Sashe 98
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ALLAH sarki rayuwa kenan, shi rashin sani yafi dare duhu, kuma sanin gaibi sai ALLAH duk jarumtar umma da alkunyarta dole zata ajiyesu agefe tayi duk abunda take ganin ya dace akan 'yar tata tilo da take kallo amatsayin sauran farincikin da yarage mata aduniya, saboda rashin sanin ainahin abunda kefaruwa ga Nuraddeen da batayi ba , ba itaba hatta iyayen nasa dake tare da wud'anda suka aikata son ransu akansa basu san abunda kefaruwa ba, Basu san abunda akayi masa ba har yakoma haka balle ita, abune gaibi dabai bayyana agaresu ba, amma komai nisan dare gari zai waye kuma SANNU SANNU bata Hana zuwa...in Sha ALLAH da sannu ALLAH zai bayyana komai kuma yawarware dukkanin wani qullin da basuda masaniya akansa, ya haskake duhun dake gabansu suka kasa ganosa kuma ya yaye masu duk wani shamakin daya zamo silar wanzuwar wannan qaddararriyar matsalar data cutar masu da d'a.
A b'angarensu Rashida kuwa little nawucewa Fatima tanufi d'akinta tana bubbuga mata qofa tana kiran sunanta, tanajin yanda sautin kukanta ke tashi alamun tana jinta amma taqi zuwa tabud'e qofar, tasowa Dr nura yayi yadafa kafad'arta ta juyo ya girgiza mata kai alamun ta qyaleta tace amma Dr tana buqatar wani akusa gareta dazai rarrasheta kuma kasan tana fama da matsalar bp nan kada yazo ya tasar mata, jawota Dr yayi yana fad'in, ki k'yaleta babu abunda zai sameta, ahalin yanzu tafi buqatar kad'aici fiye da komai, mubarta tazubar da hawayen shine zai sama mata sassauci azuciya fiye da ace anhanata fitar dasu, wallahi matar Ina tausayin rayuwar yarinyar nan, tun daga lokacin datayi qoqarin sauya ra'ayin mahaifinta akanta yayi mata abunda takeso ALLAH ke jarabtarta har zuwa wannan lokacin, idan tafita wannan saita shiga waccan kuma duka adalilin rayuwar auren da tayi iqirarin cewa tana so, ubangiji nayi mata hakanne saboda yagwada qarfin imaninta agaresa, kinga kuwa tanada dalilin zubar da hawayenta ko don tasamu qarfin canye jarabawarta, sau da dama kukan da mukeyi akan damuwarmu yana taimaka mana wajen yaqi da ita sab'anin shirunmu dake mummukar zuciya har yasanya mana raunin da zamu iya yaqi da damuwar tamu balle mucanye jarabawowin mu.
Suna nan zaune afalo har little yayo wanka yadawo fatima tasa shahida da alokacin tanada shekaru goma sha biyu ta zibo masa abinci, Saida yaci yaqoshi sannan yafara dube dube yana tambayar Fatima ina gwoggonsa wato Rashida, don yasan idan tana nan to tabbas bazataji dawowarsa daga makaranta ba kuma taqi fitowa, kasancewar har lokacin bata fitoba balle taci abincin rana yasa Dr yace yaje ya had'a mata abincin ranarta yakai mata tana d'aki, yayi hakanne don yasan ahalin yanzu shikad'aine zata iya saurara kuma ya kusanceta taji sanyi aranta.
Shahida ce tayi saurin riqa masa tray d'in daya d'auko da abinci tabi bayansa dashi, sau kusan uku yana qwanqwasa mata bata bud'e ba kafin can yasoma kiranta, gwaggo, gwaggo kibud'e qofa yaci gaba da fad'a yana dukan qofar, tanajin murayarsa da sauri ta taso tabud'e qofar, qura mata idanuwa yayi ganin yanda sukayi ja had'e da kumburewa kafin yajuyo yakarb'i tray d'in ahannun shahida yana fad'in sannu sister, sannan yashiga daga ciki had'e da sake tura qofar da qafa tarufe, Saida ya ajiye tray d'in a saman gado daga gefe sannan yadawo ta gabanta ya zauna, yanaci gaba da kallonta cikin natsuwa yanason karanto damuwarta, little yarone Mai matuqar natsuwa da sanyin hali, koda yatashi baiyi irin qiriniyar nan ta yara ba saboda rashin son hayaniyarsa, yanada matuqar tsinkaya da kuma fahimtar abubuwa da sauri, musamman ga mahaifiyarsa da akoda yaushe yake jinta har tsakiyar ransa, duk da bawata shaquwa bace sosai tsakaninsa da ita saboda gaba d'aya kulawarsa ta ta'allaqane akansu Dr da kuma su umma da ammie, amma yana jinta aransa tun daga lokacin da yasan cewa itace mahaifiyarsa wacce tahaifesa da cikinta, saboda kulawar da yake samu awajensu Dr baisan cewa basune suka haifesa ba sai lokacin da hajia nafeesa taci masa mutunci tare da zazzagesa shida umma, anan ne yagano cewa yanda yake d'aukar ammie amatsayin kakarsa dady kuma kakansa ashe ba hakan neba, umma daya d'auka amatsayin matar dady kawai ashe itace kakarsa, gwaggo kuma itace 'yarta wato mahaifiyarsa basu Fatima da Dr ba,
Cikin natsuwa yace waya b'atawa gwaggona rai haka har ta zubar da hawayen da suka kumbura mani idanuwanta?, d'ago kai tayi ta kallesa sai taji wasu sababbin hawaye sun zubo mata tasake fashewa da wani kukan tare da jawosa tarungumesa, sunjima ahaka kafin tatsaida kukan nata had'e dasa hannu tana share hawayen da suka jiqa mata fuska tana fad'in, kana so kasan wanda yab'atama gwaggonka rai?
Da sauri ya d'aga mata kai yana gogen 'yan hawayen da suka zubo masa sanadiyar kukan da yaga tanayi, wani irin nishi mai sanyi tayi sannan tace dashi, abbanka ne little, abbanka shi yasani wannan kukan da naga kanayi.
Cikin farinciki yamiqe yana dudduba ko ina cikin d'akin had'e da cewa, abbana yadawo ne gwaggo? A ina abban nawa yake?, yaushe yadawo ne gwaggo amma kikak'i kirana?, Abba, abba.., ya shiga kiransa yana qoqarin fita.
Saurin dakatar dashi tayi tana kallonsa had'e da cewa, kadena kiran sunansa don bazai amsa ba, kadena nemansa don bazaka tab'a ganinsa ba kuma kadena tunanin zaka had'u dashi nan kusa kamar yanda nake fad'a maka don bazai dawo ba,
Dawowa yayi ya zauna kusa gareta yana fad'in, Amma gwaggo ke kike bani labarinsa akullum tayanda zuciyata tacika da qaunarsa da kuma son ganinsa da jin muryarsa, ke kika sanya mani tunanin cewa zanga mahaifina nan kusa alokacin da ake shegantani, gaba d'aya mafarkina da kuma muradaina sun ta'allaqane alokacin da zan had'uwa da mahaifina kamar yanda ako yaushe kike fad'amun cewa nan kusane bada jimawa ba amma meyasa yau zaki rusa mani su tahanyar cewa nadena tunanin abubuwan da nake fatan zuwansu gareni akoda yaushe?, duk wannan maganar da yake cikin tausasawa da kuma sanyin murya yakeyi matasu,
Riqo hannunsa tayi tace, nasan ni nasa maka wannan tunanin da kuma shauqin soyayyar mahaifinka dason ganinsa, duk nayi hakanne cike dasa ran cewa zai dawo agaremu, amma sai gashi yau da bakinsa yafurta cewa bazai dawo agaremu ba har abada, yazab'i yarabu damu ya zauna acan wata qasar shida wud'anda yake ganin sun fimu saboda rud'in abun duniya, dakansa yasanya wuqa mai tsananin kaifi ya kashe alaqar dake tsakaninsa damu sannan yayi amfani da kalamai mafi d'aci da kuma quna da rad'ad'i ya tunb'ukemu daga cikin rayuwarsa, don haka a matsayina na mahaifiyarka bana son kasake yimani magana akansa da kuma abunda ya shafesa, ina son ka kashe duk wasu mafarkai naka da kuma muradanka matuqar nina haifeka.
Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, gwaggo idan nayi hakan meye makomar rayuwata?, Wace sheda zan bayar ga mutanen dake shegantani?, wane irin qwarin guiwa zan samu wajen martabaki a matsayinki na mahaifiyata bayan kinsa sharud'd'a masu matuqar nauyi agareni da zasu hanani tsayuwa ako ina inbugi qirji cewa ni d'an halak ne?,
A razane tamiqe had'e da d'aukesa wani irin zazzafan mari hawaye nazubo mata a fuska saboda jin d'acin kalmar da yayi taqarshe sannan ta nunasa da yatsa tana cewa, ko kayarda ko karka yadda kai d'in d'anane kuma kai d'an halak ne ba shege ba kamar yanda mutane suke fad'a, kuma yazama dole kasa a ranka kuma kayarda da hakan azuciyarka.
Ganin yanda b'acin ya bayyana a fuskarta qarara da kuma tsantsar qaunarsa a idanuwanta yasa yariqo hannuwanta ya zaunar da ita yana share mata hawaye had'e da cewa, kiyi haquri gwaggo idan nab'ata maki rai kuma kiyafe mun, na amince da sharad'inki nafarko amma don Allah kijaye nabiyun, kibarni in rayu da mafarkaina nason had'uwa da mahaifina da kuma muradaina akansa domin zasu tsaya mani wajen yaqar duk wasu kalaman cutarwa akaina,
Hannunta ta aza a kuncinsa had'e da cewa, katabbata haka yarona?, Yace sosai gwaggo, tayi murmushin da iya saman d'eb'enta ya tsaya sannan tashiga labarta masa irin firar da akayi da mahaifinsa kamar yanda talabarta masa rayuwarsa da ita acan baya kafin abubuwa suzama hakan, wani wajen tana fad'a masa tana 'yar dariyar da tafi kuka ciwo wani wajen kuma idan takawo fad'a masa tana hawaye, duk da qananan shekarunsa haka yayita bata magana don yana nuna mata yanayin yanda rayuwa kezoma bawa kamar yanda akoda yaushe take lurar dashi, don kam gwargwado yasamu gatar ilimi da tsantsar tarbiya daga garesu, saida yaga damuwar da take ciki tad'an ragu sannan yajawo abincin daya shigo dashi ya zubata tare da miqa yana cewa, kici abinci gwaggona, jarumar uwa, d'aya tamkar da dubu, linzamin rayuwata kuma hasken idaniyata, kinsan da ALLAH kuma yasan dake shiyasa yake shiga dukkanin lamurranki har yake jarabtarki aci, kiqara haquri in Sha ALLAH ranar cikakken farincikinki nazuwa, ahankali nake maki fatan canye duk wata jarabawarki da qaruwar imaninki had'i da lafiyarki, SANNU SANNU dai Bata hana zuwa..da yardar ALLAH sai kinzamo zakaran gwadin dabi aduniya, Ina sonki sosai mahaifiyata kuma inafatar zakici gaba dayi mani addu'ar cimma mafarkaina domin duk halin abbana shima Ina matuqar sonsa.
Wani irin sanyi taji azuciyarta tare da yima ALLAH godiya daya batashi amatsayi d'anta, ko ahaka aka tsaya ta tabbata batayi asarar auren da qurciya tasata iqirarin sonsa ba ba tare da tasan qalubalen dake ciki ba wanda ayanzu take nadamar yinsa arayuwa.
Bayan kwana biyu dady dasu umma da ammie sukazo gidan saboda tattaunawa akan matsalar don tun ranar bai koma d'auko zancenba sai yau saboda bayason abun ya haifar masu da damuwa tsakaninsa da umma.