← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 160

Sashe 66

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mmn Rashida yakamata kitsaida kukan nan haka kada wani abun yazo ya sameki, muyi haquri ALLAHn daya bamu Rashida shine ya d'oro mana wannan jarabawar damu har ita, mubita da addu'a idan har tana raye Allah ya bayyana mana ita, idan kuma ya amshi abursa, to ALLAH kasa tayi shahada kuma yasa tadace da aljannah fiddausi."

"Amin malan, Amma bana tunanin zan iya dakatar da wud'annan hawayen zuba bayan narasa 'yata tilo aduniya, wacce dukkanin burina da kufa farincikina aduniya ya tattarane akanta, musamman idan ina ganin abubuwan da zasusa dole nariqa tunawa da ita, sai nadingaji tamkar lumfashin zai d'auke, wlh ba mutuwa nakewa Rashida gudu ba domin dolece akan kowane mai rai, wahalar da nake tsoratar mata ita da abunda ke cikinta shikesani zubar da wud'annan hawayen."

Shiru baba yayi kafin ya dafata had'e da cewa, "nikaina idan nakalli d'akincan yakan tuno Mani da rayuwar da tayi aciki, haka shima Nuraddeen mijin nata, aduk sanda naganesa gabana na tsananta fad'uwa sai inji kamar zan ganesu ne atare, wannan yasa nafara tunanin yin nisa da garinnan da duk wani abu da zai nadinga tunowa da b'atan nata, daga baya kuma nayi tunanin cewa to idan da mutuwane tayi shima zan kasa rayuwane a inda muka rayu da ita?, Sai kawai naji na gamsar da kaina nahaqura kawai naci gaba da rayuwata anan, Amma yanzu wannan yanayin da nake jina aciki suna kamanceceniya da wanda kika bayyana mani kinaji, don haka idan kin amince yau d'innan zamuyi nesa da garinnan, wataqil hakan zai rage mana damuwa da rad'ad'in da mukeji aranmu, qilama yasama mana farincikin da bama tsammanin samu anan gaba."

"Na amince da hakan malan, Amma ina zamu tafi?."

"Wannan kuma ALLAH shikad'ai yasani kuma duk inda ya zab'a mana daidai ne agaremu."

Nan suka shiga tattaunawa tare da shawarwari akan tafiyar tasu, sun amince kuma sunyarda da shawarar da junansu suka yanke don haka suka tashi suka shiga kakkamta duk wasu abubuwan da suke buqata da bazaya gagaresu d'auka ba, wanda mafi yawanci suturar jikinsu ce sai 'yan kud'ad'ensu da sukayi ajiya da wud'anda suka samu na jinya da sauran abubuwansu masu muhimmanci, koda qarfe hud'u tayi nadare sun shirya tsaf, ana kiran sallar farko na asuba suka silale suka bar garin bayan baba ya ajiye wata takarda adaidai bakin qofar gidan idan anshigo daga ciki..

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Barakallahu lakum😍 naga comment d'inku kala kala akan tafiyar iyayen Rashida, Wanda mafiya yawancinku basu so hakan ba kuma beyi masu dad'i ba, Karku manta sau da yawa ALLAH kan tsarowa bawa wata qaddara arayuwarsa yayin gujewa wata qaddarar tasa. inbaku manta ba iyayen Rashida mutanen qauyene basuda zurfin tunani da hankaltar cewa zamansu agarin shine daidai domin akowane lokaci 'yarsu zata iya dawowa idan tana raye kuma sune nafarko da zata fara nema, damuwarsu d'aya shine, fita daga cikin halin quncin rashinta da suka shiga da kuma yanayin ciwon da suka fito daya kusa kaisu ga rasa rayukansu, A tsoron kada su sake fad'awa cikin qaddarar shiga wani quncin da zai jawo masu ciwon da yafi wancan yasa suka koma fad'awa cikin qaddarar rashin had'uwa da 'yar tasu, to haka abun yake ko a zahirance acikin yanayin rayuwarmu ta yau da kullum, alokacin da muke qoqarin gujewa wata qaddarar tamu to muna sake fuskantar wata qaddarace ta daban da ALLAH yarubuto muna acikin littafinmu, tabbatuwar wannan qaddarar akanmu shike tilastamu da aiwatar da abunda zai zamo silar wanzuwarta, idan mun duba, ko a musulunce ALLAH ya halastawa bawa idan yana cikin tsananin kunci da takurar rayuwa da yayi hijira daga garin da yake zuwa wani garin saboda yasamu sauqi matuqar ba annoba bace, don haka kuyi haquri👏 idan da rai da rabo Rashida zata sake had'uwa da iyayenta, abunda kawai banida tabbaci akai shine, a Ina?, Yaushe ne?, Awane lokaci kuma awane waje?,😍 Domin samun amsar sai kun jure bibiyarmu acikin wannan littafin, SANNU SANNU dai Bata hana zuwa....😍 Luv you guys fillah_💞

Page___50💎

Cikin sa'a sukayi nasarar ficewa daga anguwar ba tare da kowa ya gansu ba, daga su sai jikukunansu guda biyu na kaya da kuma 'yar jikka ta ratayawa irin ta maza dake sagale a kafad'ar baba suka nufi tasha, sunjima zaune abakin wani shago kafin baba yatashi yaje ya d'ibi ruwa a randar dake ajiye bakin qofar masallacin dake cikin tashar yayi arwala, Saida ya d'ibi wasu a buta yaje ya kaiwa umma itama tayi arwalar had'e da ciro sallayar da sukazo da ita cikin kayansu ta shimfid'a sannan yabar wajen da sauri jin antayar da sallar yana fad'in,

"Kibi jam'i maman Rashida Ina fitowa zamu shiga motar duk da muka samu tagama lodi."

Ana gama sallar addu'a kad'ai yayi yafito da sauri da sauri tare da tallabar jikukunan nasu dake gabanta yana fad'in. "Hanzarta maman Rashida naji motoci sun fara tashi."

Tofi tayi acikin hannayenta dake sama bayan tagama yimasu addu'ar ALLAH yazab'a masu wajen zuwa mafi alkhairi arayuwarsu had'e da shafawa sannan tamiqe tanad'e sallayar tabi bayansa, suna isa motar Niger na d'agawa wacce ita yaso su samu don d'azu yana arwala yaji drivern motar nafad'in passinger biyu ya rage masa tacika, sai gashi kafin ya d'oko kayan nasu su iso wajen har ansamu ciko, shiru yayi had'e da ajiye jikkunan yana kallon umma da sai yanzu ta ida qarasowa wajen,

"Ai har motar tacika, kingata can yanzu tawuce" yafad'a cike da damuwa don baya son abunda zaizo ya dakatar dasu daga tafiyar wanda hakanne yasa ma ya kasa sanar da d'an uwan nasa.

Murmushi tayi tare da cewa, "ka kwantar da hankalinka, inda tanufa qilan zuwanmu can d'in ba alkhairi bane."

"Hakane kuma."

Yabata amsa tare da nufar rumfunan da motocin kowace jaha ke tsayawa lodi, duk motar daya duba bai wuce yaga mutum biyu ko ukku aciki har yawuce kusan motocin jahar, gombe, sokoto, katsina, adamawa da kuma bauchi babu inda yaga mota takusa cika balle tashi, har yajuya zai bar wajen yaji ana fad'in.

"Borno mutum uku, mutum uku borno."

Da sauri ya juyo yanufi inda motar had'e da cewa driver borno zaije.

"To kashiga, saura mutum biyu." Karan motar yafad'a yana sake d'aga murya yana fad'in "mutum biyu borno."

A sauri baba yasake matsawa kusa dashi yace "ai mu biyune nida matata."

Yana rufe baki saiga cikon mutum d'aya an samu, da d'an gudu gudunsa yaje yakira umma tare da d'oko masu jiku_ kunansu, miqa hannu umma tayi takarb'i d'ayar ganin sunyi masa yawa saboda yanayin yanda yake tafiya tunda ba lafiya yacika ba yayi saurin wucewa yana fad'in. "A'a kedai d'aga qafarki muje."

Suna zuwa akasa kayansu bayan mota suka shiga drivern ya tayar da motar suka bar tasha, suna hawa titi had'e da kama hanyar tafiya baba yarufe idanuwansa had'e da sakin wata irin ajiyar zuciya, kallonsa umma tayi itama tana ajiyar zuciyar tare da aza kanta saman kafad'arsa tana karanto addu'ar tafiya yayinda mutum ya hau abun hawa, wacce tafito daga bakin mafificin halitta kuma ya tabbatar mana da cewa duk wanda yayita alokacin daya hau abun hawansa zaiyi wata tafiya to ALLAH zaikaresa da ga sharrin duk wani abunqi dake cikin tafiyar da sharrin qarfe ko kuma had'ari, zai sanya tarin alkhairai masu d'imbin yawa acikin tafiyar tasa da yardar ALLAH.

_"ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBARU subhanallazi sahhara lana haza wama kunna lahu muqrinin, wa inna illa rabbina lamunqalibuun, allahummah Inna nas'aluka fi safrina hazal birri wattaqwa, waminal amali ma tarda, allahummah hawwan ala safarana haza wad'wi Anna bu'udahu, allahummah antasswahibu fis safri, walkhalifatu fil ahli, allahummah inni a uzu bika min wa'thaa'issafri, wa kaabatil manzwari, wasuu'il munqalabi fil mali wal ahli."_

Domin samun fassarar wannan addu'ar zaku iya duba littafin hisnil muslim, addu'a ta tis'in da shida (96) don nemawa kai kariyar ALLAH daga sharrace sharracen miyagun mutanen dake kan hanya da kuma munanan had'urran da sukayi yawa alokutan tafiye tafiyenmu,

Tana addu'ar hawaye nazubo mata a fuska, hannu baba yasa yagoge mata had'e da cewa.

"Kinsan inda muka nufa yanzu?"

Girgiza masa kai kawai ta iyayi tana mai tunanin yanda duniya tajuye masu daga farinciki Mai yawa na bayan shekaru zuwa baqincikin da basusan iya adadin lokacin da zasu d'auka dashi kafin yabarsu,

"Jahar borno muka nufa kuma Alhamdulillah akwai wani babban mutum dana sani acan abokin alhajin da nake saro takalma a shagonsane ana cemasa alhaji shu'aibu maiglass, muna yawan had'uwa dashi idan yaje wajensa ni kuma naje kaimasa kud'insa in amso takalmi, yanda alhajin kejin dad'in mu'amalar kasuwanci dani yasa wata rana ya had'ani dashi muka gaisa har yake fad'amun ai aminin sane yana zowa daga borno me shima yayi sayayar kayan glass nayin qofofin zamani, to tun daga lokacin duk yazo in muka had'u sai yayi mani alkhairi don babban mutumne sosai, kinga idan munje sai munemi gidansa kafin musamu inda zamu zauna.

"Shikenan duk da dai mutum bashida tabbas amma tunda ba muda wata mafitar ALLAH yasa hakan shiyafi zama alkhairi kuma yakaimu lafiya."

"Amin, ki kwantar da hankalinki in Sha ALLAH babu wata matsala."

"ALLAH yasa." Tafad'a tana share qwalla a idanuwanta.

••• ••• •••
Baffa Ali kam yayi sanyi sosai akan abunda yafaru, yayi dana sani mai yawa akan biyewa harkar mata da yayi wacce ta jefasa cikin halin qaqa nikayi, yayi nadamar shiga al'amurran Yaya hawwa Amma duk da haka yana jin tsanar baffa mai tsanani azuciyarsa bisa abunda yasa akayi masa shida iyalinsa a matsayinsa na d'an uwansa, hakan yasa tunda suka dawo yafita harkar kowa yana rayuwarsa shi kad'ai, baruwansa da kafatanin mutanen gidan acewarsa suma munafukaine tunda aka kasa samun wanda zaiyi belinsa acikinsu, had'uwa dubu kuwa idan zasuyi da baffa bazai d'aga Kai ya kallesa ba balle yasa ran zai gaishesa, dama dama baffa Usman yakan d'an saki jiki dashi sugaisa yawuce shima d'in ba sosai ba, Kuma hakan ko kad'an bai dami baffa ba saima addu'ar neman shiriya daga ALLAH.
Chapter 66 · 0% Book details