← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 160

Sashe 141

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya klw alhaji, cikakkiyar surarka da kamalarka na kalla naga irin zubin da ubangiji yayi maka na salihhan bayi dake da matuqar hangen nesa amma kai ka kasa fahimtar hakan balle har ka hango abunda nake son lusar da kai nan gaba, fisabillahi amatsayina na mahaifiya nagaji da irin hukuncin da kakeyiwa 'yata, na d'au tsawon shekaru ina yimaka biyayya batare dana damu da akan daidai kake ba ko akasin hakan, nayita addu'a nayita jiran ranar da kai da kanka zaka fahimci kuskurenka ka gyara amma ka kasa, asalin sahabin manzon ALLAH (s.a.w) dake da sunanka tabbas yanada zuciya sosai amma ya kasance mai tsananin fahimta da saurin sauka da uzuri koda kuwa ga yarone balle babba, akwai qissarsa da aka kawo cewa wata rana yana zaune masallaci sai yaji wani bawan ALLAH na sallah a raka'ar farko ya karanta fatiha sai yakaranta qul a'uzu birabbin nas, yana jin haka ya tashi da sauri yaje gida ya d'auko takobinsa ya tsaya bayan wannan mutumen yana jiran yaji mezai karantawa a raka'a ta biyu idan ya karanta fatiha, sai yaji ya sake karanta qul a'uzu birabbinnas kamar yanda yayi d'azu."

"Mutumen na sallamewa sayyida umar ya kallesa yace wlh ka kuru, daka karanta wata sura bayan qul'auzu birabbinas dana sare kanka da wannan takobin nawa mai tsananin kaifi, sai mutumen ya tambayesa dalili sai yace baya halatta mutum ya karanta fatiha da wata surah a raka'ar farko idan ya tashi yin raka'a tabiyu yace yakaranto wata surar data yimasa dad'i sai kace mai karatun jarida, dolene yakaranta surar dake bima wacce yakaranta a raka'a tafarko ko kuma aya araka'a tabiyun, shiyasa nasan daga qul'a'uzu birabbinnas babu wata surah nazata zakayi wasa da alqur'anin ALLAH ne na d'auke maka kai sai naji ka maimaita surar wannan dalilin shiya qwaceka daga mutuwa a hannuna yau". _(to sai mu kula yin hakan laifine acikin sallah, idan ka karanta surah araka'ar farko idan zakayi ta biyu to surah dake bimata zaka karanta ma'ana ta qasanta, idan kuma ayoyine to cigabansu zaka karanta, ubangiji ALLAH yasa mudace👏)_ kaga anan sayyidina umar yayi zuciya sosai da tasashi zuwa ya d'auko makami akan abunda yaji kuma yayi hasalar da tasa har yake tunanin zai iyayin kisa, amma da yayi haquri yabi abun ahankali har zuwa qarshen sallar bawan ALLAHn nan sai ya sauka daga fushinsa tunda yaji abunda yake tsammanin zai faru ba haka bane kuma abun bai faru ba, sai ya janye hukuncin da yayi niyar d'auka akan wannan bawan ALLAHn tare da yimasa bayanin da zai ilmantar dashi anan gaba, to don me kaima bazakayi koyi dashi ba?, Kayi haquri alokacin da kaji cewa abunda kake tsammani ba haka bane?, don mi bazaka janye hukuncinka ba tunda abunda kake gudun faruwarsa bai faru ba?, Don mi baza kayi uzuri ga 'yarka ba kajawota ga jiki kafahimtar da ita dalilinka na rashin son aurenta da yaron wanda kagano hakan wataqil zaisa ta ilmantu akan girman soyayyar iyaye ga 'ya'yansu ita kesa su yanke masu hukunci cikin b'acin rai saboda qaunar da suke yimasu don tsoron karsu fad'awa halaka.?, Maganar gaskiya ni baka kyauta mani kuma baka yimani adalci, idan kai baka buqatarta akusa dakai ni Ina son na ganeta akusa dani mu zauna tare muyi fira irinta uwa da d'iya, tafad'a mani damuwarta inbata shawara akai Amma duk saboda kai narasa wannan damar, wannan wane irin son kaine kake dashi haka, kullum kai kanka baka damuwa da damuwar kowa idan ba taka ba."

"idan ma hukunci ne kake yimata ai ya isa haka, izuwa yanzu itama tasan me ake cewa d'a da mahaifi, bana tantama duk yana cikin jarabawarta da ALLAH ya karb'e mata rayuwar 'yarta saboda tafahimci irin girman soyayyar dake tsakanin iyaye da d'ansu ta fahimci pain d'in da iyaye ke shiga alokacin da wani abun da basa so zai sami d'ansu, b'acin haka ALLAH ya sake jarabtata tahanyar fasa jikinta aciro mata 'ya'ya duk da kasancewar alokacin zata iya rasa rayuwarta, Ina tsammanin ta wannan fannin kad'ai izuwa yanzu tasan me ake cewa iyaye kuma tasan girmansu, to don me bazaka yafe mata ba, ko kafiso sai ranar da akazo aka cemaka tamutu ko kuma shi mijin nata daka tsana ya mutu sannan kafashe da kuka kace kayafe mata?, Alhaji umar" tafad'i ainahin sunansa wanda ya sashi d'agowa da qarfi yana kallonta, tabbas yau yakaita qul don bazai iya kawo rana d'aya ba d'aya tab'aji ta furta sunansa haka kai tsaye, Saida ta share hawayenta da tafin hannuwanta sannan taci gaba da cewa.

"Ka rabu da mugun nama, ka rabu da dokin qarfe, ka yafi 'yarka tazo garemu na roqeka da ALLAH da girmansa, idan kuma ba haka ba wlh wannan zuciyar taka bazata kaika ko Ina ba kuma zata sa kayi nadama mai yawa arayuwa don na tabbata har yanzu kana sonta kuma kana tsananin qaunarta fiye dani, yanzu haka 'yarka nada tsohon ciki kuma shima tiyata za'a yimata akaro na biyu yarage gareka ka sauko daga fushin da kakeyi da ita ko kuma akasin haka, ita dai mutuwa rigar kowace kuma zata riskemu aduk lokacin da taga dama, ba lallaine afito maka da ita da raiba domin ba ahannunmu rayuwarta take ba don haka kana da damar canza abunda yakasa canzuwa cikin shekaru bakwai a cikin daqiqa d'aya idan kaso."

Tana gama fad'ar haka tamiqe ta lunke dardumar da tayi sallah akai sannan take ta watso ruwa ta dawo tanemi gefe ta kwanta, shi kuwa gaba d'aya yau kalamanta sun kashe masa jiki cikin sanyin murya yakira sunanta had'e da cewa.

"A yanzu na fahimci cewa a cikin hukuncin da nayi nine mai laifi, a duk tsawon wannan lokacin Ina d'aukar 'yata a matsayin ita keda laifi shiyasa na koreta daga gidannan, Amma yanzu Dana fahimci nine mai laifin yakamata nahukunta kaina tahanyar barin wannan gidan tunda shine hukuncin da nake zartarwa ga mai laifi, ALLAH shine sheda tuni nayafewa batool bana fushinda ita amma sai nakejin matuqar zanci gaba da ganinta wannan baqinciki data jefani aciki awancan lokacin zai iya cigaba da addabar zuciyata har iya qarshen rayuwata, shiyasa nakasa cewa tadawo gareni."

Ita dai Bata sake tankasa ba saboda ayanzu ta gama yanke hukunci akan zataje ta zauna da 'yarta matuqar wud'annan maganganun da sukayi basusa ya haqura ba bazata sake cemasa ya haquran ba, dolene itama tagwada masa irin tata zuciyar awannan karon don tagaji, ganin taqi tankasa yasa shima ya juya ya kwanta kalamanta nayi masa yawo a qwaqwalwa, har akayi kiran sallar asuba Abba bainsamu ya runtsa ba daya rufe idanuwa batool yake gani, gaba d'aya hankalinsa yabi duk ya tashi babu wacce take so da gani idan ba itaba gashi dare yayi balle yakirata awaya yaji muryarta ko zai samu sassauci, ALLAH ALLAH ya dingayi safiya tawaye yakira ta har aka kira asuba, haka ya daure yayo sallah yadawo yayi zaune yana jiran har gari yafara haske yakira yanda hankalinta bazai tashi ba idan taga kiran amma da yake jiya bai samu wani isasshen bacci ba sai baccin yayi awon gaba dashi.

A can cikin barcin nasa ya soma yin mafarkin daya matuqar tayar masa da hankali wanda bayan mintuna talatin da kwantawarsa ya farka cike da tashin hankali ya saki wata irin qarar da tasa hajia mama dake kitchen rugowa wacce saida ta karad'e gidan gaba d'aya, a yanayin data ganesa yana faman zufa duk da a.c dake kunne yasata ajiye fushin da takeyi dashi ta matso kusa garesa sosai tana fad'in,

"Lafiy alhaji?.." ko rufe baki batayi ba saiga su uncle h da dawowarsu daga masallaci kenan sukajiyo sautin qararsa suka shigo sugani ko lafiya,

Kasa magana yayi inbanda hawaye da zufan dake keto masa babu abunda yakeyi, a gefe gefensa su uncle h suka zauna suna goge masa zufan tare da sake tambayarsa, daqyar ya iya sake bud'e baki yace....

_Hi gusz, me yafaru ne da Abba?, Wane mafarkine yayi daya jefasa acikin wannan yanayin?, try and find it by your self🤣 the first person dana fara karanta comments d'insa naga yabada amsa daidai da mafarkin Abba to tabbas shi keda page d'in gobe sukutum in sha ALLAH, wannan alqawarinane in ALLAH yabani Aron rayuwa😅a kafta my fans🤞🏻luv you much😘_

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Masha ALLAH, jinjina agareki tare da gaisuwa ta musamman had'e da fatan alkhairan ALLAH sutabbata agareki aduk inda kike gwanaty😅 *SARATU UKASHATU ISAH (MUM NUSAIBA)* Ina godiya bisa yanda kike bibiyar wannan littafi da yanda kika hakaito inda mafarkin Abba yanufa, a gaskiya naji dad'i kuma kin burgeni sosai, though akwai da yawa wud'anda suka amsa tambayar daidai da taki amma kece wacce cikar alqawarina ya tabbata agareki kasan cewar ke kika rigasu bada amsa, namatuqar jin dad'i da nishad'antuwa yanda naga comment d'in fans na playing ta ko'ina sanadiyar hakan kuma nagode maku sosai jaxakumullahu bikhair, tabbas kud'in abun alfaharina ne saboda yanda kuka juri bibiyar wannan littafi nawa duk da tsawon nisan zangon da yayi batare da gajiyawa ba, ubangiji ALLAH yabaku aljannarsa da rahamarsa bigairi iqabin wala hisabin👏THANK YOU ALL ONCE AGAIN🤝_

Page___99💎

Da qyar Abba ya iya bud'e bakinsa yace hajia mama tamiqo masa ruwa, fridge taje ta bud'e ta d'auko gorar ruwa mai sanyi takawo masa ya karb'a ya bud'e marfin yafara sha da sauri da sauri tamkar wanda yakwana da yini bai sha ruwa ba har saida ya shanye ruwan tas sannan ya ajiye gorar saman bed side had'e da goge bakinsa, duqar da kansa yayi na mintota tamkar mai nazarin wani abun kafin ya d'ago kai yace.

"Na shiga uku ni da kaina zan jawowa yarinyata shiga cikin wani hali da zan gwammaci mutuwata akan rayuwata, na tabka kuskuren da ayanzu ni da kaina nake tsoron qoqarin gyaransa saboda gudun kar abunda nagani yafaru."

Cikin rashin fahimtar wasu daga cikin maganganunsa hajia mama tace.

"Kamar ya alhaji?, Taya bawa zaiyi kuskure kuma yayi nadamar aikatasa ace kuma yana tsoron gyaransa?."
Chapter 141 · 0% Book details