Sashe 117
Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A cikin motar ya sha ruwa, kamin ya buɗe biscuit ya ɗan ci kaɗan yana faɗa musu inda zasu kai shi. A masallaci unguwar ya ce a aje shi, suna yin parking da sauri wani ya fito daga cikin motar yazo ya buɗe masa yana sare masa, umarni ya basu na suje sai ya nemesu. Ba musu suka sake tsara masa suka koma cikin motar suka juya. Yi yayi kamar be kula da mutanen da suke kallonsa ba, yayi alwalarsa ya bi jam'i, har aka gama sallar kowa da abunda yake faɗa, wasu wai ya zo bincike ne, wasu kuma wai akwai wanda zai kama, shi dai yana gama sallah la'asar ya kanyar kwanar da zata sadashi da gidansu Lamido,daman daga masalacin zuwa cikin gidan babu wani nisa sosai. Hango mustafa da yayi yasa shi sauri juyawo ya ciro wayarsa a aljihu ya neman number direban Mai Martaba da yake gidansa da suka sauka da ke Kaduna.
Cikin mintuna da basu bi goma sha ɗaya ba sai ga direba ya iso, be faka ko'ina ba sai gaban Abdool da sauri Abdool ya buɗe ya shiga, yana nuna masa inda zaije.
Mustafa na zaune gindin wani icce yana kallon motar har suka faka ta dai-dai ƙofar gidan su Lamido. Ya maida hankali sosai da son ganin wanda zai fito daga motar, sai kawai yaga baƙuwar fuska ta fito daga gidan gaba mazaunin direba yana buga ƙofar giɗansu Lamido.
“Waye...”
Suka amsa daga can ciki kamin ɗan uwani ya fito waje ganin mai buga ƙofar.
“Shiga ciki ka ce Abdallahi daga Katsina yana sallama da Namra”
“Toh ya juya da gudu ya koma”
Shi kuma direba ya juyo dan mayarma da Lamido saƙo.
“Wai Ance bata nan”
Yaron ya faɗa yana tsaye jikin ƙofar gidan. Abdool ya buɗe motar da kansa ya fito.
“Kije ka ce idan bata fito ba, ni zan shigo”
Yace da yaron babu alamar wasa a maganarsa, haka ma a yanayinsa. Da gudu yaron ya koma, ko minti biyu ba'ayi ba sai ga Namra ta fito cikin farin Hijabi ta doso inda yake. Yana kallonta dukan natsuwarsa taje gareta, kalaman daya tara zai watsa mata marar daɗi sai duk ya neme su ya rasa har ta ƙaraso kusa da shi ta tsaya.
“Ban ce kar ka sake zuwa nan ba? Jiya jiya ban maimaita maka wannan maganar ba? Ka ɓace ka bar ƙofar gidan nan”
Ta faɗa a tsawace, fuskarta babu annuri. lumshe ido Abdool yayi ya buɗe ya kalleta.
“Kina burge ni idan kina ba ni Umarni, da ma ace bakin ki be iya faɗar ƙarya ba, kin ce ba ki da aure bayan kina da shi”
“Idan na maka ƙarya nawa zaka ba ni? Miye ribata idan na maka ƙarya bayan ka tambaye tsakani da Allah?”
“Amman ƴan gidanku sun tabbatar mana da kina da aure, Asim be sake ki”
Wani irin kallon ta jefa mata mai cike da tashin hankali da mamaki.
“Ina ka san ƴan gidan mu? Waya faɗa naka sunan mijina? Waye kai? Me kake nema a gare ni”
“Naje har gidanku ne neman auren ki, kuma sun tabbatar min da kina da aure, auren ki be mutu ba”
Ta ɗora hannu saman kai.
“Na shiga uku na lalace, ka ɓata komai yanzu shikenan ba za su karɓe ni ba, miyasa baka bari na faɗa musu mutuwar aurena da kai na ba? Kaico na ni Namra, duk inda na dafa taɓen mi yake yi, ka cuce ni shiyasa ka tambaye ɗan ka ƙara jefani a halin baƙinciki da damuwa? Wayyo ni Allah na”
Ta juya da sauri ta koma ciki tana kuka. Shi dai kallonta kawai yake har ta gama faɗa masa abunda zata faɗa masa ta juya ta shige. Jikinsa yayi sanyi sosai, ko bata faɗa masa ba yasan there's something behind those words and tears da ya ga suna zuba a idonta. Juyawa yayi zai buɗe motar ya shiga sai ga Mustafa ya iso.
“Ranka ya daɗe naje kai maka kayan aka hanani shiga, kuma aka ƙi karɓa wai baka nan”
Ko kallonsa Abdool be yi ba ya ɗaga masa hannu.
“Na bar maka”
Ya shige motar, cikin rashin jindaɗin rai. Tun kamin su bar unguwar kalaman Namra suka riƙa dawo masa, idan ya tuna hawayen da ya ga suna zuba a idonta sai yaji wani abu ya tsaya masa a zuciya marar daɗi.
“Ranka ya daɗe ina za muje?”
Ya tambaya ganin har sun hau titi amman Abdool be ce da shi komai ba.
“Masaukin Mai Martaba”
Ya faɗa cikin sanyayiyar murya mai nuna mutun yana cikin damuwa.
-----------------------------------------------------------------
Ku yi haƙuri da wannan.
*72*
Da kuka Namra ta shiga gidan, bata kula su Neina da ke tsakar gidan suna gyaran giɗa ba ta wuce ɗakin Uwani, saman katifa ta faɗa tana cigaba da rera kuka.
Duk mamakine ya kama su, daman tun jiya ba su gane ma kanta ba.
“Uwani je ki gani mana”
Lamido ya faɗa yana kallon Uwani, duk ya ji babu daɗi ganin tana hawaye.
Da sauri Uwani ta tashi ta shiga ɗakin, hannu ta kai ta ɗago Namra tana tambayar
“Lafiya miya same ki?”
Sai kawai Namra ta faɗa jikinta ta cigaba da kukan. Jin kukan nata ya ƙaru yasa Neina shigowa ɗakin.
“Ke lafiya miya same ta?”
“Wallahi nima ta kasa min magana, sai kuka take”
“Toh Allah dai ya sa lafiya, ko wani ne ya mutu?”
Sai a lokacin Namra ta samu ta girgiza musu kai, tasa hannunta ta share hawayenta.
“Mutumen da ya zo yanzu, shi ne mutumen da ya zo jiya, kuma shine mutumen da ya kaɗe Lamido”
Ba shiri Neina ta zauna sake da baki dan shan labari, Uwani kuma ta yi ma Namra kallon Mamaki.
“To miyasa kawo shi? Miya ce miki”
A nan Namra ta kwashe labarin abunda ya faru, ta faɗa musu, sai dai bata yarda ta faɗa musu sanin da ta yi masa a Katsina ba.
Dukansun cika da tsananin mamaki, bama kamar Neina da take ganin kamar lokacin da ya zo gidan ba su yi ido biyu da Namra ba.
“Amman Namra in ban da abin ki miye abun kuka a ciki? Ke da Allah ya kawo miki ɗauki? Yanzu ko abunda tsohon mijin nan na ki ya yi miki ai wannan idan kika duba sakamako ne Allah zai miki”
Uwani na kai aya. Namra ta yi mata kallon baki fahimce ni ba.
“Ya ƙara ɓata min komai Uwani, yanzu iyaye na sun ji aure na ya mutu, kuma za su yi tunanin ko nice na tura sa neman aure na, idan yanzu na koma gida ban san mi zan ce musu ba”
Neina ta ɗaga kai ta kalleta
“A yadda na fahimta, idan har yana son ki da gaske ne, hakan ba zai sa ya ƙi ki ba”
“Ya so ni, ko ya ƙi i, ni duka ɗaya ne a guri na, ban shirya mutuwa sau biyu ba, ban shiryawa yaudara Namiji ba, wani na Namiji ba zai sake ɗiga min baƙinciki a rayuwata ba, na rufe shafin Namiji a rayuwata, dan haka ni ba shi nake ji ba, iyayena na ke ji da makomata”
Duk shiru suka yi, suna sauraren kukan da take rerawa. Kamin hankalinsu ya koma kan sallamar da Mustafa yake yi. Neina ce ta tashi ta fita Uwani kuma ta tsaya yana bawa Namra haƙuri.
“Maraba da Mustafa, yau an dawo shago da wuri?”
Ya zauna saman kujerar tsakar gida ta mata, yana faɗin
“Wallahi yau ban ma je ba, ya mai jiki?”
“Jiki yayi sauƙi Alhamdulillahi”
Lamido ya amsa da kansa yana miƙa masa hannu su gaisa.
“Allah ya ƙara sauƙi, naga kun yi wani babban baƙo ne a waje, amman kamar be shigo cikin gidan ba”
“Eh gurin Namra ya zo ɗan'uwanta ne”
Cewar Lamido, kamin Neina ta amsa da
“Wai Ɗan Sarki nan ne da ya kaɗe ka, shine ya zo wai yana son ta, kuma har yaje can gida ita bata ma sani ba”
Da sauri Lamido ya kalli Neina, wani irin abu ya daki ƙirjinsa, be ji daɗin maganar ba, kuma be ji rashin daɗinta ba, sai ya samu kansa cikin wani kalar yanayi na dabam.
“Me ta ce masa? Ai na ga ta dawo da kuka”
Ya tambaya kamar ba komai, sai a baɗini yana jin zuciyarsa kamar ta rabe biyu. A nan Neina ta kwashe labarin da Namra ta faɗa musu ta faɗa ma Lamido.
“Ba duka maza ne ƴan iska ba, ba duka maza ne mayaudara ba, ba a taru aka zama ɗaya ba, yadda wani yake da kwaɗayi ba haka wani yake da shi ba, ba a taru a zama ɗaya”
Ya faɗa a hankali yana kallon wani gurin kamar mai nazari. Har Neina ta buɗe baki zata yi magana, sai Mustafa ya jinjina kai ya ce.
“Amman abun da ya ba ni mamaki, wannan mutumen yayi min kama da wanda na sani, kuma shine mutumen da ya aiko yaronsa ya kira nia ka bani wanki, ya ɗauki dubu goma sha ɗaya ya ba ni wai na wanki ne, har yake labarta min wai shi ɗan'uwan ku ne, kuma yana zuwa gidan, da neje kai masa wankin sai aka ce baya nan, ina nan kuma zaune sai na gansa, ina masa magana wai ya ba ni tufafin”
Lamido ya riƙe baki.
“Wallahi ba mu da wani alaƙa da shi, ai baka nan lokacin daya kaɗe ne da ka gani, anya ba yana da wata muguwar manufa ba ce akan yarinyar nan da mu ma?”
Neina ta yi saurin rufe masa baki.
“Dan Allah ka rufa mana asiri, ɗan Sarki ne”
“Dan yana Ɗan Sarki fa? So what? Ba a da ikon faɗar gaskiya, ku kuke tsoron sa”
Mustafa ma ya saka baki.
“Kai da ka rufa ma kan ka asiri. Ko ma minene iya karka ka yi addu'ah ka zura na mujiya”
“Wallahi ba zan yi ba, ba zan zuba ido wani ya cutar da yarinyar nan ba, iya wahalar da tasha ta ishe ta haka”
Ya faɗa cike da ɓacin rai. Mustafa ya miƙe tsaye bakinsa cike da maganganun da be samu furtawa ba, yana musu Allah ya sauwaƙe.
“Amin an gode Mustafa”
Neina ce ta amsa da haka, Lamido kan hankalinsa na can wani gurin.
ABDOOL POV.