← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 160

Sashe 62

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___47💎

Saida ya miqa jaririn wajen Fatima ita kuma takaima Rashida shi sannan yakoma ya d'auki malamin ya maidashi gida, abakin qofar gidansa ya tsaya cikin mota bayan ya ajiyesa yana jiran yakawo masa magungunan da za'afara yiwa Nuraddeen amfani dasu, ba'afi mintuna biyar ba yafito riqe da wata leda 'yar madaidaiciya, bud'e motar yayi had'e da zaunawa a mazauninsa daya tashi yana kallon gefen driver inda dr. nura yake zaune yafara yimasa bayani,

"Dr. Ga wannan ruwan, ma'u kalne, za'a dinga zubasu kullum cikin ruwan wankansa marfi d'aya aduk lokacin da za'ayi masa wanka, sai wannan shi kuma garin hulbane, za'a d'ebi kamar qaramin cokali d'aya sai asaka marfi uku na wud'an can ruwan ma'u kal d'in akwab'asu waje d'aya sai ashafe masa jikinsa dashi kafin ayi masa wankan har na tsawon mintuna bakwai zuwa takwas lokacin maganin yabushe sai a mummurje masa shi sannan ayi masa wankan." ya qare fad'a yana nunama Dr. nura wata gora aciki dake cikin ledar tare da wani qullin garin hulba d'aure ga leda baqa, wasu qananan kwalabe guda biyu ya sake nuna masa had'e da cewa.

"Su kuma wud'annan man zaitun ne da kuma zaitu lawwiz (man tafarnuwa), za'a had'asu waje d'aya adinga d'iga kad'an a hannu ana yimasa man shafawa dashi bayan angama masa wankan sai kuma wannan, shi kuma garin habbatussauda ne, za'a dinga samun gawashi (garwashin wuta) idan angama shafa masa wud'an nan mayukkan dana gama yimaka bayani sai a turara masashi kafin asa masa sutura, sai wannan kwalbar ita kuma"

Wata doguwar kwalbace ya d'ago yana nuna masa sannan yaci gaba da cewa, "wannan zallar Zuma ce 'yar misra aciki don tafi kyau, garariya ce ita babu wani surki acikinta, adinga lasa masa ita tunda sassafe kafin yasha nono, sannan ana bashi ita akai akai ko yaushe, hakama idan zasu kwanta lokacin kwanciya ta tabbatar an lasa masa ita ko kad'ance yasha."

Wata baqar ledar ya sake ciro daban da wani ganye acikinta had'e da garin magani da kuma kwalbar man zaitu simsim (man rid'i) ya miqa masa.

Kariqe wannan daban mahaifiyarsa zata dinga amfani dashi, wannan ganyen na na'a na'a ne, zata tafasashi sai tasaka cokalin zuma d'aya acikin ruwansa kofi d'aya, tasa wannan man rid'in shi kuma marfi d'aya tajuya sosai tasha da d'an zafinsa, wannan garin maganin shima zata dinga d'ibarsa tana turare jikinta dashi, in sha ALLAH sukad'ai zasuci gaba da karya duk wani mugun sihiri ko tsafi ko shafuwar aljanu ga duk wanda ya kiyaye amfani dasu, ta lizimci sauraren karatun alqur'ani kuma idan son samune a qauracewa duk wasu kalle kalle har zuwa lokacin da yaron zai samu lafiya, akula sosai, kada adinga barin yaron shi kad'ai domin hakan zai iya dawo mana da komai baya tahanyar sake qoqarin cutar dashi da zasu iya samun damar yi, balle yanzu da suke a fusace, kad'an suke jiran koda 'yar qaramar damace su sake samu don d'aukar fansar hanasu cimma burinsu da akayi, don haka akula sosai kada asake ayi wasa da hakan."

Malamin yaqarasa maganar yana miqawa Nuraddeen gaba d'aya ledar daya zo da ita, karb'ar ledar yayi sannan yamiqa masa hannu sukayi misabaha yana qara yimasa godiya sosai.

"Ba komai Dr. Ubangiji ALLAH dai yasa mudace, mutanene yanzu basuda d'igon tausayi da imani ko kad'an azuciyarsu inba guda guda ba, badon haka ba me wannan d'an qaramin halittar yayi daya isa ace ancutar dashi?"

"Abunda na dad'e kenan Ina mamaki malan, yanda na lura da irin wahalar da yaron ke matuqar sha bakad'an ya girgizani ba, mun kwashe kimanin watanni uku a asibiti ana abu guda amma babu wani sauyi da aka samu, wannan dalilinne yasa da yayata hajia maijidda tazo dubasa take bani shawarar mukoma gida dashi anemi maganukkan musulunci wataqil ALLAH zaisa a dace, dama kuma ni tuntuni na gama yanke wannan shawarar araina don haka kawai sai naji naqara samun qwarin guiwar yanke wannan hukuncin kuma alhamdulillah ga dukkan alama za'ayi nasara."

"Dama haka abun yake, wani lokacin maganin cuta na tare damu ko ince akusa damu amma saboda yanda muka bawa asibitocinnan muhimmanci fiye da komai saimu barsu muje can muyita shan wahala, muyita kashe kud'ad'enmu a banza bayan ALLAH ya halasta mana neman kowane irin magani aduk inda yake matuqar babu shirka aciki ba wai muce ala dole saina asibiti ba."

"Tabbas hakane malan, ubangiji ALLAH yasa mudace."

"Amin ya ALLAH"

"Malan nawane kud'in maganin?"

"Dubu talatin ne gaba d'aya amma idan wannan yaqare za'a dawo a karb'i wani, sau uku za'a karb'a hacikin wata uku shikenan angama.

Ciro kud'in yayi yamiqa masa tare da sake yin godiya sannan malan yafita shi kuma yaja mator yabar wajen,

Kamar yanda malamin yayi masa bayani haka yayiwa Rashida da Fatima bayani, sannan yaroqesu da su kula sosai kada suyi wasa da maganin nasa, maido kallonsa ga Rashida yayi yace.

"Maman baby aduk lokacin da zakiyi wani abun kitabbata kin kawosa wajen fatima, kada ki kuskura kibarshi shikad'ai kinji ko?."

"In Sha ALLAH."

Tafad'a had'e da sa kuka tana mai yimasu godiya bisa kulawa da taimakon da sukeyi mata, aranta tana mai tabbatar da cewa sunyi mata halaccin da har tamutu bazata tab'a mantawa dasu ba kuma bazata iya biyansu abunda suka yimata ba

••• ••• •••
Baba da umma kuwa duka sun samu sauqi sosai don babu inda baba baya zuwa saidai har yau hannunsa da qafarsa basu koma daidai yanda suke ba, babu wani cowo dake damunsu yanzu inba rad'ad'in rashin 'yarsu da kuma tunaninta ba, daidai da sekon d'aya basu tab'a mantawa da itaba ko cire tunaninta aran suba, yanda baba yasamu lafiya sosai yasa yau da likitoci sukazo round aka basu sallama, baba balarabe na kasuwa umma takirasa ta sanar dashi, ba'afi mintuna goma ba sai gashi yazo da mota cike da farinciki suka kwashi kayansu tare da yima sauran majinyatan dake tare dasu sallama suna masuyi masu addu'ar ALLAH yabasu lafiya suma sannan suka wuce zuwa gida.
Suna barin assibitin motarsu baffa na tsayawa, nan wani dake jinyar d'ansa shima ya sanar dasu cewa d'azu aka basu sallama basu dad'e da barin asibitin ba, godiya yayimasa sannan ya juya yakoma cikin motar drivern ya tayar suka nufi yarimawa, adaidai bakin qofar gidan suka tsaya baffa yakira baba balarabe ya sanar dashi sunanan qofar gida sunzo duba baba shida iyalansu, cike da farinciki yabasu izini shigowa, da kansa yaje yatarbosu dag qofar gida had'e da yimasu iso zuwa ciki, hannu biyu suka tarbesu tamkar babu abunda yatab'a faruwa, inda nan take malan balarabe ya aika aka siyo masu ruwa masu sanyi kowa yasha sannan aka shiga gaggaisawa tare da yimasu umma yajiki, Inna Bilkisu kuwa yanda kikasan itace Yaya hawwa haka kurum taji tsananin kunyarsu bazata bari ta iya had'a idanuwa dasu ba sai wani sissinne kai takeyi, bayan an gama gaggaisawa ta soma jajanta masu akan abunda yafaru had'e da basu haquri, dukkaninsu babu wanda yace uffan inba aunty marwiyya da tun d'azu malan balarabe yakirata yasanar da ita batun sallamar, itace tafara zuwa ta gyaggyara masu gidan kafin su iso, suna isowa suka taddata har tagama tagyara ko Ina, cikin nuna yarda da qaddara tare da barwa ALLAH komai tace, "Babu komai Bilkisu, bawa ai baya tab'a kaucewa qaddararsa, munyi Imani da ALLAH ya qaddarowa Rashida haka kuma munasa ran tunda bawani yayi mata ba ko yaushene ALLAH zai bayyana mana ita."

Tana rufe baki sukaji muneera dake can gefe riqe da ledar pure water tana tsutsa tace,

"Kai ka kai, Wlh ALLAH kidena yiwa ALLAH qazafi, baruwansa acikin b'atan aunty Rashida, duk inna hawwa ce da innarmu da kuma baffana, su sukayi mata wannan abun tab'ata, Nima anso asakani aciki waccan inpeston (inspector) da suka kamamu aka kulle suka wankeni dama ni ban aikata komai ba sune sukayi, ya nura ne nake so kuma wlh ALLAH yanzu ma nadena sonsa, babu ruwana dashi ko ya nura?"

Tafad'a hannunta acikin kai tana susa tana kallon Nuraddeen da gaba d'aya kunya tagama rufeshi awajen ya sadda kanshi qasa, bashi kad'ai ba hatta su baffa Usman da sauran mutanen da sukazo tare sinne kai sukayi cike da wata irin matsananciyar jin kunya, da qarfi aunty marwiyya tajuyo tana kallon Nuraddeen ranta a b'ace tace.

"Dama Nuraddeen mahaifiyarka itace silar b'atar 'yar 'yaruwata?. Tirqashi billahil azhim rai baifi rai ba, dama nadad'e Ina zargin ko dasa hannunta aciki saboda yanda tanuna mana tsantsar tsanar da takeyi mata lokacin da muka kaita, naso tun alokacin na taka mata burki amma Yaya maryam tahanani saboda darajarka da mutuncin bayin ALLAH dake tare daku, to wlh bazata yuyu ba shari'a da ita sai tafiddo mana da yarinyarmu tun daganan ko har qarshen rayuwarmu, danqari maqari daga had'a sinnar ma aiki sai salwantar da rayuwar yarinyatabiyo baya.."

"Dakata marwiyya! Daga jin yarinya tafad'i magana saiki hau akai kifara wud'annan maganganu marasa dad'in ji, don ALLAH kiyi shiru mubi komai ahankali." Baba balarabe yafad'a yana mai kokonto akan maganganun, d'ago kai baffa yayi cikin karyewar murya yace.

"A'a Balarabe, kabarta tafad'i duk abunda ke cikin ranta hakan zaisa tasamu sassucin da mu muka kasa samu alokacin da muka gano gaskiyar wannan al-amarin, kudena kokwanto akan maganganun da waccan yarinyar tafad'a domin duka gaskiyane, nakasa sanin wane mataki zan d'auka a lokacin da abun yafaru shiyasa nayanke shawarar sanarda hukuma domin suyi bincike akan wud'anda nake zargi, wato matata mahifiyar Nuraddeen sai qanena Aliyu da kuma matarsa wato mahaifiyar waccan yarinyar, duk tsawon wud'annan watanni da aka d'auka sunacan kulle a hannun hukuma ana bincike wanda jiya bincikensu ya tabbatar masu da cewa akwai sa hannun iyalina aciki tare da wani boka da suka had'a kai akayi mata asiri, wanda hakanne yayi silar barinta gida, wannan shine gaskiyar abunda yafaru." Yaqare maganar yana goge hawayen dake zubar masa cike dajin d'acin abun aransa.

Cike da mamaki da al-ajabi su baba ke sauraren maganganun dake fitowa daga bakin baffa har zuwa yanzu daya dasa aya, cikin kuka umma tajingina kanta ajikin bangon d'akin tana fad'in.

_"Hazbunallahu wani'imal wakeel, qadarallahu wama sha'a fa'ala,"_
Baba kuwa wata irin ajiyar zuciya ya sauke had'e da cewa.
Chapter 62 · 0% Book details