← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 173

Sashe 36

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kusan biyar na yamma hankalinta ya dawo jikinta, har ta gane inda take kwance, gurin duk ya bace da jini, sai dai har yanzu mararta na mata ciwo da zuji ga wani uban nauyi da take jin cikinta yayi.
Daker ta unƙura ta shiga banɗakin, nan ma zubewa tayi ƙasa saboda rashin ƙarfin jiki, haka sare-saren jini ya riƙa fita daga cikinta tana kuka. Bata samu sassauci ba sai gaf da magariba, sannan ta samu ta tashi ta wanke jikinta ta gyara gurin cikin rashin kuzari ta dawo ɗakinta ta kwanta ƙasa idonta har wani lumshi suke.

Daker ta iya amsa sallamar da Mardiya da Dillaliya suke, sai dai bata iya tashi ba har Mardiya ta samu meta a gurin.
Yanayin yadda ta ga Namra yayi matuƙar ɗaga mata hankali, da sauri ta ƙarasa kusa da ita ta tashe ta zaune.

“Subhanallah, Namra me ya same ki?”

Cikin dauriya da ƙarfin hali Namra tayi mata magana.

“Jini ne yayi min zuba, kuma marana ciwo take sosai”

“Ko ki tashi muje asibiti?”

“Ba zan iya tafiya ba”

“Zan riƙa ki, tashi ki saka tufafin ki muje, kuma dillaliya tana falo tana jiran ki”

“Ki ce mata ta shigo”

Ta faɗa tana wani irin dantsar baki. Mardiya taje ta shigo da ita. A tsatsaye suka gaisa da ita ta miƙawa Namra kuɗin tana mata sannu.

“Allah ya sauwaƙe amman gara kuje asibiti, daman nace bari na kawo miki cikon kuɗin ne, inya so gobe sai na zo na kwashe kayan”

Kai kawai Namra ta iya ɗaga mata, ta juya ta fita tana mata Allah koro sauƙi.
  Ƙyar idon Mardiya kan kuɗin da Dilalliyar ta bawa Namra. Namra ma bata kuɗin take ba ta lafiyar ta take.

“Ki tashi ki shirya bari naje na kira mai Napep”

“Amman za a same su da daren nan? Kin ga magariba tayi kar muje asibitin ba kowa”

“A'a Asibitin Malam Yakubu zamu nan kusa take kuma shi ko yaushe yana karɓar marar lafiya, musamman irin wannan”

Ta kai Hannu ta ɗauki kuɗin da suke gefen Namra ta saka cikin bed side drawer.

“Bari a aje kuɗin nan har mu dawo”

Bata tsaya jiran abunda Namra zata ƙara cewa ba, ta juya ta fita da sauri. Cikin ƙarfin hali Namra ta tashi ta saka pad ta zura doguwar riga, ta saka Hijabi ta fito falo ta zauna, yana sauraren yadda kanta ke tsarawa ga jikinta duk yayi mata babu daɗi.

Tana haka Mardiya ta dawo.

“Tashi muje gashi can ƙofar gida”

Ta riƙa suka fita tana mata sannu, a hankalin Namra take takawa kamar mai koyon tafiya har suka isa bakin gate ɗin, da taimakon Mardiya ta shiga Napep ɗin. Sannan Mardiya ta kalleta tace

“Ina Keys ɗin a rufe gidan?”

“Na manta shi yana can gefen dinning, dan Allah ki ɗauko min jaka na, ki ɗauko dubu biyar cikin kuɗin nan da Dillaliya ta kawo”

Da Tau ta amsa ta koma cikin gidan zuciyarta cike da saƙe-saƙe. Lokacin data shiga Kitchen ta fara shiga ta ɗauki ashana, sannan ta shiga ɗakin ta ɗauko jakar data san Namra na saka atm ɗinta, kuɗi da kuma wasu abubuwan a cikin sannan ta bude dorowar ta ɗauko kuɗin ta ciri kubu biyar ta saka a jakar Namra, sannan ta ɗauki sauran ta saka wata ƴar ƙaramar jaka dake jikinta mai kamar pose ɗin tsofi, sai ta warware zagenta ta ɗaga pant ɗinta sa saka jakar cikin pant ɗinta sannan ta ɗauki ɗankwalin Namra ta ƙyasta ashanar ta liƙa masa ta jefa saman gadonta.

Sai ta fito da sauri ta ɗauƙi keys ɗin ta rufe falo, sannan ta nufi gate gabanta na mugun faɗuwa ƙirjinta kamar zai fito.
Nan ma sai da ta tsaya ta rufe gate ɗin, sannan ta shiga Napep ɗin tana miƙawa Namra jakarta. Har mai Napep ɗin ta tashi Napep ya fara tafiya idon Mardiya yana kan gidan, zuciyarta cike da wasi-wasi. Namra kam idonta a lumshe yake ta jinginar da kanta jikin Mardiya tana yadda Mararta ke mata zugi.

KALSOOM POV.

Har ta isa gida tana tunanin abunda zata faɗawa iyayenta, taya zata iya faɗa musu dalilinta na dawowa gida? Bata samu mafita wata ƙarya da zata musu ba, hakan yasa taja bakinta tayi shiru duk juyin duniyar nan da Momi tayi akan Kalsoom ta faɗa mata dalilin na dawowa gida sai taƙi, bata ce shi yace ta dawo gida ba, kuma bata musu wata ƙaryar ba.

“Bari Dady kun ya dawo idan ni baki faɗa min ba, shi ai kya faɗa masa, haka kawai ki ɗauko akwati ziƙi-ziƙi ko kunya ki tafo gida, auren an samu daker anyi yanzu shine kike son ki kashe ko? Tau baki isa ba Wallahi”

Duk irin faɗan da Momi tayi Kalsoom bata yarda ta faɗa mata abunda ya faru ba, hakan yasa Momi kira Dad a waya ta labarta masa abunda yake faruwa. Cikin ƴan mintuna ya baro office ya dawo gida. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ya rufe Kalsoom da faɗa akan ta faɗa masa dalilinta na dawowa gida amman ta ƙi.
Da kansa ya ɗaga waya ya kira Hilal yace yana nemansa, a lokacin Hilal yana tsakar aiki ne hakan yasa ya nemi Dad yayi masa lamani har zuwa dare.
  Daren na yi sai gashi ya zo gidan, a nan ma yayi sallah isha'i, sai fira yake da Dad kamar Abbansa. Har suka shigo cikin falo sannan Dad yake tambayarsa ko akwai abunda ya shiga tsakanin su da Namra. Murmushi Hilal yayi ya wayance sosai kamar ba shi ba.

“Dad ni ai nayi mamakin da kace min Kalsoom ta zo gida ɗazu, dan gaskiya ni ban san wani rashin jituwa daya shiga tsakanin mu ba, sai dai ɗan abunda ba a rasa ba na kishi tsakanin ta da abokiyar zamanta, amman kasan rai ajizine ban sani ba ko nayi mata wani abun da ba zata iya faɗa min ba shiyasa ta kawo ƙarana”

Dad yaja tsaki yana girgiza kai irin nasu na manya.

“Kai sha'anin mata sai haƙuri, ni Wallahi na ɗauka wani abun akayi ma, babu yadda ba muyi ba amman yarinyar nan taƙi tayi magana”

Dad ya tashi ya shiga ciki gurin kiran Kalsoom. Hakan yasa Hilal gyara zamansa yana mai jindaɗin da Kalsoom bata faɗi abunda ya faru ba. Dad be daɗe ba sai gashi ya dawo falon tare da Kalsoom da Momi.
A kujera ɗaya ya zauna da Momi Kalsoom kuma ta zauna ƙasa kusa da Momi.

“Tau gashi nan shi dai yace be san wani abu ya shiga tsakanin su ba, ke sai ki faɗa idan akwai abunda yayi miki wanda be sani ba, ko kuma yayi miki shi cikin kuskure”

Ɗagowa tayi ta kalleshi, shi ma sai ya tsare ta da manyan idonsa, har sai da taji ba zata iya ɗaukat kallonsa ba, ta kawair da nata idon. A hankali ta kira sunan ta.

“Kalsoom, Dan Allah kiyi haƙuri ki yafe min, idan har akwai abunda nayi miki a cikin rashin sani ko da kuskure, koma da gangan kin san ɗan'adam aziji ne”

Ji tayi kamar yasa sarƙa ya ɗaure dukanin ilahirin jikinta, sai ta kasa sake ɗaga ido ta kalleshi, kuma ta kasa furta komai. Har Dad ya gama faɗansa da yake mata akan zamantakewar aure da haƙuri. Momi ma ta ɗora da nata sannan suka tashi suka basu guri.
Tasowa yayi daga inda yake zaune ya zauna ƙasa kusa da ita jikinsa na gogar nata, yasa hannunsa ya riƙe nata, fuskarsa kuma daf da nata ta yadda suna iya shaƙar numfashin juna.

“Babe tashi muje gida, na gode sosai da baki faɗawa Dad abunda ya faru”

“Ba zan iya bin ka gida ba, saboda ka riga ka furta duk ban biya ka ba, a bakin igiyar aurena”

“Kuskure na, na san nayi amman dan Allah ki yi, ba zan sake ba”

“Ni ba zan zauna ba, ai ka riga ka nuna kuɗin sun fi rayuwar aurena daraja”

“Shiiiiiiiiiii”

Ta ɗora lips ɗinsa saman nata, yana goga mata hancinsa.

“Ba haka nake nufi ba, zuciya na ne ya kawo har nayi wannan furucin kuma yanzu ina nadama”

Kawarda fuskarta tayi ta unƙura zata tashi, sai ya danneta da dukan ƙarfinsa.

“Don't try me, ba ki da wannan karfin bana son Dad da Mom su san halin da muke ciki, dan Allah Kalsoom kiyi haƙuri idan ma zuciyarki bata natsu ba, idan mun koma zaki iya biyana”

Be sake ta ba har sai da yawun bakinsu sukayi taraiya. Sannan ta tashi ta koma ciki, shi kuma ya fito waje yayi ma Dad sallama. Ita kuma ta ɗauko akwatinta ya karɓa ya saka a mota sannan suka tafi.
Tun da suka kamo hanya ta kalli inda take yake ba, idonta na kam gefen gilashin motar gurin ti-ti. Murmushi yayi ya kai hannu ya shafi fuskarta.

“Na san abunda na yi ban kyauta ba, amman dan Allah kiyi haƙuri, i love you so much”

Uffan bata ce masa ba, bata kuma sakar masa fuska ba, har suka isa gida. Shi kuma duk ya damu, wani irin sha'awarta yake jin tana masa yawo a jiki ga shi be ga alamun sauƙi a tare da ita ba.
Suna shiga cikin falon ta wuce ɗakin. Yayi kamar ya bita sai kuma wata zuciyar ta hana shi, sai kawai ya nufi ɗakin yaransa inda yake jin ihunsu. Da gudu suka zo suka rumgune shi.

“Eyyyy Daddy welcome”

Ɗaya bayan ɗaya ta riƙa shafa kansu, daga bisani ya kai hannu ya ɗauki Rafiq ya rumgume.

“Daddy Ammyn Rafiq ta fita wai gurin aikinta suna nemanta, tace mu zauna har ka dawo”

Ezzah ta faɗa tana wasa da ribon ɗin dake hannunta.

“Kuma tace idan ka tambaya mu faɗa maka ita ce ta ɗauki kuɗin dake cikin closet na ka”

Wani irin abun ɓacin rai ya taso yayi matsa tsaye a zuciya, yana auna irin rainin da Rashida tayi masa, taya zata fara yi masa abunda bata saba ba har tasa ya zargi Kalsoom.
Rufe ido yayi saboda wani mugun ɓaci rai da yaji ya rufe shi,

“Daddy are you okay?”

Yayi murmushin ƙarfin hali yana kallon Ezzah.

“I'm fine, Kuje ɗakin Anty ku ta dawo”
Chapter 36 · 0% Book details