← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 160

Sashe 127

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna ruqayya nakaiwa Yusuf da baffa Usman da wani abokinsa sun tallabo baffa Ali da baimasan inda kansa yake ba baffa na biye dasu don bayada qarfin da zai iya riqa masu shi zasu je asibiti.

Fashewa tayi da kuka tana sallallami baffa yace taje takirawo Inna ruqayya ta sanar da ita kuma tadena wannan kukan don kada ta tayarwa da mutanen gida hankali.

Koda tafad'owa Inna ruqayya cewa tayi taje tajiya zata bisu daga baya ita baccin bai isheta ba, girgiza kai kawai Inna Bilkisu tayi tare da cewa.

"ALLAH ya sawaqe," tabar wajen,

Koda suka isa asibitin dake nan cikin qauyen don yanzu anqara gyarata sosai fiye da shekarun baya da sauri aka amshesa, gwaje gwaje suka fara yimasa kafin suyi masa wani abun inda suka tabbatarwa dasu baffa saidai akaisa can asibitin cikin gari saboda gaba d'aya qafar tarub'e.

Jiki narawa baffa yakoma gida ya sauyo kaya tare da d'auko d'an sauran canjin da take dasu ajiye, hankalinsa atashe ya sanar da baba nusaiba halin da ake ciki cike da damuwa, ganin yanda duk yabi ya hargitse yasa tashiga kwantar masa da hankali tana gaya masa cewa yayi Imani da ALLAH shiya jarabcesu sai suyi qoqarin canye jarabawar ta hanyar qarfafa zukatansu da kuma imaninsu, sosai yasamu raguwar damuwarsa ta d'auko masa abunnkarinsa da rarrashi da ban magana tasamu ya karya daqyar sannan yafice yana mai addu'ar ALLAH yasa takasance abokiyar rayuwarsa har a aljannah.

Yana komawa asibiti ya tarar shima baffa Usman har yaje ya dawo ya d'auko tashar mota suka d'auki baffa Ali sukayi general hospital dake cikin gari dashi,

Suna isa likitoci ska amshesa aka shiga yimasa gwaje gwaje nan take suma suka tabbatar masu da cewa qafar tasa tarub'e tun daga tafi har zuwa Rabin cinyarsa wanda yazama dole acire qafar gaba d'aya har cinya in ana so ya samu lafiya, idan kuma ba haka ba to ciwon zaici gaba da tafiyane har can cikin jikinsa, idan sun amince ga takarda nan sai susa hannu saboda agaggauta yimasa aikin kafin ciwon yakai inda ba'a buqata bayan an fad'a masu wasu maquddan kudd'i da zasu biya.

Basu tsaya wata doguwar shawara ba nan take sukasa hannu atakardar sannan sukaje sukasa wata babbar gonarsu da suke da ita su uku ta gado akasuwa wanda daqyar suka samu aka basu rabin kud'in ak'asa sauran kuma sai nan da kwana uku za'a basu suka karb'a sukayo asibiti, kasancewar kud'in na isa ayi aikin har su rage yasa suka amince suka karb'o kud'in suka biya aka yimasa aikin.

Tsawon kwana uku baffa Ali yayi kafin ya farfad'o Amma sau d'aya Inna ruqayya ta tab'a zuwa dubasa shima d'in tabiyo ta asibitin ne tana bara tahad'u dasu Rashida d'ayan baffa napep ta ajiyesu sunzo kawo abincin, shinefa tabisu suka shiga tare lokacin yana bacci, kasancewar baffa ne awajen yasa baima kulata ba balle yayi mata fad'a akan abunda ta aikata, shi kuwa baffa Usman dake cike da ita baya samunta gida ko yakoma balle yayi mata zancen, dama yanda sukeyi yau idan baffa yawuni asibiti sai baffa Usman yaje kasuwa, gobe kuma baffa yaje kasuwa baffa Usman ya zauna a asibiti shi Kuma Yusuf da wani abokinsa suke kwana anan.

Tsabar daqiqancinirin na Inna ruqayya kai tsaye tanufi wajen kan baffa Ali dake bacci tana bubbugawa had'e da kiran sunansa.

"Ali, Ali, Ali katashi, nifa da akwai inda zani yanzu, bazaka tashi ba?, Shikenan ALLAH yasawaqe, dama naji ance karasa qafarka kaga dole naqara maida himma wajen nemo mana abunda zamuci, shikenan an qara mayar mana dakai cima kwance gurgu da bayada amfani dama haka ake son ganinmu, wlh dai ALLAH ya isa ga Wanda yasa aka cire maka qafa, da Wanda yabada kud'i aka cire qafar da wanda ya tuqo motar da aka d'aukoka da qafafuwanka aka mayar dakai gurgi, da wanda yasayi motar da wanda ya gina asibitin da wanda yakarantar da shegennlikitan yanda ake cire qafar duk ALLAH ya isar mana."

Taqare maganar had'e da fashewa da kuka tana sharar majina da mayafinta, shi kam baffa abunma dariya yabashi don yaga haukan natama yayi yawa.

Ganin bai tankata ba yasa taja qafafuwanta tabar d'akin, tana fita tafara bin mutanen dake jinya tana kuka wai su taimaka mata aiki aka yiwa mijinta anka cire masa qafa basuda kud'in magani, haka tazagaye asibitin tana fad'a tasamu kud'inta sannan tafito ta tabar asibitin tana harhad'a kud'in da tasamu, daidai zata fita bakin gate d'in taga wani dattijo a tsaye da alama wani yake jira, ai kuwa tayi tsaye tana roqonsa, kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai har wacce yake jira ta qaraso cikin napep ta sauketa.

Da d'an sauri ta qaraso tana fad'in kayi haquri maigida, napep d'in tamuce ta tsaya muje ko,

Amarya idan kinada hamsin d'an taimakawa tsohuwar nan tun d'azu ta nace tana bara kuma banida canji, irin 'yar jikkarnan qarama ta hannu da ake d'unkawa tabud'e taciro d'ari tana fad'in.

"Bari nima nabata hamsin sadaka gami da taka d'ari kenan, ALLAH yaba baffana lafiya."

'Dago kan da zatayi suka had'a ido biyu da mahaifiyarta wato Inna ruqayya, da sauri takarb'e naira d'arin sannan tace,

"ja'ira nice..."

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___91💎

Yauma kamar kullum Inna ruqayya tafito zataje wajen baran data saba tajawo qyauren qofar d'akinta tana rufewa had'e da gyara mayafinta saiga baffa Usman yafito daga cikin d'akinsa shima, kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai muneera na kwance bakin qofar d'aki tasa qafa ta zungureta tana fad'in.

"Ke kasa uwar bacci tashi muje inda mukafi wayau don indai zamu yini mukwana acikin gidannan saidai takaici ya kashemu don babu abunda za'a iya tsinana mana yanda muke so, tunda ubanku yanzu bayada mamora kullum yana can kwance."

Tafad'i hakanne saboda tab'atawa baffa Usman rai data gani wajen a tsaye, muneera da itama yanzu tad'an miqe hanyar da zaka iya fahimtar takwana biyu aduniya tunda babu wata cikakkiyar kulawa da za'ace tana samu ta tashi zaune tana buga hamma had'e da cewa.

"Inna wai don ALLAH fita baran nan dolene?, Wlh nagaji da yawon nan bana sonsa, muyi haquri da taimakon da muke samu daga hannun 'yan uwan baffanmu in Sha ALLAH zai wadatar damu."

Batare data tanka taba tajawo sandarrta da kwanon da suke fita baran dasu sannan ta d'auki wata jikka irin ta d'unkawar nan tayi majalmajal ta rataya tamiqi hanya, saida takawo saiti da baffa Usman sannan tajuya tana cemata.

"Inzaki taso mutafi sai kitaso in bazaki taso ba kuwa sai kiyita zama anan, yunwa da baqinciki su zasu illataki acikin gidannan kigano cewa da dangin uban naki da kike fad'in suna taimaka maki basuda amfani don wlh saita kasheki batare da ankula kiba, banda abunkima to me nasama yaci balle yabawa naqasan sa da har kike iqirarin suna taimakonmu, mu inba tarin baqinciki ba me alaqa dasu tahaifar mana tunda basa son ubanku basa qaunarsa basa bid'ar had'a jini dashi don tsabar baqinciki, ai saiki zauna cikin gidan kigani in zasu iya tsinana maki wata tsiyar shasha da batasan kanta ba ni kinga inda nayi"

"To Inna kijirani mana."

Muneera tafad'a tana b'ata rai, shidai baffa Usman ko kallonta beyi ba balle yasa ran zai iya tankata, jin abunda muneera tafad'a yasashi d'ago kai yana kallonta kafin yakira sunanta.

"Muneera.."

Juyowa tayi tana qoqarin saka takalummanta had'e da cewa "na'am baffa Usman."

"Kina buqatar fita tare da ita?" Ya tambayeta fuskarsa a d'aure.

Saida takalli fuskar Inna ruqayya dake tsaye ta aza kwanon saman kanta sannan ta maido kallonta ga baffa Usman had'e da girgiza masa kai tace.

"A'a baffa, wlh nagaji da yawon barar nan, banda walaqancin mutane da tozarci babu abunda muke fuskanta, wani zubinma har zagi ake had'a mana dashi."

Baki bud'e Inna ruqayya ke kallonta kafin tace.

"Don uwaki don ubaki amma ai muna samo kud'i ko?, Yo zagi zai laqekine ko zai fito maki ajiki."

"Amma Inna.."

Saurin dakatar da ita baffa Usman yayi had'e da cewa.

"Bashi nake son jiba muneera, kinada ra'ayinne ko bakyada shi Ina so na sani a matsayina na yayan mahaifinki."

"Bana ra'ayi baffa nafi son inzauna gida abina,"

"Shikenan komawarki ki zauna, daga yau naharamta maki zuwa bara kuma duk wanda ya tilastaki to 'yan sanda zasu shiga tsakanina dashi saboda inada iko akan 'ya'yan d'an uwana."

"Baffa Inna bazata bani abinci ba..."

"Bana son shashanci muneera, indai kinyarda yayan mahaifinki nake to kibi abunda nace batare da sab'awa ba, ni kuma nayi maki alqawarin zanyi maki duk abunda yakamata ace yayi maki."

Washe baki muneera tayi don tasan halin baffa Usman fad'a da cikawa ne, qarasawa tayi kusa dashi had'e da cewa.

"ALLAH baffa zanyi yanda kace, amma harda aure zaka yimun?"

"Zanyi maki muneera inkina buqatar hakan kuma kinada wanda kike so..."

"Uban kuturu yayi kad'an wlh, ba wanda ya isa hanani fita bara da 'yata, Ina ni nahaifi abita ba wani ba? Maza kitaso muje kafin na sab'a maki" Inna ruqayya tafad'a tana laqame kwanon acikin hamuttatta, baffa Usman bai tankata ba yashige d'aki abinsa don yasan kowace muneera, batada babbar damuwa duniya irin ahanata abincin da zataci kuma tunda har taji yafurta cewa zai yimata komai tofa babu wanda ya isa ya sake tirsasata batun zuwa yawon bara tunda dama bata so tagaji, qarasawa muneera tayi kusa da ita takarb'i kwanon baran da jikkar da sandar Inna ruqayya tazata binta zatayi sai taji tace.

"Inna ki ajiye batun fita baran nan don ALLAH kizo mukoma cikin gida, su baffa zasu taimaka mana kinga koba komai zamu muhuta da cin mutunci da mutane keyi mana"

Tun kafin yarufe baki Inna ruqayya ta wafce jikkarta tare da kwanon, zata karb'i sandar muneera ta ja baya da ita had'e da cewa.
Chapter 127 · 0% Book details