← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 160

Sashe 126

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina fatar hakan zata kasance atare damu, yanda muka rayu atare kuma mumutu atare, zuciyata nafad'amun cewa soyayyar da muke yiwa junanmu bazata bari d'ayanmu ya rayuba matuqar babu d'aya, "
"Idan ma hakan tafaru Abu sumayya to tabbas rayuwar wanda aka Bari bazatayi amfani ba domin Babu mahad'inta aduniya, Ina matuqar tsoron zuwan wannan ranar domin bazan juri rashinka ba Abu sumayya."

"Haka nima gimbiya bazan iya rayuwa babu keba."

"Da gaske?"

"Fiye da gaskiyarma idan akwai yafad'a tare da sake jawota ajikinsa suka nufi saman gadon" suna dariya.

_Ina ganin haka nafito aguje had'e da cewa Saida safe duk da ba lallaine su jini ba tunda basu san dani ba_😅🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️asuba tagari.

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___92💎

Haka rayuwa taci gaba da kasancewa a b'angaren su baffa wani lokaci farinciki wani lokaci kuma baqinciki musamman idan sun kalli halin da d'an uwansu ke ciki yanda rayuwa ke basa wahala amma yakasa fahimta, ga matarsa gaba d'aya ta gujesa yanzu, babu wata kulawar da yake samu daga wajenta saboda yanda ta qara kwand'arewa a lokaci d'aya, Babu Wanda ya isa gareta kuma babu maiyi mata magana taji sai abunda take so, ta maida bara umrun azhimun tare da bashi muhimmanci fiye da komai arayuwarta, duk iya qoqarinsu baffa na ganin sun dakatar da ita hakan ya cutara dole suka haqura suka zuba mata idanuwa amma abun na matuqar cimasu tuwo aqwarya,

Ganin irin yanayin da baffa Ali ke ciki na rashin samun cikakkiyar kulawa yanda yakamata duk da d'ansa Yusuf na iya yinsa yasa suka yanke shawarar kaisa asibiti saboda basuda lokacin zaunawa subashi kulawar data dace tunda kowanensu na wajen kasuwancinsa matarsa kuma batada lokacinsa tana can wajen bara, gashi magani akeyi amma kamar ba'ayi, saboda tsananin baqar zuciya baffa Ali ya nuna masu baya buqatar taimakonsu, sunyi sunyi dashi har sun gaji amma fir yaqi amincewa dole suka haqura shima suka saka mashi idanuwa don kowacce duhu to baiji zawo ba,

Wasa wasa qafar baffa Ali ta sake kumburewa wasu ruwa nafita daga cikinta masu shegen wari, tun baffa Ali yana haquri da jurewa har yakai yafara kuka saboda tsananin azabar ciwon dake damunsa, reras yake zaunawa yayita kuka Amma babu wanda ke kulasa sai yusuf, baffa Usman kuwa dama yayi zuciya yafita al'amurransa yana jiran lokacin da zai gano cewa shayi madarane yakawo kansa da kansa in taqamarsa kafiya da mugun riqo azuciyarsa,

Da daddare yau baffa Usman na kwance yajiyo ihun d'an uwansa na kuka yana qarawa saboda azabar data kaimasa karo yana kiran sunansa yazo ya taimakesa ya kawo masa d'auki, yaso ya qyalesa har sai yaqara gano kuskuren da ya aikata amma qarfin jinin zumunci dake gudana a tsakankaninsu yasa yakasa aiakata hakan, saukowa yayi daga saman gadon da yake kwance tare da jawo wayarsa ya zura aljihu sannan yabud'e d'aki yanufi d'akin da baffa Alin yake lokacin qarfe uku da minti biyar na dare, koda yashiga ya isko yusufa rungume dashi shima yana kuka had'e da tofa masa addu'a, yana ganinsa yafara qoqarin qwace jikinsa daga yusufa tare da riqo qafafuwan baffa Usman yana fad'in.

"Ku taimakeni Usman ku kaini asibiti, mutuwa zanyi don ALLAH ku taimaka mani kada narasa rayuwata, wayyo Usman qafata zan mutu."

Duqowa baffa Usman yayi saiti dashi had'e da cewa.

"Bazaka mutuba Ali said dai idan dama lokacinka yayi, kaga abunda muke guje maka tun farko rayuwarka, d'an uwanka kuma yayanka uwa d'aya uba d'aya ka zauna kana goranta masa don ALLAH ya jarabcesa da lalurar da tazaunar dashi waje d'aya kana yimasa dariya da kuma isgilanci, to yau gashi kaima ubangiji ya damqeka, Ina waccan lafiyar da kake tinqaho da ita?, Ina alfaharin da kakeyi na kanada qarfin yawatawa duk inda kake so don ALLAH ya aramaka lokaci?, Dubeka kagani yanda ALLAH yayi da kai yanzu wa gari yawaya tsakanin kai da kuma shi da ka dinga yiwa dariya?"

Wasu zafafan hawayene suka sake karyikkewa baffa Ali yana kuka yace.

"Kadubi ALLAH da girmansa kutaimaka mani ku kaini asibiti, inajin tamkar ana jawo lumfashina daga qasan qafata izuwa bakina, yanzu haka kokuwa nakeyi dashi ta yanda banida tabbaci akan zaici galaba akaina ko kuma ni naci galaba akansa, kutaimakeni, kutaimakeni, kutaimakeni, kutaimakeni 'yan uwana fisabilillahi badon halina ba."

Shidai Yusuf banda kuka babu abunda yakeyi, tausayinsa yasa jikin baffa Usman macewa yaciro wayarsa a aljihu yakira baffa ya sanar dashi halin da d'an uwan nasu ke ciki, cikin daren baffa ya taso ya bud'e qofa yanufi gidansu baffa Usman jikinsa na rawa ba tare da yadamu da yanayin daren da ake ciki ba sai addu'a yake abakinsa har ya isa, baffa Ali naganinsa ya sake bud'e baki kai kace qaramin yarone yana gumza saboda azabar ciwo.

"Yaya kutaimakeni, qafata, zan mutu, zan mutu yaya, wayyo qafata,"

Kasancewar baffa mutumne mai raunin zuciya nan take zuciyarsa ta karye ganin yanda qanen nasa ke kuka shima yafashe da kukan.

"Innalillahi wa Inna ilaihirrajiuun, Ali kayi haquri, ka kira ALLAH in sha ALLAH bazaka mutu ba, yusuf bani ruwa a kofi."

Yafad'a tare da zaunawa gabansa saman wata kujera dake jikin bango don bayada qarfin iya jurewa tsayuwa hawaye nacigaba da zubo masa.

Baffa Ali kuwa sai nishi yakeyi yana fad'in.

"ALLAH!, ALLAH!!, ALLAH!!!.."

Kamar yanda yaji baffa yace yakira ALLAH yadena ihu da kukan da yakeyi baffa Usman natsaye yana kallonsa, aransa yana tunanin dama akwai ranar da d'an uwan nasu zai ajiye baqar zuciyarsa ya nemi taimako daga wajensu?, Tabbas ALLAH shine mabuwayi acikin al'amurransa maiyin yanda yake so alokacin da yake buqata, muryar baffa yaji yana fad'in.

"Usman karb'i ruwan nan katofa masa addu'ar da ada Rashida tayi tofamun a ruwa Ina sha alokacin da ina fama da lalurarnan, zaka tunata?"

Ko rufe baki baiyi ba sukaji baffa Ali yayi carab ya riqe sunan Rashida yana fad'in.

"Rashida, Rashida, kiyimani addu'a, Rashida, Rashida Ina kike, don ALLAH kitaimakeni, yaya, yaya, Yaya ku kira mani ita tayi mani addu'a, don ALLAH yaya ku kirata ta taimakeni."

Gaba d'aya zafin ciwo yasa yarud'e yafara fitar da sabbatu, amsar ruwan baffa Usman yayi yana girgiza kai, aransa yana fad'in ko shegema da ranarsa, wato yau Rashidar da suka tsana yake neman tazo ta taimakesa, duk da dai yana jin tausayin halin da yake ciki amma yana ganin koma meye ya samesa shi yajawowa kansa kuma dama ita SANNU SANNU bata hana zuwa...duk abunda mutum ya shuka sai ya girbesa, tofa masa addu'ar yayi aruwan ya duqa ya bashi yasha sannan baffa yace yad'an yayyafa masa aqafar, wani irin qara yasaki lokacin da ruwan suka saukar masa saman qafa don jiyayi tamkar an watsa masa ruwan zafi, ataqaice dai ranar su baffa basu koma runtsawa ba dasu harshi, kwana sukayi suna abu guda sanin cewa ko sun fito alokacin bazasu samu abun hawa ba, nan take baffa Ali yafita hayyacinsa banda sabbatu babu abunda yakeyi har aka kira sallar asuba, baffa yafara zuwa shida Yusuf sukayi sallah sannan da suka dawo baffa Usman yaje yayi tasa.

Duk wannan abun dake faruwa Inna ruqayya na d'aki abinta kwance tana sharqar bacci saboda baqin yawon baran da tasha, gaba d'aya batasan me akeyiba kai in kaganta tamkar wacce aka yanke sai faman kakari takeyi sai da Inna Bilkisu da itama baccin yayi mata qaura a idanuwa taje ta qwanqwasa mata qofa, shima d'in tafi mintuna biyar kafin ta taso tabud'e tana yatsina fuska cike da gajiya,

"Lafiya dukan qyaure a tsakar daren nan?" Tafad'a tana sakin wata uwar hamma kamar zata had'iyeta, d'anja baya Inna Bilkisu tayi sannan tace mata.

"A'a ba dare bane ruqayya, asubace ni Ina kukan Ali ya tadake tun d'azu kina can, sai yanzu na lura da ashe d'akin rufe yake bacci yayi maki nauyi baki farko ba."

"Eh! to meya samu Alin ne?"

"Inaga zazzab'insa ne yad'an motsa nima yanzu zanje wajen naga yanda suka tashi."

"Mtss.! Nagode ALLAH da banji ba, da yanzu ya hanani d'an baccin nan, wlh yafiye rakine, meyasa lokacin da Yaya yayi jinya shi bai ishi mutane ba har ya warke, saishi zaizo ya fitini kowa, ALLAH Toni bazan iya ba?."

Tsabar tsoron ALLAH yasa Inna Bilkisu takwashi jikinta tabar wajen tanufi d'akin Yaya hawwa tana mamakin yanda mata ke iya juyawa mijinta baya haka bayan tarabasa da kowa nasa, ta izasa wajen kashewa da kuma binnewa ga abubuwan da basu kamata ba ace yanzu ta juya masa baya, koda yake ba wannan ne farau ba agidan saidai ace ALLAH yasawaqe.

Tana shiga d'akin Yaya hawwa ta iskota zaune tana can carbi, kasancewar gaba d'aya idanuwan Yaya hawwa sun dena gani tuntuni yasa tana jin motsi tafara tambayar waye awajen don ba laifi yanzu tana d'an iya magana duk da bawani fita maganar keyi sosai ba.

"Nice Yaya!"

"Kece wa?" Yaya hawwa tafad'a cikin muryar dake nuna antsufa sosai.

"Nice Bilkisu tawajen Usman, nazone inga ko kin samu tashi kiyi sallah!."

"Aiho! Balkisu ce?, Natashi tun d'azu, sautin kuka nakeji shiya hanani bacci."

Saida Inna Bilkisu tanemi waje ta zauna sannan tace.

"Bari Yaya, Ali ne ciwon nasa ya tashi wlh gwanin tausayi, gaba d'aya jiya basu runtsa ba."

"Waye?"

"Ali nace"

"Wane ali?."

"Ali na nan gidan."

"Bayada lafiya ne?."

"A'a! keko Yaya har kin manta ai yafi shekaru dashi ko kin manta.?"

"Namanta balkisu, shi take wannan ihun?"

"Eh, kinsan kuwa abun yayi masa nauyi ace babban mutum yana kuka da ihu irin haka ai kasan shi kad'ai yasan yanda yake ji, ALLAH dai yabashi lafiya."

"To Amin balkisu, ALLAH yakyauta Kuma ya rabamu da son zuciya."

"Amin Yaya, Bari naje na duboshi."

"To kigaida shi."

Yaya hawwa taqare maganar cikin irin yanayin yanda tsofaffi ke magana, ta tabbata cewa wannan na cikin hukuntawar da ALLAH keyi masa bisa abubuwan da suka aikata tare da ita, don ita gaba d'ayama bata san abubuwan daya aikata shida matarsa daga baya ba.
Chapter 126 · 0% Book details