Sashe 9
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana isa ya tarar anyi transfer d'insu zuwa psychiatric clinic Amma saboda ta tashi daga baccin sai kuka su Abba da hajia keyi saboda yanayin da take ciki, gaba d'aya ta yayace ward d'in da qara tana buge buge, hatta nurses d'in dake kula da ita sun fara jin tsoronta hakan yasa suka kasa matsawa kusa da ita balle su samu damar yimata allurar da aka saba yimata, umurni wani likita yabasu dasu taru sufara d'aureta sai suyi mata allurar, tana ganin sun nufota da igiya tayi wani irin qaraji daya sasu saurin watsewa gaba d'aya, tana ganin haka ta tashi da gudu zata fita suka kamota, yunqurawa takeyi da duka qarfinta tana son kwacewa daga hannunsu amma da yake su kusan biyar ne takasa saidai takoma tana wani gumza kamar zakanya, kasa kallon yanda suke d'aureta Abba yayi da sauri ya qarasa wajen yana kuka tare da d'an doddo kawa nurses d'in sandar da yake tokarawa yana fad'in,
"Kucika mun 'yata, kada wanda ya d'aure mun ita, kubarta don ALLAH ku k'yaleta nace" dakatawa batool tayi daga kucce kuccen da takeyi tana sauraren muryarsa tare da k'ura masa idanuwa, hakan yasa sukaga damar da zasu ida d'aureta Amma kafin kace me har batool ta ankara, yayumo wacce ke kusa da ita tayi tare da cijeta ga hannu har saida taciro fatar jikinta, fad'a Dr. Yafara yiwa Abba akan yabari suyi aikinsu Amma yaqi gashi har yajawo ta jima d'aya daga cikinsu, haquri hajiya mama tabashi sannan tarik'o hannun Abba had'e da cewa "alhaji don ALLAH kayi haquri kabarsu suyi aikinsu" kwace hannunsa yayi daga riqon da tayi masa ransa a b'ace yace
"Bazan iya kallonsu suna cigaba da d'auremun 'ya haka ba sai kace dabba." Kallon likitan yayi had'e da cewa,
"Kai dr, Ina kun sallamemu ko? To kubarni ni nasan yanda zanyi da 'yata koda zata kasheni Amma kar wanda ya sake d'aureta" yana rufe baki ya duqa kusa da ita tare da cire mata igiyar ya jefa masu sannan ya fara yimata magana a hankali "batool, batool, zakije gida?" Bai rufe baki ba tajawo qarfen qarin ruwa dake gefenta ya fad'o masa saman kai har saida yafasa masa goshi, da sauri shurahbil yanufo wajen amma Abba ya d'aga masa hannu, hannu takai da niyara chakumo wuyansa amma jinin da tagani nafita a goshinsa yasa tadakata, ja da baya tafarayi a tsorace kamar wacce kejin tsoron a doketa, batare da Abba ya damuba ya mik'a mata hannu ta k'ara matsawa a tsorace, haka yadinga matsawa wajenta tanaja da baya har ta isa jikin gadon ta runtse idanuwanta, ganinsa gab akusa da ita yasa tafara bud'ewa ahankali, ga mamakin nurses da likitan dake wajen sai sukaga Yana mik'a mata hannu tariqo ya mik'e da ita tsaye har lokacin yana riqe da hannunta, juyowa yayi zai fito da ita suka dinga jayewa suna kallon ikon ALLAH, biye take dashi amma ta tattakure kanta abayansa tana nonnoqe kai yace
"Kungani ko, nasani qarfin soyayyar da 'yata keyimun bazai bari ta watsamun qasa a idanuwa ba duk dako bata cikin hayyacinta, shurahbil zo mutafi."
Cike da farinciki hajia mama takai hannunta zata rik'ota ta bugemata hannu tana k'ara shigewa bayan Abba, juyowa Abba yayi yace ma hajia mama "kik'yaleta kada ta sake birkicewa kuma"
"Amma yakamata katsaya aduba maka goshinka"
"Babu komai tunda jinin ya tsaya nadawo daga baya a gyaramun ko kuma naje chemist"
Shurahbil dake neman shiga a gabansu ne yace
"Abba acan clinic d'in zamuje ne"
"A'a gida zanje da 'yata, matuqar ta wannan hanyar da naga sunbi zasu kula da ita to bazan barta anan ba, zantafi da ita gida inbata kulawar daya kamata kuma nasamo manya manyan likitocin da zasu dinga duba mani ita"
Ai kuwa haka akayi babu yanda Dr. Bayyi dashi akan kada yatafi da ita gida ba Amma yaqi, dole suka barshi ya wuce da ita don rigimar tsohon tafi k'arfinsu Babu yanda zasuyi, sunyi fad'a har sun gaji saidai shurahbil yayita basu haquri.
Wajen shiga mota ma haka Abba yayita fama da ita don k'in shiga tayi sai da yayi ta mata dubaru sannan ta amince tashiga motar, Amma duk wanda ya aza qafa da sunan ya shiga ciki sai tayo kukan kura akansa, hakan yasa daga Abba sai kuma shurahbil dake jan motar suka shiga, hajia mama da kuma mahaifiyarsu shurahbil da gwaggo dake rik'e da jariran saidai abba yakira uncle hussain yace yazo ya d'auki da motar sa daya bari don data shurahbil ce su suka tafi....
_AFUWAN DA JINA SHIRU BAYAN KWANAKI, NAJE GANIN GIDANE 'YAN UWA DA KUMA ABOKANAN ARZIK'I SHIYASA KUMA KUNGA SUMA AKWAI BUQATUWAR ACE SUN SAMU LOKACINA, NGD DA SAQONNINKU DA ADDU'O'IN ALKHAIRI ALLAH YABIYAKU DA ALJANNAH FIDDAUSI,👏🏻😍KUCI GABA DA BIBIYAR WANNAN LABARIN AHANKALI DOMIN *SANNU SANNU* BATA HANA ZUWA SAIDAI ADA'DE BA'A KAIBA🤣ONE LUV FILLAH😉🤞💋❤️_
*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___7💎
Al-amarin batool kam sai addu'a saboda ako yaushe sai qaruwa yakeyi, gashi Abba yabuga kai ga qasa shi baza'a kaimasa 'ya asibitin mahaukata ba, mutum ne shi mai kafiya da kuma zuciya hakan yasa su uncle h suka zuba masa idanuwa domin babu rarrashin da basuyi masa ba da kuma lurar dashi amma yakafe kai da fata, musamman yasa aka gyara mata d'aki d'aya yasa duk aka ciccire abubuwan da suka shafi qarfe da zasu iyasa tajima kanta aka fiddasu sannan ya d'auko wani k'warraren likitan k'wak'walwa yafara dubata, wasu allurai likitan ya rubuta da za'a dinga yimata kullum ko wace k'waya d'aya dubu ashirin kuma Abba ya amince, lokacin dasu Uncle h sukayi yunqurin dakatar dashi da kuma nuna masa cewa kud'in sunyi yawa rufesu yayi da maseefa har Saida suka koma bashi hak'uri,
Kimanin watanni biyu kenan ana Abu d'aya amma babu wani sauyi, babu wanda ke matsawa wajenta tak'yalesa idan ba Abba ba hakan yasa kullum cikin hidimarta yake gwanin ban tausayi, abincinta da abun shanta duka shine hakama idan za'aba yaran nono shike karb'arsu yaje dasu cikin dubara ya lallasheta tabasu kuma batayi masu komai indai yana tsaye, duk da k'wak'walwarta bata aiki tana matuqar jin tsoronsa, zancen wanka ne kawai ba'a yimata saboda bazata bari ba shi kuma Abba babu kyautawa ace shi zai yimata, sau d'aya yasa su hajia mama suyi mata yana bakin toilet d'in ya tsareta ai kuwa sunsha cizo da yakushi, tun daga ranar sukace bazasu koma ba, gwaggo ma m takoma tun ana sati d'aya da sallamosu, lokaci lokaci takan kira hajia mama ta tambayi lafiyar jikokinta da kuma ta batool tayita kuka tana addu'ar ALLAH yabata lafiya, haka barrister kamal shima yakan zagayosu idan yasamu sarari wajen aikinsa tare da kayayyaki masu yawa yace aba yaransa.
Shurahbil kuwa ko yaushe yana bisa hanyar neman Dr. N.I na kimanin wata biyu kenan bayada labarinsa kuma baya samun lambobinsa idan yakira, yau kamar an tsunkulesa yana kwance ya tashi had'e da zura jallabiyarsa ya nufi asibitn da Dr. N.I ke aiki don duk bid'ar daya yimasa hankalinsa bai tab'a kawo masa da yaje can ba.
Yana zuwa ya tambaya aka kaishi har office d'insa, cikin sa'a kuwa ya iskota, ajiyar zuciya yayi tare da yiwa ALLAH hamdala sannan yatura gambun ya shiga, Dr.N.I na ganinsa ya mik'e cikin fara'a yana fad'in,
"Ahh! Baban yara kaine a office d'ina?" tare da mik'a masa hannu suka gaisa, murmushi shurahbil yayi tare da sosa qeyar kansa sannan ya zauna saman kujerar da yake nuna masa yana fad'in,
"Ya zanyi Dr tunda kab'oye mana, nayi nemanka har nagaji ban sameka ba, har nasarawa anguwarku naje amma nakasa samunka sai yau nayi tunanin zuwa nan asibiti kozan sameka."
"Ayya malam shurahbil, ai kayi raggon azanci, kaida har unguwar mu kaje meyasa kak'i tambayawa, ai ko qanqanen yaro katambaya akaika gidana za'a nuna maka, duk da dai nad'anje qauyene wajen wani bincike sai jiya nadawo, yanzu nake cewa anjima Idan narage abubuwa zan shiga asibitin, ya masu jiki hop dai da sauqi ko?"
"Eh alhamdulilah za'a ce amma ambamu sallama ko ince transfer zuwa psychiatric clinic sai dai Abba bai amince mukaje ba, marar lafiyar na nan gida"
"Subhanallahi meya faru da itane?." Shiru shurahbil yayi kafin yafara labartawa Dr.N.I halin da batool ke ciki, bai b'oye masa komai ba hatta likitocin da Abba kefaman d'aukowa da allurorin da akeyi mata duk saida yafad'a masa, ya matuqar tausayawa halin da batool ke ciki da kuma yaranta, yajima zaune batare da cewa komai ba kafin yace,
"Shurahbil karka damu in Sha ALLAH zan taimaka maku kuma kakwantar da hankalinka da yardar ALLAH zata samu lafiya."
"ALLAH ya yarda Dr. Nagode sosai" Shurahbil yafad'a Yana goge k'wallar data zubo masa a idanuwan,
"Badamuwa, anjima da marece zanzo saika sanarwa da iyayen naka idan sun amince saika kirani tunda kana da lambata kafin lokacin yayi"
"Shikenan Dr. Amma wud'annan lambobin sun dena aiki ko zaka bani wadda zan iya samunka direct" dariya Dr. N.I yayi kafin yace
"Ka kira in sha ALLAH zaka sameni yanzu" dama rufe wayoyin yakeyi duk lokacin daya je k'auyen saboda muhimmancin abunda yaje yi, shikesa Idan yatashi hutun wata d'aya yake d'auka don yasamu isasshen lokaci, har sunyi sallama da shurahbil zai fita ya dakatar dashi tare da d'aukar biron dake gabansa da Kuma 'yar guntuwar takarda ya sake rubuta masa wata private no d'insa da bakowa ya sani ba yabashi had'e da cewa
"Ka gaida mani da twins da kuma qannensu"
"Zasuji in sha ALLAH nagd sosai Dr " sannan yawuce zuciyarsa cike da farinciki sai kace wanda aka tabbatarwa da cewa zata samu lafiya.