameen, dan shi duk a tunaninsa a zuci yayi wannan addu'ar.
Ummi tana son ɗan ta sosai, ta kan damu da damu damuwarsa, ta fi kowa son farincikinsa, saboda ta san zafinsa.

Abdallah Ahmad Mai-doki. Ɗa ɗaya namiji gurin Hajiya Zuwaira. Kuma ɗa na uku a jerin ƴaƴanyen Mai Martaba sarkin katsina na uku III, wato Alhaji Ahmad Abdallahi Mai-doki, jiki gurin Isma'il Mai-doki sarkin Katsina na farko.
Shine ya gaji sarautar kakansa, tun bayan da sarautar ta bar gidansu, sanadin rasuwar kakansa. Bayan rasuwar Sarkin Katsina na biyu, sai aka ɗauko sarautar aka bawa mahaifin Abdallah, wato Ahmad Abdallah Mai-doki.

Matan sa biyu a yanzu, bayan fitar Ummi ya auro Hajiya Salamatu, wace ta kasance ita ta biyu a yanzu. Hajiya Zuwaira (Ummi) Ta sha gwargwarmaya da uwar gidansa Hajiya Shafa, dan zame mata tayi muguwar kaza, mai hana shiga akurki. Hajiya Shafa ta haifa masa ƴaƴa bakwai, Mashkur ne na farko, sannan Salwee wace ita ce ta biyu, sannan Ummi ta Haifi Abdallah, wanda mai martaba ya saka masa sunan babansa, hakan yasa bata taɓa faɗar sunansa sai dai ya kira sa da Yarima ko Babana.
Mar martaba yana matuƙar son Ummi ganin ita ce ƴar'uwarsa kuma itace tafi kula da shi sama da Hajiya Shafa, hakan yasa zaman gidan ya gagareta, saboda irin son da yake nuna mata.
Babu inda Hajiya Shafa bata shiga ta fita ba, har sai da taga ta raba aurensu da Mar matarba, ba tare daya sani ba yayi mata saki uku lokaci ɗaya, kuma ya karɓe ɗansa, Abdallah a lokacin yana ɗan shekara biyu da wata uku. Son duniya nan Mai Martaba ya ɗauka ya ɗora masa, saboda son da yake ma uwarsa, sai kuma akayi sa'ah ya zama ɗa na gari gurin iyayensa, duk kuwa da faɗi tashin da yasha kamin ya kawo inda yake yanzu. Mai martaba ya so ya kaishi waje karatu amman Hajiya shafa ta hana, tasa aka kai ɗanta.

Haka tasa aka riƙa tura masa kuɗi da sunan karatu ashe yana can yana holewa da ƴan matansa, har yayi karatun ya gama be dawo gida da kyakkyawan results ba. Abdallah da yayi karatu a Nigeria sai ya fishi ƙoƙari da basira, sosai hakan ya ƙarawa Mai matarba ƙaunarsa, bayan ya gama degree a nan sai ya turawa waje yayi Master's. Hakan yasa Hajiya Uwani ma da tazo daga baya ta ɗauki ƙiyayyah ta ɗora masa, kowa cewa yake Mai Martaba yafi son sa da kowa.

Bayan fitar Ummi a gidan Mai Martaba, sai auri Alhaji Dahiru, mahaifin Haleema da Meesha da Fauza, tana da goyon ƴar autar ta, Amal ya rasu. Tun daga lokacin bata sake aure ba, sai tayi zamanta a gidan da take ita da yaranta, daman ba guri ɗaya suke da abokiyar zamanta ba. Da aka raba musu gado sai ta riƙa juya dukiyar tana business da ita har abun ya bunƙasa.

Abdallah mutum ne mai tsantsan da kai, da kuma taka tsantsan da duniya, duk da irin tarin dukiyar mahaifinsa da ta mahaifiyarsa da kuma sarautar da suke da ita, be taɓa sa yayi unƙurin wulaƙanta kowa akan hakan ba.
Yana yawan samun matsala da Ƴan'uwansa a lokacin da yake gurin mai martaba, ganin irin son da yake masa, da kuma irin rufin asirin da Allah yayi masa, ga kuma aikin da shine sillar ɗaukaka a duniya.
Baya son fitina ko tashin hankali, hakan yasa ya tattara ya dawo gurin Mahaifiyarsa, sai ya warewa kansa part ɗaya a gidan, daman can ya zuba musu securities. Ko kaɗan Mai Martaba be so hakan ba, amman dole ya haƙura ganin hakan shine mafita a garesu gaba ɗaya.
Kuma hakan be rage ƙaunarsa a zuciyar Mai martaba sai ma ƙaruwa da tayi, dan a yanzu ne Abdallah yake nuna masa kulawa da biyayyar fiye da da. Ga kuma zumuncin daya ƙaru tsakanin Mai Martaba da Ummi, kasancewar Kakansu ɗaya, daman can auren gida ne aka yi. Idan har zai cilasta Abdallah yin abu to sai dai ya kira Ummi ya faɗa mata, dan baya tun karar Abdallah kai tsaye da abunda ya san zai iya sosa zuciyarsa.

Ya kan zauna yayi fira da shi kamar abokinsa, shine yafi kowa sanin sirrin Mai martaba, gashi ya karanci mahaifinsa sosai, da ido kaɗai zai oya gane abunda Mai martaba yake so ko ƙi.
A duk lokacin da suke tare baka taɓa ganin danuwa a fuskar Mai matarba, idan ba su yi labarin zamanin baya ba, tun Abdallah zai ɗauko masa firar matsalar tsaro da kuma sauran matsalolin da suke damun ƴan negeriya, ko kuma na siyasa.

Wani lokacin kuma idan ya shiga faɗar Mai martaba, zai zauna a kusa da shi ya riƙa karatun alƙur'ane, Mai martaba na sauraro, hakan kuma ba ƙaramin daɗi yake masa ba. Ga shi kuma Major abunda Mai martaba ya daɗe yana mafarki Allah be ƙaddari zai yi ba, ɗansa yayi.
Major General Abdullah Ahmad Mai-doki, an officer of very high rank in the army. Sunan ma kawai idan an faɗa daɗi yake ma Mai maraba.

*Back to Story*

****
Sai da ya bar cikin asibitin gaba ɗaya sannan Mama ta koma ta zauna, sai taɓe baki take, ita dai bata san ko waye ba amman zuciyarta na nasalta masa babban mutum ne, sai dai alaƙar dake tsakaninsa da Namra ne ya tsaya mata a rai.
Bata jiyo abunda suke cewa ba, amman dai ta ga Namra ta tsaya ta yi magana da shi, rai ta ya sosu tana jin kamar tana taya ɗanta kishi, sai yanzu take jin rashin natsuwa a lamarin Namra ya saukar mata.

‘To idan bata san shi ba, ya za'ayi tayi magana da shi? Miye ma na wani biyota har asibiti? Ko ƙe tsakanin su Allah masa ni’

A baɗini take zancen, a zahiri kuma sai taja tsaki, ta gyara zamanta, tana kalle-kalle kamar baƙuwar asibitin.

NAMRA POV.

Tsaye ta tararda shi jikin window, yana kallon wani ɓangare na asibitin.
Har Sallamarta daya amsa be sa ya juyo ba, jar sai da aje abincin ta ƙarasa inda yake tana murmushi.

“Haka ake so Allah ya ƙara lafiya”

Ya kalleta a karkace, yana mai jindaɗi har cikin ransa, shi kansa ya san yana daf da komawa dai-dai, dan yana jin kuzari a jikinsa sosai, ga kumburin kansa nan duk a cire.
Shi kan sa ya san he has to fight for his life, just to achieve his goal, he needs so many things and many things need him, so there's no point of giving up.

“I'm just trying na ga samu sauki sun sallame mu Next week”

“Inshallah indai har kana takawa haka zasu sallame mu da wuri”

Ta faɗa tana shafa bayansa, daɗi har fal har cikin ranta. Bayan ya ci abincin ta zuba masa ruwa ya sha, sannan ya ɗauko masa zancen gyara gida.

“Har yanzu Mama bata je kasuwa ba”
Chapter 54 · 0% Book details