← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 160

Sashe 69

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya akayi haka baffa?, Ga abinci nan Inna Bilkisu ta aiko yusuf ya kawo tund'azu."

"Ai nasani Nuraddeen, wannan ina fitowa daga police station ne nagata ana siyarwa saita burgeni nace bari nasiyo mana."

"To baffanmu, ALLAH yasaka maka da alkhairi." Nuraddeen ya qarasa maganar had'e da ajiye kwanon agabansa, saida yafidda ledar ya saka cikin shara tukuna sannan ya dawo ya d'ebo masa ruwa cikin durom d'in yazo ya ajiye agabansa, har zai juya baffa yace.

"Zo zauna muci mana, ko kaci wancan d'in ne."

Azahiri baiya jin cin abincin amma ganin yanda mahaifin nasa ya tsaresa da idanuwa yasa yaje ya wanko hannuwansa yasa hannunsa suka soma ci, tunda suka fara babu wanda ya koma cewa uffan har suka kusa gamawa, cire hannu baffa yayi ya d'auki ruwan yasha ya yiwa ALLAH godiya sannan yace.

"Nuraddeen ya zancen tafiyarka? Naga lokaci sai sake gabatowa yakeyi"

Da qyar Nuraddeen ya iya had'iye abincin dake cikin bakinsa kafin ya d'ago kai yana tankwashe qafafuwansa yace.

"Baffa maganar tafiyar nanfa ni na haqura da ita gaskiya, bana tunanin zan iya sa qafa inbar qasarnan mahaifiyata na cikin wannan yanayin, bacin haka ma baffa nifa har yanzu bancire tsammanin cewa Rashida zata dawo ba, jikina yana bani cewa duk inda take Ina ranta kuma tana cikin damuwa kamar yanda nake cikinta, bana son lokacin da zata dawo ta isko bana qasar, hakan zai sakata cikin shakku da kokwanto cewa nadamu da b'acewarta, shiyasa kawai nake tunanin gwara inzauna in bawa mahaifiyata kulawa har zuwa lokacin da ALLAH zai dawo da Rashida agareni.

"Nafahimceka Nuraddeen, Kuma nayarda da zancenka, Amma karka manta dama tana zuwa ga bawane sau d'aya arayuwa, sai kuma sa'a idan tasa ALLAH yasake baka wata damar, batun mahaifiyarka kabarshi a hannuna zankula maka da ita har lokacin da zaka dawo, zanyi hakanne don ALLAH da kuma zamowarta uwa agareka amatsayinka na d'a tilo da nake so fiye da komai arayuwata."

"Ita kuma matarka Ina so kayarda dani, na d'aukarma alqawarin zanci gaba dasa anayi maka sauka da addu'a har zuwa lokacin da ALLAH zai bayyana mana ita, zanyi qoqarin fahimtar da ita komai alokacin da tadawo izuwa gareka kuma na sadaka da ita akaro na biyu, na tabbata zata fahimceni tunda yarinyar nada ilimi da kuma fahimta.

Shiru yayi cike da son mahaifin nasa ya fahimci abunda yake nufi, baya son abunda zaisa Rashidarsa taji wani shakku azuciyarta akan soyayyar da yake yimata tahanyar barin qasar alokacin da bata tare dashi, nisawa yayi kafin yace

"Baffa.."

Da sauri baffa ya dakatar dashi tahanyar d'aga masa hannu yana fad'in.

"Shikenan! Na fahimceka ALLAH yasa hakan shiyafi alkhairi, Yana gama fad'ar haka yamiqe zuciyarsa a cunkushe duk da yayi qoqarin hana hakan ya bayyana a fuskarsa amma saida nuraddin ya fahimci hakan.

Toilet baffa ya wuce shi kuma yamiqe ya d'auke kwanon sannan ya Ida gyarawa, yana tsaye baffa yafito ya watso ruwa tare da canza wasu kayan yace dashi.

"To ni zan fita, zanje wajen baffanka akwai mganar da nake son tattaunawa akan mahaifiyarka dashi."

Bai jira jin amsar da zai basa ba yafice don baya son ya fahimci rashin jin dad'insa akan hukuncin da yake qoqarin yankewa kansa wanda yazab'awa rayuwarsa. Zaune Nuraddeen yayi akan katifa yadafe kansa da hannayensa duka yana furta, "Rabbi yassir wala ta'assir."

Yajima ahaka yana tunanin yanda rayuwa tayi masa d'aurin goro tahanyar rasa farincikinsa Rashida da kuma gudan jininsa dake jikinta, a b'angare d'aya kuma tsananin damuwar da yake ciki ta halin da mahaifiyarsa ke ciki dake neman tsaida dukanin al'amurransa, yanzu kuma ga fushin mahaifinsa na nema ya bayyana agaresa ta dalilin hukuncin da yaga yafi dacewa agaresa, miqewa yayi yabar gidan shima bayan yasa kwad'o ya rufesa sannan yanufi police station d'in,

Bai wani sha wahala ba inspector najida tasa aka kaishi inda take don ancanza mata waje saboda yanzu Bata qarqashin kulawar hukumar, tamkar ajiya take a hannunsu shiyasa aka kaita can cikin wani d'aki abayan station d'in daya tab'a gobara ya qone, tun daga kan tagogin wajen da qofofi duk sun qone, haka ma samansa abud'e yake saboda qonewar da rufin yayi, asalima nan jami'an 'yan sandan ke zagayawa domin biyan buqatocinsu na yau da kullum wato fitsari da bayan gida, duk wata rana da iska ko ruwan sama da akeyi akanta suke qarewa gashi an d'add'aureta gudun kada ta tsere, suna nufo wajen Nuraddeen yafara yatsine fuska yana toshe hanci saboda tsananin warin da yakeyi yana bin d'an sandar da kallo Mai cike da tarin tambayoyi har suka isa inda take, da sauri ya saki hancinsa yana zaro idanuwa waje hangota da yayi kwance cikin wajen dake kama da juji hannuwanta da afafuwanta d'aure da gudu ya isa wajenta tare da tallabota izuwa jikinsa batare daya damu da yanayin da take ciki ba yana fad'in.

"Innar mu, innar mu."

A hankali ta d'ago kanta tana kallonsa kafin ta saki wata irin muguwar qarar da tasa baisan lokacin daya saketa ba ya koma gefe, wani qaqari tashigayi kafin yaga anfara juyata cikin qonanniyar dattin dake cikin wajen ana birgima da ita tamkar wata halittar da batada qaffuwa, qananun gilasaiyen dake wajen ne suka shiga yayyanke mata jiki tana cigaba da wata qara mai cike da nuna tsantsar azabar da take ciki, ganin haka yasa yasake zuwa ya tallbota yariqeta yana kuka yana fad'in.

"Kidena innar mu, don ALLAH kidena innar mu kada kijima kanki."

Rungumeta yayi tsam don kada ta kucce masa yana aza kansa bisa jikinta, ganin haka yasa tasa baki ta kaimasa cizo ahannu har saida taciro da naman jikinsa amma yaqi sakinta saima sake rungumeta da yayi sosai yana kuka yana fad'in "kibari innar mu."

Yanayin qugi da gumzar da qarar da takeyi yasa inspector najida da sauran 'yan sandan zagayowa sukayi tsaye suna kallon ikon ALLAH, lallae duk lalacewar uwa uwace kuma baza'a tab'a iya shiga tsakaninta da d'an taba.

Wani yunquri tayi da yasa d'aurin dake hannuwanta faccewa da qarfi ta turesa gefe har saida yabugi jikin bangon wajen ya dawo, 'yan sandan naganin haka suka shigo wajen had'e da qoqarin rirriqeta, ganin tana neman tafi qarfinsu yasa wani d'aya daga cikin 'yan sandan qaqqarfa ya d'auketa kyakkyawan marin da yasa saida ta kife qasa, wani irin kukan kura Nuraddeen yayo kansa had'e da cakumar wuyansa ya kaisa jikin bango ya shaqesa yana fad'in.

"Kai waye da har zaka dakarmun mahaifiya agabana?, Kasan me ake kira da uwa kuwa?, Kasan muhimmancinta ga 'ya'yansa da zaka dokarmun abita?."

Maganar takeyi idanuwansa sun kad'a sunyi jawur ga wasu irin jijiyoyi sun taso masa a goshi yana turo idanuwa awaje."

Jin yafara kakari yasa wasu 'yan sandan dawowa wajen suna qoqarin janyesa amma gaba d'aya su ukun ya turesu yafara kaimasa naushi a fuska da ko ina ajiki, dukansa yakeyi yana fad'in.

"Wayace ka daki mhaifiyata?, waye yace ku d'auremun ita haka?, Akan me zaku kawota anan ita ba dabba ba?"

Duk d'an sandan daya nufosa sai yakai masa duka hakan ya b'atawa inspector najida rai nan take tbasu damar suyi masa duka, ai kamar jira sukeyi suka rufar masa da duka Saida suka yi masa liqis sannan suka qyalesa tace a d'aukesa ajefasa cell.

Ranta a b'ace takira baffa lokacin yana wajen baffa Usman suna tattaunawa akan asibitin daya dace akai Yaya hawwar ta sanar masa da abunda Nuraddeen yayi nayiwa 'yan sandansu duka a police station d'in.

Jikinsu narawa shi da baffa Usman suka nufo wajen kowane da abunda yake saqawa aransa.

••• ••• •••
Kwanan Dr.nura biyu yana rage aikace aikacen daya isko sun tarar masa a asibitin tasu sannan ya nufi anguwarsu umma agarin yarimawa, awannan karon bisa mashin yake tunda baizo da motarsa ba shiyasa batare daya sha wata wahala ba yasamu wani mutum ya tambayesa zancen iyayen Rashida da har lokacin yaga gidan a kulle da kwad'o.

Nan mutumen ya sanar dashi komai har yana d'ora masa da "yanzu haka ina tabbatar maka cewa babu Wanda yasan inda iyayenta suka nufa balle asan halin da suke ciki."

Wani irin jiri ya d'ibesa da yasashi saurin dafe bushiyar iccen dake kusa dashi yana fad'in.

"Hazbunallahu wani'imal wakeel, wannan wane irin mummunan labari ne kunnuwana suka jiyomun."

"Abun gaskiya ba dad'i sai haquri." Mutumen yafad'a had'e da wucewarsa, koda ya d'ago kai daga jimamin da take ciki da niyar yimasa wata tambayar sai yaga har yabar wajen, bai bar anguwar ba har saida yasake tambayar mutum uku don ya tabbatar da abunda nafarkon yafad'a suna bashi amsa iri d'aya da tasa sannan yabar anguwar jikinsa a sanyaye, kwana biyu yaqara kafin yakoma borno cike da tunanin irin amsar da zai baiwa Rashida idan ta tambayesa iyayenta, daga qarshe dai ya yanke hukuncin zai bari har zuwa wani satin idan sunje taganema idanuwanta ammashi tabbas bazai iya fad'a mata ba.

Sosai yayi qoqarin sakin jikinsa lokacin daya koma amma saida Fatima tafahimci akwai abunda ke damunsa, yanda ta tsaresa da tambaya yasa ya sheda mata komai ba tare daya b'oye mata ba tare da shawarar daya yanke, nan take tagoya masa baya tan kukan tausayin Rashida akan halin da zata shiga idan sukaje ta tarar iyayen nata basa nan. rungumeta yayi yana lallashinta don yasan halinta sai takai gobe tan kuka har yakai ga Rashida tafahimci abunda ke faruwa.

A b'angaren little Nuraddeen kuwa yayi wayau sosai don har ya iya zama, sak kamarsa da Rashida ke dad'a fita da kagani babu tambaya kasan yaron tane. Wani irin so takeyi masa marar misaltuwa da yasa Bata qaunar abunda zai sashi kuka ko kad'an, duk Wanda ya kallesa sau d'aya sai yaqara saboda yanayin jikinsa da kuma tsabtarsa shiyasa duk wanda ya gansa sai yayi sha'awar d'aukarsa, a daddafe suka hau yima Rashida Shirin komawa gida ita da little sai murna takeyi, katsar watsar tasamu satin ya qare wani yashigo yakama gobe zasuyi tafiyar don harda Fatima za'a.
Chapter 69 · 0% Book details