← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 160

Sashe 37

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nuraddeen yafad'a had'e da sakinta yana yimata cakulkuli, cikin mintuna qalilan ya mantar da ita duk wani b'acin rai da takeji azuciyarta.

Rayuwa kenan haka ALLAH ke jarabtar bayinsa da sukayi imani dashi akoda yaushe, baffa dai gashi da rai amma wasu abubuwan sun buwayesa, duk fitinar da akeyi yanaji Amma Babu halin tashi, ahankali yaji damuwa naneman tayar masa da ciwonsa yayi saurin jawo hisnul muslim d'insa yana karanta addu'o'in hammu wal hazan (damuwa da baqinciki) cikin ikon ALLAH yaji komai na gushe masa, Saida yaji yasamu sassauci da salama acikin ransa sannan ya ajiye yaci gaba da ambaton ALLAH.

Bayan sallar magrib su baffa Ali sun dawo don basu shigo gidan ba saida suka gama sallah, baffa ya zayyane masu duk abunda yafaru agidan wud'anda kunnuwansa suka jiyo masa, sosai baffa Usman yaji ba dad'i sab'anin baffa Ali da yace.

"Ni wlh Yaya nazata wani abun mai muhimmancin ne yasa ka tsaidamu gashi tun d'azu yunwa nakeji, ai indai muneera ce da uwarta abunda ma yafi haka zakaji, ni bari inje inci abinci inaga yafimun."
Yana gama fad'a yamik'e ya wuce sashensa, cike da mamaki suka bishi da kallo kafin su ahiga tunanin nemo mafita,

Baffa Ali na shiga ko sannuda zuwa babu inna ruqayya da tun d'azu take zaman dakon isowarsa tace.

"Alhamdulillah muje malan, wlh yau saika qwatarwa 'yata haqqinta akan cin zalun da aka yimata."

"Ke ruqayya fara bani abinci tukuna yunwa nakeji." Yafad'a yana zaunawa saman tabarmar dake shimfid'e abakin qofar d'akin, sanin zai iya birkice mata idan tamatsa masa da zancen yasa taje takawo masa abincin ta ajiye agabansa, ruwa taje ta d'ebo takawo masa jikinta har tsima yakeyi ta zauna tabasa labari,

Yana gamawa tashiga bashi labarin qarya da gaskiya ya mik'e cikin b'acin rai yanufi shiyar Yaya hawwa yana k'walla mata kira, iskota yayi zaune tana cin abinci bisa 'yar barandar dake cikin rumfarta akan kujerar tsugunno ta tsakar gida shima yanemi waje ya zauna.

Saida takai loma abaki ta had'iye sannan yace.

"Ina jinka Ali mike faruwa?"

Cikin kwantar da kai yace. "Haba Yaya hawwa yanzu ace agabanki yaron nan zai kama 'yar uwarsa yayi mata mugun duka baki d'au mataki ba."

"Uwarta taja mata." tabashi amsa atak'aice tanaci gaba da tura lomar tuwonta hankali kwance.
"Koma dai meye ai kamata yayi ace kin hanasa tunda 'yar tawa ba jaka bace kuma ko meye ai kece kika jamata, babban abunda kebani takaici shine keda kikace bakyason yarinyar nan kin tsaneta meye na wuni kullum a d'akinta? Kodai yanzu kin fara amincewa da zab'in barene."

"Hmmm! Ali kenan, wai ku atunaninku zuwa d'akinta da nakeyi na ALLAH ne? Yaro man kaza ai duk wanda yace baya sonka to tabbas har amutu bazai tab'a sonka ba, ai tsuntsu biyune nake jifa da dutsi d'aya don haka ka kwantar da hankalinka, wannan shashashar 'yar taka ita nakeyiwa yaqi amma ita da mahaifiyarta suna neman b'atawa shiyasa na zura idanuwa saboda kada ad'agoni, duk wani shiri nawa ya kammala don gaba d'aya nagama aiwatar da abunda na karb'o wajen malan bakada imani, k'waya d'aya yarage ina kammalasa zakaga aiki da cikawa.."
Yaya hawwa taqarasa maganar had'e da miqewa tana d'auraye hannunta agefen d'akin. dashe hauru baffa yayi had'e da cewa.

"ALLAH yaya hawwa?"

"Naka wasane Ali, an fad'a maka ja da baya tsorone, ai tuni nashirya maka maina tsaf da zan yaqi waccan yarinyar mai kama da miyagun mayu, yanda nakejin natsaneta yanzu bana tunani zan iya d'aga mata qafa har sai tabar gidannan don haka idan harkana son gurinka yacika dole kadakatar da uwar iyayin nan da muneera daga shiga sha'anin Nuraddeen, inba haka ba kuwa to dasu b'ata mun aiki k'wanda na tabbatar na dakatar dasu nida kaina."...

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___28💎

To shikenan Yaya hawwa yanzu nai magana, amma tuntuni sai zuba idanuwa nakeyi naga matakin da kikace zaki d'auka amma shiru yau gshi kimanin watanni hud'u kenan da kawota. "Kaji dai abunda nafad'a maka koma meye kawai kazuba idanuwa kagani."
Tafad'a tana qoqarin shigewarta d'aki, seda safe yayi mata sannan ya wucewarsa yana ayyana abubuwan da zasu faru idan burinsa ya cika.
Yana fita Kai tsaye waje yayi sai bayan sallar isha'i lokacin har karfe 9 tawuce, yana shiga sashensa inna ruqayya ta sake tarbarsa da maganar cewa yayi "Kai ruqayya matsalata dake rashin hak'uri, yanzu dai ki kwantar da hankalinki munyi magana da Yaya hawwa kuma tace tana nan ta d'aukar mataki akan al-amarin."
"Hmm wane mataki zata iya d'auka akai bayan duk abunda yafaru dasa hannunta itace ummul aba isu tana kallo ya narkarmun yarinya agabanta batace komai ba, Kai nifa wlh nagama gano bata son auren yarinyar nan da yaronta, kaduba yanda take kashe wuni ashiyarta kuma wai don ta Rena mana da hankali tace bata sonta."

"Ashsha ana baki kina roqo, Bari in fad'a maki wlh yarinyar nan Yaya hawwa bata qaunarta tuni taje takarb'o magani wajen malan bakada imani..." Nan ya kwashe duk yanda sukayi da Yaya hawwa ya sanar da ita, lokacin muneera na kwance can acan gefen gado kafin takoma d'an d'akin da take kwana, Inna ruqayyace tace tabari har mahaifinta yadawo taji matakin da aka d'aukar masa na dukan daya yimata, wannan dalilin yasa tayi kwancenta nan ita da qannenta maza su uku ciki harda yusuf tana jiran dawowarsa.

Baffa Ali daya saki baki yanata bata labari kawai sai yaga muneera ta taso tana susar kai tanufo inda suke zaune gefen gado tana fad'in.

"Baffa ni babu ruwana da matarsa kawai so nake ku a auramun shi, wlh baffa Ina son ya nura sosai." Zarar idanuwa baffa Ali yafarayi don bai zata muneera na cikin d'akinba da ko kad'an bazaiyi wannan maganar agabanta ba,

"Yi haquri muneera, ai zancen yanda za'ayi aurenne muke tattaunawa." Inna ruqayya tafad'a had'e da riqo hannunta, turo manyan lab'b'anta tayi cike da rashin iya magana tace,

"Wallahi Inna qaryane, ai duk Ina jinku maganine zakuyi ko korar masa mata, yo a maimakon haka kuyi mani magani na auresa kurum.." da sauri tajawota had'e da toshe mata baki shi kuma baffa Ali ya dafe kai don yasan ALLAH kad'ai ke hana muneera taje ta watsa wannan magana, abunda basu sani ba hatta Yusuf idanuwansa biyu basuyi bacci ba qannensa ne kawai baccin ya d'auka. "Shiii muneera kirufa mana asiri kidena wannan zancen kada wani yajiki, yanzu da kike wannan maganar mu ba yarinyar mukeso tafara fita ba sai ke kuma ki auresa, kinjimun shashashar yarinya."
Inna ruqayya tafad'i hakan tana murgud'e mata bakin da hannu data toshe mata shi.

"Kai Inna da zafi." Muneer tafad'a itama tana jaye mata hannun sannan taci gaba da cewa, "ni ku aura munshi a haka ko mata dubu garesa ALLAH zan auresa balle d'aya, so kukeyi sai na sake shekarewa aci gaba da cemun kwancen gidansu nura wlh ALLAH ni nagaji da jira."
Taqarasa maganar tana fashewa da kuka, takaici ne yarufe baffa Ali kamar yatashi ya rufeta da duka shima, Amma yasan hakan na iyasa tafallasa komai don ba qaramar sakarya bace, lallashinta suka shigayi tare da tabbatar mata da cewa itama wannan shekarar kota halin qaqa saita auri masoyinta ya nura sannan suka samu tawuce d'akinta takwanta, fad'a baffa Ali ya shiga yiwa Inna ruqayya akan meyasa bata sanar masa da muneera na d'akinba ai da bai d'auko zancenba agabanta.

"Yo kukan da taci yau ai sanin matakin da aka d'auka akansa kad'ai zaisa taji sanyi azuciyarta shiyasa nace ta zauna har kadawo."
Tsaki yayi had'e da juyawarsa ya kwanta cike da takaicinta da ita har 'yar tata.

A 'bangaren su Nuraddeen kuwa ana gama sallar isha'i yadawo gida, d'akin baffa ya shiga ya gaishesa tare da yimasa ya jiki lokacin suna zaune shida Rashida tagama b'ab'balla masa maganinsa yasha bayan tazuba masa abinci yaci tana karanta masa wasu addu'o'in dake cikin littafin (adda'u wad dawab) littafin daya qunshi nau'o'in cutuka da kuma kalolin maganukkan da za'asha ayi amfani dasu don samun waraka, d'aya daga cikinsu take fad'awa baffa alokacin, wuri yanema a gefe ya zauna yan sauraren bayanin da take yiwa baffa. "Baffa kaga wannan addu'ar ana karantata ga duk wanda ciwo yayi masa tsanani kuma aka rasa gano kowane irin ciwone ke damunsa, sai a nemi ruwa masu kyau acikin madaidaicin kwanon shan ruwa, sai a nemo kanwa da gishiri a zuba aciki, anemo albasa itama a yayyanka ta aciki sai marar lafiyar yasa duka hannayensa acikin ruwan bayan ya saka duk wud'ancan abubuwan da aka buqata sai ya karanta qula quzzai (falaq, nasi da kuma ikhlas) kenan, sannan yakaranta ayatul kursiyu karatun na sauka acikin ruwan da hannayensa ke ciki, sannan sai ya karanta wannan addu'ar kamar haka
( _Bismillahi arqiq, wallahu yashfik, min kulli da'in mardud, wamin kulli aynin au aynil hak'k'imu ALLAHU yashfik, allahummah rabbannas, ashfi bil ba'as washfi antashshafi'i laa shifa'a illa shifa'uka, shifaa'allahu laa yugadirus saqama_).
sai atofa acikin ruwan acire hannayen daga ciki, sai a d'ebi ruwan marar lafiyar yasha sannan ya tauna albasar dake ciki, asake d'iba yayo wanka dasu sauran sai a dinga watsawa ko ina a cikin d'akin da yake ciki ana fad'in ( _ikhrij aduwwallah_) har ruwan su qare, to da yardar ALLAH duk marar lafiyar da aka dage anayi masa haka ko ya dage da kansa yanayi zai samu sauqi da ikon ALLAH, kaga zuwa gobe idan ALLAH yakai ranmu sai mufara baffa saboda ba'asan in da dace yake ba ko ba haka ba."

Cike da farinciki baffa ya dafa kanta had'e da cewa. "Hakane 'yata, ALLAH yayi maki albarka kuma yasa adace."

"Amin baffa."

Tafad'a tana rufe littafin fuskarta d'auke da murmushi, juyowa tayi gefen da Nuraddeen ke zaune ta gaishesa had'e da yimasa sannu da zuwa sannan tamik'e tabar d'akin tana yiwa baffa seda safe.
Chapter 37 · 0% Book details