← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 160

Sashe 68

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk mutanen dake wajen sun matuqar tausaya masa ganin yanda hankalinsa ya tashi alokaci d'aya kowanensu nafad'in albarkacin bakinsa akan tafiyar baba batare daya sanar da d'an uwansa ba, duk dako mafi yawancinsu sun san dalilin da yasa suka aikata hakan.

Baki suka dinga bashi kafin sufara watsewa d'aya bayan d'aya ya rage daga shi sai su Hassan da hussaini da basu jima da isowa wajen ba d'auke da kwandon abun karin da aka had'o masu da flaks d'in ruwan zafin tea. Sai Kuma maqwabcinsu dake gefe zaune shima yana gwada kiran wayar baba.

Auntynsu gaba d'aya Yaya maryam baba balarabe yakira ya sanar da ita abunda ke faruwa nan take ita da mai gidanta suka iso wajen cikin tashin hankali suma, nan ya shaida mata abunda yafaru jiya da iyayen Rashida sukazo wanda yake tsammanin shine dalilin da yasa suka yanke shawarar barin garin saboda baqinciki da quncin da suke ciki.

Fashewa tayi da kuka tana fad'in "Amma wannan mata ta cucemu ta rabamu da 'yarmu da kuma d'an uwanmu, ubangiji ALLAH ka isar mana, ALLAH ka isarwa Rashida da iyayenta."

Kasa cewa komai baba balarabe yayi sai jinjina kai da yakeyi, haka Yaya maryam taci gaba da kukanta tana yiwa Yaya hawwa ALLAH ya isa bisa rusa masu farinciki da tayi, wata irin ajiyar zuciya maigidanta ya sauke kafin yace.

"A gaskiya wannan baiwar ALLAH tacutar da mutane da yawa kuma in Sha ALLAH haqqoqansu bazasu barta ba, yanzu Kai balarabe duk ka tambaya nan maqotansa basuda wani labari akan inda sukaje ko wani saqo da suka bari kafin sutafi.?"

"Na tambayesu Yaya sunce basu san komai ba akan tafiyar tasu, ni ina tunanin tun cikin dare sukabar garinnan." baba balarabe yafad'a yana murza goshinsa saboda ciwon kan da yaji yana nema yarufesa,

Kallon Yaya maryam yayi dake shartar majina tana dannar wayarta da alama itama gwada kiransu takeyi yace.

"Yaya maryam kidena wahalda kanki bazaki samesu ba, nakira yafi a qirga amma ban samesu ba."

To yakamata asa ab'alle gidan ko za'a samu wani saqo da suka bari don natabbata bazasu tafi haka ba har sai sunbar wani saqon," maigidan Yaya maryam ne yafad'i haka tare da zuba hannayensa a aljihu.

Maqwabcin su sake gefe zaune baba balarabe yayiwa magana da ataimaka masu da wani abun da zasu iya b'alle kwad'on dashi, cikin gidansa yashiga yake ya d'auko zarton ya kawo masu, kallon babban d'ansa da zai wuce da alama gona yayi had'e da cewa.

"Qasimu zoka taimaka kayanke masu kwad'onnan."

Baba balarabe yafara shiga bayan anyanke kwad'on sannan Yaya maryam Mai gidanta na biye dasu abaya, tsafa suka isko gidan babu alamar an hargitsa komai aciki kafin sutafi, Yaya Maryam tashiga dudduba ko ina cikin d'akin ta hargitsesa amma basuga komai ba, sallamar aunty marwiyya data shigo tana reren kuka tasata fitowa tsakar gidan dasu baba balarabe ke tsaitsaye, kuka takeyi had'e da lailayo miyagun addu'o'i kala kala tana yiwa Yaya hawwa, rarrashinta suka shigayi da bata magana kafin su yanke shawarar fara nemansu a tashoshin motar dake cikin qauyen nasu da zagaye.

Wani yarone yayi sallama had'e da cewa. "Wai mai mashin yace yana jiran matar da yakawo takawo mashi kud'insa" sai alokacin aunty marwiyya ta tuna da aibata sallami mai mashin d'in ba, kawai yana ajiyeta ta tahowarta, nera d'ari baba balarabe yaciro ya miqawa yaron tace a'a yabari taje dakanata, a tsakiyar zauren gidan jikkarta takucce tafad'i wajen saurin taje ta sallamesa tare da bashi haquri, tana duqowa ta d'auki jikkar idanunta sukayi tozali da takardar da baba yarubuta duk an tattaketa.

_KUYI HAQURI ZAN NEMEKU ADUK LOKACIN DA NAGA DACEWAR HAKAN, DAGA 'DAN UWANKU BASHAR"_

Shine abunda ta gani a qasan takardar da har tayi nufin wucewa tabarta, da sauri ta d'auka tana kakkab'e qasar dake jiki ta koma cikin gidan bayan taba yaron kud'in yakai masa tace yabashi haquri,

"Balarabe, balarabe."

Tadinga kiransa tun kafin takai cikin tsakar gidan tana gyara mayafinta da jikkarta dake nema su sub'uce mata.

Kad'an yarage suyikaro dashi a daidai bakin qofar shigowa tsakar gidan da sauri yaja baya yana fad'in.

"lafiya marwiyya ko sun dawo ne?"

Takardar ta miqa masa hannunta narawa ya karb'a yana binta da kallon mamaki kafin ya maida kallon nasa ga takardar, saida ya karanceta tsaf sannan ya d'ago kansa yana kallon aunty marwiyya,

"Waya baki?" Ya tambayeta don ya tabbatar da rubutun dake ciki nad'an uwan nasa ne.

"A tsakiyar zauren nasameta ajiye a qoqarin d'auko jikkana data fad'i wajen saurin in sallami mai mashin."

Juyawa yayi yana kallon Yaya maryam dake tsaye ita da maigidanta suna jiran jin ba'asi tare da takawa ya isa wajensu, cikin raunin muryar dake tabbatar da irin sanyin da jikinsa yayi yace dasu.

"Wannan itace abinda mukayi tsammanin Yaya bashar zai barmuna muketa nema kuma Alhamdulillah gata mun samu." Da sauri Yaya hawwa takarb'i takardar don gaba d'ayansu sunyi boko saidai baiyi wani zurfi ba daga bakin sakandirene suke ajiyesa, wannan dalilinne yasa abaya baba ya kafe akan sai Rashida tayi karatu sosai saboda alwashin daya d'auka akan cewa zurfin karatun da bai samu yayi ba zaisa 'ya'yansa suyisa kosu nawane.

Karanta takardar Yaya maryam tafarayi da qarfi kamar haka.

_Assalamu alaikum 'yan uwana, fatan alkhairi mai yawa da kasancewa cikin amincin Allah arayuwarku har zuwa lokacin da ubangiji zai sake had'a fuskokinmu daku, haqiqa samun 'yan uwa kamarku abune daya isa mutum yayi alfahari dashi har iya qarshen rayuwarsa, Ina Mai godiya agareku bisa kulawa da d'awainiyar da kukayi nida iyalina, mungode ALLAH yabaku aljannah da rahamarsa, nasan alokacin da kike karanta wannan takardar kuna cikin halin tashin hankali da damuwa saboda rashin sanin inda muke, Ina roqonku daku kwantar da hankalinku, muntafine bisa Imanin cewa hakan da mukayi shine mafi alkhairi agaremu, shine hukuncin da zai sama mana sauqi da rad'ad'in abunda mukeji aranmu, don haka muna roqon addu'arku akoda yaushe, nagode 'yan uwana Ina alfahari daku, musamman balarabe daya zamemani ginshiqi arayuwa,_
_KUYI HAQURI ZAN NEMEKU ADUK LOKACIN DA NAGA DACEWAR HAKAN, DAGA 'DAN UWANKU BASHAR_

Kusan atare sukayi ajiyar zuciya gaba d'ayansu kafin Yaya tace.

"Assha bashar, meyasa zakayi haka?, Meyasa zaka jefa kanka da iyalinka uwa duniya don gushewar farincikinka? duka wannan damuwar tasu akan Rashida ce, to gashi sun gudu sunbar garin, idan ALLAH yakuma nufi farincikin nasu dawowa agaresu shikenan sun sake nisanta kansu dashi?."

"Lalle kam Yaya sun ragon azanci duk da dai bamusan ya suke jiba, amma muyi masu addu'a kamar yanda ya buqata, ALLAH yasa rabon had'uwarsu da 'yarsu ne ya fishshesu." Baba balarabe yafad'a yana sake sakin ajiyar zuciya akaro na ba adadi.

Sosai ganin takardar yad'an sa sun samu natsuwa, sun jima agidan suna jajanta abun kafin sufito baba balarabe yabayar asawo masa wani kwad'on ya kulle gidan dashi, bayan ya kulle ya miqama yaya maryam makullan tace yabarsu hannunsa kafin suyi tunani akan abunda ya dace suyi tunda baza abar gidan haka ba.

Sai da mijinta ya goyata ga mashin d'insa suka wuce sannan yaraka aunty marwiyya bakin titi itama tahau mashin, suna wucewa shima shima yawuce yana maijin duniyar tayi masa wani iri daban.

••• ••• •••
Duk wani bayani daya kamata boka yayima su inspector najida yayi masu shi ba tare daya basu wata wahala ba, anan ya tabbatar masu da cewa shima baisan inda baqin aljanin daya turawa Rashida ya kaitaba, ataqaice ma shi aljanin baiyi nasarar shiga jikinta ba kuma ma yanzu baya tare dashi saboda anqoqqonasa ya bijire masa, shi kansa yanzu tsoronsa yakeji saboda yanda yake cutar dashi tare da azabtar dashi, koda inspector najida takira baffa yazo Police station d'in tayi masa bayani, ya matuqar jin dad'in cewa aikin shed'anunbaiyi tasiri akan Rashida ba, dama shi yanada matuqar yaqini akan hakan saboda riqon ibadarta, abunda kawai baiji dad'in jiba shine rashin sanin inda suka kaita lokacin da sukaci nasarar d'auketa, addu'a yayi had'e da roqon ALLAH ya gaggauta bayyanata.

Nan yasaka hannu akan ayi releasing case d'in akayi komai aka gama, har ya juya zai tafi inspector najida tace.

"Baba ya batun Inna hawwa.?"

"Ku saketa kawai." Yabata amsa atak'aice tare da juyawa yabar station d'in.

Har ya tare abun hawa zai hau sai kuma ya juyo ya dawo wajen inspector najida, koda ya shigo office d'in kanta na duqe tana ida cike sauran information d'in daya kamata kafin ya ajiye file d'in inda ya kamata.

A hankali ta d'ago kai ta kalli baffa tace. "Baba ya akayi?"

"Akan maganar hawwa ne, Ina so ku ajiyeta kafin nasamo asibitin da za'a kula da ita, koba komai ta haifamun d'a wanda nake alfaharin samunsa aduniya." Rufe file d'in dake gabanta tayi ta ajiye biron data gama rubutu sannan ta d'ora hab'ar bakinta akan hannuwanta data had'e waje d'aya tana kallonsa, murmushi tayi sannan tace.

"Baba kanada zuciya mai kyau, haqiqa da maza zasu kasance masu duba alkhairin matansu komai qanqantarsa arayuwa koda sun rabu dasu, to ina da tabbaci akan mata bazasu wahala aduniya ba sosai, haqiqa kayi qoqari ubangiji ALLAH yasaka maka da alkhairi."

Murmushi baffa yayi had'e da cewa. "Amin 'yata nagode ALLAH yayi maki albarka ya d'aukaki acikin al-amurranki,"

"Amin" ta amsa masa had'e dajin dad'in addu'arsa....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___52💎

Baffa nashiga gida ya tadda Nuraddeen yafito daga wanka yana shiryawa, cike da girmamawa ya tarbesa tare da karb'ar ledar daya shigo da ita ga hannu yana fad'in.

"Sannu da zuwa baffa."

"Yawwa Nuraddeen, barka da rana wanka akayi?."

"Eh baffa, Ina son inje dubo innar mu ne."

Batare daya tanka saba yawuce bakin katifar dake cikin d'akin ya zauna.

"Nuraddeen zubikke abinda ke cikin ledar nan awani kwano kazo muci yunwa nakeji"

Acan gefen d'an madaidaicin durom d'in dake cikin d'akin Nuraddeen ya d'auko wani kwano cikin kwandon da suke kife kwanonin abincin da suke amfani dasu yazo ya d'auki ledar ya zube soyayyar doya da k'wai d'in dake cikin ledar daya zo da ita yana fad'in.
Chapter 68 · 0% Book details