← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 173

Sashe 53

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ya zube”

“Ayyah Sorry”

“Sorry too”

Duk maganar da take masa yana amsa mata, kansa na saman nata ne, sai a sannan ya riƙa hannunta, ya matsar da ita daga jikin motar ya rufe motar, ya jata zuwa ciki.

A falo ya zauna, sai ta zauna kusa da shi, tana ɗan shafa bayansa, a tunaninta zubarwa cikin ne be masa daɗi ba.

“Doc kayi haƙuri Allah zai sake baka wani”

Ya kalleta.

“Haka ne, Kalsoom do me a favor”

“Na me?”

“Ki min alƙawarin zaki kula da yarana zaki basu kyakkyawar tarbiya, and komai suka yi ba zaki gundura da su ba”

“Baka da buƙatar na maka alƙawari, amman miyasa kayi min wannan maganar na?”

“Zan raba muku gida ne, da Rashida zan wareta daban, ke zaki zauna a nan tare da yara”

“Miyasa?”

“Ita ta buƙaci haka”

“Kuma ta yardar ta bar min yaran?”

“Eh amman ba na son ki faɗa musu hakan, ni zan yi magana da su, ko da sun dawo karki faɗa musu Mamansu ta kwanta asibiti”

“Okay”

Ta faɗa a sanyaye, ita dai ta san ba lafiya ba, yanayinsa da kuma hukuncin daya yanke ya tabbatar mata haka.

“Bari na haɗa maka tea”

Ta tashi ta nufi kitchen, zuciyarta da tunani kala-kala, ko dai Rashida ce take da hiv! Shiyasa yake ta mata tambaboyi a baya? Kuma yanzu zai raba ta da ƴaƴanta, ai ba zai raba ta da su haka kawai ba, kuma yadda take ganin damuwar nan ta masa yawa ta san ba'a raba ɗayan biyu ba.
Har ta haɗa masa tea ta kawo masa tunanin take.

Fuskarsa ta tsurawa ido sosai, lokacin da zata miƙa masa tea, tana son gano gaskiyar zarginta, idonsa sun rine irin na ɓacin rai ɗin nan da damuwa idan sun yi ma mutum yawa.

Har zata ce masa wani abu, sai kuma wata zuciyar ta hana ta, sai kawai ta zuba masa ido har gama shan tea ɗin ya tashi ya nufi ɗakinsa.
   Ita kam sai da ta gama abunda take sannan taje tayi wanka ta saka kayan bachi ta nufi ɗakin nasa, daman yau girkinta ne, ganin be shigo ɗakinta ba, ba zai hana ita ta kai kanta ba.

Washe gari har Kalsoom ta haɗa musu breakfast, idonsa biyu amman ya kasa tashi, jikinsa ya ɗibge kamar marar lafiya.

“Doc breakfast is ready”

Ta faɗa tana tsaye daga bakin ƙofa. Da ker ya ɗago kai ya kalleta.

“Je kiyi yau bana jin yunwa”

Ya unƙura ya tashi, ya nufi banɗaki. Ita kuma ta juya cikin rashin jindaɗi, ta fice. Wanka yayi ya fito, ya shiryar cikin ƙananan tufafi, ya feshe jikinsa da turare sannan ya fito falo cikin wani yanayi marar misaltuwa.

Ummu Faisak ya gani a falon zaune tana gaisawa da Kalsoom, tana ganinsa ta fara masa wani kallo ƙasa-ƙasa, sannan ta gaishe shi.

“Lafiya ƙalau ya ma su jiki?”

“Da sauƙi, ita ma tace na zo na ɗauko mata wayarta”

“Ta farka kenan?”

Kalsoom ta tambaya.

“Eh ta farka”

Kalsoom ta kalli Hilal

“Bari na tashi na shirya sai mu wuce tare na ganta”

“Ba yanzu ba”

Ya faɗa fuska ba yabo fallasa. Ba jira abunda zata sake cewa ba ya fice.
Kalsoom sai duk ya ji babu daɗi, Ummu Faisak ta buishi da kallon tana ayyana irin mallakar da Kalsoom tayi masa, har yake ƙoƙarin mantawa da Rashida a nan take, da ada ne aka ce bata da lafiya da duk ya bi ya haukaci amman yanzu dubu yadda rana ta fito be je ba, sannan ya hana Amaryarsa taje.
Wani dogon numfashi taja ta sauke irin an gulma ta tashi ta nufi ɗakin Kalsoom.

A hanyarsa ta zuwa Asibiti, Hajiya ta kira shi ta tambayi jikin Rashida, ya amsa mat d taji sauƙi, sai kuma g kiran Alhaji Bashir ya shigo, sai da Hilal yayi parƙing sannan ya ɗauki kiran suka gaisa sannan ya tambaye jikin Rashida.

“Ya Madam da jiki?”

“Jiki Alhamdillah, jiy ne ta samu miscarriage”

“Ayyah Allah ya bat lafiya”

“Amin Amin na gode”

“Dan Allah idan ka shiga, ka bani ita mu gaisa, Asma'u zata zo anjima Inshallah”

Ya kashe, sannan ya buɗe motar ya fita, duk inda y bi gaishe shi ake har ya isa ɗakin.
Wasu ƴan'uwanta ya tarar suna mata sannu ciki har da wasu Nurses da suke aiki gurin. Sai da ya fara gaida Momy sannan ya amsa gaisuwar da ƴan'uwan nata suke masa, ya nemi guri ya tsaya ya kafe Rashida d ido.

Momy ce ta fara fita sannan suma duk suka fita, ka barsa cikin ɗakin shi kaɗai sai ita, jin tayi kamar tace kar su fita, dan bata da idon kallon Hilal balle bakin yi masa magana.
Shi kuma ya tsare ta da ido kamar mai auna hawa da saukar numfashinta.

“Yanzu ba ki ji kunyar kan ki ba Rashida? Kina da aure ki bi wani namiji a waje? Wannan wane irin ƙazanta ne? Miyasa kika ɗauki zina ba komai ba? Idan kika mutu a yau mi zaki cew Ubangijinki? Me na rage ki da shi? Wanda kika bi miya fi ni da shi?
Ko kum kawai sheiɗan ne ya ƙawata miki yin haka? Kin manta ke uwar yara uku ce? Miyasa Zina ta burge ki Rashida? Ashe son da kika nuna min duk na ƙarya ne tun da har zaki iya ba wani halalina, kin lokacin da kike hana min kan ki a baya? A haka nake haƙuri ina bin ki har Allah yasa na haɗu da Kalsoom na aure, amman ko d mafarki ban taɓa tunanin aikata zina ba.

Tsakanin jiya zuwa shekaran jiya tausayinki nake, ina tunanin halin da zaki shiga idan babu a rayuwarki, amman yanzu nayi tunani baki buƙata na, sam ni da ke ba mu dace ba, nayi baƙinciki nayi nadamar da kika zama uwar ƴaƴana, faɗa min wanene wannan mutumen?”

Tun da yake maganar, bata balle shi balle tace wani abu, hawaye kawai take, irin hawayen nan da wani ke bin wani. Ya matsa kusa da ita ya ciro takardar take aljihunsa ya aje mata.

“Aure na da ni da ke yau ya ƙare, na sauwaƙe miki kije ki auri wanda kike ganin ya fi ni, ki dauwama ke da shi a duniyar da kuke son kasancewa”

Ɗagowa ta yi tmda sauri ta kalleshi, irin kallon nan da bata san tana masa ba, yau ta rasa gane duniyar da take, sama take ƙasa take, mafarki take ko gaskiya ne? Da gaske Hilal ne ko waninsa? Taya zata rayu ba da Hilal ba? Gidan ta da ƴaƴanta a yau sun zama mallakin kalsoom ba ita ba.

A saman gadon ta matsa can nesa ya rumgune kanta tana zubar ido kamar mai ganin aljanu. Ko kaɗan tausayinta a yanzu kam be ziyarci zuciyarsa ba, dan yasan ta cancanci fiye da haka, sai kawai ya juya ya fice daga ɗakin, cikin wani irin zafin rai da baƙinciki.

NAMRA POV.

Bata jin ko ta faɗama Anty Amarya sun yi wata, zat yarda dan ganin take kamar cewa zatayi shi ma haɗi ne, kuma bata iya tambayarta wani kuɗin, sai kawai ta kira ta da wayar Asim tace mata be bari ba yace ta bari har yaji sauƙi sai su zo tare, Anty Amarya bata jidaɗin hakan ba, sai dai babu yadda ta iya tun da mijinta ne.

Da dare Namra kasa, bachi tayi har sai da taje wani BQ dake maƙota ka d nasu ta nemi ƴar fulanin data zo ta taya ta kwana. Duk da haka har safe ba yi bachin kirki ba dan hankalinta be kwanta da gurin ba.
Da safe sai ta aika yarinyar ta siya musu ice su ɗora girki, a abun da bata taɓa ba a rayuwarta yau gashi zata yi. Kamin yarinyar ta dawo, sai taje waje ta ɗauko duwatsu ta haɗa murhu, kamin yarinyar ta dawo sai ta zauna saman bolcony tana kallon gidan.

Tunani take na ranakun baya, lokacin da Anty Amarya take saka ta girki da gas ko electric amman ta ƙi yi ta riƙa faɗin wahala, yau gashi zayi da abund bata ma taɓa gwada kunna wutar da shi ba, yau ga ta a ɗakin da babu katifa balle gado, duk wani abu mai muhimmanci a rayuwart i zuwa yanzu ta rasa shi.
Hawaye ne suka silalo mata sai tayi saurin gogewa, ganin ƴar fulanin ta doso inda take ɗauke d icen.

Sai kusan 12 ta gama girkin abun ka d wacce bata saba ba, sai ta zuba ma yarinyar ta zuba ma su Mama na su sannan ta zuba sauran a kula, sai ta janyo ruwa a rijiya, ta shiga banɗakin BQ ɗin tayi wanka, sannan ta fito ta shirya cikin atamfar jiya ta saka Hijabi ta ɗauki kular ta fito, yau kam a bakin gate ma ta samu Napep, tayi sa'ah an sauke wata ne, sai kawai ta shiga ya ɗauki hanyar asibiti da ita.
Suna kaiwa Babban titi, aka riƙa musu hannu akan su tsaya, amman ta hana mai Napep ɗin tsayawa, har sai da suka isa bakin asibitin. ta fito tana miƙawa mai Napep ɗin kuɗinsa, ta tsaya jiran ya bata canji, sai ta motar ta faka kusa da ita. Abdool ya fito ya nufo ta jiki na rawa. Kamin ya ƙaraso har Mai Napep ɗin ya bata canjinta ta kunna kai cikin asibiti, shi kuma sai sauri yake ya ci gabanta.

Mama na gurin zamanta ta sinƙayo yadda Abdool ya biyo Namra har cikin ward yana ƙoƙarin cin gabanta, sai ta tashi tsaye, ta matsa can baya tana leƙen su, ta tattara hankalinta gaba ɗaya ta mayar gurin.

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

                        _Written by_
*Khadeeja Candy*

*PAGE - 40*

NOT EDITED ⚠

“Haba baiwar Allah, Wannan wane irin jan'aji ne? Dan Girman Allah ki tsaya ki saurare ni”

Abdool ya faɗa yana haɗe hannayensa, alamar yana roƙonta. Girman Allah daya haɗa ta dashi ne yasa ta tsaya har ta ɗaga kai ta kalle shi.

“Malam ni Matar aure ce”

“Matar aure mai igiya uku ko kuma matar aure kalar aure”

“Matar aure mai igiya uku, dan haka kar ka sake bina”

Wani irin faɗuwa gabansa yayi, a take gumi ya fara zubo masa, a take launin idanuwansa suka canja.
Chapter 53 · 0% Book details