← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 173

Sashe 39

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ai ba itace abun tausayi ba, Yayanki ne shi da ba shi da kowa sai Allah ita kau har iyayenta suna da abun hannun su”

“Ita ai da tausayi Wallahi”

“Hmmm Allah dai ya kyauta kawai”

Namra na fita ta ƙara wayar a kunne tana dda ƙoƙarin gyara muryarta kar Anty Amarya ta gane tana cikin damuwa.

“Anty”

“Na'am Namra y jikin mijin na ki”

“Ya ji sauƙi”

“Allah ƙara lafiya Wallahi Abbah kin ya hana na dawo duba shi, ko jiya sai da nayi masa magana sai ma masifa ya riga min, Abban ki ya kira ki?”

“Ba komai ai yaji sauƙi, be kira ni ba wayana ya faɗi ban sani ba ko ya kira”

“Har yanzu baki daina halin ki na sakarci ba ko? Ya faɗi ko dai kin siyar?”

“Wallahi faɗuwa yayi”

“Namra ki yi hankali da mutane, ba kowa ne yake son ya gan ka a cikin alheri ba, wani yana baƙincikin yaga kana jindaɗi, wasu fa hassadarsu ba ƙarama bace, kowa abunda yake ƙoƙarin yi ya ture ka daga jindaɗin shi ya shiga, ko kuma ya ture ka duk ku rasa, ba kowa bane zai so ki tsakani da Allah ba, idan kina da shi kowa naki ne, sai ranar da kika rasa komai zaki gane masu son ki da gaskiya

Wani ƙiyayyar tasa a ɓoye take ba zaki taɓa ganewa ba, haka zai ta miki zagon ƙasa har sai ya ga kin rasa komai sannan hankalinsa ya kwanta, dan haka kiyi tunani sosai da duniya, idan baki da hankali mutanen duniya za su miki shi, ki rage damuwa a ran ki ki sawa ran ki sassauci”

“Na gode Anty”

Ta faɗa har cikin ranta, kalaman Anty sun mata daɗi, sai dai tasan ba kowa Anty ke nuna mata ba, sai Asim dan tana tunanin kamar da biyu ya aureta, gani take har yanzu Anty bata yarda da Asim ba.

“Allah ya ƙara masa lafiya, na kira wayarki ban samu ba, shine Maryam ta karɓo min number Asim”

“Eh ai naga line Maryam ne, na gode sosai”

“Tau Sai anjima”

“Okay

Daga haka suka yi sallama. Wayar na yankewa wa Namra ta tsara text ta tura mata Anty Amarya a wayar Maryam.

“Maryam... Zo ki karɓi wayar ki”

“Na'am”

Ta aje system dake jikinta, ta taso ta nufo ɗayan ɓangaren inda Anty Amarya take. Tana karɓar wayar text na shigo, Anty Amarya bata kula ba, ta miƙa mata wayar ta nufi gurin sha'aninta.

_Anty ina cikin matsala, bana iya faɗa miki a waya nasan faɗa zaki min, dan Allah ki taimaka min da kuɗi ko kaɗan ne_

Maryam ya gama karanta saƙon taja wani dogon tsaki ta danna deleted ta goge saƙon.

“Ai fa kullum haka zai riƙa saki kina yi, tun da yaga be samu abunda yake so ba, kai mutanen duniya nan da abun haushi da mamaki suke, ala dole dan auri yar masu kuɗi kai sai kayi arziki, to sai kaje ka ci ubanka, ya mayar da ita saniyar tatsa”

Ta koma mazauninta tana mai jin haushi Namra da Asim ɗin.

KALSOOM POV.

Hilal na kallonta ta girgiza masa idonta da hawaye.

“Wallahi ban aikata ba, ban san wannan mutumen ba Wallahi”

Hannu Hilal ya kai ya ɗauki hotunan yana kallo. A-uzubillah hotunan babu kyau kallo, Kalsoom ce tsirara ita da wani, wani gurin yana kissing ɗinta wani gurin kuma tana kissing ɗinsa.
Ɗaya bayan ɗaya ya riƙa duba hotunan har ya gama sannan ya kalleta yace

“Kin san wannan mutumen”

“Wallahi ban san shi ba, ban taɓa ganinsa ba”

Ta faɗa da kuka.

“Daga ganin wannan ma ai haɗi ne, i trust my wife's ba zaki aikata irin wannan abun ba, duk yadda akayi wannan abun shirya sa akayi”

Ta ƙara fashewa da kuka

“Wallahi sheri ne kawai, na rantse da Allah ban taɓa ganin wannan mutumen ba”

Shiru Hilal yayi kamar mai nazari.

“Ina suka samu hoton ki?”

“Wallahi ban sani ba, dan Allah ka yarda da ni Wallahi sheri ne”

“Na yarda sheri ne, daga gani ma ai kasan haɗi ne, daɓ ga fatar fuskar ta banbanta dana jikin hoton, kuma miyasa ba a kawo lokacin da bana nan ba, sai da ina nan? za a iya haɗa irin wannan hoton a computer? But i can't believe is taya suka samu hoton ki?”

“Wallahi ban sani ba”

“Baki sani ba kamar ya? What kind of nonsense is this? Aljani za a turo ya ɗauki hoton ki ko me?”

Durƙushewa tayi ƙasa tana kuka.

“Wallahi ban sani ba Hilal na rantse da Allah ban aikata ba”

“Naji baki aikata ba, faɗa min ta ina suka aka samu hoton ki?”

Ya faɗa a tsawace irin zuciyarsa ta fara kawowa ɗin nan.

“Wallahi ban sani ba, ni ban turawa kowa hotona ba”

Ɗuƙawa yayi a hasale ya kwashe hotunan ya nufi ɗakinsa da su. Wani irin zugi zuciyarsa ke masa, baƙin kishi ya taso masa.
Haka ya tiƙa duba hotunan kamar wanda zai haddace su, shi dai what he believe Kalsoom ba zata aikata haka ba, sai dai kuma kansa ya ɗaure har yana jin tunaninsa na ƙoƙarin canjawa.

Bedside drawer sa ya buɗe ya zuba hotunan ya rufe, sannan Shirya cikin ƙananan kaya ya feshe jikinsa da turare ya ɗauki atms ɗinsa ya saka a aljihu da wasu ƴan canja, sannan ya ɗauki wayarsa da keys, ya fice daga ɗakin fuska babu annuri.

Sheshekar kukanta ya ɗago da hankalinsa i zuwa gareta, ashe duk tsawon lokacin tana a gurin tana aikin kuka, jikinsa ya mutu yaji ba daɗi ganin kamar shine silar hawayenta. Ƙarasawa yayi kusa da ita ya ɗafa ta

“Kalsoom Calm down, nima fa wayayyen mutum ne nasan za a iya haɗa wannan, amman kin ƙi ki bawa zuciyata damar yarda da hakan”

Ɗagowa tayi ta kalleshi tana kuka fuskarta da majina nashe-nashe.

“Wallahi ban sani ba, ni ban turawa kowa hoto na ba”

“Kina da grp ɗin da kika chat da maza ko?”

Ta ɗanyi shiru tana tunani.

“Grp ɗaya ne, shima kuma na koyon sana'ah ne, kuma ban taɓa magana a grp ɗin ba Wallahi, Instagram ɗina da Facebook tun da nayi aure ban sake hawan ko ɗaya ba Wallahi”

“Good indeed, kina instagram ba? Kina facebook?”

“Amman tun da nayi aure ban sake shiga ba”

Zaunawa yayi kusa da ita yana cire password ɗin wayarsa.

“Ba ni handle ɗin ki”

“Kalsoom_Miss-Arewa”

Instagram ya shiga yayi searching sunanta, sai ga account ɗinta. Yadda ya riƙa ganin hotunan ta sai wani baƙin kishi ya motsa masa.

“Duba nan, yanzu miye amfanin waɗannan hotunan? Kina tallar kan ki kamar ba mace ba, miye abun burgewa a sakin jiki wasu mazan na kallo, ke a ɗaukar ki duk wayewa ce ko? Dole ne sai kin sa hotunan ki a instagram ko facebook?”

“Wallahi ni ba da wata manufar na yi ba”

“Nasan ba wata manufar kika yi ba, su yanzu waɗanda suke da wata manufar ai sun ɗauka sun yi yadda suke so da shi. Duk abunda addini yake hana ƙu baku ganewa, duk abunda kika ga musulunci yace a bar shi barin shi yafi alheri amman baku ganewa, dubi wannan abun wani gurin ma ai rabin jikin ki a waje, ba editing kaɗai ba har asiri sai a ɗauki hoton ki ta nan aje a miki”

Yaja tsaki yana mai miƙewa tsaye.

“Kamin na dawo ki tabbatar kin goge duka hotunan ki da suke facebook da Instagram, ban hana ki yin chat ba amman ban yafe ki yi da wani namiji ba da aurena, duk mazan nan nan friends ɗin ki yi unfriend ɗin su, kuma Wallahi kar na sake ganin hoton ki a social network”

“Wallahi ni daga yau ma na daina chat ɗin gaba ɗaya, amman ka yarda da ni dan Allah”

“Idan ban yarda da ke ba, zan zauna ina magana da ke haka? Very soon an gano wanda yayi wannan abun, akwai mai son shiga tsakanin mu ne”

Gabansa ta dawo ta risina ta riƙe ƙafafunsa.

“Na gode Allah ya saka mana”

Ɗagota yayi ya rumgume. Zuciyarsa cike da kishin hotunan can daya kalla, duk da yasan cewar ba haɗi ne amman yana kishin hakan.
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

                             Website
         www.khadeejacandy.com.ng

*PAGE - 30*

NOT EDITED ⚠️

Ƴan ƙuɗin da suka mata  saura a jakarta, da kuma dubu ashirin ɗin nan Hajiyar gidan ta bata, su ne take ta maneji ta su tana siyen abinci.

A kullum gidan su Mardiya take kwana, wani lokacin har zanenta take ɗaurawa, kamin ta ɗinka kala biyar a cikin kuɗin. Tayi ta zuba ido tana jiran kuɗin Anty Amarya har ta gaji, tun tana sa ran zata ta kira wayar har ta gaji da jiran ta fara tunanin wata mafitar.
  Da ta fito daga gida kai tsaye ta nufi gidansu Hajiya Saratu, har ta isa zuciyarta na nuna mata illar abunda zata yi, ko ba komai zai nisanta ta da Ubangijinta, sannan duk wanda yasan abunda ta aikata mutuncinta zai zube a idonsa, ashe Allah zai jarrabeta da wani matsi har kuma ta nemi tsaɓa masa, idan har ta yi haka bata kasance cikin nagartaccin bayi ba.

Juyar da fuskarta tayi gefen ti-ti tana kallon motocin dake kai da kawo, hawaye na silalawo daga idonta, wani bangare na zuciyar yana ƙoƙarin rinjayarta akan idan har ba ita ba, bata da wata mafita, babu kuma wanda zai taimake ta sai ita. Haka ko wane bawa zuciyarsa take nasalta masa alheri da sheri duk ɓangaren daya rinjaye ka shi zaka aikata.
Hannu ta kai ta share hawayenta, tana mai jin ƙyamar abun a ranta, yanzu idan taje garin aikata ta mutu fa? Me zata cewa Allah? Haƙiƙa an jarrabi wasu gabaninta da suka yi haƙuri kuma sai Allah yayi musu mafita, kuma bayan ita za a jarrabi wasu a bayanta, haka Ubangiji yake jarraba bayinsa dan ya auna imaninsu da kuma yarda da ƙaddara.
Chapter 39 · 0% Book details