← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 160

Sashe 27

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike gidan yake maqil da 'yan uwa da abokanan arzik'i na nesa dana kusa da suka zo taya umma da baba murnar aurar da 'yar tasu tilo, duk wanda ka kalla awajen kasan cewa cike yake da tsantsar farinciki saboda yanda fuskokinsu ke d'auke da annuri anata gudanar da buki wan shagali.

Fuskar baba cike da fara'a ya shiga cikin gidan bakinsa d'auke da sallama yana rarrab'awa ta gefe gefe saboda yanda gidan yacika maiqil da 'yan buki sai faman shiga raha akeyi wasu na shiga wasu nafita, duk inda yabi sai faman gaishesa akeyi ana tayashi murna tare da ALLAH sanya alkhairi, da qyar ya samu ya shiga ciki had'e da nufar wani d'aki da suke ajiye kayayyaki aciki yasa wata tobashiyarsa ta kirawo masa umma dake can tsakar gida tasha adonta cikin wani had'ad'd'en leshi wanda saika duba da kyau zaka iya gane itace, yajima zaune cikin d'akin yana tunanin shikenan yau zai rabu da 'yarsa tilo da yakeji har cikin qoqon ransa kafin umma tasamu takuccikke daga baqin dake dad'a shigowa tanufo inda take, a jigace tashigo cikin d'akin tana fad'in, "ai sai kuyi babu wanda zan sake d'ebowa abinci in zaku tashi kuje kud'ebo da kanku ku tashi, ai Kuma 'yar takuce bani kad'ai nahaifeta ba balle kubarni da aiki, don haka ni nagaji bazan qara yimaku wani abunba, shikenan daga kara saiku barni da aiki."

Murmushi baba yayi yana kallon fuskarta sannan yace, "haba uwar amarya, wannan irin fad'a haka da kikeyi halan keda wa."

"Nida matan balarabe mana, su daya dace ace suke tarbar baqi suna kai masu abinci shine sunka koma gefe kowace ta hakince sai kace tukane suna kiran akawowa wance da wance abinci, sun barni ni kad'ai ke hidimata sai kuma fareeda 'yar wajen yaya maryama."

"A'a'a to wannan maganar tafi qarfina tsakaninki ne da qannenki ba Mai shiga tsakani, ni dama zancen kai amarya ne yakawoni kinga gari ba guda ba.." kafin yaqarasa tayi saurin cewa,

"To ai sai anyi sallar la'asar za'aje ko kuwa?"

"A'a, bayin ALLAHn nan sun roqi alfarmar abasu amaryarsu su wuce da ita don gaba d'aya suka zo d'aurin auren tare da motocin d'aukar amarya, don haka kishiryata in sha ALLAH yanzu zasu wuce da abussu"

"Amma malan bamuga 'yan biko ba haka zamu miqa masu ita kamar..."

"Haba maman Rashida kada kice komai da yanzun da anjima duka d'aya ne, kuma shi biko ai al'adace ba addini ba don haka kiyi hak'uri tunda har iyayensa maza sukayi magana tamkar sun turo bikon ne, aje ashiryota gamunan muna jiranta muyi mata hud'u ba sai suwuce."

Jiki a sanyaye umma tafita tamkar wacce k'wai ya macewa a ciki, duk tsawon kwanakinna bata tab'a d'aukar cewa tabbas zata rabu da 'yar tata ba sai yanzu, cikin k'arfin hali tanufi d'akin da Rashida ke ciki kwance tana kuka bayan andawo da ita wajen wanka ita da 'ya'yan malan balarabe qanen mahaifinta su uku, sunyi lallashi har sun gaji sun qyaleta suna ganin umma tashigo duk suka mik'e suka fita, dai dai wajen kanta umma taje ta zauna tare dasa hannuwa ta d'ago kanta, cikin kuka tafad'a ajikinta tana sheshheka, ko kad'an umma ba tayi yunqurin hanata ba domin itama kanta kukan ne yazo mata, saida sukayi mai isarsu sannan cikin muryar dattako umma tafara yimata magana har lokacin tana jikinta.

"Rashida kuka bai kamaceki ba, domin wannan ranar farinciki ce agareki da kuma mu iyayenki da Allah yabamu ikon ganin mun sauke d'aya daga cikin haqqoqanki daya d'ora mana kuma ranace da kika dad'e kina jiran zuwanta don haka kinatsu ki saurari abunda zan fad'a maki amatsayina na mahaifiyarki." Share hawayen da suka sake zubo mata tayi sannan tasa hannuwanta ta tallafo fuskarta tana share mata qwalla had'e da cewa.

"Rashida! Ina so kibud'e kunnuwanki kiji abunda zan fad'a, gidan aure da kike gani ba wajen zaunawa kace zaka huta bane ko kace kayisane don kasuwanci, wajene na gwaggar maya don meman lada da kuma aljannarki, shi gidan miji wajene da zaki jajirce wajen nunawa duniya nagartar gidanku da kuma ahalinki, duk wata kima da darajarki annan ne zaki tabbatar da ita ta hanyar nuna kamalarki ga ahalinda zaki riska ku zauna dasu, mijinki shine aljannarki kuma shine farincikin ki na duniya da lahira, haquri da kike gani shi ginshiqine na tabbatuwarki isashshiyar mace awajen mijinki, shi kuma ladabi da biyayya sune zasu zamo maki tubalin da zai mai dake kasaitacciyar mace awajen mijinki, girmama iyayensa abune da zai qara maki kwarjina da tarin soyayya azuciyar maigidanki, kauda kai kuma da iya dad'ad'an lafuzza ga 'yan uwansa shi zaisa su soki har su zauna dake lafiya, kwanciyar hankalin da zaki bawa mijinki ita kuma jigoce ta yalwatuwar arziqinsa, kyautatawa da yin alkhairi ga mutane shizai jawo maki girmamawa ga manya da yaran da kike tare dasu, kiriqe ALLAH, ki guji abun hannunki, kibi mijinki kiyiwa mahaifiyarsa biyayya tamkar yanda kike yimani ga duk abunda bai sab'awa ALLAH ba, rashin kunya, tsiwa da sakin baki acikin mutane sukan xubarwa da mutum kima da daraja don haka ki nisancesu, Ina mai roqonki da duk k'arfin tsanani da wahala kada kid'aga harshenki akan na mijinki, idan son samune kada ki zalinci kowa kibari ke azalinceki da SANNU SANNU ALLAH zai yi maki sakayya, shi khairan da sharran duka 'yan aikene duk inda ka aikesu za suje kuma su dawo maka, kiyi k'ok'ari kishuka alkhairi don ki girbesa, kizama mai haquri da juriya sannan kizauna da kowa lafiya, kiriqi tsafta nasan kinada ita amma ki qara haka girki shima duk da bani da wani haufi akai amma ki kula sosai wajen kiyaye lokacin yinsa da wajen dafasa, banda almubazzaranci ko rashin yiwa miji godiya ga duk abunda yakawo, kiriqi addu'a da azkar na safiya da marece da lokacin kwanciya insha ALLAH zasu zamo maki fitila arayuwarki, ki guji fushin mijinki, ki nesanta da duk abubuwan da kikasan baya so ta hakanne zaki samu cikakkiyar natsuwa a gidan aurenki, Ina roqon ubangiji da yayi maki albarka, yakare mani ke aduk inda kika shiga ga sharrin mutum dana aljani, ALLAH ya albarkaci dukkanin zuri'ar da zaki samu ya kareki daga fad'awa ko wace irin fitinar rayuwa ta duniya da kuma lahira."

Duk da Rashida nacikin damuwar rabuwa da iyayenta hakan bai hanata jin dad'in lafuzzan mahaifiyarta ba agareta, gaba d'aya zuciyarta da kuma qwaqwalwarta sun gamsu da nasihohin data yimata kuma tayi alqawarin zatayi aiki dasu komai rintsi komai wuya, cikin sheshhekar kuka tace,

"Amin ummata, zan kula da duk abubuwan da kika fad'a mun kuma nayi maki alqawarin zamowa mai tsananin haquri da yiwa mijinta biyayya tamkar yanda naga kinayi." Rungumeta umma tayi tana murmushi had'e d cewa,

"A'a Rashida, bana so kiyi yanda kikaga inayi nafiso kiyisu fiye da yanda nakeyi kinji ko?." Cikin kuka tace,

"In sha ALLAH, ummata zanyi, don ALLAH kiyafemun duk wani abu Dana yimaki, ummata Ina matuqar jin kewar rubuwa dake." Taqarashe maganar tare da naniqeta ajiki tamkar zata tsagata ta shige tana mai k'ara tsananta kukanta,

"Rashida kenan! wake maganar yafiya anan bayan ummanki cike take da soyayyarki da kuma alfaharin samunki taya har za'ayi kiyi wani laifi kome qanqantarsa agareta kuma har yasamu muhalli acikin zuciyata?, Babu komai tsakanina dake face tarin d'inbin albarka da nake yimaki fata awajen ALLAH" cireta tayi daga jikinta sannan tamik'e taci gaba da cewa, "kije kishirya Rashida mahaifanki na jiranki a d'akin kaya kinji ko?." Tana gama fad'ar haka tajuya tafice daga d'akin, wajen qanwarta aunty marwiyya tanufa tayi mata magana akunne sannan tawuce wajen bak'in da suka shigo yanzu, da sauri ita kuma aunty marwiyya tashiga d'akin da Rashida take tasa ta tashi tashiga toilet tayo wanka da ruwan turarukka masu qamshi sannan tasa ta tsuguna saman turaren wutan da tana fitowa ta isko tahad'a mata, bayan yagama shiga jikinta tabata wani had'in madara daya sha kayan gyaran ni'imar jiki tace tashanye sannan tahau kimtsata yanda ya kamata, ba'afi mintuna ishirin ba sai gashi tafito da ita cikin had'ad'd'iyar shiga mai kyau da kuma d'aukar hankali, duk inda Rashida ta gotta sai zuba qamshi takeyi fuskarta a lullub'e, daidai lokacin malan balarabe yashigo cikin gidan yana fad'an afito da amarya anbar mutane zaune suna jira, ganinta yasa yayi shiru tare da nufar d'akin da d'an uwan nasa ke ciki suna jira, acan aunty marwiyya tanufa da ita suka shiga kan Rashida naqasa har lokacin tana zubar da k'walla, Saida ta duqar da ita agabansu sannan ita kuma tajuya tabar d'akin, naseeha sosai suma suka yimata sannan suka aika aka kirawo umma itama ta sake yimata wata sama sama, rungume baba tayi tana kuka mai tsima rai tare da roqonsa gafara nan take shima yaji kukan na nema ya kucce masa, da sauri yamiqe yana fad'in "nayafe maki Rashida ALLAH yayi maki albarka" ya fice daga gidan yana goge hawayen da suka zomasa, wajen umma tanufo ta sake rungumeta tana kuka umma ta dafa kanta had'e da cewa,

"Kitafi gidanki cikin amincin ALLAH da kuma yardarsa Rashida, ALLAH ya albarkaci rayuwarki yakareki ga dukkanin sharrin shaid'an da kuma ahalinsa" tana gama fad'a itama tajuya tayi cikin gida tana hawaye.

Aunty marwiyya ce tazo tarik'ata sai kuma yaya Maryam (yayarsu baba) dama tuni ansanar da 'yan bukin duk mai halin zuwa kai amarya ya gyara yanzu za'a kaita ba sai anjima ba kamar yanda aka tanada, Kai tsaye aka fiti da Rashida tana reren kuka yayinda suna isa bakin gida suka tarar da motar da aka tanada don amarya har anbud'e ana jiran isowarta, aunty marwiyya ta duqar da ita tana mai rad'a mata akunne cewa ta tashiga da _"Bismillah tawakkaltu alallah wala haula wala quwwata illah billah"_
Chapter 27 · 0% Book details