← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 173

Sashe 159

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Gari zan shiga, amman zan dawo ajima saboda zamu je wani biki da za'ayi a faɗar Mai Martaba, kuma an gayyace mu kinsa ɗansa abokina ne”

Ya faɗa irin yana alfahari ɗin nan.

“Okay to a dawo lafiya, kar dai aje ayi gane-gane”

“Ni wa zan gani, ga ni da ke cikin gida”

Matsowa ta yi ta masa kiss, sannan ya juya ya tafi tana ɗaga masa hannu.

WHAT DO YOU EXPECT NEXT...?

[7/28, 10:15 PM] Khadeeja Candy♥: *91*

Kamar yadda Ummi tace mata a duk ɗakin da ta shiga ta kan zauna a tsakiyar ne har ta gama gaisuwar ta tashi, bata yarda ta haɗa ido da matan mai martaba. Sai dai a yadda take tararda ko wanne falo tana auna yawan family da mai martaba yake da su a gidan, wata ƙila kuma saboda tana amarya ne suke zuwa ganinta.
Bayan ta gaishesu aka kaita ɗakin Hajiya Shafa, sai aka kawo musu abinci da drinks. Bata ci komai ba duk kuwa da irin matsa mata da suka riƙa yi. Ana yin sallah magariba duk suka shiga shiryawa, wasu motocin Abdool ya aiko aka ɗauki su Maryam aka mayarda masaukinsu domin suma su shirya. Bayan sun wuce wata cikin ƴaƴan Hajiya Shafa ta shigo tana faɗin.

“Hajiya tace Mai Makeup zata zo ta gyara miki fuskarki, kuma za a kawo miki kaya ki canja”

Namra ta amsa da to. Har Amal ta buɗe baki ta gatsawa yarinyar magana sai Meesha ta riga ta.

“Ai ko har Ummi ta yi magana da mai Makeup zata zo yanzu ta mata”

“Auoak”

Yarinyar ta faɗa sai ta juya tana tafiya cike da isa ta fice. Amal taja tsaki tana binta da harara.

“Wai yarinyar nan tun ɗazu nake ganin tana ta wani shauƙi”

Meesha ta zaro ido.

“Ina ruwanki? Amal me yake cikin kan ki?”

“Aljanuna akai na”

“Ƴar gadon baƙar magana duk abunda kika yi sai na faɗawa Ummi”

Ta tsuƙe baki ta juyarda fuska. Around eight o'clock mai Makeup ɗin ta iso. Namra bata yarda an mata makeup ɗin ba sai da ta yi sallah isha'i.

Ƙarfe tara dai-dai Abdool ya aika aka kwaso ƴan'uwan Namra aka kaisu tsohuwar faɗar Mai Martaba inda aka shirya taron.

Sai tara da kwata Amarya ta iso barori na take mata baya, farin lace ne mai shegen kyau da farar Alkyaba, fararen takalmi da farar sarƙa, mai video na biye da iya ita yana ɗauka har aka ta kai zamanin da aka tanadar mata dan ta zauna. Bayan kamar minti biyar da zamanta Abdool ya shigo shi da abokaninshi, farar shadda ce jikinshi da fararen takalma sai farin rawani da farar alkyaɓa, kallonsa take kamar yadda kowa yake kallonsa, ita kanta ta san ta yi sa'ar miji, yadda yayi mata kwarjini da haiba ga fuskarsa sai annuri take, ɗaya bayan ɗaya yake tafiya ana masa kirari ana koɗashi. A kujerar da Namra take zaune ya zauna sai masu busar suka koma gefe suka cigaba da busar. Ko ina ka duba masu kaki kake gani sun cika gurin wato gayyar Abdool ne kawai sai kuma na ƴan'uwansa. Saboda Mai Martaba be gayyaci kowa ba walima ce da ya shirya a cikin gidanshi domin addu'ah kawai da kuma son tara family ɗinsa guri ɗaya, wannan walimar ta al'ada ce da ya saba shiryawa a duk lokacin da ya aurar, ko da kuwa mace ce zai gayyato mijinta azo gidan ayi walima.

Yara da rabi Mai Martaba ya iso, daman matanshi sun daɗe da isa gurin tun kamin amarya da ango su isa. Karatun alqur'ane aka buɗe filin da shi sannan Hajiya Shafa ta miƙe tsaye ta karɓi microphone tana yi ma kowa barka da zuwa.

ASIM POV.

Tsaki yake ja lokaci zuwa lokaci kamin ya kalli wanda ya shigo motar yanzu ya ce.

“Kaga Mubarak bana son jira, na tsani jira wallahi, ni da nasan haka zaka ɓata min lokaci ba zan je ba wallahi”

Mutumen ya kalleta yana murmushi.

“Sorry Man ai gani na zo yanzu”

Asim ne yake driving har suka isa Kan wurin sarki, ba a basu damar shiga ba duk da guest pass ɗin da suka nuna, sojoji ne jibge a gurin babu abunda suke sai kai da kawo suna ta ƙoƙarin ganin su bada tsaro agurin. Har Asim yaja motarsa su koma sai Abokinshi ya hana shi.

“Bari na kira shi”

Wayarsa ya fiddo ya kira wayar ƙanen Abdool wanda suke uba ɗaya wato Zayyan.
Bayan ya faɗa masa abunda ya faru sai ya miƙawa Sojan wayar suka yi waya, sannan aka buɗe musu page ɗin suka shiga. A gate na buyu aka nuna musu inda zasu faka motarsu, sannan suka fito sojoji suka tantance su sannan aka buɗe musu gate ɗin suka taka da ƙafa suka shiga harabar gidan.

Ba Zayyan ne kawai a gurin ba, domin yasam abokansa da yawa sun je bikin dan haka ya kira wani abokinsa yayi directions ɗinsu inda ake bikin saboda gidan ya kasu kashi kashi. Fitowa yayi ya shiga da su saboda yasan duk yadda zai faɗa musu ba ganewa zasu yi ba.

Wani kalar baƙauye Asim da abokinshi suka zama tun a bakin ƙofar shiga, a takw ya manta da a katsina yake, saboda gurin ya koma kamar sabuwar Abuja, daman tun farkon shigowarsa gidan ya gane shi ɗin ba kowa ba ne a cikin masu kuɗi, dan ya fahimci ko akaifar Mai Martaba be kamo ba indai akan dukiya ne. A bakin ƙofar faɗar ma sai da aka tantance su sannan aka basu guri suka sshiga. Ko da suka shiga Malama Hauwa na tsaye tana gabatarda ƙasida akan haƙoƙin mijin aka mata. Har Asim ya zauna be gane Namra ba ce saboda ta canja gaba ɗaya ta koma kamar ba ita ba, sai da ya gama gaisawa da waɗanda ya sani a gurin sannan ya zauna ya natsu tare ta tattara hankalinta gaba ɗaya ya mayar gurin mai wa'azin. Kama da Namra yake gani a fuskar Amaryar sai dai wannan kamar ta fi Namra kyau da haske, baya iya ganin angon saboda rawanin da ya rufe masa fuska.

“Kamar Namra wallahi”

Ya faɗa a fili yana kallon abokin na shi, fuskarsa with so much confused.

“Wacece Namra?”

“Matata mana”

Har abokin yasa dariya sai yayi saurin rufe bakinsa tunawa da inda suke.

“Haba Asim kamar wanda ya sha wani abu, matarka ɗan sarki zai aura? Look at you”

Ya ciro wayarsa ya kira yaron daya saba bashi labarin halin da Namra take ciki sai aka yi rashin sa'ah be ɗauka ba. Sai kawai ya kira wani abokinsa da ke sokoto dan gaba ɗaya natsuwarshi ta bar jikinshi. Miƙewa yayi tsaye da zimmar fita daga gurin saboda ƙarar loudspeaker ba zata bar shi yayi magana yadda yake so ba, miƙewarshi ke da wuya ya hango Maryam ta je tana magana da Namra a kunne.

“Wallahi wannan Matatace, Namra ce Wallahi”

Abokin yayi saurin riƙo shi ya zaunar domin shi kaɗai yake jin abunda Asim ke faɗa, hankalin kowa yana can gurin amarya da ango.

“Matata ce wannan wallahi”

“Na ji matar ka ce muje gida”

Ya faɗa dan yana ganin kamar Asim baya cikin hankalin kansa.

Asim ya fisge hannunshi zuciyarsa na mugun bugawa da ingizashi yayi duk abunda zai yi.

“Baka yarda da ni ba?”

Biyu daga cikin mutanen da suke gurin ne hankalinsu ya dawo gurin Asim, har ɗayan ta tambaya ganin yadda Asim ke hucin hanci.

“Wai miya faru ne?”

“Wannan matar yake cewa Matarshi ce”

“Asim ko ka sha wani abu?”

Ɗayan ya faɗa yana kallonshi.

“Babu abunda na sha gaskiya na ke faɗa wallahi, matatace wannan”

“Ka rufa mana asiri mu fita gurin nan lafiya, wane irin matarka wai? Matarka zata fita daga gidan ka ta auri wani?”

“Tana gidansu ai tana gidansu, ita ce matata ta farko da na fara aure”

“Ka sake ta ko? Shi kuma ya aura ai daman na ji ance bazawara ce ya aura”

“What...? Wallahi wannan Namra ce”

Zayyan ne ya juyo yana kallon Asim dake kumfar baki, yana sauraren abunda yake faɗa, sai ya baro mazauminsa ya dawo kusa da Asim ya zauna yana faɗin.

“Ina fatar dai lafiya”

Da lafiya ƙalau duk suka amsa mashi suna murmushi, sai Asim ya girgiza kai ya ce.

“Ba lafiya ba, wannan matar matatace wallahi”

Wani wawan kallo Zayyan ya aika masa.

“Baka da hankali Asim wallahi, ƙa fara shaye-shaye ban gayyace ka a nan dan ka ɓata min rai ba, tashi ka bar gurin nan”

“Kana tunanin bana da hankali ko?”

Asim ya nuna kanshi yana ƙoƙarin tashi tsaye..
[7/30, 7:12 PM] Khadeeja Candy♥: *92*

Zayyan yayi saurin riƙe shi

“No karka ja kanka wahala a gurin taron nan, muje waje na saurareka wata ƙila kana da hujja”

Yana faɗar haka, ya miƙe tsaye suka fita daga faɗar suka nufi wani ɓangare na masarautar sai ga wasu abokansa sun biyo bayanshi.

“Faɗa min taya wannan matar ta zama matarka?”

Asim ya natsu sosai yana tsara irin ƙaryar da hankali zai ɗauka.

“Wannan yarinyar sunanta Khadija amman Namra muke kiranta, sunan mahaifinta Manjo Usman Zamau a sokoto yake da zama, ni kuma ai kasan ɗan sokoto ne ko? A can muka haɗu da ita a makaranta iyayenta basa so na a haka muka yi aure daga baya itama ta fara tsanata sanadin hakan ta gudu da cikina kuma ba gidansu ta koma ba sai taje wani gurin daban domin na aika nemanta a gidansu aka ce bata zo ba, daga lokacin ban sake sakata a ido ba, sanadin hakan nayi aure na auri Mardiya yanzu kuma ga wannan amaryar da na yi, kuma ta inda na tabbatar da wannan itace tana da ƙanwa Maryam wacce ta yi magana da ita a yanzu”

Zayyan yayi shiru yana nazari, tabbas ɗan'uwansa bazarawa ya aura kuma ƴar sokoto idan be manta ba kamar Mai Martaba ya taɓa faɗa masa ƴar tsohon soja ce bayan haka kuma sunanta Namra.

“Amman kai baka sake ta ba?”

Abokinshi ya tambaya.

“Idan na saketa mi zai sa na zo yanzu na ce matatace”

“Lallai akwai jan aiki, ta yaudari Abdallah kenan”

Zayyan ya faɗa yana zuba hannayensa a aljihu.

“Ka min wani lamani mana Asim, ka haƙura har a gama walimar nan sai na samu Mai Martaba na faɗa masa”
Chapter 159 · 0% Book details