← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 173

Sashe 77

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Allaahumma munzilal-kitaabi, saree'al-hisaabi, ihzimil-'ahzaaba, Allaahumma ihzimhum wa zalzilhum. اللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ الأَحْزَابَ، اللَّهُمَّ اهْزِ مْهُمْ وَزَلْزِلْهُمْ ”

Gabanta ya faɗi da farko, kuma ta tsorata sai dai addu'aj ɗa tayi yasa taji tsoron ya guje mata a take. Daman addu'ah ce ta neman tsari daga makiya.

Sai kawai ta koma ciki ta cigaba da wanke-wankenta. Wani irin ƙwallowa tayi Rafiq dake bachi ya buga. Ba shiri tayi bar wanke wanke ta nufin ɗakin yaran. Ƙasa ta tararda shi yana fisge-fisge kamar wanda za a cirewa rai.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta ƙarasa da sauri inda yake ta ɗaukesa tana girgixawa. Amman ina ido da jiki duka a ƙafe sai wani ƙogi yake yana kallon silin, aje shi tayi ta nufi ɗakinta da gudu ta ɗauki wayarta ta kira Hilal.

AMIRA POV.

Tana shiga ɗakin ta tararda komai na ɗakin pink color ne, sai manyan hotunan Amal dake jikin ginin ɗaki har da waɗanda ta yi ƙasar waje, wani gurin tana tare da Abdool wani gurin kuma da Ummi wani da Meesha wani da Fauza sai kuma wanda suka yi da Haleema, ma bin su shine wanda tayi da duka familynsu Hilal yai ma Ummi side hug yai mata kiss irin na nuna tsatsar ƙaunar nan na ɗa da uwa.
Wanda Amal tayi da Hilal ta fi tsurawa ido tana kallon yadda Hilal yake feeding ɗin Amal ranar birthday ta. Hannu ta kai ta shafa hoton tana murmushi.

“Kai na daɗe ina mafarki Abdool, kai ne irin mijin da nake so, sai yanzu na gane dalilin daya sa na bar gida na, ashe rabo ne kirana, saboda kai akayi ni Abdool nima kuma saboda ni aka yi ka, haƙiƙa ban yi sadaukarwar banza ba”

Ta juya ta jingina da ginin gurin ta lumshe ido tana sauke wani sayyayen numfashi.
Babu wanda take gani sai Abdool, rayuwarta da tasa take hangowa irin jindaɗi da kuma rayuwar da za su yi idan ya aureta.

Bayan tayi wanka ta maida tufafin dake jikinta ta zauna ta ci abinci tana ƙara ƙarewa ɗakin kallo. Ta jinjina kai

“Lalai ba ƙaramin dukiya Abdool ya tara ba shi da mahaifiyarsa, amman ina mahaifinsa yake? Ina jin baya nan gidan dan gidan be nuna alamun gidan sarauta ba”

Ta sauke ajiyar zuciya tana auna kanta a matsayin matar Abdool. Irin kallon da yayi mata take tunowa yadda idonsa yake da fari har wani ruwa ya kwanta a ciki kamar balarabe. Tashi tayi ta ƙasara gurin madubi tana kallon kanta, bata da munin da namiji zai ganta yace baya son ta. Idan har baka yabe ta ba to ba zaka kusheta ba.

Shukura ce ta dawo da dare ta kawo mata abinci sai ta kunna mata tv ta ɗauki wasu ɗaga cikin kayan da Amal za tayi amfani da su, da dukan alama Amal ɗin ce tasa a ɗauko mata har da ƴar ƙaramar iphone ɗinta.

________________

Ni kam nace Kar Hajiya ta lalata mana Asim 😏😏
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *52*

KALSOOM POV.

Ta yi masa kira biyar be ɗaga ba, ga dukan alamu suna tiyata ko meeting dan shi kaɗai ne yake hana sa ɗaukar wayarta.

“Wayyo Allah na na shiga uku Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta furta cikin muryar kuka hawayen na bin fuskarta, zubewa ta yi a gurin hannunta ɗaya saman kai, ɗayan kuma riƙe da waya tana ƙoƙarin kiran Hilal. Still be ɗaga ba, a nan ta jefar da wayar ta koma ɗakin da Rafiq yake tana kuka. Wannan karon abinda ta gani ya bata tsoro dan har kumfa yake fitarwa a bakinsa.

Da sauri ta ɗauke shi ta fito da gudu ta nufi harabar gidan tana ihu. Mai gadin ne yayi kanta yana tambayar ba'asi. Ganin halin da yaron yake ciki ya sashi sallalami tare da karɓarsa ya girgiza.

“Hajiya ki kira Alhaji ki faɗa masa”

“Na kirasa be ɗaga ba”

“Ki sake kiransa kar yaron nan ya mutu”

Jin an ambaci mutuwa yasa ta ƙara rikicewa ta falla da gudu ciki, ta koma ɗakin ta ɗauki wayarta a inda ta jefar da ita.
A rikice ta kira numbersa wannan karon tayi sa'ah kira ɗaya ya ɗaga cikin muryar daya saba mata a duk lokacin data kirasa

“Maman yara...”

Kukanta da yaji yasa gabansa tsinkewa ya faɗi.

“Kalsoom what happend?”

“Rafiq ne Hilal ka zo gida yanzu kar ya mutu...”

Tana jin haka ya katse wayar ya mike daga zaman tattaunar da suka gama yanzu-yanzu ya nufi gidan hankali a tashi. @360 ya hau titi duk hankalinsa sai ya tattara ya koma gida, zuciyarsa sai yayo masa take, wani abun Rafiq ya hau ya faɗo ko kuma wuta ta jashi, kwata-kwata be kawo ma ransa abinda ya tarar yaron na yi ba. A firgice ya fito motar ya nufo gurin da Kalsoom take riƙe da Rafiq tana kuka.

Ya sa hannu biyu ya karɓe sa ta juyo da sauri ya nufi mota, dan babu lokacin tsayawa tambayar abunda y same shi.
Komawa tayi ciki ta ɗauko Hijabinta ta saka, ta ɗauki jakarta ta fito da sauri kamar tana son haɗaw da gudu, sai kuka take irin mai nuna tsantsar tashin hankali. Ba tare data kulle gidan ta fito titi, tari adai-dai sahu ta hau, tana faɗa nasa inda zai kai ta. Be sauketa ko ina ba sai American hospital inda Hilal yake aiki, sai da ta sallami mai Napep ɗin sannan ta nufi emergency duk da bata da tabbacin can ɗin ne ya kai shi ko a'a. Wasu nurser ta tambaya, suka tabbatar mata da xuwansa da kuma ɗakin daya nufa da yaron. Da gudu ta ƙarasa gurin tana share hawayen da suka ƙi su tsaya mata.

Kai da kawo ta riƙa yi ita kaɗai tana jiran fitowar Hilal ko kuma wasu daga cikin, amman shiru har kusan mintuna arba'in da takwas.
Sannan wasu Nurser suk fito daga ɗakin, ita kuma ta zura kai sai leƙo take ko zata ga wani halin da Rafiq yake cikin.

Hilal ne ya fito, sai ya janyo ƙofar ya kulle. Fuska babu annuri ya nufi office ɗinsa, ba tare da kula ta ba, balle ma ya bata amsar tambayar da take masa.
Binsa tayi a baya tama tambayarsa amman be kula ta ba har sai da ya shiga office ɗin. Ita kuma duk hakalinta ya tashi a tunaninta ko Rafiq ya rasu ne.

“Me kika ma Rafiq ? Ya aka yi ya ci guba?”

Itace tambayar da Hilal ya fara mata suna shiga office ɗin. Ras ras ras gabanta ya faɗi har jakar dake hannunta ta faɗi idonta na kan Hilal tana kallonsa hawaye sai zuba suke mata ba tare data sani ba.

“Gu....Ba....Bah...”

Ta maimaita cikin rawar muryar tana mamakin furucin daya fito a bakin Hilal. Shi kuma sai kallonta yake fuska babu annuri.

“Eh guba, ya aka yi ya ci guba?”

“Wallahi ban sani ba, amman Rafiq ko abinci safe be ci ba, bachi ma yake, sai kawai na ji ƙyalowarsa ina shiga ɗakin na tararda shi a ƙasa yana fusge-fisge”

“Be ci komai ba guba zata zo ta shiga jikinsa ne? Ni dai a sanina indai ba batir ɗin remote ba mu da wani abu mai guba, da Rafiq zai yi saurin ɗauka ya saka a baki”

“Ban gane ba me kake nufi?”

“Ina baki damar da nake baki ne Kalsoom dan ki samu damar zama uwa a gurin ƴaƴana, kuma dukansu kamar marayu suke a gare ki tun da babu uwarsu a tare da su, babu abinda Ezzah bata faɗa min amman bana kulawa saboda na ɗaukeki a mtsayin uwar data haife su, a tunani ba zaki taɓa musu abinda be kamata ba but wannan yayi yawa, idan ba shi akayi ba taya kamar Rafiq zai ɗauki guba ya ci?”

Ta yi shiru ta kasa magana, sai idonta ne suke magana. Jikinta ya mutu lis har ji take kamar ta zube a gurin. Ba ita ce ta bashi gubar ba, bata da tabbacin gubar ce ma yaci tun da tasan be karya ba, sai dai kuma bata da abinda zata wanke kanta, dan tage gun da kalaman Hilal suka dosa.

“Idan na cutar da Izzah na kashe Rafiq me zan ji?”

“Nima ban sani ba Kalsoom, ban sani ba, wata ƙila ba ki son zama da su ne ko kuma kin gaji da su, amman ni ina son ƴaƴana fiye da yadda nake son rayuwata, kuma zan iya barin komai a kan ƴaƴana, dan sune zasu zauna da ni ko a wane hali nake ciki ina ta avoiding abinda kike ma yaran nan Kalsoom but you cross your limit”

Bata ce masa komai ba, tasa hannun hijabinta ta goge hawayenta, ta duƙa ta ɗauki jakarta ta juya jiki ba gwari ta fice. Binta yayi dan zuciyarsa na raya masa ɗakin da Rafiq yake zata je. Hanyar da zai kai mutum ward ɗin ta nufa ga dukan alamu can ta nufa, tun da ga hanyar fita harabar asibitin nan ta bari. Daga inda yake ya ɗaga muryarsa ta yadda zata iya jiyosa yace

“Kalsoom don't, we don't need you for now”

Tsayawa tayi cak! Kamin ta juyo ta soma takowa ta dawo inda yake. Sai da ta kawo daf da shi sannan ta ɗaga muryar cikin zafin rai ta ce.

“Thank you, thank you so much”

Ta faɗa in low voice sannan ta juya, hawaye na cigaba da zuba a fuskarta ta nufi hanyar data zai fitar da ita harabar asibitin.

NAMRA POV.

Tun faɗan da suka yi da Asim ya fita bata sake saka shi a ido ba sai washe gari, ita kaɗai ta kwana a gidan, tana aikin data saba na kuka, bayan ta faɗa ma Allah buƙatarta.
Chapter 77 · 0% Book details