← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 173

Sashe 93

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin faɗa Meesha ta ƙarasa tana jin kamar ta kama Haleema tayi mata shegen duka. Ita Haleema ji take kamar ta daki yar'uwarta. Har sai da Ummi ta katsa musu tsawa.

“Haleema kar na sake jin irin wannan kalamin a bakin ki, Aisha ke kuma ya isa tun da ba cewa aka yi za a aura masa ita ba, ku Shafa min lafiya dan Allah ku tashi ku bani guri”

Duk miƙewa suka yi suka fita, ban da Amal data laƙe jikin Ummi ita ala dole sai an dafa maya makaroni.

“Ai kema kin iya dafawa, Amal har mota kike tuƙi fa amman ki zo kina min abu kamar jaririya, idan yanzu aka miki aure ai sai zama dan kin girma, ba kece auta ba autana tana nan zuwa”

Ummi ta faɗa da raha a fuskarta. Amal ɗin tasa dariya dan tasan abu ne mai wahala a yanzu.

“Za a ce tsohuwa ta haihu”

Ummi ta tiƙi bayanta tana dariya

“Yes Tsohuwa maman Amal, tashi ki cire uniform”

Tashi ta yi ta fice tana dariya.

*NAMRA POV*

Kamar yadda suka saba yi duk mai ciwo, bayan ta faɗa masu matsalarta sai suka bata gwajin jini da fitsari, suka sa kuma taje ta yanki sabon kati dan duba wacan matsalar nata na robar dake hannunta dan a bayanin da ta yi ma likita ya fahimci ciki ne a jikinta. Sai dai bashi da tabbacin haka tun da ta faɗa masa tana saye da roba, duk da yasan ana samun irin wannan matsalar a wani lokaci.

Awan fitsari kawai ta samu yi, a take, na jini cewa suka yi sai da yamma ta zo ta karɓa, su kuma waɗanda zasu dubata a ɓangaren robar sun tashi aiki.
Tun da karɓo results ɗin ta kasa ta buɗe dan bata son ta ga abinda yake ciki, tasan idan har ciki ne tana cikin matsala dan bata gama warkewar ciwon mahaifarta, kuma ga roba jikinta ace tayi ciki tasan duka ƙarin matsalar ne. Ko da ta koma gurin likitan yana shirin tashi, har ya haɗa kayansa, a tsai-tsaye ya duba takardar tana fuskarsa da mamaki ya ce

“Kina ɗauke da juna biyu”

Ras ras ras gabanta ya faɗi, sai ta faɗi saman kujera tana hawaye. Da sauri likitan ya aje kayan hannunsa.

“Hey wannan ba wata matsala bace ana samun irin haka daman, amman abunda yafi zan rubuta miki hoto sai kije ayi hoto a bincika lafiyar cikin, kuma ki tabbar kin je an cire miki wannan robar”

“Doc mahaifa tana da matsala shiyasa aka samun robar”

“Ba lallai ne har yanzu matsalar ki tana nan ba, shiyasa nake son ki yi hoton”

Ya ɗauki wata takardar yayi rubutu ya miƙa mata.

“Kije ayi miki hoto, zuwa gobe sai ki kawo na duba ki, ko kuma ki dawo wani likitan ya duba ki, ki kwantar da hankalin ki ba wani abu nima mai ɗaki na ta taɓa haka”

Jakarsa ya ɗauka ya rataya ya face. Sannan ita ta tashi ta fito tana hawaye, maimakon taje gurin hoton sai kawai ta yanke shawarar komawa gida dan ita har yanxu jikinta na bata ba ƙalau take ba, balle bata da kuɗin da zasu isheta hoto tun katin ganin likita na asibitin ma kusan ɗari bakwai ne.

Tun cikin Napep take ta kiran Asim amman ya ƙi ya ɗaga saboda yana gaban Hajiya, wacce ta zame masa kamar uwa a yanzu, yadda yake jinta ko Mama data haife sa baya jinta haka nan.
Hakan yasa ta yanke shawarar tura masa saƙon karta kwana.

Ƙin ɗaga wayar yayi dan akwai yana gaban Hajiya, ita ta jidaɗin hakan da yayi ko ba komai tasan ya girmamata, gashi tun da yazo gidan be taɓa fita da sunan yaje gida gurin matarsa ba.
Sai da ta gama lissafa masa abunda zai siyo mata sannan ta bashi kuɗin tana murmushi ciki ladabi ya karɓa ya tashi ya fice.

Sannan Hajiya tayi murmushi ta maida dubanta ga ƙawarta, Hajiya Ubaida.

“Gaskiya yaron nan yana da ladabi ina kika damo shi?”

“Uhmm tsuntsune daga sama gasasshe Allah ya bani daga gyaran gate”

A nan ta kwashe labarin komai ta bawa Aminiyarta yadda suka haɗu da sharaɗin data gundaya masa da kuma zaman gidan da yake, da kuma ƙudirinta a kansa.
Hannu Hajiya Ubaida ta bata suka taɓa

“Shegiya Sadiya duk abunda kika sawa gaba sai kin ga bayansa, hala yarinyar mai kyau ce?”

“Tana da kyau wallahi ta haɗu ba ƙarya, sannan kin ga na samu dama biyu, daman Alhaji Usaini ya dame ni na samo masa sabin shiga, wai duk wanda nake kai masa basa da ladabi kuma an taɓa amfani da su, kwana biyu sai su fara masa tsageranci”

“Ai kin san manyan mutanen nan sun fi son tsaida mutum ɗaya, wanda zasu riƙa amfani da shi kullum”

“Eh shi ma haka yace, wai idan yana bin irin guys ɗin nan za'a iya gane shi, yafi son tsaida mutum ɗaya, kuma kin ga irin wannan zai fi jindaɗinsa dan ga alama zai yi ladabi, sannan garin su ɗaya, idan ta kama ya koma can ma, ni sai ya barmin matar a nan, dan ba zan taɓa nuna masa ina don matarsa ba, shi wata rana zan iya buƙatarsa”

Hajiya Ubaida ta ƙalƙyale da dariya.

“Ke Allah dai ya yafe mana, ya shirya mu”

“Amin kedai ai ina son tuba amman sai nan gaba, dan bana son Zeenat ta san halin da nake ciki”

“Gaskiya kam, ai ƙara ai daina da wuri kar azo aji kunya”

Hajiya Sadiya tayi fuskar tausayi kamar mai tsoron Allah da gaske, tana kallon Hajiya Ubaida wacce sana'arsu ta zama ɗaya.

*ASIM*

Be wuce kasuwar ba, sai da ya bi ta gida dan jin abinda Namra zata faɗa masa, badan saƙonta da yaga ni babu ma abunda zai sashi bi ta gidan. Kamar baƙin haɗari haka ya doshi gidan bakinsa ƙumshe da maganganu kala-kala, dan gani yake a yanzu shi ma ya kai matsayin da zai iya faɗawa magana son ransa, balle Namra da yake gani kamar banza.

A ɗaki ya tararar da ita kwance sai hawaye take. Daker ta ɗago ta kalleshi, duk da tana cikin yanayin damuwa hakan be hanata, kallon irin shigar dake jikinsa ba. Takalmin dake ƙafarsa kaɗai zasu iya kaiwa dubu 10+ balle wando da T-shirt.
Be ji zai iya zama a ɗakinba, sai kawai ya tsaya jikin ƙofa yana mata wani kallo, azuciyaraa yake hantararta ganin yadda ta ƙara lalacewa.

“Ya aka kika samu ciki?”

Wani kallo tayi masa zafin furucinsa yana zuciyarta.

“Kamar ya? Ina da wani mijin ne bayan kai”

“Ni ya za'ayi na sani, yanzu ai ba a shedun mutum”

“Shigowarka Asim irin wannan furucin zaka min? Tun da kasa ƙafa ka bar gidan nan babu ruwanka da ni kamar ba matar ka”

“Ya kike so nayi Namra aikin zan bari na zo na tisaki gaba nayi ta kallo ko me? Yanzu ma a hanya nake saƙon da kika min ne yasa na biyo”

Kawarda kai tayi ta haɗe hawayen da take da tabbacin idan har suka fara zubar mata bata san lokacin tsayawarsu ba.

“Daga Asibiti na ke likita ya ce ina da ciki, kuma akwai roba a jikina”

“To ya aka yi haka?”

“Nima ban sani ba, amman yace min daman akan samu hakan wani lokaci, yace naje nayi hoto aga lafiyar cikin, Asim ina tsoron ko mahaifata bata gama warkewa ba”

“To a zubar da cikin mana”

Miƙewa tayi tsaye tana kallonsa.

“A zubar fa kasa kasan abunda kake faɗa?”

“Na sani mana, Namra wannan ba lokacin samun yara bane, muna planning na neman kuɗi kuma yara zasu shigo, ki duba irin wahalar da muka sha a baya yanxu kuma hanya ta fara buɗe mana sai kuma haihuwa ta zo, gaskiya ni ban shirya ba”

“Ni kuma na shriya Asim, ni nake da matsalar da nake da a mahaifata kuma im ready to give birth saboda nima haihuwata aka yi, Allah ba xai bani kyauta na jefar ba”

Cikin wata murya tayi furucin muryar da bata san tana da ita ba sai a yau. Shi kuma ya gyara tsayusarsa yana mamakin ta

“Wallahi Namra sai yanxu na gane lallai ke ba masoyiyata bace. Kin manta lokacin da nake cewa kije ki cire robar nan amman ki ƙi, ko wannan zubar da ciki da kika sha ban san lokacin da kika sha ba, wata ƙila kin yi zubar da cikin ne shiyasa har mahaifarki ta samu matsala, sai yanxu da kika ga zan yi kuɗi ko shine zaki nuna min baƙin hali ki ɓullo min ta haihuwa, to ni ban shirya haihuwa yanzu ba dan haka dole a zubar da cikin nan”

“Wallahi tallahi ba zan zubar da wannan cikin ba, ko da kuwa wannan cikin yana nufi ya rayu, ni na mutu”

“Haka kika ce?”

“Haka na ce kuma haka xaka gani”

“To sai dai ki zaɓa ko ni ko cikin nan...!”

Wani kallo tayi masa na ƙara tantance zancen daya fito daga bakinsa. Shi kuma sai ya ɗaga mata kai dan ya tabbatar mata da maganarsa.

“Yes Idan har baki xubar ba sai dai kije can gidan ku ki haife ɗan, ke kan ki ba samun lafiyarki bane ace kin haihu cikin kuɗi kuma a lokacin mahaifarki tana lafiya ƙalau, na baki lokaci ki yi tunani akai”

Juyawa yayi ya fice, zuciyarsa cikr da tabbacin abinda yayi be yi kuskure ba.

*ANTY AMARYA POV*

Sai da dare Abbah da Hajiya Barau da Anty suka samo ganin lefen da ka kawo, Abbah ya yaba sosai, Hajiya Barau ma ta yaba amman yabon baka yabon daya zame mata cilas dan sam bata jidaɗin ganin yadda aka zubawa ƴaƴan Anty wannan uban lefen ba. Hindatu kala 54 Maryam kuma 79 cikin su kuma babu shege balle ɗan iska.

“Allah yasa alheri ya nuna mana lokacin, amman na ɗauka Namra zata xo tarbon lefen nan”

Anty Amarya taji babu daɗi, sai dai bata nuna ba, sai kawai ta ce.

“Ta so tazo mijin nr ya hana ta yace wai ta bari dai nan gaba sai su zo tare”

“Allah ya taimaka, lefe yayi mashallah”
Chapter 93 · 0% Book details