Sashe 19
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Nauyin bakin da kayi wajen sanar dani soyayyarka har sai dana sallamawa mahaifina akan duk zab'in daya yimun, wannan shine dalilina domin jiya mahifina yazab'o mun wanda zai aura mani kuma har yabiya sadakina, yanzu haka kwanaki goma sha biyune suka ragemun nazamo mallakinsa kuma ni bazan iya hana hakan ba." Dariya yafara mata har yana riqe ciki don gaba d'aya ya fahimci batasan cewa shine mijin da take iqirarin mahaifinta ya zab'a mata ba, yana kallon yanda ranta yab'aci amma yakasa tsaida kansa har saida yayi mai isarsa sannan yace " yi hak'uri ranki shidad'e abunne dole inyi dariya.." yaqarasa maganar had'e da d'ago kansa amma ga mamakinsa sai ya hangota ashe tuni har tabar wajen tana gab da isa gida,
Da sauri ya cimmata yana kiran sunanta, tsayawa tayi tanajin zuciyarta kamar tafad'o saboda takaicin fad'a masa sirrinta da tayi Ashe dama shi ba sonta yakeyi ba tunda har ya iya yimata dariya a daidai wannan lokacin daya kamata ace dukkanin su suna cikin damuwa, qarasowa wajen yayi had'e da rik'e kunnuwansa yana gumtse dariyar dake neman sake fito masa yace "yi hak'uri matata natuba kinji"
K'walalo idanuwa awaje tayi had'e da girgiza kai irin bakasan abunda kakeyi ba tace "malan matar kafa kace? Karka manta yanzu nagama fad'a maka cewa antsayar mani da mijin da zan aura kuma har yabiya sadaki kwanaki kad'an suka rage a d'aura mana aure amma ka aza mani dariya saboda kasan Kai d'in bada gaske kake sona ba shiyasa bak damu ba, dama nasan bazaka iya aurena ba tunda banida ilimin boko kawai kafad'i hakanne don ka yaudareni."
"Subhanallahi Rashida mekike cewa hakan, nifa Ina mamakine akan yanda bakisan cewa nine mijin da zai aureki ba, kituna ke d'alibata ce, idan babu soyayya taya kike tunanin zan iya zaunawa ina bibiyarki haka? Ni da kike gani bantab'a soyayya ba kuma ban tab'a bawa wata mace dama ba tashiga rayuwata sai ke, to don me da zan yaudareki Rashida, ita soyayya Babu ruwanta da ilimi ko akasinsa kawai shiga takeyi a zukatan da ALLAH yaga cancantarsu da juna, kiyi hak'uri da banjira amsar da zaki bani ba na gabatar da kaina awajen iyayenki, wlh Rashida sonki nakeyi da gaskiya Kuma aurenki nakeso nayi kizamo mallakina kuma uwar 'ya'yana"
"Don ALLAH malan kadena fad'ar haka, kadena k'ok'arin cusamun sonka azuciya, wud'annan kalaman naka zasu iya sake jefani cikin maraicin rashinka alokacin dana zamo mallakin wani, tun ranar daka furta mani kalmar so nake shan wahala domin duk motsin da zanyi Ina tsinkayo sautin kalmomin a kunnuwana, meyasa zaka nemi sake turani cikin damuwa da wud'annan zantuka naka."
"Amma Rashida meyasa baki tambayi baba kowaye yazab'a maki?"
"Saboda bana son nasan koshi waye?"
"Koda nine Rashida?."
"Taya zaya zamana cewa kaine" tunanin fad'a mata komai yayi saboda yakawo k'arshen wannan jayayyar tasu tunda ya fahimci batada wata masaniya akan komai gyara tsayuwarsa yayi sannan yashiga labarta mata abunda yafaru ranar da yazo gidansu wanda shine silar daya kai mahaifinta aranar makarantarsu daga nanne ya gano shid'in abokin mahaifinsa da bashida lafiyane har zuwa jiya da sukaje dubosa shi kuma dama ya sanar da mahaifinsa cewa yana son yanema masa aurenta Kuma kasancewar aminaine sosai yasa mahaifinta ya amince, nan take akayi komai aka gama bisa amincewar iyayenta da kuma nasa, yana kaiwa nan ya lumfasa had'e da cewa, "to Rashida kinji abunda yafaru kuma Ina fatar zaki amince dani d'ari bisa d'ari ki aureni, cike da mamaki wata irin kunya tarufe Rashida don gaba d'aya yanda yabata labarin haka taji baba yana bawa ummashi amma arayuwarta bata tab'a kawowa shi d'inne ba, wani irin farinciki takeji aranta marar misaltuwa, ahankali tabud'e baki tare da sunkuyar da kanta k'asa tace,
"Kayi hak'uri malamina" sannan tabar wajen aguje, dariya yayi yana binta da kallo har tashige gida, wani yaro yakira tare da bashi ledar dake hannunsa yace yashiga wancan gidan yakaima Rashida sannan shi kuma yawuce zuciyarsa fal cike da farinciki.
••• ••• •••
A b'angaren yaya hawwa kuwa wato mahaifiyar Nuraddeen kasa amincewa da kuma natsuwa tayi akan komawar yaronta garin saboda yarinyar da zaya aura se take ganin kamar duk abunda yasamu yanzu ita da iyayenta zai baiwa, hakan yasa tayanke shawarar zuwa wajen wani malamin tsibbo tace tana son tunkafin ayi auren a tabashi da ita a saka mashi tsanarta ta yanda koda ranar d'aurin aurensu ne bazai yarda ya aureta ba sai a maye soyayyar da yake yimita akan 'yar qanen mahaifinsa wato muneerat, duk iya tsibbo da bugun k'asar da malamin zaiyi yayi don ganin kozai iya cin nasara Amma ya kasayi daga k'arshe sema cemata da yayi ta tashi tatafi don babu abunda zai iya, domin wannan auren ko tana so ko bataso dole sai anyisa saboda arubuce yake acikin qundin qaddarar yaronta da babu wanda ya isa ya hana ko kuma ya sauyasa hakan, Wanda kuma duk yayi yunqurin hanawa to tabbas babu ko shakka dole zai mutu don bazai iya ja da alqawarin ALLAH ba.
*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏😭_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___15💎
Wasa wasa gini yafara girma saboda aikin akeyi ba dare ba rana, duk wani tanadi da baffa yayi sai daya fiddosa yabawa baffa usman yace ayi duk abunda yakamata kafin lokaci yayi don baya son aikin yakai har lokacin da za'a kawo amarya, acewarsa hakan yafi da ace ankawo yarinyar mutane cikin matsuwa inda bazata samu sakewa ba, sosai duk wanda ya kalli baffa cikin natsuwa zai fahimci bakad'an yake matuqar jin jiki ba, ammasaboda qarfin hali akoda yaushe qoqarin b'oye hakan yakeyi don gudun kada adakatar da auren.
Ita kuwa yaya hawwa kullum cikin masifa take wai ama faman kashewa k'asa kud'i a banza anqi atanada Amma tun daga baffa har zuwa baffa Usman Babu wanda ya tankata inba baffa Ali dake sake zugata akan ccewa inbatayi da gaskeba duk nan baffa zai qarar da kud'in gashi yana jinya abarta da wahala, sake rufe idanuwa tayi ita ala tilasa a ajiye ginin inyaso Nuraddeen d'auki shigihwa guda a cikin shigihun dake sashen nasu a gyarawa yarinyar, nan ma baris baffa yayi da ita saima cigaba da bada kud'i da yakeyi ana cigaba da aikin, tayi masifar tayi har tagaji don kanta tabari amma babu abunda ke dad'a b'ata mata rai irin yanda taga ana narkewa wajen kud'i da irin manyan shanun da yasa aka kama aka sayar, hakan ba k'aramin takaici da bak'inciki yake sata ba idan ta tuna, gashi har yanzu takasa had'a kud'in da malam bakada imani yace tahad'o wajen yimata aiki balle tasan ko meye madafarta, wata shawara ta yanke aranta na zuwa wjen baffa ko zata samu cikon kud'in da take nema wajensa, kwance ta iskoshi duk ya had'a zufa saboda wutar da aka d'auke sai zafi ya taso masa,
"A'a malan kaid'ai kake a d'akin ba kowa? Sukuma 'yan albarka sun d'auke wutar duk zafi yataso, kai ALLAH dai ya rangwanta mana" tafad'a tana jaye labulayyen taga saboda iska yashigo sannan taqaraso wajensa ta tallabosa ya tashi zaune yana fad'in "wash! bi ahankali hawwa, bayannan inajin yana yimun zafi sosai"
"Sannu malan, sai hak'uri kasan dama shi sauqi ahankali yake shiga, ALLAH dai yabaka lafiya."
"Amin hawwa." Yafad'a yana kallonta cike da mamaki don yasan wani abun take so, bai qarasa tunanin da yakeyiba yaga ta d'auko mafefeci tafara yimasa fiffita had'e da cewa, "malan kaga aurennan ya matso gashi babu fashi sai anyisa kuma inada buqatar inyi wasu 'yan gyare gyare, shine nace mezai hana ko 'yar dubu goma ka qara mani insamu in gyaggyara kafin lokacin ya qaraso" murmushi yayi don dama uasan za'a rina, indai hawwar daya sani ce Babu yanda za'ayi kaga tana yimasa wud'annan abubuwan batare da tana son wani abu daga garesa ba, d'an nisawa yayi sannan yace,
"Hawwa dubu gomafa kikace?, Yanzu ke ko hidimar gyaran inda yaronnan zai zauna da nakeyi bakya gani har zaki zomun da wannan zance, haba hawwa ai kamata yayi ace kinkawo nahannunki anqara dasu bawai kinemi karb'a ba"
"Amma naga ainima duk hidimarce zanyi ko malan, ko kafiso akawo yarinyar nan babu wani abun kirki da aka tsinana agidan?."
"To meza'ayi tunda dai naga ba kishiyarki bace balle kice haka, in Kuma maganar abubuwan da za'aci a rarrabane to kibari lokaci yayi ina sane dasu, mufa wajen ango muke ba amarya ba balle muce wata hidima zamuyi."
"Dakata malan kawai idan bazaka bayar bane kafad'amun Amma bazai yuyu kazauna kana fad'amun yanda ranka keso ba." Taqarasa maganar had'e da miqewa ta jefar da mafefecin gefe,
"Meyayi zafi haka daga magana hawwa karki manta yaronnan d'an mune mu muka haifesa kinga kuwa gaba d'aya hidimar tamuce dani dake kuma yakamata ace kema kin kawo taki gudun mawar, ni nazatama kina can kina qoqarin had'a masa lefe ashe aiki nizai qararwa." Ya iyar da zancen yana dariya, wani irin mugun tsaki taja sannan tabar d'akin, girgiza kai yayi yace "ALLAH ya shiryeki hawwa."