← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 173

Sashe 164

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da ke labartawa Mardiya abunda ya aikata ta cika da tsananin mamakin da al'ajan ita kanta idan bata manta ba ya taɓa faɗa mata ya saki Namra.

“Amman Asim ba ka sake ta ba?”

Ya warga mata wani mugun harara.

“Uban waye ya saketa? Na sake ta zan dawo na ce matatace? Ko da na na sake ta a dole ta bani ɗa na domin da cikina ta gudu, wallahi duk abunda za'ayi sai dai ayi amman sai na dawo da Namra gidana”

“Taya zaka dawo da ita gidanka bayan ta zama matar wani? Ya kake magana kamar wanda baya cikin hankalin kansa”

“Hankalinki na ara na ke amfani, sakaryar banxa a duk ta fiku dan ita ba kuɗi na take so ba ni take so, kuma tana zuwa nan ta samu ciki ku fa kin je ki ɓarar da mahaifarki kin zubar da yaranki tun kamin ki shigo gidan ni nayi nadamar aurenki Wallahi”

Magana yake kamar zai cire haushin dake ransa a kanta. Ita kan zuciyarta ya kawo sosai dan me zai aibantata.

“Karka so ma min maganar banza kana son matarka ka sake ta ka auro ni, ba nan kake faɗar laifinta ba, sai yanzu dan ka gama more jikina sannan zaka ce kayi nadamar aurena? Ai ni ƙara ma da Allah yasa ban haihu da kai ba, mutum kullum sai kusanceka sai dai yabi ta bayanka ba ta inda Allah ya hallata masa ba”

“Ai dan kuɗina kika auri ne ba dan kuɗi na ba zaki aure ni ba, ƴar iskar banxa mai bin mazan waje”

“Ai ni wallahi allura ce cikin ruwa ko da kuɗinka sai da rabonka, yanzu ai ka auro wacce ta fini ko? Gata nan na gani”

“Namra dai zan dawo da ita sai dai ki mutu, ai ga alhakin mutane nan saman kanki kullum cikin gobara kike, ɓarauniyar banza ko ɓera be kaiki sata ba, duk inda nayi ajiya a gidan nan sai kin ɗauka, jahilar banza ashe ma ko karatu baki yi ba, shiyasa kike nan kamar dabba”

Ƙyalƙyalewa tayi da dariya.

“Mahaukacin banza Namra kan ta maka nisa sai gani sai hange daman can ba ajinka ba ce nice daidai kai, Namra kan ta yi gaba shine kake mata hassada ko? To Wallahu kayi kaɗan kai da dawo da Namra a gidan nan sai dai mai sunanta, ko kuma a mafarki daman can baka san tana da martaba sai yanzu”

“Wallahi kika sake wata magana marar daɗi sai na sakeki a cikin daren nan, kuma ki zuba ido ki gani kina cikin gidannan zan daqo da Namra sai dai ki mutu, wallahi ko zaki ran rasa raina ne sai na dawo da ita, ita ai nasan tana so na”

Tsire baki tayi ta tashi ta bar masa gurin zuciyarta cike da ɓacin rai. A daren daga shu har ita da tsoro suka kwana saboda tunanin ko sojojin zasu sake biyoshi su zo gida su hallakashi.

Da safe jikinsa sai ya ƙara yin tsami har idon ɗaya ya kumbura, ɗayan kuma daman tun jiya ya kumbura. Ƙafar da yake tsingilta da ita sai ma ya kasa takata gaba ɗaya.
   Yana son yace Mardiya ta ɗora masa ruwan zafi ya gasa jikinsa amman babu dama tun da sun yi faɗa tun jiya da dare. Haka ta riƙa mulmula saman tabarmar dake falon sai tunanin yadda zai ɓullowa lamarin yake. Yana haka sai ga dogaran Mai Martaba ya aiko a tafo da shi, babu ruwansu da uzuri balle su tausaya masa umarnin Mai Martaba suke bi kuma ya zame musu dole su cika shi. Da aka je da shi can ne Mai Martaba yasa ya kira ƙanen Mahaifinsa da na mhaifiyarsa ya sanar da su halin da ake ciki, sannan ya kira waɗanda suke bakori
ya sanar da su halin da ake ciki. Mai martaba da kansa ya aika da Mota aka ɗauko na bakori sannan ya aika ɗayar a sokoto dan a ɗauko wasu daga cikin familynsa.

LAMIDO POV.

Tun da ana sauran kwana uku a fara bikin Namra ya bar gidan saboda baya son wani abun da zai kusantarda shi ga bikin. Sai dai a gida su Neina basu yi mamakin hakan ba, daman sun sa ran haka zai faru, tausasa masa zuciya kawai neina ta riƙa tana faɗa masa ita da shi ɗin basu dace ba, sai dai ta nuna masa jindaɗinta akan kyautar da Abbah yayi masa na kuɗi yace a kawo musu, ga kuma aikin da yace an samo masa, sai duk suka riƙa murna suna faɗin zaman Namra yayi musu amfani a gidan.

Uwani ce ta riƙa cewa ta so ta ga Namra amarya, daman komai yana da lokaci gashi ya wuce har suke ɗauko zancen zaman da tayi a gidan suna yaba tarbiyarta da kuma irin haƙuri da tayi da zama da Asim duk da basu sanshi.

A duk dare Lamido yana kwantawa da tunanin Namra a ransa, har ga Allah yana son Namra kuma ya so ya aureta saboda kawai ya nuna mata ba duka talaka ne azzalumi ba, kuma yaso ya tarairayeta ya muna mata rayuwar jindaɗi sai dai Allah be nufa ba a dole ya barwa Allah komai. Ko da yaushe yana ƙirga kwanakin da aka ƙara na bikin har aka kai asabar ranar da aka aka ɗaura mata aure, ranar wuni yayi kamar marar lafiya gaba ɗaya yaƙi ya sake ko abinci kasa ci yayi,Neina ta lura da hakan ta saka shi a gaba tana nuna masa halin rayuwa tare da ƴi masa tambihi akan abunda duk Allah be rubuta naka bane ba zai zama naka ba, tayi masa nasiha sosai wacce ta shiga jikinasa kuma ya yarda da hakan ɗin Allah ya ƙaddara babu yadda ya iya.

Ranar Monday da safe Abbah ya kira shi bayan sun gaisa Lamido yake tambayar ya hidimar biki, sai Abbah ya roko masa da zancen yana son su haɗu a Katsina yau.

“Lafiya Abbah”

“Lafiya ƙalau, ina son mu haɗu da kai acan kuma bana son ka rigani isa dan haka ina son ka tashi tun yanzu”

“Ok inshallah, amman a ina zan sauka?”

“Idan ka shiga Katsina ka kira ni”

“Okay Abbah”

Daga haka ya katse kiran zuciyarsa cike da ruɗani, yasan Abbah ba zai nemi ganinsa haka kawai ba, amman kuma me yasa yake son su haɗu ɗin kuma a Katsina? Haka yaƴi ta saƙe-saƙe har yaje ya gaishe da Neina ya faɗa mata sai kawai tayi masa addu'ah ta kuma bashi ƙwarin guiwar zuwa.

Ɗumamen da Uwani ta yi yaci ya kora da ruwan tea sannan ya shiga yayi wanka ya shirya cikin ƙanƙanen lokaci ya kama hanyar Katsina zuciyarsa cike da zullumi, sai dai hausawa sunce karka ji tsoron kira kaji tsoron laifin da ka aikata.

NAMRA POV.

Ummi na fita sai ta ɗalle gadon ta lumshe ido tana da shakar ƙamshin turaren Abdool dake jikinta saboda rumgumar da yayi mata ɗazu da safe. Meesha ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo sai ta shiga bathroom ta haɗa mata ruwan wanka mai ƙamshi da ɗumi, bayan ta haɗa ta fito ta nufo gurin da Namra take ta ɗan taɓa ta kaɗan tana murmushi.

“Adda Namra zaki yi wanka za a maida ƙe gidan Mai Martaba, kuma ga wasu nan zuwa su ganki”

Namra ta buɗe idonta dake cike da hawaye ta miƙe tsaye, sai Meesha ta ɗauko mata tawul sai dai Namra bata ɗaura tawul ɗin ba ta sai da ta shiga bathroom ɗin. Ta samu ƙarfin jiki sosai lokacin da tayi wanka ruwan zafin ya gasa mata jiki sosai, ga ƙamshim turare kamar karta fito.

Ko da ta fito ta samu shadda ash color saman gado aje da mayafi ja kamar yadda aikin shaddar yake, sai kuma kayan ciki wato underwears. Bata shafa mai ba dan bata jin yin wani kwalliya gaba ɗaya hankalinta baya jikinta, sai kawai ta ɗauki shaddar ta saka ta ɗaura ɗankwalin ta ɗauƙi jan mayafin ta yafa ta zauna gefen gado tana murza yatsun hannunta. Sai ga Haleema ta shigo da turen abinci Meesha kuma ɗauke da drinks.

“Ummi tace ki ci abinci Mai Martaba ya aiko kiranku tare zaku je”

“Ba da ita zamu yi walima ba?”

Meesha ta tambaya

“Haka Ummi tace wai ko basa nan za ayi walima”

Tashi suka yi suka bata guri yadda zata samu ta ci abinci. Amman har suka dawo yadda suka bar abincin haka suka tararda shi, Meesha ta lallaɓata akan ta daure ta ci abinci amman ta ƙi ita yanzu ba abinci ne a gabanta ba.

Sai da aka fita da ita aka sakata cikin mota sannan Ummi ta dawo ɗakin ta sake wani shirin ta fito tana kiran Hajiya Sadiya da wata ƴar'uwarta guda ɗaya wacce zasu je tare. Amman sai Hajiya Sadiya ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ba zata je ba, aka yi aka yi tace ba zata je, har sauran ƴan'uwanta suka ce a canja aje da wata mata sai kawai Ummi ta kashe ƙafafunta da cewar ai ƙara ita dai tun da Asim ya taɓa mata aiki kuma har tasan da sakin Namra. Ba su ba har Namra sai da tayi mamakin jin kalamin Ummi, domin Asim be taɓa faɗa mata cewar yayi aikin a gurin Hajiya Sadiya ba, sai a lokacin ta tuna da ya taɓa faɗa mata uwar ɗakinsa ai macece. A nan kowa ya saka baki akan ƙara ita taje ɗin saboda tasan shi, sai ta sake nuna ƙin son zuwa ɗin a nan wasu kecewa ko dai tasan da wani abu ne idan ba haka be mai xai haka taje bada shedan akan matar ɗanta tun da Abdool zama ɗa yake a gareta.

“Bama fa lallai Asim ɗin yaje ba saboda Mai Martaba ne ya kira ni yace na zo da ita da kuma wasu ƴan'uwana ba lalle bane ya zama Asim ɗin yana nan, wata ƙila ma wani zancen ne zai yi daban”

Cewar Ummi tana ƙoƙarin kawar da Hajiya Sadiya tunani, sai dai hakan be hana ƴan uwanta tursasa taje ɗin ba. Babu yadda ta iya a dole ta shiga motar aka je da ita, uta kanta ba dan tana gudun abunda zaije ya dawo ba da babu abunda xai hana ta faɗi gaskiya game da Asim.
Chapter 164 · 0% Book details