← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 173

Sashe 82

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa yayi ya koma motarsa. Suma suka shiga tasu, da hau titi sai da ya ɗaga musu hannu sannan ya cigabansu da mugun gudu.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *55*

*NAMRA POV.*

Yau kan ta ɗan samu sauƙi ba kamar jiya ba. Dan yau har aiki ta samu tayi, ta gyara gidan tas sannan tayi wanke-wanke, sannan ta shiga tayi wanka. Ta shirya cikin baƙar abaya sannan ta fito harabar gidan ta ɗauko murhunta na gawai ta ɗora girkin rana.
Bayan ta ɗora ta tashi ta koma cikin ɗakin ta ɗauko tabarma da filo ta shimfiɗa, dan ta soma jin ciwon kan na taso mata.

Bachine ya soma ɗaukarta, sai gyangyaɗi take, bata son yin bachi ta bar girkinta ya ƙone. Hakan yasa ta tashi ta wanke shimkafa ta zuba ta gyara wutar sai ta koma ta xauna tana kallon gate dan horn ɗin ta take ji ta yi yawa.

Bata jin za ta iya zuwa ta ga mai horn ɗin, duk da tana jin a gidan ake horn amman bata zaton za tayi wani baƙo mai mota, da zai iya zuwa gurinta yanzu.
Kwantawarta tayi tasa ɗan tsinƙe tsintsiya tana gyara akaifarta. Bata ɗago ba har sai da aka turo ƙofar gate ɗin aka shigo. Sannan ta ɗan juyo taga ko waye ne. Ganin Anty yasa ta tashi tsaye da sauri tana mamakin ikon Allah. Mafarki take ko gaske? Anty ce ko aljanarta? Tsaye tayi a gurin kamar an dasata. Idan har da gaske Anty zata yi farinciki ganinta dan tayi marmarinta sai dai kuma bata fatar amAnty taga ganta a halin da take ciki.
Bata gasgata Anty bace har sai da ta ƙaraso inda take ta dafa tana mata kallon mamaki dan duk yadda Yasmin ta faɗa mata sai taga abun yafi haka muni.

“Namra...!”

Rumgume Anty tayi ta fashe da kuka. A maimakon Anty ta rarrashe ta sai kawai ta tureta daga kafaɗarta.

“Wane irin hali ne wannan Namra? Jibe ke, a haka kike zaune kamar baiwa? Namra me yake ƙwaƙwalwarki? Kina rayuwar da ko amafarki ban taɓa tunanin za kiyi ba?”

“Idaba nake Anty, bautar Allah na ke, talauci da arzki duka na Allah. Da ace talakawa Allah yayi mu da sai dai mu hange wasu masu kuɗi suna sha'aninsu, mu muna cikin talauci. Dan kawai ina ƴar mai kuɗi ba shi yake nuna zan dauwama a daular duniya ba, duk wanda yayi arziki dole ne arzikin ya barsa ko kuma shi ya mutu ya bar arzikin, amman ba'a dauwama da duka biyu”

A natse take maganar cikin hikima tana son Anty tayi ma maganarta karatun ta natsu, ƙoƙarin lurar da Anty take kwaɗayin dukiya ba zai sa ta ƙi zaman aure ba. Ajiyar zuciya Anty ta sauke, tabbas ba xata iya canja abinda Allah ya rubuta ga Namra ba, amman tana ganin rashin dacewa a zamantakewar auren ta, wanda abu ne mai wahala da iya ɗauke idonta akan haka, bayan kuma tasan Asim ɗin ba dan Allah yake zaune da ita.

“Namra wannan rayuwar bata kamace ki, ƴar gata ce dubi inda kike zaune, yaushe gidan ya ƙone? Baki faɗa ba? Kina tunanin zurfin ciki zai miki magani ne?”

Ta share hawayenta ta hannun rigarta.

“An daɗe da yin gobarar, ban faɗa ba ne saboda ba lalle bane ku yarda a wacan lokacin”

“Je ki haɗa kayan ki, gida zamu je yanzu, zaman ki a gidan nan ya ƙare, an faɗa min har dukan ki Asim ya ke Namra wai me ke toshe miki ƙwaƙwalwa ne?”

Gabanta ya faɗi, tana jin rashin kyautawa a abinda Anty take ƙoƙarin aikatawa, dan me zatayi tattaki dan kawai ta kashe mata aure?

“Abbah ne yace ki zo da ni?”

“Ki shiga ki ɗauko hijabin ki na ce...!”

Anty ta katsa mata tsawa... Ja da baya Namra ta yi tana hawayen

“Ba zan biki ba Anty, Abbah ya faɗa min kar na kuskura na tunkaro gidansa da sunan saki ko yaji, ya nanata min lokacin da naje gida, ya ce duk na zauna masa a gidan sai dai ya kore mu ni da ke. Ba zan kashe miki aure ba, ba zan ƙara jefa kai na a halaka ba, mutane ba zasu jefe ni da biyu ba, ace na kashe miki aure kuma na bijirewa mahaifina”

Har cikin zuciyarta take faɗin haka, dan ta haƙiƙance a ranta ba zata taɓa biyar Anty ba, ba zata ja mata wani zagin ba, sai ace taje ta kashe mata aure. Bayan kuma tasan Abbah ba zai taɓa yarda ta zauna a gidan sa ba, ta kuma san Anty zata iya rabuwa da Abbah akan ta.
Wani irin kallo Anty take mata na mamaki da rasa abinda zata ce mata.

“Namra ke ba cikakkiyar mutum ba ce, ke rabin mutum ce! Ban san wanda ta haife ki bayan ni ba, da sai nace ke ba ƴata ba ce, ina da sanyin hali amman be kai ka ki ba ke sakarya ce, marar hankali dabba wace bata san ciwon kan ta ba. Na yi tunanin kin yi hankali na ɗauka kin gane inda duniya take a yanzu, ashe ke wawuya ce....”

Cikin zafin rai da ɓacin rai Anty take maganar sautin muryarta na fita ko'ina da ace ba babban gida bane da tuni an yi musu taro. Hawayen takaici.

“Na yi hankali Anty kuma zan zo gareki idan har Allah ya ƙaddaro rabuwa da tda Asin ya bani takardar sallama”

“Tam Allah ya ba ku haƙuri zama”

Ta duƙa ta ɗauki carbinta daya faɗi sannan ta miƙe tsaye ta kalli Namra da kyau da kyau. Sannan ta juya ta soma tafiya jiki ba ƙwari.
Rugawa Namra tayi a guje ta sha gabanta ta rumgume ƙafatunta, tana kuka sosai.

“Dan Allah Anty karki yi fushi da ni, dan Allah ki fahimci ne”

“Ba zan taɓa fushi dake ba Namra, ba zan tdine miki ba, Allah yayi miki albarka, idan kin lalace dole za a ce ƴata ce, idan kin ɗaukaka dole kuma ace ƴata ce, amman ba zan sake wauwayar gidan auren ki da Asim ba ko da kuwa gawarki ce a ciki, kar kuma ki sake roƙo na komai, ba zan baki ba matuƙar ba ki yi hankali ba kisa wannan a zuciyarki...!”

Ta janye ƙafarta ta bar Namra nan tana aikin kuka, ta nufi gate hawaye ya gangaro a idon Anty. Wani irin kuka Namra take, kukan da ita kanta ta manta when last tayi irinsa, ko ba komai tasan ta ɓata ran Anty, tabbas Asim ba mijin aure ba ne, amman ta yi alƙawarin zama da shi har iya rayuwarta dan kawai ta cika umarnin Abbah. Idan har ta bi Anty a yanzu duniya zasu zage ta ita da Anty kuma zata ƙara ɓata ran Abbah.

Tashi tayi taje gurin gate ɗin ta tsaya tana kuka, tana kallon motar Anty har ta suka bar unguwar. Sai ta zube a gurin ta ƙara fashewa da kuka tan mai jin kamar ta falla da gudu ta bi Anty.

Iya hawayen da Anty tayi a gidan Namra ne hawayen tausayin Namra, har ta suka isa gida bata sake wasu hawayen ba, dan yanzu ta fahimci Namra ba abar tausayu bace tun da bata tausayin kanta. A hanya Namra nata kiranta amman ta ƙi ta ɗaga wayar.
Su Maryam tun kamin ta yi musu bayani suka fahimci komai tun daga yanayinta da kuma ganin ba a zo da Namra ba.

Bayan ta huta ta faɗa musu abinda ya faru, duk basu jidaɗi ba, musamman Maryam da tafi so zafin rai, kasa haƙuri tayi har sai da ta kira Namra ta yi mata faɗa kamar wata yayarta.

A ɓangaren nan kam
Haka ta wuni cikin kuka daman aikinta ne shine ya zame mata abokin fira. Sai goman dare Asim ya dawo kamar yadda ya daba yana ganin yanayin Namra ya san ba lafiya ba, amman saboda mugun hali yaƙi ya tambaye ta damuwarta.
Sai ƙoƙare kai mata buƙatarsa yake. Ture masa hannun tayi ta tashi zaune cikin ƙunar zuciya ta ce

“Aikin kenan, Asim ka rako maza duniya, kai wayayye amman wayewar ka bata maka amfani ba, babu ruwanka da damuwa kai dai na gurka kawai ka ci, dare yayi ka kawo min buƙata, shine kawai...!”

Nuna kansa yayi duk da ɗakin babu wani haske sosai.

“Ke ni kika faɗa ma wannan maganar? Wuyanki yayi kauri ko Namra? Kin rai nani saboda bana da naira saboda ni takala ne ko?”

“Idan har talaucin ya dame ka miyasa baka yi ihun arxikin ya zo maka ba? Miyasa idonka ya rufe akan neman abinda za ka mutu ka bari, kai ne baƙon arziki shiyasa kake yawantar faɗarsa”

Tashi yayi ya ƙara motsa kusa da ita da zimmar dukanta, jikinsa har bari yake.

“Ni kike faɗawa wannan maganar Namra? Ni sa'anki ne?”

Mari ya kai mata ta gauce, ta fita waje da sauri. Bata zame ko'ina ba sai inda take girki, wuƙa ta ɗauko ta shigo ɗakin da ita idonta a kafe irin yau ba imani ɗin nan ta nuna sa da ita.

“Karka kuskura kace zaka taɓa ni Asim, zan iya kashe ka Asim, baƙin cikin da yake rai na zan iya juye maka shi a yau, tun da ka shigo gidan nan baka tambaye damuwa na ba, baka tambaye waya mutu waya rayu ba kai dai kawai matsalarka ka sani, saboda kai na ɓata ran mahaifina, saboda kai yau mahaifiyata ta koma gida cikin ɓacin rai, na kira ta bata ɗaga ba Maryam.ta kira ki babu irin cin mutumcin da bata min ba duk a kan ka Asim. Tam ya ƙare yanzu wuta ba zata sake cin ƙara ba, sai dai quta ta ci wuta...!”
Chapter 82 · 0% Book details