← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 173

Sashe 121

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da aka soma shigo da kayan har aka aje,be ji motsinta a falon ba hakan ya tabbatar masa da tana kitchen, kai tsaye ya nufi kitchen ɗin, fuskarsa ɗauke da murmushi. Ta baya ya yi hugging ɗinta ya aika mata da kiss a gefen fuska.

“Me kike girkawa?”

Wuƙar dake hannunta ta aje ta juyo tana dariya.

“Hancin ka zan girka”

“An ya zaki iya cin hancin na?”

“Kwarai kuwa ta yadda Amaryar nan da taga baka da hanci zata ce ta fasa auren”

Ƙyalƙyalewa yayi da dariya, ya zageye kunkurunta da duka hannayensa.

“Shikenan sai ki kashe min kasuwa ko?”

“Eh mana ai ƙara ni kaɗai zan riƙa ganin kyan ka”

Ya riƙa hannunta yana dariya.

“Zo ki ga wani abu”

Gabanta yayi mugun faɗuwa, haka kawai ta annayana a ranta ba abun alheri ba ne, cire hannunta ta yi cikin na shi.

“Bari na juya miya sai na zo”

Be mata musu ba, ya juya ya fice. Ta ɗauki minti goma a kitchen ɗin tana ta fargabar fita, duk da bata san abunda zai nuna mata ba, tana ji a ranta kamar ba alheri ba ne. Ba ƙaramin dauriya ta yi ba kamin ta wanke hannayenta ya juya miyar sannan ta nufo ƙofar falo.
Tana ganin akwatuna jere a tsakiyar falonta, bugun gabanta ya ƙaru, idonta kuma ya cika da hawaye. Ga invitation card da kwalayin minti da cinka a saman akwatunan mai yawa ana ɗora. Jikinta yayi sanyi sosai, hawayen dake maƙalle a idonta ya gangaro zuwa kumatun ta.

“Ashe haka Rashida ta ji lokacin da za a auro ni ko?”

Ta faɗa muryarta na rawa. Ɗagowa Hilal yayi ya kalleta, sai ya miƙa mata hannu alamar ta zo, sannu ta fara takowa har ta kawo inda yake ta miƙa masa nata hannun. Sai ya zaunar da ita ƙasan kujerar ya ɗora mata hannayensa saman kafaɗunta, kasancewar shi yana saman cushion zaune ne.

“Ki duba ki ga idan akwai abunda babu zan ƙaro”

Kai ta girgiza ta miƙe tsaye.

“A'a ni nabar mata kayan duka ka kai mata, ina da kayana”

Shima.ya miƙe tsaye.

“Na sani ai, ba tsirara na auro ki ba”

Sai ta yi ƙasa da kanta tana hawaye. Hannunsa ya saka cikin nata yaja zuwa ƙirjinsa, sai kawai ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi.

“Sorry dear, zan canja miki komai idan kina buƙata, just be strong”

Kuka tayi sosai har sai da ta ɓata mishi gaban riga da majina, sannan ta sake shi ta nufi toilet ɗin falo saboda amai da taji ya cika mata baki.

ASIM POV.

Tun safe ya tashi ko da goma tayi yana cikin garin sokoto, A hotel ɗin Shukura ya kama ɗaki, sai da ya ɗan huta sannan ya kira Ubangidansa ya sanar masa da ya iso. Ya bashi tabbacin sai dare zasu gana, da alama can zai kwana inda yake, dan ya faɗa inda zai same shi a gidansa da ke Sama road.
Fitowa yayi ya biya kuɗin wuni ɗaya, sannan ya ɗauki hanyar gidansu, zuciyarsa cike da nishani, yana mai jin kansa lallai shi a yanzu wani ne.

Ko da ya isa unguwarsu ƙarfe ɗayan rana yayi, dan haka irin mazan nan masu zaman kashe wando duk basa nan sai da yamma suke zama, kasancewar unguwar minannata, haka suke da yamma ta yi, amman hakan be hana wasu ganinsa ba, dan tabbatar da shi ɗin ne yasa wasu gayu zuwa su bashi hannu shi hannu su gaisa suna masa yaushe gamu.

“Kai ke da wannan?”

Ɗaƴan ya faɗa yana nuna motar dake kusa da su.

“Eh Wallahi sai a taya mu addu'ah”

“Toh Allah ya taimaka ya tsare. Kace kai ma ka shigo gari, ko da yake kana sirikin Manjo Usman ai dole ka hau wannan motar”

Ɗan murmushi yayi.

“Babu ɗigon dukiyarsa nan”

Duk dariya suka yi, ba dan sun yarda ba, sai suka ƙara gaba suna nasu zancen.

Da farinciki ya shiga gida, yana doka sallama kamar wani baƙo. Da gudu Mama ta fito dan tabbatar da muryar ɗan na ta ne ko bashi ba, ganinsa yasa ta daki ƙirji tana ƙare masa kallo

“Ibrahim kai ne? Allahu akbar”

Ta shiga shafa kayan jikinsa tana kuka, shi kam sai dariya yake yana kallon ƙanensa dake sanye da uniforn ɗin makaranta suna kallonsa. Da alama suma basu gama tabbatar da shi ɗin ba ne.

“Ji yadda kuka tsaya kallo na”

Sannan suka yi dariya suka rugo a guje suka rumgume shi, suna murna. Sai da suka gama zumuɗinsu sannan Mama ta ɗauko tabarta ta shimfiɗa masa tsakar gida, ko zama be yi ba sai ga maƙota sun soma shigowa ƴan ganin gwan, kar ayi ba su, dan kace kwabo har labari ya fara zaga unguwar.

Ya sha gaisawa da mutane sosai, dan sai a lokacin wasu ke masa ya jiki. Sai kusan La'asar ya samu keɓewa da Mama suna tattauna lamuran duniaya.

“Amman wannan matar Allah yayi mata tausayi, irin wannan hidima haka? Ko dai auren ka zata yi? Allah dai yasa taimakon Allah ne take maka”

“A'a ai matar babbar macece, kuma ta san ina da mata, Allah yayi mata tausayi ne kawai”

“Ai har gobe na Allah basa ƙarewa, Allah saka mata da alheri, ba irin waɗannan lalataccin mutanen ba, ai na so ka zo da Namra ta yadda zaka je kaita su ga irin buɗin da Ubangiji ya yi maka”

Ya ɗan yi shiru kamin ya ɗora da.

“Ai na saki Namra...”

Mama ta daki ƙirji tana buɗe baki tare da gwalo ido.

“Kai ɗan nan? Yaushe?”

“Yanzu an kusa sati biyu gaskiya, bata zo nan ba?”

“A'a wallahi ai da tazo da sai mun samu labari”

“Daman na yi tunanin ba zata zo nan ba, amman nasan duk inda taje dole zata dawo”

“Hmmm ai ƙara ma daka sake ta, sai mutane gane ba dukiyar ubanta bace,dan nasan yanzu duk wasu haka zasu ɗauka, kai lokacin ma da baka da lafiya har da masu cewa wai ubanta ne ya ɗauki nauyin komai, ko zaka maida ita sai nan gaba”

“Wallahi Mama ina sakinta sai abubuwa suka buɗe min komai yanzu ba ni da matsalarsa, yanzu haka zuwan da na yi na zo ne na faɗa muku na samu matar aure kuma zan siya muku gida mai kyau na miliyan biyu haka sai ku zauna”

Tashi Mama ta yi tana rawa, kamar wata bayarabiya sannan ta ɗire tana ma Allah godiya tare da sujada.

“Kai ɗan nan Allah ya zuba maka albarka, da mahaifinka na nan da rai da ya gode maka”

Dariya yayi yana mai jin kansa sosai da sosai. Sun deɗe suna fira kamin ya cire kuɗi mai yawa ya bata wai ta siyo kayan abincin, gida kuma ta sa abincika mata idan an samu ayi masa magana. Sai da magariba ta yi. sannan ya yi wanka ya canja kayan daya zo da su, ya gyara jikinsa ya bar gidan sai ƙamshin turare ya ke.

RASHIDA POV.

Juyi kawai take saman katifar da saboda wani mugun ciwo da zuciyarta ke mata, tea ma daker ta iya tashi ta haɗa ta sha.
Bata yi mamakin ganin irin kiran da take ta samu daga ƙawayenta ba, ciki har da Asmee, sai dai bata damu da ɗauka ba dan a tunaninta ko zasu tambayeta dalilin barin gidan iyayenta ne, taji zafi sosai da taga har da ƙawayen da take nesa da su ne cikin masu kiranta, babu shakka labarin barin gidan iyayenta ya same su kenan.

Wannan tunanin yasa ta ƙara jin wani irin zafi ya rufe mata zuciya, yana ɗaya daga cikin dalilin daya sa ta ƙaurawace whatsapp saboda yawan tambayar gaskiyar mutuwar aurenta da ƙawayenta ke yi, wasu kuma suna jajanta mata akan mutuwar Rafiq.
Yanzu ma wayarta ce take ringing, wannan karon Momi ce dan haka ita kam ba zata ƙi ɗaukar wayarta ba, cikin hali na kamar marar lafiya ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta.

“Hello Momi”

“Ke Rashida kin san abunda ya ke faruwa kuwa?”

Ta tashi zaune da sauri cikin rashin gane zancen da Momi take mata.

“Miya faru?”

“Kina da labarin Hilal zai ƙara aure?”

“Eh na taɓa ji amman ban tabbatar ba”

“Kin san Teema ce matar da zai aura”

Haka maganar ta riƙa yi ma Rashida yawo cikin kai har tana jin kamar ɗakin ya juya mata.

“Wace Teemar? Ba dai ƙawata ba ko?”

“Ita fa”

“How true it's?”

“Ga Iv nan Ummu Faisak ta zo da shi, ko ba ita bace Fatima Jafar Mai Goro?”

“Ita ce, ta ya hakan zai faru?”

Tayi saurin kashe wayarta ta kira Asmee, bugu ɗaya ta ɗauka.

“Hello na kira baki ɗauka ba, kinji abunda yake faruwa kuwa?”

“Da gaske ne kenan?”

“Ashe kin ji”

Ta katse kiran ta jefar da wayar saman katifa cike da tashin hankali, rasa gane ta yi inda take sama ne ƙasa ne, duniya ne ko lahira, sai juya mata ɗakin ke yi, tana numfashi guda guda.

“It can't be Teema, idan har ta tabbata da gaske ne sai na ci Uwarki...!”

Ta faɗa cikin wani irin zafin rai, a take ta zari mayafinta ta fice.

YASMEEN POV.

Yana jefar da scul bang ɗinsa, yasa hannu yana ƙwaƙwala gurin kashinsa, yana tafiya ararrabe ya nufi kitchen.

“Momee na dawo”

Be same ta a gurin ba, sai Mai mata raino ya samu tana girka mata abinci.

“Ina Momee”

Ya faɗa yana jan rigarta.

“Tana ɗakinta”

Juyawa yayi da fuskar kuka ya nufi ɗakin nata, yana cigaba da ƙwaƙwala gurin kamar mai jim ƙaiƙayi. Da hannu ɗaya ya tura ƙpfar ɗakin ya shiga.

“Momee na dawo, kin ce zaki ba ni chocolate da safe”

Harara ta watsa masa dan ta tsani wannan soshe-soshen da yake yawan yi.

“Ba zaka cire hannunka a nan ba? Zan ci ubanka Adnan idan baka daina saka hannu a gurin ba, kai ƙazami ne ko?”

Ya yi saurin cirewa.

“A'a Momee ciwo ne yake min”

“Bari Dadee ya dawo ya saka maka magani, yana can ɗakinsa”

Ya faɗa, dan hana kowa ya saka masa ganin sai shi kaɗai, hakan yasa ya aje ganin gurinsa shi kaɗai zai riƙa saka masa ganin.

“Zo mu gani”

Ta aje Namra dake hannunta, ta riƙa wandon makarantarsa ta cire, sannan ta sake cire pant ɗinsa.
Chapter 121 · 0% Book details