← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 173

Sashe 55

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Eh wai cewa tayi tun da ga wannan kuɗin Anty ta turo miki, ta ce a bar wacan a siye magani da shi, kin ga daman rantuwa tayi abunda yayi saura sai ta mai da mata”

“Kuɗin da Anty ta tura min har na biya bashin gado da su, sauran zan siye tufafi ne da wasu abubuwan kuma Anty tace na siye waya”

“Amman ai kin ci kin ga zinarin ki? Da kin siyar sai a ƙara ayi lalura, idan Allah yasa na warke sai na siya miki wani, wanda ya fishi ma zan siya miki”

Ta ɓata fuska tana kallonsa.

“Ni gaskiya ba zan siyar da zinari na ba, shi ƙadai ya rage min na kuɗi, kuma ko na siyar sana'ah zanyi da kuɗin, dan ba zan riƙa zuwa ina roƙon kowa komai ba”

Ya taɓe baki yana mata wani kallon.

“Hmmm Namra kenan, kina min kallon talaka ko? Har zan ce ki ranta min zinarin ki yi min complain, an faɗa miki zan dauwama a talauci ne hala? Kina ganin bana da mafitar da zan biya ki ko? Nima zan yi kuɗi Namra, zan yi arxiki irin kuɗin da baki taɓa mafarkin Asim zai yi ba, akwai buƙatar nayi kuɗi ko dan na rama bikin da aka min”

“Idan nayi magana zaka ga laifi na, haba Asim shikenan sai ace kullum nice zan riƙa biyar dangi ina roƙon su abu? Yau da gobe sai Allah, na rasa komai dana mallaka, sauran kuɗin nan daya rage min da shi nake cefane, kuma siyen abinci ba haƙƙina bane, kai Allah ya ɗorawa amman ka ɗauki kuɗin nan ka bawa Mama, idan nayi magana kace rantowa kayi alhalin kuɗinka ne na adashe!”

Dammm ya wulga mata wani kallo da mugun faɗuwar gaba. Ya akayi ta sani? Ina ta ji?Ko dai Mama ce tayi subul da baka ta faɗa mata. Ƙoƙarin kare kansa yake yana naɗe tabarmar kunya da hauka.

“Allah sarki rayuwa, talauci be yi ba, a yau har ni kike tunanin na ɓoye miki wani abu, yau ni kike yi ma gori akan kin siye abinci, ai ban san ba dan Allah kika aure ni ba sai yau, kina ganin kamar ba zan iya rayuwa babu ke ba ko? Kina ganin kamar da arzikin ki nake ci ko? Kina ganin ke kika min magani ko? Da gaskiyar Mama yanzu cewa za ayi duk ni na ƙarar miki da komai na ki, daman haka kike so ace na auro ki na zo na aje ki ina cin amanarki ko? So that ki samu damar fakewa da na yaudare ki, daman na san ba dan Allah kika aure ni ba”

Tun da ya soma kwarara zantukansa kallonsa kawai take tana mamakin kalamansa, wasu zantukan ma bata san inda suka dosa ba. Yau kam ya fara fito mata a kowaye shi, ya bayyana mata abunda zuciyarta ta soma zargi akansa.

“Na bar jindaɗin gidan mu, na zabe ka. Na watsar da karatuna na bika, saboda kar kace na yaudare ka. Na sadaukarda komai nawa saboda kai, amman duk ban tsira ba? Irin kallon da kake min kenan? Nice ya kamata ace na zarge ka tun lokacin da na ji abunda kuke magana kai da Mama amman na taushe zuciyata ina ƙoƙarin yaƙi da ita akan ka, ka kan nuna son iyayena su taimaka kama amman duk be sa na zarge ka ba, miyasa baka tausayina ne? Yanzu na gano dalilin rashin son da Mama take min, kuna min kallon wawuya wacce bata san ciwon kanta ba.

Son ka ne Asim shine ya rufe min ido na kasa ganin laifin ka, babu irin furucin da ba amin ba akan ka, amman na dage sai na aureka, a tunani na kana min irin son da nake maka ne”

Ta ƙarasa maganar murya ƙasa-ƙasa irin kifi musulmim nama, tana hawaye. Shi kam tsire baki yayi ya kalleta

“Kowa ya sani ba tsakani da Allah kika aure ni ba, sai da wanda zai aureki yace ya fasa sannan aka nemo ni, yanzu kuma kina son yin amfani da damar da kike da ita na rashin lafiya ki kula wasu mazan a waje”

“Me kake nufi?”

“Kin fi kowa sanin abunda nake nufi, waya kawo ki yanzu cikin asibitin nan? Ina kallon yadda ya rako ki ya koma, ko kin maidani mahaukaci ne, talauci ba yin kaina bane Namra, dan ina talaka ba zaki wulaƙanta ni a banza ba”

Ta miƙe tsaye tana masa kallon mamaki, har kofin ruwan dake hannunta ya zube.

“Ka zarge ni da komai, amman ban da Zina, dan ban sha nono ba, mahaifina be yi da ƴar wasu ba, dan haka ba za'ayi da ni ba, ban aikata zina ina budurwa ba, ba zan aikata da aurena ba. Kai butulu ne Asim wanda be san hallaci ba, ɗan bushiya mai soke uwar goyonsa a baya....”

Tasss ya watsa mata yatsunsa biyar a gefen fuskarsa, a zaune da yake, sai wani zanzana yake kamar ya riƙota yayi ta dukanta.

“Kim fita da ainahin kalar ki Namra, daman kin min duk abunda kika min ne dan wata rana ki min gori? To mina samu a auren naki? In banda baƙar ƙaddara miye ke bi na?”

Dafe kuncinta tayi ta juya a guje tana wani irin kuka mai taɓa zuciya, ta fice ɗaga ɗakin.

RASHIDA POV.

Kukanta ne ya shigo da su Momy a ɗakin. Duk tambayar da suka mata kasa amsawa tayi sai kuka take kamar wace aka cirewa rai.

“Ya sake ni Momy ya sake ni! Na shiga uku na lalace na ba ni Momy mutuwa zan yi, Wayyo Allah na”

“Me kika masa?”

Momy ta tambaya hankali a tashe. Ta kardar kawai ta iya nunawa Momy tana kuka sosai.
Da sauri Momy ta ɗauki takardar ta buɗe.

“Ni Hilal a yau na saki Rashida saki ɗaya”

Momy na gama karantawa ta rufe takardar tana faɗin

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Sai ta riƙata, ta zaunar saman gado tana girgizata, ganin tana ƙoƙarin fita hayyacinta.

“Ke Rashida kwantar da hankalin ki zan sa ya maida ke kin ji?”

Ta rirriƙe Momy gamgam tana zare ido.

“Da gaske Momy?”

“Da gaske mana, ki kwantar da hankalin ki kinji? Zan yi magana da shi”

“Toh”

Tayi zurun kamar sabuwar mahaukaciya. Sai kallon Ummu Faisak take wace ta shigo yanzu.

“Lafiya miya same ta?”

Ta ƙarasa da sauri tana tambaya. Momy bata iya faɗa mata komai ba ta fita ta kira likita, yayi mata allura, cikin ƙanƙanen lokaci ta samu bachi.
Sai da suka fito sannan Momy take labarta mata abunda ya faru cikin yanayin damuwa.

“Af ai da sauƙi tun da sakinta kawai yayi be kashe ta ba, ai a yanayin yadda ya bar gida na ɗauka yana zuwa zai kashe ne ma, kin ga yadda yake ji da matar nan? Hmmm”

“Aiko idan ka ganta kamar ta ƙwarai, ƙo dai wani abun ne ya haɗa su?”

“Ai haka ƴan matan zamani suke, suyi miki laflaf su kwace miki miji sannan su koreki, ai wannan saki daga gani bana banza bane mace na ciwon zubar ciki kuma asibiti gurin iyayenta? Hmmm”

“Ai yanzu sai an bincika za a ji ko minene, bari na faɗa ma Daddyn”

Cikin yanayin damuwa da ɗaurewar kai Momy take maganar.

Hilal ko da ya koma gida ya tarar yaransa sun dawo, daga gidan Hajiya, ko wanne fuskarsa babu walwala sun saka Kalsoom gaba, kamar su mata kuka.

“Hey kids”

Ya faɗa yana ƙokarin zaunawa sound so cool and funny. Sai duk suka nufo shi suna faɗar.

“Daddy wai Hajiya tace mana Ammyn mu ba lafiya tana asibiti”

Ya ɗan sosa kansa, sam ya manta yace kar Hajiya ta faɗa musu. Kalsoom dake ɗauke Rafiq ta nufo shi tana faɗin

“I try to explain but.. ”

Da ido yayi mata alama da tayi shiru yaja hannunta ya zaunar da ita kusa da shi, ya kalli yaran.

“Listen kids Maman ku ta ji sauƙi sosai, har ma tace na gaishe ku”

“Daddy ina son na ganta”

“Ba zaki ganta yanzu ba, amman ajima zan kira miki ita a waya ku gaisa”

“Tau”

Ulfah ce ta wayance, jin ance taji sauƙi, Ezzah kam ƙin sakewa tayi sai ƙoƙarin kuka take.

“Duk sun ci abinci, amman ita ta ƙi ta ci”

Ƙalsoom ta faɗa tana kallon Ezzah. Hilal ya kai hannu ya riƙo hannunta.

“Sweetheart ki ci abinci kin ji? Mamanki tana nan lafiya”

Kai kawai ta ɗaga masa ta share hawayen da suka zubo mata, ta nufi ɗakinsu.

******
Rashida bata farka ba sai dare, tea aka bata ta sha sannan ta kora da magani. Yanzu nen abunda ya faru ɗazu yake dawo mata, a ƙwaƙwalwa, da sannu-sannu take tuna komai, sai ta gane ashe ba mafarki ne take ba.
A hankali hawaye masu zafi suka fara sauko mata, zuciyarta na ƙona kamar garwashi.

Taya zata juye rayuwa babu Hilal? Taya zata bar ƴaƴanta a hannun Kalsoom? Yanzu me zata faɗawa iyayenta? Ga kuma ciwon dake jikinta, da wannen zata ji? Wani irin kuka take irin kukan nan na baƙinciki da baka son kowa ya ji.

Wayarta ta janyo ta buɗe password ɗin, kamin ta taɓa komai sai ga saƙwanin sun taso sama, na mutane da kuma mtn.
Na number Amira ta fara buɗewa, cikin ƙarfin hali ta ƙaranta, ta yi reply sannan ta aje wayar gefe tana kallon ƙanwarta Sa'adatu take bata haƙuri.

“Momy tace zatayi ma Daddy magana sai su yi magana da Hilal ɗin”

“A'a bana da buƙata nice nace ya sake ni, karki bari Momy ta kira shi, kije kice nace karta kira shi”

“Amman Adda...”

“Kawai ki faɗa mata, nice nace ya sake ni, kije ki faɗawa Momy”

Sa'adatu ta tashi ta fice tana hawayen tausayin ƴar'uwarta. Rashida ta share hawayen da suka zubo kata tana kallon wayarta dake ringing.
Number Hilal ta gani, har tayi kamar karta ɗauka, sai kuma ta danna picking ta kara a kunne, muryar Ulfah ta ji tana mata ya jiki kamin Ezzah ta karɓa.

“Ammyn wai kin ji sauƙi?”

Cikin yanayin damuwa Ezzah ta tambaya, sai kawai Rashida ta fashe da kuka.
Chapter 55 · 0% Book details