← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 160

Sashe 101

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ahankali ya sauke wata irin ajiyar zuciya had'e da juyowa yana kallon yanda take sheshshekar kuka, kan ya ankara yayi qoqarin rarrashinta da bata magana kawai yaga ansa qafa anshureta, ransa ab'ace yajuya don yaga wane marar imanine ya aikata mata haka shima yaji an d'aukesa wani irin zazzafan mari.

Hajia nafeesa ce sai faman huci takeyi kamar zata fashe ashe tun d'azu tana tsaye abakin part d'inta tana kallon duk abunda ke faruwa sakamakon hasken qwayaqwayin daya mamaye harabar gidan, ganin batool da tayi durqushe agabansa shiya fusatata tanufo wajen cike da takaici har tayi masu haka?, Cikin wani irin matsiyacin kallo dake nuna tsantsar tsanar da take yimasa tace, meye alaqarka da 'yar uwata, koso kakeyi kajawomun irin abun kunyar da kayo gado tun asali don kana butulu marar halacci?, to bari nafad'a maka, wlh hanyar jirgi daban take data mota, kuma ruwa ba sa'an kwando bane sannan kaje katambayi magabatanka kaji, akwai tsantsar banbanci tsakanin d'an halak da kuma shege, koda yake ba lallai bane ace sunsan haka, balle har su iya fahimtar da kai, daga yau bakai ba 'yar uwata domin ita jininta halastacce ne ba gurb'atacce ba, inba haka ba duk abunda yafaru dakai kai kajawo...

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___75💎

Tun cikin daren batool tahau shirin kayanta, hajia nafeesa dai nabiye da ido tana kallonta, saida takammala tsaf sannan tashige toilet ta watso ruwa, kallo d'aya zakayi mata tabaka tausayi saboda yanda idanuwanta suka kukkumbure akan kukan da taci amma sai qoqarin sakin fuskarta takeyi tana son nuna babu wani abun da yake damunta, kitchen tawuce ta had'oma kanta ruwan Lipton saboda yanda takejin bata sha'awar sama cikinta komai tadawo falo ta zauna tana kurb'a ahankali batare data tankawa qananan yaran hajia nafeesa dake faman mugun wasanni atsakiyar falon ba, shakur ne yashigo fuskarsa ba d'igon walwala ko kad'an yanemi waje kusa da ita ya zauna yana faman shinshinar qamshin body spray d'in dake tashi ajikinta,

Wata uwar harara ta zabga masa had'e da miqewa takoma d'ayar kujerar taci gaba da kurb'ar ruwan Lipton d'inta hankali kwance,

Miqewa yayi yasake binta zuwa inda take zaune shima ya zauna yana qare mata kallo tun daga sama har qasa yana lasar baki, sake miqewa tayi zatabar wajen yayi saurin sa hannu a fusace yariqo hannunta yana fad'in.

Wai yane malama dana zauna saiki tashi, meye kika gani ajikina da bakya so, kallonsa tafarayi sannan takalli hannunsa daya riqe nata dashi alamun yacikata amma yaqi hakan ya fusatata ta yadda cup d'in a saman center carpet d'in dake tsakar d'akin don dama ta shanye abunda ke ciki ta d'aukesa wani irin azababben marin da yasa ya saketa ba shiri ya dafe kuncinsa, cikin halin ko inkula ta d'auke cup d'in had'e da juyawa tanufi kitchen zata mayar da sauri ta tsaya sanadiyar jin da tayi yabiyo bayanta,

Cikin takaici tajuyo tana kallonsa tace, lafiya malan kake biyata.

Kamar sakarai Shakur ya amsa mata da, batool ni kika mara don kinga ina sonki?".

Eh, yanzuma zan sake marin naka idan ka sake yunqurin tab'ani, anfad'a maka so haukane? Ko ko anfad'a maka ana so dolene?, To bari nafad'a maka ni ba sa'ar kabace don matsayin uwarka naka tunda qanwar mahaifiyarka nake, don haka kadena ganin ka girmeni sosai wannan girman dole kabani shi ka ajiye shashanci agefe, ni banida lokacin yaro irinka.

Tana rufe baki taji hajia nafeesa nafad'in, eh lallai batool d'an nawa kike neman yaqunawa haka?, Shi kike kira yaro bayan yabaki shekaru d'aid'ai har goma sha d'aya aduniya?, to shikenan naji shi yarone, shi kuma wancan shegen fa da kike tsaya kulawa, shi kuma menene?.

Oho! bazan iya ganewa ba don tarbiyarsa Bata barni na iya fahimtar ko shekarunsa nawa ba, ban damu ba koma jaririne shi amma kijawa yaronki kunne, karya kuskura ya sake tab'ani idanko ba haka ba...bata ida qarasawa ba hajia nafeesa ta d'aga hannu zata kaimata mari tayi saurin riqe hannun tana cewa.

Daga lokacin da kika kira mahaifina kika sanar dashi qarya da gaskiya akan masoyina, daga lokacin ne nima nadaina ganin duk wani mutunci naki da kuma kimarki, daga lokacin kika rasa dararjar da har zaki iyasa hannu ki dakeni in qyaleki, ko wancan marin da kika yiwa masoyina, rad'ad'insa dana dad'e inaji ajikina bai barni na iya haqura ba har saida narama masa ga d'anki, gashinan kuma ki tambayesa, yanzu idan yayi qoqarin sake maimaita abunda yayi mani, to tabbas shima wancan dayan marin da kikayi mani to tabbas kuwa zan sake ramashi akansa, kitsaya a iya huruminki nake 'yar uwatace ko ince 'yar uwar mahaifina, kada kisake kice zaki sake qoqarin shiga rayuwata domin bakida hurumi akanta, har yanzu lokaci bai qure maki ba domin akwai sauran burbishin kimarki da nake gani sanadiyar zamowarki silar dana had'u da farincikina, idan kuwa ba haka ba to ina baki tabbaci akan zan zubar da sauran kimar taki dake idanuwa na nayi maki abunda sai kinyi dana sanin shiga gonata, kuma kamar yanda kikace Abu sumayya yarabu dani to zaiyi hakan ammafa nawani d'an lokaci, shima d'in bisa umurnin mahaifiyarsa ne don kada ki d'auka cewa kinyi nasarar rabamune idan kinga hakan, Ina so ke kuma idan har kin isa ga d'anki kuma yatabbata shi d'in d'an halak ne to kice yarabu dani, yadena bibiyata domin bana sonsa kuma bana qaunarsa.

Shaqo wuyanta shakur da tuni yakai qololuwa wajen fusata yayi yana huci ya had'ata da jikin bangon kitchen d'in data nufa yana fad'in.

Kinyi qarya kice zaki walaqantani akan wani shege da ba'asan aslinsa ba, halama waye ubansa da zaki zab'esa akaina?, to bari kiji nafad'a maki duk duniyar nan idan ta taru babu wanda ya isa yarabani dake, shi d'in wa da zaki fifitasa akaina?, Yaron daya tashi agabana cikin inuwar d'an uwana data mahaifina da suka yimasa sutura shi zaki nemi had'awa dani? to bari kiji in fad'a maki, idan ma mafarki kikeyi toki farka don narantse bakida miji aduniya saini, don haka kizuba mugani...., yana kaiwa nan ya jefar da ita gefen kujera yawuce fuu...kamar zai tashi sama yabar wajen, har ya kusa kai bakin qofar fita cikin qarfin hali ta tashi tare da cewa, kai sakarai,

Cikin b'acin rai yajuyo tayi murmushi had'e da cewa, Ashe kasan sunanka?, to bari nima in buga maka kashedi akaina kamar yanda kayimun, nunasa tayi da hannu had'e da murza 'yan yatsunta har Saida sukayi qara sannan tace, karubuta ka ajiye, ni d'innan mallakin Abu sumayyace wato 'yar da zan haifa mana nida shi don haka kadena wannan mafarkin nacewa zaka zamo mijina, waye kai kuma wa kake dashi da kake tunanin zai tsaya maka? Aunty nafeesa ce dake qoqarin amfani da zafin ran mahaifina? Ko kuwa zuciyarka da batada qwarin guiwar da zata iya fighting da tawa har taci galaba akanta?, to bazasu iya ba domin ni inada tsayayyu a hannun damata da kuma haguna, sannan zuciyata jarumace da zata iya fuskantar duk wata matsala kuma ashirye nake nabada rayuwata akan wannan d'an yaron daya tashi aqarqashin inuwar gidannan aka yimasa sutura, don haka ni dakai shege kafasa.

Kanta yayo a fusace da sauri hajia nafeesa da tayi tsaye tana kallon tsantsar rashin kunyar da batool ke zuba masu tariqesa tana fad'in.

Qyaleta shakur, jeka d'akinka kawatsa ruwa ka huta, duk rashin kunyarta kaine zakayi maganinta, tayi iyayinta don SANNU SANNU Bata Hana zuwa, in Sha ALLAH sai tazo hannunka a matsayin matarka kayi duk yanda kake so da ita kaji ko?,

Mere baki batool tayi had'e dayin tsaki tabar wajen tana fad'in, lallai kuwa iska na Shirin wahalda mai kayan kara.

Wani irin naushi yakaiwa bango yana huci yace, mom nifa bazan iya jurewa irin wud'annan walaqancin ba, kinajin yanda yarinyar nan ke fad'in maganganu amma kice duka na haqure, bazan iya ba.

Yaqare maganar a fusace had'e da barin wajen zuciyarsa na tafarfasa.

Bayan sati d'aya lokacin har little yawuce makaranta ita kuma batool takoma gida, tun ranar da takoma mahaifin nata kefushi da ita saboda abunda hajia nafeesa tafad'a masa kuma daya tambayeta kai tsaye ta amsa masa da cewa maganganun da hajia nafeesa tafad'a gaskiyane tana soyayya dashi saidai ba shege bane kamar yanda tafad'a kawai hassada ce da tsabar baqinciki dake cinta yasa tafad'i hakan don tab'ata masa suna.
Chapter 101 · 0% Book details